← Book details Wata Kishiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 107

Sashe 31

Wata Kishiya Complete Hausa Novel · about 5 min read

tayi murmushi tace "Tome kike nema yanzu a duniya mrs AASARAKI?" Hajiya Saude tayi yar dariya tace "Babu duk abinda nake nema nasamu.." Abulle ta amshe da "Kinsamu kuwa har abada..." Duk suka kwashe da dariya, dai-dai suka iso bakin motar hajiya Abulle sukayi sallahma tashiga dreva yajata suka fice a gidan, seda hajiya saude taga ficewarta a gidan kana ta koma side dinta zuciya cike da nishadi. Yau kimanin 1month kenan da kwana daya tana dafa masa abinci yana ci yana koshi, amma basu taba haduwa da juna ba, sbda kullum hajiya saude cikin kara jaddada mata warning takeyi kan Karta shigar mata harkar miji infect ma karta bari ya ganta kwata-kwata dan zata iya kasheta a kn mijinta! Wannan itace kalmar datafi bata tsoro a tattare da hajiya sauden kuma daga ganin yadda take maganar tasan tabbas zata aikata hakan har fin hakanma sbda ta fuskanci ba imani a lamarin matar. Tinda ta fara dafa masa abincin ya tsinci kansa dason ganinta yayi-yayi iya dabarunsa danya ganta be ganinta. Sede ko data ajiye abincin ya fito ko kuma daya wuce tashigo dan gudu gudu takeyi inta shigo side dinsa Ta fice. haka kawai yake tsintar zuciyarsa da mutuwa ason ganinta lokuta da dama ma da tunanin san ganinta yake bacci se yayita mafarke mafarke a kan harya ganta amma bega face dinta ba, sede a mafarkinsa kawai yana ganin farar mace tarr tarr amma be taba ganin fuska ba. Yau tin 9:am ya tashi sbda mafarke mafarke daya dingayi na yarinyar yau mafarki yayi wai tayi serving dinsa da abincinta me dadih amma fuskarta da nikab tana sanye da ash color din hijjabi a mafarkin. Yana tashi yayi wanka ya shirya cikin kayansa na zaman gida na hutu masu launin light golden, ya gyara sumar knsa tsaf ya feshe jikinsa da perfumes dinsa se sauri sauri yakeyi, yau kamata yayi yaje office amma yaki zuwa saboda yanaso yaga ko wacece me dafa masa abincinnan me dadih, tsawon 31days yanacin abinda ta dafa yau yayi alqawarin seyaga ko wacece. Tsayawa yayi gaban madubi yana karewa knsa kallo yayi kiba yayi fresh har wani tumbi ya fara ajewa yasan duk aikin dadin abincin yarinyar ne ke habbaka jikinsa, sajen dake zagaye da kyakyawar fuskarsa ya kara kwanciya luf fuskarta tayi wani azababben kyau. Daga kansa yayi ya kalli agogon bangon dake dakin dai-dai ya buga 9:30am lallai ya tabbatar yau yanaso yaga wacece boyeyyiyar me dafa masa abincin dadinnan a 30mnt yayi wanka ya shirya shida yake daukar awanni in zeyi wanka da shiryawa. Sauri-sauri yayi ya zira lallausar slifas dinsa na zaman gida, ya fice a dakin ya ya sakko Kasan benen Ya kalli kofar dinning room dinsa yaga ya nuna white din light hakan ya bashi tabbacin tini tashigo ta ajiye masa breakfast dinsa ta fita, ji yayi beji dadih ba jiki a sukwane ya karasa yayi breakfast din ya zauna nan yaki tashi dan yau ya ayyanawa ransa seyaga wannan ko wacece, yana nan zaune ya tuna yana tsammanin wani kira, tashi yayi zuwa upstairs dinsa, domin ya dakko wayoyinsa yana shiga dakin ya tadda wayar na ringing ya karasa ya dauka, nan wayar ta dauke masa hnkli har 30mnt suka shude sannan suka gama wayar, sakkowa kasan yayi da wayoyinsa a hannunsa ya isa dinning room din tini an shigo an kwashe komi, haushi ya kamasa ya koma falon ya zauna yana jiran har ta kawo masa abincin rana, yana nan yana jira dadih da iskar sanyin AC ya ratsashi har ta shigo ta fita itama bata gansa ba sbda ta kofar kiching zuwa dinning room din tashogi. Shi kam gogan kiran sallar azahar ne ya tashesa ya mike hadi da salati yana mejin wuyansa ya kage masa sbda kusan a zaune yayi baccin, bawai jin dadin kwanciya yayi ba kawai baccinne ya masa zuwan bazata. Idanuwansa ya sauke a kn saman kofar dinning room din, ya ga ta nuna white light haushi ya kuma kamasa yasan baccinnan ne ya cucesa dabeyi baccin ba tabbas dole ne zeji shigowar mutum. Toilet din dake manne a falon ya shiga ya dauro alwala ya fice a falon zuwa masallacin dake cikin gidan, be dawo ba se after 2:pm. Direct dinning room ya isa ya zauna yayi sarving knsa da dadd'an abincinta, ya cika tumbinsa taf ya zauna ya kasa ya tsare yana jiran zuwanta, kawai se wayarsa dake falon tayi rurin neman agaji mikewa yayi ya nufa falon nasa, ya duba yaga number din abokin aikinsa ne dauka yayi ya kara a kunne nanma wayar ta kuma dauke masa hankali har tazo ta kwashe kyn ta fita dasu be sani ba, seda ya gama wayar ya dawo dinning room din nanma bakin ciki ya kuma rufesa ganin ta kwashe komi ya juya ya koma saman zuciya fal rashin dadih.... Da daddare ya fita zuwa meeting dan haka be samu damar cin abincin data ajiye masa ba, 2tyms tana zuwa tana dubawa danta kwashe kwanukan taga beci ba seta barsu har zuwa 1:am sannan ya dawo gidan direct dining room din ya nufa a gaggauce yana shiga dai-dai ta juya baya zata bar dining room din hannunta rike trea din abincin data kawo a tunaninta bazeci ba shiyasa tazo kawai ta kwashe jin shigowar mutum ya dakatar da ita daga bude handle din dazata kaita kiching din, sbda kamshin jikinsa daya haifar mata da mutuwar jiki hadi dajin bugun zuciyarta very pass, nan take tayi mutuwar tsaye batare data juyo ba, se numfarfashi take saukewa akai akai, kai kace karya tayi aka kamata hannu dumu dumu. *Ni bana gajarta labari komi sena fadeshi dallah-dallah ashata yadda tazo pls...* Vip 1k normal 500 0542703718 Saadatu Abdullahi gt bank shedar biya ta nan 08101626484 ko M.T.N card. 'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE selling MTN data with this cheap price MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month Airtel,9mobile and Glo also available. *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* Whatsapp OR Call *08066268951*
Chapter 31 · 0% Book details