← Book details Wata Kishiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 107

Sashe 103

Wata Kishiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Inajin yarannan kmr jinina ne me martaba.." Salma ta fadi still tana kwallah. Me martaba ya dago ya kalleta yaga tana kwallah yace "Nima haka nakeji wlhi salma,, kinga yaran sak d'ana danafiso a duniya,,, munaso musan wacece wannan uwar yaran kuma waye uban yaran, in zeyu kawai uwar da uban su bar mana yaran ko kudi sukeso semu basu mu su bamu yaran..."cewar me martaba. Hajiya salma ta dago ta kalleshi tace "In bazasu bamu ba se in bisu gidansu wlhi ina san yarannan bani sauran in daukesu duka.." Duk dr na tsaye yana kallansu sede besan me suke cewa ba sbda bejin hausa shi ibra ne. Murna mara misaltuwa salma da Me martaba suka shigayi. Salma tayi tayi me martaba ya bata sauran yaran yaki sede ta rike dayan ta hakura shikam ya hakimce ya zauna yaki bada yara kai kace shine ubansu. Ba jimawa jakadiya ta dawo da uban kayayyaki kama daga na babys har zuwa wanda uwar baby zata bukata duk seda jakadiya ta kawo, datazo taga babys din itama seda gabanta ya yanke ya fadi, ganin yaran sak Abdoljalal, macen kuma sak hajiya salma,. Seda jakadiya ta kasa daurewa tace "yarannan se naga kmr suna kama da farin cikinki mamanmu, ita kuma macen tana kama dake uwar dakina..."jakadiya ta fadi cikin mamaki. Salma dame martaba suka hada idon kallon junansu "e wlhi kinga ikon Allah ko.." Cewar salma. "Babban ikon Allah ma kuwa..." Cewar jakadiya da mamaki ya daskarar da ita, amma kuma seta tuna ba a mamaki da ikon Allah. Almuqri'ah ta farka cikin aminci taga yaran da ubangiji ya bata kyauta, ita kanta seda gabanta ya fadi ganin kamannin yaran da ubansu ya baci, se macen de ta rasa gane dawa take kama ita, amma tafi kaf yaran kyau da farin fata kmr a tabata jini ya fito. Seda Almuqri'ah tayi kukan farin ciki, tayima hajiya salma dame martana godiya. Se a yanzu be suka fahimci bebiya ce, se tausanta ya kara ratsasu. Salma dame martana zuciyoyinsu na cike da zallar tambaboyi ga Almuqri'ah amma sede ba halin hakan ganin halin da take ciki. Tashiga bawa yaran nata nono suka amshe kmr suna jira, nan suka zuko nonon se adduarh take musu dasa musu albarka, a zuciyarta tana ayyana inama ace Abdoljalal na nan yaga yaran nasa har hudu reras. Jefi jefi Almuqri'ah nata bin hajiya salma dame martaba da ido, se yanzu take kara ganin kamanni su da Abdoljalal. "Ikon Allah..." Shine abinda Almuqri'ah keta fadi a ranta yayinda zuciyarta ke yawan faduwa inta kallesu. Da kyar me martaba da salma suka bari yaran sukasha nonon uwarsu suka koshi suka amshesu suka rungumesu in suna rike da yaran wani irin yanayi suke shiga. Satinsu daya a asibitin Almuqri'ah tasamu sauki aka sallamesu suka koma gida da niyar nurse zata dinga zuwa duba Almuqri'ah din sbda dinkin da aka mata a ciki.. Suna komawa gidan hajiya salma tabawa Almuqri'ah part daya ita da yaranta,.wata iriyar kulawa salma ke bawa Almuqri'ah da yaranta da kullum suke gunta ta musamman. Me martaba da salma da jakadiya kullum suna part din da Almuqri'ah take, ga yara na hannunsu sallah kawai kesasu ajiye yaran a hannunsu Almuqri'ah na mamakin irin san da suke nunawa yaran nata zata iya cewa ko ita bata sansu kmr yadda su suke sansu. Byn dasowarsu da sati daya salma ta kasa daurewa , suna zaune a kayataccen dakin Almuqri'ah ta kalli Almuqri'ah ta kalli me martaba dake zaune, da kuma jakadiya dake zaune. "Baiwar Allah ki bamu labarin wacece je dan Allah? Wanene uban yarannan naki dasuke tsananin kama da d'ana dana haifa da cikina..." Cewar salma. Gaban Almuqri'ah ya yanke ya fadi jin abinda hajiya salma tace. "Suna kama da d'anki? Nima kunamin kamanni da baban yaran nawa.." Almuqri'ah ta fadi cikin zallar mamakin data jima dashi a ranta, ganin hajiya salma nasata a tsananin dmwr kewar mijinta wasu lokutan ko baccin kirki bata iyawa sbda tasan mijinta na cikin zallar tsananin dmwa da tashin hnklin rashinta a kusa dashi musammanma cikin jikinta. Dukda da bebanci tayi maganar amma duk sub fahimci me take nufi. Me martaba da salma suka kalli juna. "Dan Allah wanene ku a ina mijin naki yake?'' Cewar salma. Almuqri'ah tayi jim kana ta basu lbrin dalilin barowarta gidanta da mijinta na aure, tace ta bar gidanne kawai sbda kishiyarta zata kasheta data fahimci tanada ciki. (Almuqri'ah ta boye musu abubuwa dayawa ta basu short labarinta da Abdoljalal da saude) sukaji tausanta me tsanani, nan take duk sukaji sun kara santa soyayya me tsanani, yayin da zuciyoyinsu duk suka cika da kwad'ayin san ganin waye uban yaran nan na Almuqri'ah. "A ina yan uwanki duke?'' Cewar salma. Almuqri'ah ta basu lbrin cewa batq da kowa se kakarta kuma bata kasar tana can kasar waje gun nema mata lafiya, wani ya dauki nauyin nema mata lafiya a kasar wajen sbda su basu da komi, kuma su ba yan nigeria bane su yan sudan be.(tade boye musu Ainifin dalilin zuwanta gidan Abdoljalal tade bayyana musu abinds ze bayyanu sauran ta barwa ranta.) Me martaba da salma duk suka karajin tausanta sosai. "Ki zauna damu pls har Allah yayi ikonsa, kakarki ta dawo Nigeria se itama tadawo nan gidan da zama, harde ubangiji yasa ki koma gidan mijinki knji..." Cewar salma. Ba musu Almuqri'ah tace "Toh...ngde Allah ya biya da Alkhairi ." duk suka amsa da Amin, komi tace suna fahimta dukda da bebanci take magana. Hk kawai Almuqri'ah taji ta aminta dasu 100% kuma tana kaunarsu 100%.. "Wani suna za asawa yaran naki?'' Me martana ya tambayi Almuqri'ah ganib time nata tafiya bawa yaran wuduba da sunansu ba... Almuqri'ah ta rasa mezatace kawai seta tsinci kanta dacewa "Asa ma macen sunan mamana,(shine sunan data bawa salma mamanta take ce mata...) Mazan kuma asa musu sunan daya dace kawai..." Ta fadi da bebanci. Me martaba da salma sukaji dadin karamcin da yarinyar ta musu, ba bata lokaci me martaba yama yarinyar huduba da sunan salma, mazan daya yasa sunansa, se daya yasa sunan abdoljalal, dayan kuma yasa sunan isma'il wato yarimansa. Seda ya gama musu hudubar kana ya shaidawa salma sunan dayawa yaran, taji ddh sosai kaf kowa yaji dadin hakan musamman Almuqri'ah dataji ansa sunan Abdoljalal kuma yace sunan dansu ne, ita kuma sunan masoyinta ne wanda ya iya cin gindinta. Almuqri'ah taga ikon Allah sosai , ga sunan dansu da sunan mijinta duk daya, haka kawai itama taji tanaso taga d'an nasu. Byn kwana hudu aka shirya bikin suna na gani na fadi, kowanni yaro aka yanka mishi sah, wato sah hudu aka yanka ma yaran.ansha hidima ywar jego tasha sutura ta arziki, dan akwati dozin biyu tama mejegon me martaba yamata dozin biyar, sukam jariran ai dozinan kayayyakin da aka musu baze misaltuba. Anci ansha a suna an raba kayayyaki na Alfarma, harda kudi aka raba na fitar hankali dukde abinda Allah ya ciyar dakai a sunan shi zaka samu. Paid book ne. Allah yasa mu gama lafiya. Ammah tasamu sauki sosai, dan haka suka tattaro suka dawo kasar nigeria, Dr mus'ab ya siyama Ammah gida ta zauna cikin aminci se godiya take masa mara iyaka, nurse mami takoma ga yaranta domin bata da miji tini ya jima da rasuwa, . har gidan mami Ammah tasa dr mus'ab ya kaita ta mata godiya mara iyaka, harda kuka, a zamaninnan ammah bata tunanin za a samu mutane irin Dr mus'ab da nurse mami. Dr yayima mami goma sha tara na dumbin Arziki arziki. Satinsu daya da dawowa kasar Ammah taji dadin jikinta sosai, tanata ci gaba dashan sauran magungunan da likitoci suka daurata a kai, a halin yanzu jikarta Almuqri'ah kawai takeson gani, tanasan taga a wani hali take ciku zuwa yanzu. Dan haka ta fara tambayar Dr kan yaushe Almuqri'ah zatazo, ko ita zataje ta ganta... Dr ya fuskanci tana da bktr ganinta sosai, dan haka yace zeyi kokarin hakan. Tinda ya dawo kasar beje gidansu ba, shima yanada bktr san ganin Almuqri'ah da Abdoljalal, dan haka ya shirya yau after la'asar ya nufa gidan Abdoljalal,. Tin daga bakin get mus'ab yaga gidan ya chanza masa sosai, securities duk sun chanza masa, dabadan Ahamad dake bakin get din ba, da sam Dr mus'ab baze samu shiga gidan ba, sbda su securities din dake aikin ynzu basu sanshi ba. Yanayin packing Ahamad yazo ya bude masa, murfin motar ya fito ya zubawa Ahamad din ido nan take yaga duk yayi wani zyru-zuru, to duk hankali ba kwance ba, abinci wannan ma se yayi da gaske yake ci, hakan yake ga gogan shi san yadena cin abinci ma sede ruwa kadai dr ke zuwa yana kara masa, shima ruwan se yaga ze mutu ake kara masa shi, duk yabi ya fice a hayyacinsa wanda ya sanshi ada inya ganshi yanzu se yayi da gaske yake iya ganeshi. Saude kam ai tinima ita wannan ta dena ci itama tadena sha se aikin yawan bin malamai kawai takeyi, dukda malaminta ya tabbatar mata da Almuqri'ah ta mutu ita da cikin jikknta amma bata hakura ba se bin wasu malaman takeyi saboda hankalin mijinta yaki dawowa gareta, tini duk tabi ta sabe tayi wata uwar ramar daba kowa itama yake ganeta ba, sbda mulkin datakeyi yanzu sam bata isa tayishi ba, asirin takeyi amma sam gani ma takeyi asirin baya Aiki,Hajiya Abulle ta dawo da ita suke yawon bin bokayen amma sam ba nasara Saude tazama kmr zautacciya, ta nemi lambar kande domin taci ubanta amma shiru lamba bata shiga, kaf maaikatan gidan mata da maza banda securities duktasa an musu duka jina jina, ta musu cin mutumci na fitar lissafi, kana ta koresu a gidan har jimmalo, gida de ya koma daga saude seme dafa mata Abinci, to yanzu bata ma da kwanciyar hankalin dazata ci abincin dan haka ba abincinma take ci ba, aikin me dafa abinci yakoma gyaran gidanta kawai. "Ahamad meke faruwa ne duk kabi ka zabge kayi duhu? Gidanma dukya chanza min.." Cewar dr mus'ab da yy mgnr cikin dmwa yayinda jikinsa ke bashi babu lafiya. Ahamad ya fara hawaye, hkn ya kara tadawa dr hankali. "Meke faeuwa? Dan Allah ka gayamin..." Ahamad ya fara mgna yana kwallah "Ranka ya dade duk mun nemi numbers dinka shiru..."
Chapter 103 · 0% Book details