← Book details Wata Kishiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 107

Sashe 29

Wata Kishiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Littafin ma'aurata ne* SAADATU BINTU ABDULLAHI (writer of Kyautar Allah) *DEDICATED TO MALAMA ALARAMMIYA AUNTY AYSHA (MAMAN RUKAYYA)* Free page8 "Abdoljalal Kaga me Aikin?'' Saude ta jefo masa tambayar ba tare data gaishesa ba. Dagowa yayi ya sake kallonta a karo na biyu yace "Banganta ba nadega abinci a dinning..." Saude ta lumshe idanuwanta ta budesu a Kansa Sbda yadda ya mata maganar ya haifar mata da mutuwar jiki,muryarsa kawai tada mata hankali takeyi."Okay yayi, daman ai banso ka ganta,,abinci kakeso shi zata dafa maka ni de kasanni da kishi kwata-kwata hankalina ya kasa kwanciya a kan yarinyar shiyasa nace bari in sameka nide ba ruwanka da ita, me aiki ce ta maka abinci kawai kaci shikenan, pls nide ka kula da kanka a kan kowacce mace..." Dagowa yayi ya sake kallonta daganin yadda take maganar yasan kishin nata ne na azabar ya motsa, dan ita bata da lissafi a kan kishi. Ba tare dayace komi ba ya mike byn ya gama cin Farfesun kifin ya isa ga inda aka tanada dan wanke hannu ya wanke hannayensa duka biyu da sinadarai. duk tana zaune tana kallonsa ya gama ya kwashe komi na kn dinning din ya kai kiching ya dawo ya kara wanke hannayensa duk tana zaune inda take, ya nufa hanyar dazata sadashi da falo ta taso ta biyoshi tana fadin "Bakaji abinda nace bane?'' A takaice yace "Naji..." A gaggauce ya bar falon ya nufa upstairs ta bishi da ido zuciyarsa na bata tabbacin zafin kansa baze taba bari ma ya kalli yarinyar ba, ita fa duk tunaninta kar yaci gindin wata saboda ita ba bashi gindin takeyi ba, hkn ke kara sata a halarar kishinsa, amma tasan gaskiya da wuya mijinta ya iya kunsantar gindin wata. wani irin murmushi ne ya subuce mata a kan fuskarta, ganin zuciyarta ta bata tabbacin mijinta baze taba neman wata ba da sigar ci ko ta sigar soyayya ma tasan da wuya danshi mutum ne dabesan reni, kuma babban mutum neshi dabazeso mutumcinsa ya bare a idon mutane ba,, juyawa tayi ta fice a side din nasa tana mejin kwanciyar hankali na ziyartarta tako ina, amma fa kishinsa na nan a zuciyarta ta tabbatar duk randa mijinta ya kusanci koda hannun wata ne ranar seta haukace, ko tacema faduwa zatayi ta mutu sbda tsabar azabar kishi. Bayan ta gama sallolin nata suka nufa side din sauran masu aikin larai ta bata abincinsu na masu aiki shinkafa ce da miya da nama yanka daya, yarinyar taci sosai kasancewar tanajin yunwa, bayan ta gama ne suka nufa side din gogan suka tadda warmers din a kiching larai ta bubbude taga yaci dayawa nan take tayima yarinyar jinjina, kana suka kwashe komi suka nufa kiching suka wanke hadi da kara kimtsa komi a kiching din, larai ta rakota har dakinta kana sukayi sallahma ta gaya mata time din tashinta 8:am zata dinga tashi kullum saboda shi gogan 10:am yake breakfast. Yarinyar ta daga ma larai kai alamar toh, Sukayi sallahma tashige dakin ita kuma larai ta nufa nasu side din. Tana shiga dakin amemakon ta kwanta kawai ta fada bathroom ba jimawa ta fito daure da Alwala, ta isa ga Waldrop ta bude hadi da zuge ghana most go dinta a sama sama ta dauko wata yar bag blue ta zugeta ta fito da Alur'ani me girma hadi da askar da carbi, ta nufa daddumar hannunta rike da Alqur'anin da askar din da carbin ta ajiyesu a gefen daddumar ta tada sallar dare dan zuwa lokacin ana neman After 1:am ne, tinda ta tada sallar nafilar bata tsagaita ba se 3:30am kana ta tsaya ta dauko carbi tayi istigfari hadi da hailala da salatin Annabi SAW, ta kara da Ya zaljalalu wal-ikram, bayan ta gama tasbihin ta ajiye carbin ta bude Alqur'ani me girma ta fara karantawa a zuciya, daga Ankabut ta fara bata tsagaitaba seda tayi izu daya, kana ta ajiye alqur'anin ta dauko askar tashiga karanto Addu'ur'in dake cikin askar din, har seda aka fara kiran asubahi kana ta ajiye askar din tayi addu'ur'inta ta shafa, ta mike ta nufa toilet ta kara dauro alwala kasancewar zuwa lokacin anata kiraye kirayen sallar asubahi ne, masallacin dake gidan tabi jam'i suka idar ta zauna tayi lazimi hadi da kara krnta arzkar har alfijir ya fara bayyana, kana ta mike ta ajiye alqu'anin da askar da carbin a kan bedside drower ta isa kn bed din da hijjabi a jikinta ta kwanta, baccin awa daya da rabi tayi, ta tashi 7:30am a gaggauce tayi wanka ta fito ta shirya cikin riga da zanin atamfa, suma duk sun kode yawancin kayayyakinta duk kodaddune, tasa kayan data cire a kwandon da aka tanada dan zuba kayan dattin. Ta zumbula hijjabi maroon ko mai bata tsaya shafawa ba, sede ta fesa perfume, ta fito ta nufa kiching din nasa, ta dauko yar takaddar da larai ta bata jiya, ta dudduba abubuwan dayakeso da safe na bangaren abincin larabawa, duba tayi taga akwai komi tashiga hada masa zallar abincin larabawa har kala hudu, 9;30am ta gama komi ta dauka ta nufa side din nasa dashi ta kofar dazata kaita direct dining room ba tare data shigo falon gidan ba tashigo, tana shigowa taga ko ina tsaf tsaf se azabar kamshi kawai ke tashi tin 6:am aka gama gyaran side din nasa. Ajiye trea din hannunta tayi a kan dinning table din ta fice ta koma ta kwaso sauran kayan ta dawo ta ajiyesu a kn dinning din tana tuna warning din hajiya saude gareta cikin hanzari ta fice a side din ta dawo kiching din wanda beda nisa da side din ta wanke komi data bata, ta gama gyara kiching din kenan larai tazo taga ta gama komi mamaki ya rufeta, ita da tazo nunnuna mata ne se kuma taga ta gama,. "Sannu da aiki..." Cewar larai. Yarinyar ta amsa mata da kai, larai tace "to tinda kin gama komi kije ki kwanta abinki zuwa 12;am seki tazo ki daura masa abincin rana..." Yarinyar ta amsa mata da kai da toh, ta juya ta kulle kiching din ta nufa dakinta larai kuma ta koma bakin aikinta, daman idanuwanta cike suke da bacci tana isa dakin ta kwanta ba jimawa bacci me azabar nauyi ya dauketa. 9:40am ya tashi yau yasamu baccin daya jima beyi irinsa ba, yasan saboda abincin dayacine ya koshi, Allah-Allah yadingayi yayi wanka shap-shap ya fito ya shirya se sauri yakeyi saboda kawai so yakeyi ya isa ga Dinning room yaci wannan daddad'an abincin, wanda da dadinsa ya kwana a ransa har mafarkin dadin abincin yadingayi. Bayan ya gama shiryawa cikin manyan kaya danyan boil dinsa light brown yasaka, se zuba mahaukacin sheki boil din keyi, ya tashi yau dajin kwanciyar hankalin dayakejin ze iya zuwa office. Ya dauko dankareren watch dinsa na zallar diamond ya mannawa tsintsiyar hannunsa, ya feshe jikinsa da turarruknsa danshi din ma'abocin kamshi ne. Ya zira hadadden bakin takalminsa wanda ya amshe lallausar kafarsa, takalmin ba karamin fito da martabar kyaun kafarsa yayiba. Ya fito dass dashi se taku kawai yakeyi cike da izza tamkar rikakken gawurtaccen namijin dawisu, tako ina ya shiga gashi dogo Sambal ba karkace. Down stairs ya sakko hannunsa rike da wayoyinsa yana tafe kamshinsa na bayyana a duk inda ya taka, daga kai yayi ya kalli saman kofar dining room dinsa yaga ta kyallaro farar wuta alamar an ajiye masa breakfast dinsa. Haka kawai ya tsinci kansa dasakin murmushin daya bayyana siririyar wushiryarsa sama da kasa, direct daga zuciyarsa murmushin ya fito, be taba murmushi a kn komi na duniya ba se yau. BA bata lokaci ya isa dinning room din batare daya ko zauna ba yashiga bubbude warmers din, kamshi abincin ya dokesa yayinda mutuwar tsaye ta sameshi, ganin abincin larabawa wanda Ummihnsa ke dafa masa. A bayyane yace "Again irin abincin ummih..." Ya bude dayar Warmer din zuciya fal mamaki nanma yaga duk abincin larabawa ne, duka warmers din seda ya budesu yaga duk irin abincin da ummih ke dafa musu ne, zaunawa yayi hadi dayin serving din kansa ya fara ci dadih ya kara kashesa nan take yaji zuciyarsa na bukatar ganin wacece wannan me irin girkin Ummih kuma har yafi na Ummihn tasama dadih. Seda ya cika tumbinsa taf kana ya tashi ya dauki warmer daya, wadda be taba komi dake ciki ba, ya isa kiching ya hada warmers din a basket da plate ya dawo dasu falon, kana ya koma ya kwashe komi na kan dinning din ya kai kiching ya zauna a falon hadi da kiran driva dinsa a waya ya sanar,dashi a shirya mota zeje office yanzu...." Ba bata lokaci aka shirya motarsa kirar Benz se motar security daya, ya hau suka fice a gidan zuwa office dinsa,...ranar wuni yayi zuciyarsa cike da tunani tunanin dadin abincin daya fara ci daga jiya zuwa yau, har ya canza kumatunansa sun fara ciccikowa, abincin daya tafi dashi office din ya Karaci da rana after azahar ya dawo gidan,,,wanka kawai yayi ya isa dinning din yaga an cikasa da abinci iri daban daban, be bata lokaci ba ya shiga bubbudewa duk abinda yakeso shi yagani kwata-kwata bega akasin abinda beso va, kuma harda kari a kn abinda yakeso dinma. Zaunawa yayi yaci ya koshi yayi nak daga jiyan zuwa yau harya koyi mugun ci saboda dadin abincin. yana cin abincin ne Kuma zuciyarsa na kara kwadaituwa dason ganin wacece ke masa wannan hadadden abincin har haka kawai yanaso ya ganta...yana gama cin abincin yaji wani irin bacci ya lullube kwayoyin idanuwansa, a daddafe ya iya kai kwanukan kn dining din duka kiching ya nufa upstairs dinsa direct ya fada bedroom dinsa ya kwanta a lallausar gadonsa be jima ba bacci me dadih wanda ke tattare da rabin kwanciyar hankalinsa ya rufesa, Alhamdulillahi daga jiya zuwa yau ni'imomi sun fara masa dirar mikiya a duk sassan jikinsa. After 6da ys,... 6:pm zaune suke a kayataccen falon hajiya Saude wanda ke sama, hajiya Abulle data zubawa hajiya saude ido suna fuskantar juya tin dazu sunfi karfin 10mnt a hkn. "Kawata kin kirani kuma kin tasani a gaba knyi shiru se kallona kkyi kmr kn samu TV?'' Cewar hajiya Abulle wadda hajiya sauden tayi kiranta da yammacinnan. Hajiya saude dake fuskantar hajiya Abulle tace
Chapter 29 · 0% Book details