Sashe 101
Wata Kishiya Complete Hausa Novel · about 8 min read
abinda idanuwanta suka gani suka dawo mata sabo fil zuciyarta tayi nauyi, idanuwanta suka kawo kwallar bakin ciki, kunnuwanta sukayi dum-dum abinda sukaji basu tabajin irin su ba har abadan,ji takeyi kamar a mafarki take, ta bude idanuwanta ta kalli saman slin din dakin asibitin, batasanma a asibiti take ba se yanzu. zumbur ta tashi zaune jikinta duk ya mutu , tamkar ba ita ba, "Dama mutuwa nayi da ganin wannan matsifar..." Ta fadi a bayyane duk tabi ta fada a lokaci kankani se zare ido takeyi, larai ta kureta da ido, matsifa da zallar bala'i kawai ta hango a cikin idanuwanta. "Ina Abdoljalal?'' Itace tambayar data fito daga bakin hajiya saude wadda tayi tmbyr kmr tayi hauka sbda tashin hankalin datake ciki ya kara dawowa sabo fil idanuwanta suka kara kawo kwallah. Larai ta tabbatar da tashin hnklin da saude take ciki babba ne sbda bata taba ganin tashim hnkli a tattare da ita ba kmr na yau, dadin da d'awa ga kwallah, bata taba ganin kwallah a idanuwanta ba se yau . "Yana asibiti a farko amma zuwa yanzu yana gida..." Cewar larai da tayi mgnr kmr tana tsoro kasa-kasa. Hajiya saude ta watsa ma larai wani irin mugun kallo ba tare datace komi ba, gabaki daya haushin kowa takeji a duniya musammanma su larai, tanada tabbacin sun san komi dake faruwa amma basu ankarar da ita ba seda Hajiya lubah tazo ta ankarar da ita, se yanzu take nadamar cin mutumcin datayi ma hajiya lubar, ta kulla aniyar kaf ma'aikatan gidan seta musu axaba mara misaltuwa. "Hakkina ne ya tabashi yasashi ciwo....Abdoljalal yaci amanata, wlhi se Amanar Allah tacishi, ..." Cewar hajiya saude,datayi mgnr yayinda zuciyarta ke kuna, hawayen idanuwanta suka kara tsinkewa. Larai ta bita da ido kawai a zuciya tace "Kede haka zaki mutu cikin rashin wayau...hakkinki din me ya dauka daze sashi ciwo kece de hakki ke dawainiya dake ,haka zaki kare harki mutu, duk abinda ka shuka shi zaka girba..." Hajiya saude ta sauke nannauyar ajiyar zuciya , ji takeyi daman ranar mutuwarta tagani da wannan ranar data gani , bata tabajin ta gaji da duniya ba kmr yau. "Ke dan bura uban ubanda ya haifo ubanki, tsinannu, yan iska butulu, dukse na hada na kwashewa kaciyar bura ubaku albarka, tsinannu, yan iska, yayan Allah bani ko yaya ne,,,,ai dani kuke zancen.... Dan bura ubaki tashi jeki kirawo nurse ta ciremin wannan ruwan banga amfaninsa a jikina ba...."hajiya saude tayi mgnr cikin azabar ruwan wutar bala'i da matsifa hadi da tashin hnklin dake cike da zuciyarta. Jin irin uban zagin data antayowa larai yasata mikewa jiki na rawa ta fice a dakin, a zuciyarta tace "Ai kadan muka gani,,,nasan duk se kinci ubanmu ko baki fadi ba, tinda baki mutu ba ai tashin hankali be kare ba a gun uban kowa,yanzu ma aka fara ..." Zuciyar larai ta shiga dukan uku uku, ta nufa inda nurse's suke cikin hanzari. "Ni saude matar saraki, yau nice mijina kecin wata mace, har yake sambatu, har ya mata ciki, wai kuma ina raye...never! Wallahi senayi kisan kai, wlhi sena zama rikakkiyar yar daba, sena dauki rayuka da dama koshi jalalun wallahi bazan barshi ba!! ..." Saude ta fadi kmr mahaukaciya bayan fitar larai a dakin. Se kuma ta tashi tsaye zumbur kamar mahaukaciya ta fasa wani irin mahaukacin gigitaccen ihu, seda kaf asibitin ya amsa gata abu ba kadan ba. Paid book ne.08101626484 Dai-dai ta fasa ihun dai-dai Nurse da Larai suna kofar dakin nata, jin ihun datayi yasasu dannawa cikin dakin a gigice suka ganta tsaye se zare ido takeyi kmr zararriya, idanuwanta duk sun kumbure, hawayenta ta kasa yi. "Ke dan ubanki karaso ki ciremin wannan tsinanninan drip din..."cewar Saude da tayi maganar da nurse. Abinka da asibitin kudi, kudinma ba yan kadan ba, nan da nan nurse din ta Kara so ta cirewa saude drip din jikinta, se uban matsifa takeyi tana zage-zage, ta fice a asibitin kmr mahaukaciya,larai na biye da ita a baya, suka fito harabar asibitin ba mota,. Larai ta kira dreva ba jimawa yazo. hajiya saude ta hau sirfafa masa zagin dabesan dalilinsana,. Ya dinga bata hkri kawai domin yasan abinda ke cinta a zuciya, dmn sun shiryawa bala'inta tini. Ya bude mata gidan bata ta shiga jikinta sam ba karfi, sun tada mota zasu bar asibitin kenan a guje doctor din dake kula da Hajiya saude, yazo ya dktr dasu daga fita, yace si basu sallametaba. Nan fa saude ta zakalkalo mata ta zagesa tass, dr yaga abu yafi karfinsa ya bata hkri kawai suka fice a asibitin. Se girgiza kawai takeyi a cikin motar har suka isa tana kukan zuci,,ta rasa ma ta ina xata fara, amma ta Ayyanawa ranta yau seta kashe Almuqri'ah, idanta idanta to tabbas ota ce ajalinsa koda hakan dazatayi shi ze zama na karshe a duniyarta daga nan se a kasheta ta yarda da hakan. Suna isa gidan ko packing dreva be gamayiba saude ta fito tabi masu gadi da ido, taga duk an chanzasu, tanaso ta tambayi larai ina wadancan masu aikin amma bala'i be barta ta tayi tambayarba. Ta nufa dakin Almuqri'ah ko kallan gabanta batayi sbda bala'in dake cinta. Tana isa dakin ta banko kofar dakin cikin bala'i da matsifa,idanuwanta cak suka tsaya a kan Abdoljalal wanda ke zaune kasan dakin duk yabi ya rame ya lalace, jikinsa duk kasusuwa sun bayyana a wuyansa tmkr wanda yayi ciwon shekara da shekaru, yanzu nan dakin yake rayuwarsa gaba daya, sallah kadai ke fita dashi daga dakin, gaba daya baya hayyacinsa, ko ruwa besha, tunanintane abincinta tunanintane abinshansa , kukansa kuma shine samuwar sassaucinsa a kan tunaninta, zuwa yanzu ya kwammaci mutuwa a kan rayuwar tashin hankalin da yake ciki, bayasan kowa a duniya for now se ita, daze bada uban kowa bnda iyayensa a bashi ita wallahi zeyi hakan, zuwa yanzu ba cikin jkinta Yake bukata ba har itama yana tsananin bukatarta. Abdoljalal ya dago shima ya zubowa hajiya sauden ido, sam ma ya mance da ita in ba yanzu ba daya ganta. Saude ta kara kuresa da ido zaune yake ya wani rakube kmr maraya sanye yake da jallabiya milk color, wani irin haushinsa ne ya turnike hajiya saude, kishi da zallar bala'i da matsifa suka turniketa. "Maci amana wato yanzuma kana nan dakin nata kenan...wallahi wallahi bazan barku ba, har kai bazan bari ba, ... Ina ita yarinyar take dan wallahi yau nice ajalalinta..." Cewar saude dake mgnr kmr zata cinye kanta dan zallar bala'i da matsifa, hnklinta ya kara tashi sosai, saboda mijinta data kara gani yau kuma a dakin yarinyar. "Abdoljalal ka cuceni!'' Ta fadi wasu zafafan kwallah na zubowa daga idanuwanta, yayinda takeji a zuciyarta koda ta kashe yarinyar da Abdoljalal din duka bazata huce takaicinndake zuciyarta ba. Tinda ta fara magana kawai kallanta Abdoljalal yakeyi, se yanzu ya kara fahimtar tsoron saude ne yasa Almuqri'ah barin gidansa, haushin saude ya rufe Abdoljalal, be tabajin ya tsani saude ba kmr yau. Saude tana kuka ta shiga dube dube a dakin tana fadinn"Ina take tsinanniyar..." Ta duba toilet taga bata ganta ba, ta dawo kan Abdoljalal tana haki kmr zuciyarta ta tarwatse. "Ina tsinanniyar take..." Ta fadi da karfi kmr zata tsage dakin. Dago red eyes dinsa yayi ya zubo mata su , zuciyarta ta fara turiri yayinda kiyayyarta ke yawaita a zuciyarsa. "Batanan ta gudu saboda ke..." Abdoljalal ya fadi kmr ze fashe da kuka. Kallan rashin fahimta saude tabishi dashi. "Ta gudu kmr ya..." Cewar saude,. Abdoljalal ya tashi tsaye yayinda jiri ke neman kwasarshi kmr zautacce yace. "Ta gudu ta barni sbda ke, ta gudun min da ciki sbda ke,...kema yanzu ki fita ki barmin gidana banasan ganinki na tsaneki..." Abdoljalal ya fadi da babbar murya, yayinda kmr ya rufeta da duka. Nan take Saude tayi mutuwar tsaye, yayinda jikinta ya dauki rawa hnklinta ya tashi, tashiga tunanin anya kuwa wannan jalaluntane?'' mamaki da tsananin tashin hankali suka rufe hajiya saude. "Abdoljalal, dan Allah kaine kuwa? Ni kake cewa in bar maka gida yau?'' Ta fadi jikinta na kara macewa yayinda tashin hankalinta ke kara ninkuwa, wai yau itace jalalu ke kora a gidansa,tabbas tasan tata ta kare, tayi babban sakaci, ta fara tunanin asiri yarinyar nan tayima mijinta wanda yafi nata sihirin karfi. "A, dake nake...ki bacemin da gani bnasan ganinki ki barmin gidana...!!!''' Abdoljalal ya fadi cikin tsananin tsawa kmr ya daketa hk yakeji. Ganin hakan yasa jikin hajiya saude macewa sosai, mamakinta ya ninku, ganin Abdoljalal na niyar dukanta, yasata ficewa a dakin kmr mahaukaciya ta fito tana fadin "shikenan ta kasheni, ta kwacemin miji, ta bashi asirin dayafi nawa yasha... Nashiga ukuna ni saude..."saude ke sambatun tana tafiya, ta daura hannu a kai, ta nufo dakinta kmr zararriya ta daukko wayarta ko gyara jikinta bata tsaya tayi ba, ta dawo compound kmr zararriya tana tafe tana sambatu, ta karaso packing space ta kwalowa dreva kira, yazo ta kalleshi ta watso masa wani ashar se kuka takeyi ta kasa controlling tashin hankalinta, dreva din ya kalleta yace "Kiyi hakuri hajjaju..." Saude da jikinta ya gamayin sanyi ga tashin hankali ga dmwa, a hasale tace "Kutmar bura uban ubanda ya haifo ubanka duniya kaida hakurin dan durin uwarka,,,,shegu si duk kune munafukan yan bura uba shegu munafukai, bari in gama da wannan bala'in na gabana, in dawo kanku duk se naci kundun bura ubaku wlhi nice ajalinku kaf ma'aikatan gidannan, bade daku aka cuceniba..." Saude ta fadi tana kuka, tashiga byn motarta, drevan data gama zagi ya kalleta kawai yaji zafin zagin amma ya shanye , ya fuskanci hakkina ke dawainiya sa ita Adduarh ya shiga mata Allah ya karo mata abinda yafi hakan, murmushi yayi a zuciyarsa yashiga motar yaja suka fice a gidan se kallan saude yakeyi tana kuka sosai harda majina ta glsss. "Sakwato zamuje..." Saude ta fadi cikin kuka kmr ranta ze fita, har tsatstsede sumar kanta takeyi da hannayenta, ji takeyi kmr zuciyarta zata fashe, duk tabi ta rame, wandan dake jikintama rawa yakeyi a kugunta. Jin tace suje sakwato Dreva ya kalli agogon motar yaga 11:pm ake nema yanzu,amma ba halin yayi magana, dole ya hau titin zuwa sakwato. Manage. Suna tafe saude na kukan bakin ciki, har mamakin kanta takeyi anya itace kuwa saude?