Sashe 55
Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mami ko da ta shiga ɗaki, neman baccin tayi sama ƙasa ta rasa shi, kwanciya kawai ta yi tare da zubawa saman ɗakin nata ido, lissafi take akan yanzu wa za ta aura? Alhaji tana son sa ba kaɗan ba, amma tana tunanin kar nan gaba zargi ya zo cikin aurensu ko wani abu daban, tun da ita zuciya sai a hankali balle ma da a wannan harkan ya sameta, sannan Abbaa kuma tana gudun a ƙara samun akasi da Umma, ko kuwa Ummu ma ta kasa haƙuri nan gaba da kawo gori da tashin hankali stakaninsu, kishi masifa ce, duk iya daurewanka watarana sai an samu akasi, sannan bata buƙatan auren da za ta yi saki ya biyo baya, Abbaa tun da ya saki Umma uwar ƴaƴansa tana ganin ita ma zai iya sakinta watarana idan ta aure sa, Alhaji kuma idan ya zarge ta zai iya sakinta shi ma, kuma bata fata da addu'an tayi aure ta fita, cikin mugun damuwa Mami ta busar da zazzafan iska a bakinta, a hankali ta buɗe baki ta ce, "Allah ka mini zaɓin alkairi, Allah Astagfirullah! Na tuba maka Ubangiji na."
Haka Mami ta kasance cikin zullumi, wan da har kan ta ya fara ciwo saboda tunani da nazari, so take ta yi auren saboda Allah kuma saboda Banafsha ma ta yi, ita ba ta da farin cikin da ya wuce mata tilon Æ´ar ta, kuma bata da burin da ya wuce ta aurar da ita cikin aminci da mutunci, dan haka za ta iya yin komai dan Banafsha, har da bayar da ran ta ma.
Daga ƙarshe Mami yanke hukuncin yin istihara ta yi(neman zaɓin Allah), tashuwa ta yi ta ɗaura alwala ta zo ta tayar da nafilanta raka'a biyu, sai da ta idar sannan ta karanto addu'anta ta gabatar da buƙatanta ga mahaliccinta, sai da ta idar ta shafa sannan ta samu nustuwa ta bi lafiyan gado ta kwanta.
Shi addu'an istihara ba wa iya aure ake yi wa ba, domin an karɓo daga jabir ibn Abdallah, cewa mun kasance tare da Manzon Allah SAW yana nusar da mu duk abin da za mu yi, mu nemi zaɓin Allah a kai(istihara), sannan yana koya mana addu'an, kaman yan da yake koya mana Surah daga cikin Alƙur'ani mai girma, kuma ita sallar istihara ba dole sai da dare ake yin ta ba, ana iya yin ta da safiya, da marece, da dare, da rana, hatta bayan la'asar da ba'a mata nafila, to mutum zai iya yin wannan sallah ta istihara, raka'a biyu sallama ɗaya, idan mutum ya idar, zai karanto addu'an kaman haka :-
ALLAHUMMAH INNI ASTAKIRUKA BI ILMIKA, WA ASTAƘDIRUKA BI ƘUDRATIKA, WA AS'ALUKA MIN FAD'LIKAL AZIM, FA'INNAKA TAƘDIRU WALA AƘDIRU, WA TA'ALAMU WALA A'ALAMU, WA ANTA ALLAMUL GAIBU, ALLAHUMMAH IN KUNTA TA'ALAMU ANNA HAZAL AMRA ( sai ka faɗi abin da kayi sallahn saboda shi anan ) KAIRUN LEE WA FI DINI, WA MA'ASHI, WA AƘIBATI AMRI, FAKDURHU LEE WA YASSIRHU LEE, SUMMA BARIK LEE FIHI, WA IN KUNTA TA'ALAMU ANNA HAZAL AMRA SHARRUN LEE WA FI DINI WA MA'ASHI, WA AƘIBATI AMRI FASRIFHU ANNI, WASRIFNI ANHU, WAƘDUR LIYAL KAIRA HAISU KANA SUMMA RADDINI BIHI.
wannan ita ce addu'an, Ubangiji Allah ya tabbatar mana da alakiran rayuwanmu, Allah ya sa mu dace.
Washe-gari da safe sai da na lallaɓa na yi wa Mamina ayyukanta, sannan na shirya na fito muka wuce tahfiz tare da Umaima, ga mamaki na Ya Danish na tsaye a ƙofa yana bi na da kallo har muka wuce, amma ni ko nunawa nasan da halittansa a wajan ban yi ba.
Mun je mun yi karatu sannan an yanke tafiyanmu musabaƙa a cikin jimeta nan da sati biyu, akan mu sanar wa iyayenmu, kamun malamai za su zo har gida a sanar wa iyayen duk wan da za'a je da shi.
Ana tashinmu muka kamo hanyan gida, tafiya muke muna hira, faɗa wa Umaima nake Dr Arshan fa kaman son ta yake, dariya tayi ta ce, "ai ke dai sam bakya gani da kyau, kina ji mutum ya ce yana da mata kuma ba zai ƙara aure ba, balle a masa maganan adalci, shi ne kike wannan batun."
Dariya nayi sabo da na tuna, masifan da nayi ranan akan ya duba ɗan uwan soja, bai Duba Mamina ba, shi ne na ce masa baya da adalci, ba zai iya riƙe mata biyu ba, haka muna hiranmu muka tinkaro gida, tun daga nesa na hangi mutum staye a ƙofan gidanmu, kuma sarai na gane Ya Danish ne, haɗe fiska nayi tare da jan staki na ce, "Mutum ba zuciya sam-sam haka Allah ya yi sa, ka gama ci mini mutunci ka zo kana ƙoƙarin lashe aman da ka yi."
Umaima murmushi tayi dan ta san da wa nake yi, kallon ƙofan gidan mu tayi ta ce, "Masoyiya a taimaki yayana, Allah jiya ma in faɗa miki shi ya sanya ni zuwa na dubo ki ko lafiya, da na ce masa ba ki da lafiya kada ki ga yan da hankalinsa ya tashi, har ya bani tausayi, na ce Allah mai iko, kaman ba shi ya gama miko rashin kirki ba, ga shi Allah ya jarabce sa da son ki, dan Allah Masoyiya ki yi haƙuri ki yafe masa ki kula sa."
Taɓe baki nayi na ce, "ke baki san waye yayanki ba ne shi yasa, baki san me ya mini ba, ni da ya Danish ko shi kaɗai ya rage namiji a duniya to ba zan aure sa ba, Malam Abbo na zan aura, Insha Allah."
Sallama muka yi da Umaima ta shige gidansu, nima na wuce namu, ina isowa ƙofanmu kaman yan da ya saba ya fara mini magiya, tambayan ya jikina yake yi amma na yi banza da shi na shige gida.
Bayan na karya na huta sai Alhaji yayi ƙira na, zuwa nayi cikin ladabi na gaishesa, amsawa yayi tare da tambayan ya karatun namu da kuma jikinsa.
Murmushi nayi na ce, "Alhamdulillah!"
Jinjina kai Alhaji yayi tare da miƙo mini, leda mai ɗan girma ya ce, "Ga kyautan ki da na yi alƙawari, sannan an faɗa mini result naki, yayi kyau sosai a ƙara mai da hankali, yanzu kuma sai ki faɗi abin da kike so ko ƴar gidan Mami, idan bai fi ƙarfi na ba, Inshà Allah zan miki koma menene."
Tun da Alhaji ya fara magana, nayi ƙasa da kai na ina wasa da yastuna, na jima da tanadar amsan da zan bawa Alhaji idan ya bani wannan daman, amma kunya nake ji na rasa ta ina zan fara, ajiyan zuciya na sauƙe tare da lumshe ido na cikin ƙarfin hali na ce, "ka yi haƙuri da abin da zan faɗa idan zai ɓata maka rai, amma shi ne iya abinda nake buƙata."
Alhaji murmushi yayi cikin yabawa da hankali irin na Banafsha ya ce, "ina sauraranki Banafsha."
A hankali na ce, "Alhaji dan Allah dan darajan Annabi da ƙur'ani, ka taimaka ka auri Mamina, dan Allah ku bar irin wannan rayuwan da girmanku, mu yaranku ba ma jin daɗi musamman ma ni, kuma nasan idan su Majeeder ma za su ji haka ba daɗi zai musu ba, dan Allah Alhaji ku mini wannan alfarman, wallahi shi kaɗai ne abin da nake buƙata daga gare ka, har ma da Mamina", ina gama magana kuka ya ƙwace mini, amma na danne sautin kukan dan kada Mamina da ke kitchen ta jiyo muryana.
Alhaji aniyan zuciya ya sauƙe tare da kallona, yana murmushi ya ce, "In Allah ya yarda Banafsha zan auri Maminki, ke dai ki taya ni da addu'a da kuma shawo kan ta, Maminki ce sai a hankali amma in Allah ya yarda wannan karon zan dage kin ji, na miki alƙawarin yin abinda bai fi ƙarfina ba, dan haka auren Ramla bai fi ƙarfina in Allah ya hukunta hakan, kema kuma ina son ki daina saka damuwa a ranki, ki kuma cigaba da yiwa mahaifiyarki biyayya."
Jinjina kai nayi cikin gamsuwa da maganansa, na gode sosai sannan na shige É—akina, wanke fiskana nayi, sannan na buÉ—e ledan da Alhaji ya bani, kwali ne a ciki, na kuma buÉ—e wa, ganin wani ranstasten kyakkyawan system tuni na stala ihu ba shiri, ihun nawa har ya jawo hankalin Mamina ta shigo da sauri a firgice tana faÉ—in, "lafiya Banafsha? Menene ya saka ki ihu?"
Cikin farin ciki na nuna mata system da ke hannuna, ita ma da mamaki take bi na da kallo ta ce, "Banafshaaa ina kika samo computer?"
Ina murmushi na ce, "Alhaji ne ya bani yanzu, wai shi ne kyauta na", ina faÉ—a na rungume Mami cikin farin ciki, ina faÉ—in ta tayani gode masa.
Abubuwan cikin ledan na ƙarisa cirowa, nan kuma wani sarƙa ya faɗo da ɗan kunnensa da zobensa, da abun hannu, masu shegen kyau da ɗaukan ido, Mami da ke staye, waro idanuwa tayi ta ce, "Gold dai?"
Ai ban staya ba, na fice palourn, amma na samu Alhaji baya palourn yana cikin ɗakinsa, komawa nayi ɗaki cikin farin ciki, ina kallon kyautan da Alhaji ya mini, sarƙan gold, system, ga kuma wani haɗaɗɗen dogon riga wan da kana gani kasan ya ci uban kuɗi shi ma, kayan ma dai ka san ba na Nigeria ba ne, farinciki kaman nayi yaya.
Mami komawa tayi ta ƙarishe aikinta, ta shirya sannan ta shiga ɗakin Alhaji, samunsa tayi yana waya da yaronsa, murmushi tayi tare da zama a ɗan nesa da shi, har sai da ya gama, ya dubeta yana murmushi ya nuna mata gefensa, amma Mami sai ta gyaɗa kai kawai, cewa ta yi, "Alhaji sannu da hidima mun gode Allah saka da alheri."
Murmushi Alhaji yayi ya ce, "Kada ki gode mini Ramla, dan kin cancanci fiye da haka a wajena, kuma duk wani wan da ya shafe ki zan masa fiye da haka, Ramla soyayya nake miki na tsakani da Allah, ranan na iso ana cikin yanayi mara daɗi ne shiyasa, amma ke ma ga naki staraban na Egypt ɗin", Alhaji ya faɗa tare da miƙa wa Mami wani jibgegen leda.