Sashe 83
Wata Kishiya Complete Hausa Novel · about 8 min read
me martaba yace "Inasan ganin ka yanzu isma'il..." Yana fadae hkn ya katse wayar hadi da shiga tunannika, damuwar Hajiya salma tana kada masa hankali babban abin damuwar tasa kuma gashi bata da cikakkiyar lafiya, duk lamarinsa ya maidashi kaddara, yanada kudade amma sam beda farin ciki. Ba jimawa isma'il ya iso falon nasa me martaba ya masa iso, ya karaso Ya miko gaisuwa game martaba ya amsa ya masa izinin zama a kn kujera yana zama me martaba yayi gyaran murya hadi da fara magana. "Waziri na rasa ya zanyi da salma a kan yarannan,..." Ya kwashe komi ya fadu a yau din ya gayawa isma'il kana ya daura dacewa " wallahi damuwar ta kaini kwano ina tunanin kawai zan nemi Abdoljalal in rokeshi ya dinga zuwa yana ganinta kodan lafiyarta, banasan wani abu ya sameta kwata-kwata..." Ya karashe maganar cikin damuwa. Alhaji Isma'i ma fuskarsa dauke takeda dumbin damuwa daman tinda ya kirashi yasan tasuniyar gizo bazata wuce ta koki ba. Cikin ladabi Alhaji isma'il ya fara magana "aah me martaba, ai a halin yanzu ko an nemeshi duk hanyar bame billewa bace, sbda bayin knsa bane, adduarh de damuka saba ita zamu Cigaba,, insha Allahu komi me wucewa ne....ita kuma gimbiya abin fa dole se an hada da amso mata adduarh, ranka ya dade dole abin da ciwo d'annan fa daya tilo gareta, wallahi tayi ma try Sosai.." Me martaba yace "Hakane Waziri...Toh shikenan Allah ya datar damu Amma ni ina ganin kawai kaddaratace haifar Saraki, gani nakeyi kamar a haka ze mutu bashi ba d'a bashi da jika, ga damuwarsa dake cikin zuciyoyinmu musammanma mahaifiyarsa, wallahi ina tsoron ta mutu ta sanadin bakin cikinsa, ina jiye masa duniyarnan..." Alhaji isma'il ya amshe da "Ai ba lefinsa bane ranka ya dade,,,, Adduarh de kmr yadda mukeyi a fari ita zamu ci gaba dayi, insha Allahu zansa malam muhammadu ya mata rubutu a kawo mata yau,,Allah ya temakeka insha Allahu aski yazo gaban goshi, yafi zafi dole se an jure, Allah yaja kwananka sarki jikan sarki...." Me martaba ya girgiza kai kawai, gani yakeyi kamar har abadan hankalin Abdoljalal baze dawo garesu ba. Alhaji isma'il ya dinga tausar Me martaba hadi da dannar zuciyarsa a kan damuwarsa,,me martaba yana tsananin kaunar waziri Isma'il, wazirinsa ne kuma majibancin lamuransa ne, da zuciya daya yake bashi shawarwari a kan damuwar dake Addabar me nmrtaba shida iyalinsa, wato damuwar Abdoljalal, dabadan karfin tawakkali ba dashi kansa me martaba baze iya taka kafafuwansa ba, shi kadai yasan damuwar dake ransa A kan Abdoljalal a kullum baya bacci yana bisa dadduma Adduarhsa daya ce tall byn ta Allah yajikn mahaifansa, a kan Abdoljalal. Seda waxiri yayi azahar a gidan kana ya bar gidan yana shiga motarsa ya dauki waya yayi dealing wata number me M kawai a jikin number din, bugu biyu aka daga wayar. Bayan sun gaisa daga cikin wayar Alhaji isma'il yace "tsarinmu kmr ba nasara mus'ab duk nasare ..." Cikin tsananin damuwa yayi maganar. Daga cikin wayar dr mus'ab yace "Da nasara ranka ya dade, Domin kuwa har yarinyar ma tasamu ciki da Abdoljalal sede cikin ya zube,...tin ranar na nemi number dinka yallabai bata shigaba..." Wani irin farin ciki ya rufe Alhaji isma'il hadi da damuwa duka, yace "Alhamdulillahi, koda cikin ya zube naji dadih da farin cikin hakan, munasa ran samun wani insha Allahu....sede akwai matsala..." Dr mus'ab yace "matsala cikinta muke ranka ya dade,,, me ya faru yanzu?'' Alhaji isma'il yace "iyayen Abdoljalal suna cikin damuwa a kn lamarinsam a yan kwanakinnan, musammamma ita mahaifiyarsa, kasan kwanaki na gaya maka zuciyarta har kumbura tayi, wlhi ina tsoron abubuwa da dama,, kwata-kwata banasan damuwar me martaba da duk wani jininsa saboda shi mutum ne gareni, shi mutum ne da Alkhairinsa baze mantuba har abadan a gareni...nasha da muka kullah Auren da yarinyar kaf matsalolin AAfimily ze tafi, Amma har yanzu naji shiru mus'ab, Abdoljalal ko mararin gida bayayi mahaifiyarsa na mararinsa tamkar zatayi hauka, in akwai wani solution din muyisa sbda hnklinsa ya dawo ga iyayensa..." Dr mus'ab yayi shiru hadi da sauke ajiyar zuciya byn ya gama sauraren maganganun Alhaji isma'il yace "Ranka ya dade duk wanda yayi hkri yana tareda nasara, akayi hakurin shekarun baya ma balle yanzu, ina ganin nasarori insha Allahu, komi yanada karshe amma banda ikon Allah, insha Allahu matsaloli zasu kau na har Abadan,..." Alhaji Isma'il yaja guntun numfashi kawai yace "Allah yasa...ka dinga yawan kirana a kan cigaban da muke samu..." Dr mus'ab yace insha Allahu ranka ya dade daga haka sukayi sallahma.... A bangaren dr mus'ab suna gama wayar da Alhaji isma'il, daman yana office dinsa ne, ya dauki car key dinsa ko dreva dinsa be tsaya nema ba yaja motarsa ya fice a asibitin direct wata Anguwa ya nufa mesuna turin wada. A dai-dai wani gida me bakar kofa na talakawa yayi packing ya fito ya nufa cikin gidan bakinsa dauke da sallahma a bakin zaure yaga Almajirai cike, kowannensu da allo se karatu sukeyi , ga wani dattijo fari sol zaune cikin almajiran sanye yake da fararen kaya, hadi da farar hula kaf gashinsa na kai dana gemu farare ne sol a kalla tsohon ze iya kai 90yrs amma sam baza ka fahimci hakan ba, sbda digirgir yake, makaho neshi baya gani kwata-kwata. dr mus'ab na shigo zauren ba tare da yayi magana ba malamin yace "Sannu da zuwa Mus'abu ka shige ciki ganinan zuwa..." Dr mus'ab yana mamakin yadda malamin ke fahimtar ya shigo gidan koda beyi mgna ba, daya shigo kasa kasa yayi sallahma yanada tabbacin malamin beji sallahmar ba amma ya gane shine. Dr mus'ab yace "Toh malam..." Ya kara taku uku ya isa wani daki ya shiga dakin cike yake da Alqur'anai warash da litattafai, manya manya da Alluna iri iri, da tawada ya samu gefe daya ya zauna kan tabarma a dakin. Yana zama Malam nata'ala ya shigo dakin idanuwansa a bude suke amma be gani sannan babu ko sanda a hannunsa ya shigo kai kace yana gani nan ko makaho ne, yasamu guri ya zauna kan buzunsa. Dr mus'ab ya gaidasa malam nata'ala ya amsa cikin mutumci. "Malam anya asirinnan dake dawainiya da Abdoljalal ze warware yadda kace tin a farko kuwa?'' Cewar mus'ab. Malam nata'ala yayi murmushi yace "Sosai ma kuwa, ai na gaya maka kaf warwarar sihirin dake kan Abdoljalal yana jikin wannan yarinyar, kuma ka sanar dani sun sadu da juna, har tasamu ciki ciki ya zube,, ka natsar da zuciyarka bamu keyi ba Allah keyi,, tin kafin kaga yarinyar da kakarta a ranar dazaka barnan aini na gaya maka kaje katsina wasu suna nan a asibitnka na katsina sunyi watanni goma basu da kudin aikin daza ama tsohuwar matar, kuma nace ka temakesu sannan akwai yarinya jikar ita mara lafiyar nace a hadasu Aure dashi Abokinka saraki, wanda nike maka addu'ur'i a knshi a kn ya dawo hayyacinsa tsawon shekaru biyar muna tare da kai kuma nake maka addu'ur'i a kn abokinka,, insha Allahu warakarsa tazo wannan yarinyar kaf itace karayar sihirinsa, komi na sirrinsa yana jikinta, sbda akwai wasu iskokai a jikinta kurmaye nesu, dasu aka haifeta sudin sune ke temakonta ako ina, Itadin de ita da iskar dake knta mata da miji nesu, sune sanadin warwarar sihirin abdoljalal , kuma nasan ko a yanzu ai ka yarda da abinda na gaya maka,, na tabbatad bakayi tsammanin ze iya kusantar wata mace ba kuma gashi ya kusanceta saduwar farko tasamu ciki, toh haka abin yake akwai rabo me tsanani a tsakaninsu, amma fa dole akwai kalubale dayawa, babban aiki ma na gaba,, babban sihiri ne ke dawainiya dashi,kasan shi Asiri gaskiyar meshi ne, dabadan temakon ubangiji bama sam ba hk akaso ganinsaba...mu kwantarda hnklinmu muci gaba da ibada sannan komi muga gani daga ubangiji ne, samu ko rashi duk daga mahaliccin da baya kuskurene..." Dr mus'ab yaji zuciyarsa ta nutsu besan meyasa ba In har ze hadu da malam nata'alah se yaji hnklinsa ya kwanta a kan lamarin Abdoljalal. "Allah yasa muji muga Alkhairi, duniya da lahira..." Cewar dr mus'ab. Malam nata'alah ya amsa da Amin.dr ya ciro kudi yan dubu dubu bandir daya, dubu dari ya mikawa malam, malam ya girgiza kai hadi dacewa "kasan bana amsar kudi ni sam , badan kudi nake maka Komi ba, inda dan kudi ne bazan maka ba, kaganni nan Allah ya wadatani da komi Alhamhamdulillahi.... ka bari inka fita kayi sadaka dashi kawai..." Dr yayi kasake yana kallan malam yana mamakin wani iri neshi malamin, 5yrs suna tare amma be taba amsar ko nera biyarba a hannun Dr mus'ab, sede kullum inya bashi yace aah kawai yayi sadaka, shi Allah ya masa komi,, ko Buhunhunan abinci ya kawo masa sam baya amsa, sede yace ya koma dasu kawai yy sadaka, sbda shi bayacin abinci, , sannan kuma beda mata, Dr na mamakin wani irin malami ne shi, sbda shide yasan malaman yanzu da shegen kwad'ayin tsiya, gasu duk bana Allah ba. "Malam meyasa wai baka amsar komi daga gareni ne dan Allah?'' Dr ya tambaya. Malam nata"alah yace "bakomai.... saboda kona amsa bansan yazanyi dasuba..." Dr ya tsuresa da ido kana yace "Kanada bukatarsu malam..." Malam nata'alah yace "sam bani da bukatarsu...kayi sadaka kawai karka kara cewa komi tashi ka tafi..." Dr mus'ab be kara masa musu ba ya masa godiya sukayi sallahma, ya tashi ya fice a gidan zuciyarsa a kullum cike takeda mamakin hali irin na malam nata'alah. Kuyi hakuri fans mura ta matsamin amma yanzu bazanyi hutun friday da saturday ba. A bangaren Abdoljalal kuwa Sati daya cir yayi yanata isa yana wani cika yana batsewa, se fushi yakeyi shi a dole wallahi ita ta zubar masa da ciki, Almuqri'ah kam shareshi tayi zuciyarta fal haushinsa, ko zuwa dakinta yadenayi, sede yasa Ahamad kullum ya dinga kawo mata abubuwan Ci dasha da sauransu, shide yana side dinsa, a kullum da bakin cikin ta zubar masa da ciki yake kwana yake tashi, ji yakeyi kamar zeyi hauka, kulawa iya kulawa yake bata amma sam baya zuwa Dakinta, kullum da Jimmalo suke wuni suna hira, shakuwa tashiga tsakaninsu a yan kwanakinnan. Almuqri'ah tasamu karfin jikinta, jinin barin datayi sati daya yayi yana zuba ya dauke.... A daddafe Abdoljalal ya iya kwanaki goma yana fushin da ita, da kyar,