Sashe 35
Wata Kishiya Complete Hausa Novel · about 4 min read
knta yayi ya daura a kan kafad'arsa yana me buga mata baya cikin sigar kwantar da hankali ya fara magana. "Bazaki sawa ranki hakuri ba ko uwar gidana?'' Kmr tana jiran yayi maganar kawai ta fashe da kuka tare da shashsheka kmr zuciyarta zata tarwatse haka takeji. Kara rungumeta yayi a jikinsa sosai yasa bakinsa a cikin kunnenta yana furta mata kalamai masu dadih, da kyar yasamu ta tsagaita da kukan amma still tana hawaye sbda batayi kukan daya wadaceta ba, ta dago knta dake jikinsa ta zuba masa ido kana ta fara magana "Zuciyata ta gaji da hkri....dan Allah Yallabainah yaushe saraki zezo gareni kmr yadda ko wacce uwa d'anta ke zuwa gareta? Zuciyata na cike da karaya a kan jalaluna dan Allah ka kirasa a waya kace yazo ya ganni inaso insa kansa a kirjina yaji dumin zuciyar uwa kmr yadda ko wanni d'a keji shima yasan shi d'a ne ba maraya ba..." Yadda take mgnr tini me martaba ya fahimci kmr tana neman fita a hayyacinta ne, Cikin muryar kwantarda hankali me martaba ya fara magana ta yadda knta ze dauka yasan abinda takeji a zuciyarta tanada dauriya a matsayinta na uwa kuma mace me rauni. "Zezo gareki insha Allahu salma, ki kwantardamin da hankalinki dan Allah kinga shekaran jiya dr ya duba jininki yaga ya hau..dan Allah salma kiji tausayina kisawa ranku dauriya kici gaba da Adduarh kmr yadda kk saba karki sabauta min rayuwarki dan Allah zan kirashi ince yazo ya ganki..." Ya fadi mgnr karshe ne dan hankalinta ya kwanta amma yasan koya kira dannasu da wuya ma ya daga, inma ya daga ba lallai yazo ba, gabaki daya tamkar basu suka haifesa ba haka yake rayuwarsa. Ajiyar zuciya ta sauke tasan mgnr daya fadi kawai danya kwantar mata da hankali ne, hawaye keci gaba da zirya a idanuwanta ta fara magana. "Nasan baze zoba me martaba,,," ta fadi hkn tana jinjina kai. Daura hannunsa yayi a kn cinyarta yace "muci gaba da Adduarh insha Allahu komi ze zama labari..." Girgiza masa kai tayi tana fadin "Kullum kullum inatayi Nagaji Wallahi, kasan zuciyata na cike da son yaronnan shi kadai Allah ya bani duk duniya wallahi me martaba ba wanda yasan me nakeji a zuciyata ko yau na fadi na mutu da yaronnan a zuciyata na mutu, San duniya da Allah yasamin duk ya tabbata ne a kan yaronnan, inaji a jikina kamar ba ranar da yaronnan zuciyarsa zata dawo garemu, .." Rufe mata baki me martaba yayi da hannunsa yace "karkiyi sabo knji iyalina, karki mnta da babu abinda yafi karfin ubangiji dan Allah kici gaba da hakurin danasanki dashi pls..." Daura kanta tayi a fuskar gadonta, ita kadai tasan wani hali zuciyarta ke ciki, gani takeyi abinda takeji ma a kan Abdoljalal koshi dayake ubansa bejin rabin abinda takeji, (wani abin se uwa kan uba baze dauka ba?. "Inaji a jikina da kunci zan mutu a zuciyata na Soyayyar Jalaludden...'' Ta fadi hakan yayinda zafafan hawaye ke kara wanke mata kumatuna.. Me martaba ya fuskanci zafin datakeji ne a zuciyarta yake kokarin fitar da ita a hayyacinta maganganun datakeyi ma daji bata hayyacinta. "Dan Allah ki dena irin wadannan kalaman, bansan sake jinsu daga gareki dan Allah ki fawwalawa ubangijin sammai lamarinki, yaronnan Allah ne ya bamushi kuma ya rubuta komi na kaddarorinmu da nashi kaddarorin , dan Allah ki maida lamarin nan inda muka saba maidashi wato ga ubangijinmu banason irin wadannan kalaman na fitowa daga gareki gimbiyata, ki kwantarmin da hankalinki dan Allah na rokeki kiji tausayina hajjajuna...." Ya karashe maganar hadi da jawota jikinsa, still se kwallah takeyi, gani takeyima kmr mijin nata be fahimtarta kwata-kwata itama bata fahimtarsa ko kadan, Son danta tilo kadai ke dawainiya da zuciyarta, a haka ma tayi kwarin zuciya dan babu jinsin balaraben daze iya jure abinda take jurewa, saboda a yarirrika da dama na duniya babu jinsin yaren daya kai balarabe san yara musamman ma ita da kwara daya tall Allah ya mallaka mata a duniya, ita fa bata ki koda yaushe ta dinga sashi a idanuwanta ba, amma yanzu shekara da shekaru be zuwa inda suke ai dole tashiga damuwa iya damuwa....lallashinta me martaba ya dingayi har yasamu ta dan fara nutsuwa ya saka mata karatun alqur'ani ba jimawa taji zuciyarta ta kuma sanyi ta dawo hayyacinta nan take bacci nannauya me cike da mafarkin Jalaludden dinta ya kwasheta. *Akwai wata a kasa fa...* *Vip 1k normal 500 0542703718 Saadatu Abdullahi gt bank. shedar biya ta nan 08101626484 ko M.T.N card duk ta wancan sim din.* selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE selling MTN data with this cheap price MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month Airtel,9mobile and Glo also available. *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* Whatsapp OR Call *08066268951*