← Book details Wata Kishiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 107

Sashe 99

Wata Kishiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

tambayoyi,zan iya muku tambaya dan Allah?..." Tayi mgnr da hausar da bata wadacetaba. dr mus'ab yace "Eh mama zaki iya mana, muma zuciyoyinmu na cike da tambaya sosai a kanku..." Ammah tace "Dan Allah su waye ku? Ku temakeni ku gayamin ina jikata Almuqri'ah,, kunce ku ba macuta bane, na yadda, zuciyarta ta aminta daku, dan Allah karku sa zuciyata tayi rawa a kanku, ku gayamin ina jikata Almuqri'ah bani da kowa a duniya se ita, dan Allah karku cutar da ita kara ku cutar dani..." Ammah tayi maganar cikin tsananin damuwa, idanuwanta sukayi rau-rau da kwallah, fargaba ya cika zuciyarta, tana tsananin bktr san ganin Almuqri'ah, idanuwanta na tsananin yunwar ganinta. Paid book ne Dr mus'ab ya cire glass din dake idanuwansa ya ajiyeshi a gefe, ya tsurawa Ammah ido, jarida tabi dr da ido. Yayi kasa da kansa kana ya fara magana cikin kwarewa"Ki kwantar da hankalinki mama Almuqri'ah na nan Lafiya lau...xan sanar dake komi daga farkon haduwarmu daku har zuwa yanzu insha Allahu, ina fatan zaki fahimceni mama..." Ammah ta gyara zamanta tace "insha Allahu, inajinka ka gayamin,....." Dr mus'ab ya gyada kai hadi da fara magana cikin nutsuwa irin ta zallar yan boko. "Ni sunana dr mus'ab,ni dan garin yola ne, amma iyayena cikakkun katsinawa ne,, inada asibiti a yola,sannan inadashi a katsina state garin iyayena da kakannina kenan,, mun hadu daku ne a katsina, kun kai 8months a asibiti na keda Almuqri'ah baki da lafiya kina fama da blood Cancer, seda nazo naga halin da kike ciki na daukeki na kawoki wannan kasar ta America, na dauki nauyin aikinki aka miki juyen jini, har kusan 3tyms...toh Alhamdulillahi ansamu nasara kin samu sauki, wannan kuma jarida nurse ce wadda take kula dake da kuna asibitin katsina, a lkcin da bakya hayyacinki,, itama jarida ta bada gudumawarta a kanki duk watannin dakukayi a asibitin ita ke biyan kudin dakin asibitin dakuke kwance a albashinta, cin Almuqri'ah da shanta da take jinyarki duk ita ce,, Bata barku a katsina ba da muka nufo nan American ma da ita muka taho domin kula da lafiyarki, tana kaunarku saboda Allah, itama jagora ce, tayi temako da dukiyarta, kuma tayi da lafiyarta, muna kara mata godiya, ubangiji ya biyata da Alkhairi Yadda ta baro yayanta a nigerian da iyayenta tazo nan ta zauna tsawon 8month muna fatan Allah yajibnceta har ta mutu..." Ammah da tini ta fashe da kuka ta amshe da amin,a zuciyarta se jinjinawa Dr mus'ab da temakon dayayi mata takeyi, bashi ba har nurse mami ma ta jinjina mata. Ammah ta kara fashewa da kuka ta kalli Dr mus'ab da mami tashiga musu godiya tana kuka hadi dasa musu Albarka mara iyaka, "ashe na Allah suna nan .." Cesar Ammah. Dr mus'ab yace "bakomai mama, ki kwantarda hankalinki....akwai wata magana kuma mama amma pls ki fahimceni wlhi ba cuta a zuciyata..." Jin yace akwai wata magana yasa Amma natsawa ta tsuresa da ido a zuciya se sa musu Albarka takeyi. Dr mus'ab ya fara magana kansa na kasa, sbda gani yakeyi kmr yayi mata lefi. "Ina me neman alfarma Daki yafemin na shiga huruminki da nayi duk da bansan ko waye kuba?na fara da neman yafiya.." Ammah tayi jim tana me tunanin meye dalilin Dr na neman yafiyarta, ta tabbatar da komi ze mata koda menene zata iya yafe mishi sbda temakon da yayi mata,. "Na yafe maka koma menene.. Amma Dan Allah ina jikata Almuqri'ah?'' Ta karashe mgnr zuciya fal rauni, se adduarh takeyi Allah yasa ba wani abu yasamu Almuqri'ah ba, mus'ab ke neman yafiyarta a kan hakan. Dr mus'ab yaci gaba da mgna knsa na kasa. "Tana nan cikin Aminci... Byn mun kawoki American,, na dawo nigeria na hada Auren jikarki da abokina Abdoljalal AASaraki..." Jin abinda dr mus'ab yace ya mummunar haifarma da Ammah faduwar gaba a fili ta maimaita "Aure!!!...Almuqri'ah akayima aure?" Ammah ta shiga tunani tunani, a zatonta ai yarinyar bata isa Aure ba saboda karama ce sosai,beci ace ta iya daukar d'ana miji ba. Dr mus'ab ya dago ya kalleta ya hango tashin hankali a kan fuskar Ammah, dan haka ya kara kwantar da murya yaci gaba da magana. "Ki kwantar da hankalinki mama wallahi bazan iya cutar daku ba, abokina ma data Aura sam ba Azzalumi bane, tare mukayi karatu nasanshi nasan gidan iyayensa,..." Ammah taji zuciyarta ta dan natsa jin klmn Dr mu'sab, ta kara aminta dasu mutanen kirki ne. Ganin ta dan natsa yasa Dr ci gaba da mgna cikin hankali. "Mun hada Auren nan ne badan mu cuceta ba wlhi, sedan temakon rayuka daga cikin hatsari, domin muna hango nasara ayin Auren, dan na fahimci ita yarinyar macece ta gari wadda duk namiji zeso samunta ga hakuri..." Dr ya dan dakata yana kallan reation din Ammah, wadda ta kara nutsuwa tana kallan dr hadi da nazarin klmnsa a cikin brain dinta na me hankali da tunani hadi da fahimta. Dr yaci gaba dacewa "Abokina Abdoljalal mutumin kirki ne sede be dace mace ba wadda tayi sanadin rabashi da iyayensa, ta rabashi da kowa nashi na duniya, nima ta rabashi dani se dan karfin kaddarar Aurensa da Almuqri'ah dake ta hannuna ya hanashi nesan tata yadda akeso...a kullum cikin dmwa da bakin cikin halin da Abdoljalal yake ciki nake kwana nake da tashi da dmwa, daga haka muka kulle da wazirin mahaifinsa kasancewar mahaifinsa sarki ne. Wazirin isma'il shima yana cikin dmwa sanadin damuwar da iyayen Abdoljalal suke ciki musammanma mahaifiyarsa da dmwar yadda aka rabata da d'anta ta tabata Ainun. A kullum cikin shawara muke nida waziri isma'il, muna nema ma iyalan na abdoljalal mafita, amma abu yaci tura har aka kwashi 10yrs yana tare da wannan muguwar mata tashi,, se daga bisani naga Almuqri'ah a asibiti na,, nasameta nace tazo office dina sukaxo ita da nurse mami, na gaya mata zan temakeki a kaiki kasar waje, amma da sharadin sede ta aure abolina Abdoljalal sannan ni kuma zan temaka muku... Ba tareda bata lokaci ba Almuqri'ah tace ta amince, sbda temakon lafiyarki da nace zanyi, danna fahimci tana tsananin kaunarki Ainun., a ranar datace ta amince nasamu ahamad ma'aikacin Abdoljalal na hannun damansa,da waziri, na gaya musu bukatata a kan hada Almuqri'ah da Abdoljalal aure,, waziri ya tambayeni meye dalilina nayin hakan,,na sanar dashi ina hango nasarar dazesa insha Allahu hankalin Abdoljalal ya dawo jikinsa, har ya koma ga iyayensa, kuma ya zama mutum tamkar ko wanni d'ana miji....na gaggayawa waxiri dalilaina masu karfi ya aminta,, a satin da aka fitar dake kasar American domin samun lafiyarki,..muka dawo gida Nigerian bayan an dauran Auren a kasa me tsarki., mukayi shawarar yadda za ayi Almuqri'ah ta tare a gidan Abdoljalal ba tare da matarsa dashi kansa sun san cewa ita din matarshi bace,,,nan ahamad ma'aikacin Abdoljalal ya kawo shawarar taje a matsayin me Aiki? Nace ta yaya? Ahamad yace ta hannun me kawo musu me Aiki gidan mesuna hajiya kande,, ba bata lokaci ahamad ya bani lambar kande, na hadata da nurse mami, nace ta gaya mata kaf gaskiyar lamarinmu a kn zuwan Almuqri'ah gidan Abdoljalal amma ta boye mata cewa dasa hannuna a ciki, ta nuna mata cewa itama wata takema aiki,, nurse mami batasha wahala ba a kan hajiya kande kasancewarta mayyar kudi, aka shirya mata komi taje ta kai yarinyar gidan Abdoljalal mukayi nasara kuma matarshi ta dauketa a matsayin me Aikin gidan,,bamu bari haka ba muka sa kande tasamu C.I.D a gidan sbda ta dinga fadin komi dake gudana. alhamdulillahi aka kaita Almuqri'ah cikin natsarar ubangiji komi ya fara settling ga Abdoljalal domin nutsuwarsa ta dawo garesa, sede har zuwa yanzu abdoljalal besan aure ne tsakaninsa da Almuqri'ah ba, Har yanzu akwai asiri me karfi a kansa wanda baze barshi ya Auri Almuqri'ah ba, sede yayita cewa beda yadda zeyi, amma kuma yanasan yarinyar, san da yayi mata ma be tabawa wata halitta a duniya irin saba Wallahi tallahi,, sannan ya kusanceta, harma yasamu ciki na farko da ita ya zube yanzu haka akwai ciki na biyu a jikinta wanda nake da tabbacin ta kusa haifarsa ma zuwa yanzu....ina neman yafiya a karo na biyu mama..." Dr ya fadi cikin sanyin murya byn ya karasa bata labarin, ya nisa. Ammah ma nisawa tayi, ta matukar tausawa a labarin da dr mus'ab ya bata na Abdoljalal, idanuwanta suka ciko da kwallah, tasan da zafi ka haifi d'a da cikinka amma a rabaku dashi wata can mace data tsincesa a sama,,,nan tashiga tunanin a wani hali kuma ita Almuqri'ah take ciki a zamanta da wannan kishiyar tata Azzaluma da dr ya gaya mata. "Bakumin komi ba wallahi,godiya ya dace na muku...,, ni musulma ce ta gaske na yadda da kaddara, duk abubuwannan dasuka faru rubutaccen ubangiji ne, sanadin hakan ne yasa kaddara da rabo suka baro mu daga kasarmu muka dawo wannan kasar muma..." Dr mus'ab da mami wato jarida suka hada baki gun cewa "Haka ne ...." Ammah ta sauke numfashi tace "yanzu ya ita jikar tawa? Kuma shi d'an ya koma ga iyayensa?"' Dr mus'ab yace "Alhamdulillahi take, tana cikin Aminci insha Allahu,,,, be koma ga iyayen nasa ba gaskiya, amma ko a haka ma Alhamdulillahi Mama, tinda yanzu shi Abokin nawa yadawo hayyacinsa ba kmr a farko ba, sannan ga haihuwa yasamu a tare da Almuqri'ah abinda basu taba samu ba da ita saude,... mungode mungode, dole mune zamuyi godiya baku ba mama..." Ammah ta jinjina kai hadi dacewa "aah muma dole muyi godiya, kuma ni Alhamdulillahi da warakar wannan bawan Allah tazamo a garemu, Allah ya karo dumbin nasara..." Duk suka amsa da Amin. Dr yaci gaba da magana "Mama ki kara kwantar da hankalinki insha Allahu in kika gama warwarewa zamu koma nigeria zansan dabarar dazanyi Ku hadu da Almuqri'ah insha Allahu, domin har yanzu Shi Abdoljalal besan ni na tsara komi ba, shiyasa bazeyu ko mun koma nigeria ba ku hadu farad da garaje, Amma insha Allahu zanyi kokarin hakan saboda itama nasan tunaninta da hankalinta na kanki, danma tin kafin taje gidan na kwantar mata da hankali tare dace mata zaki samu sauki insha Allahu, shiyasa nasamu hankalinta ya kwanta,,," Ammah tace "Bakomai wlhi, Allah de ya kareta, ya kuma basu zmn lafiya ita da mijinta, ya karya mulkin zalinci dan Alfarmar Annabi SAW,,," duk suka amshe
Chapter 99 · 0% Book details