Sashe 64
Wata Kishiya Complete Hausa Novel · about 8 min read
danta tilo kwara daya tal, wanda zata iya sadaukar da komi nata data mallaka ta hnyar iyayenta a kn danta tilo., iyayenta sunfi mijin datake aure kudi na fitar hankali ma kuwa. Ma'aikata keta aikin wannan raban na zallar dukiya ba tareda gajiyasaba. wasu in sukazo su kawo matsalolinsu na ciwuwwuka da de sauran jarabawar rayuwa, in aka isar da kukansu ga hajiya ummusalma, tace a basu kudade da dama dazeyi musu maganin damuwarsu, a kullum da kanta take tsayuwa a gaban idanta akeyin komi saboda gudun kada ayi zalinci,tafison sako ya isa ga mabukata direct. wasu daga yawancin mutane da dama, na zargin tana hakan ne saboda danta yaci shugaban kasa a nigeria, nan ko Allah kadai yasan zuciyarta, ita dazata rasa komi a batta da d'anta dase tafi farin cikin hkn a kan wannan yalwar arzikin da Allah ya mata....jiri taji yana neman kwasarta, dan haka ta koma ta zauna daga tsayuwar datake, nan take taji kanta yayi wani dum-dum kawai kamar an saukar mata da ruwan azabar ciwon kai, nan da nan kawai taji idanuwanta sun lumshe, cikin hanzari ta mike a daddafe kmr makauniya, hajiya Binta, wato wadda tafi kusanci da ita, jakadiyarta,, na ganin ta mike ta biyota a baya sauran masu taka mata baya sukayi kokarin biyosu hajiya binta ta dakatar dasu domin tini ta fahimci chanjin yanayin uwar gijiyarta. Karasowa hajiya binta tayi ta dafeta ganin tana niyar faduwa saboda ko gabanta bata gani, sosai. "Ki kaini part din baban jalalu..." Itace kalmar data fito daga bakin hajiya salma da kyar. "An gama ranki ya dade..." Cewar hajiya binta, ita ta kamota, suka nufo part din me martaba Sarki, tin kafin su karaso ya fito daga part din nasa cikin hanzari sanye da jallabiya. ya tarbeta domin yana daga window tin sadda take tsaye baking get tana kallon masu raba sadaka, yana kallanta har zuwa yanzu. Karasowa yayi ya amsheta daga rikon da hajiya binta ta mata wadda a kalla zata kai 60yrs. Dukawa tayi har kasa ta korowa me martaba gaisuwa, ina be samu damar ansawa ba, hankalinsa na kan iyalinsa farin cikinsa. "Salmanah ya akayi? Ko jikinne?'' Ya jefowa hajiya salma tambayar, saboda yau daman ta tashi batajin dadih, dama seda yace mata ma yau ta dakatar da bada sadakarnan ta bari se next friday amma taki. "Kaina ke ciwo..." Ta fadi idanuwanta na ciccikowa da kwallah, cikin hanzari ya nufa babban falonshi da ita, yanata mata sannu, ya tabbatar ciwonne ya matsa mata sosai, da bazata taba gaya masaba, tafi karfin 2weeks tana rashin lafiya a tsaitsaye ya tambayeta meke damunta tace masa bakomai, yayi-yayi a kira dr amma taki amincewa, to tabbas yanzu data bayyana ciwon yacita sosai ne. binta ta juya ta koma bakin get tana me jimamin halin da hajiya salma ke ciki, binta tasan komi, kuma kullum cikin adduarh suke a kan Allah ya karkato da ran Farin cikin uwar gijiyarsu gareta wato JALALUDDEN. A kan kujerar 3st suka yada zango, yayinda hajiya salma ta kwanta ta daura knta bisa cinyoyinsa, kwance take kn cinyoyinsa amma yana jiyo heart beat dinta, dan haka hnklinsa ya kuma tashi, ya dauki wayarsa ya lalubo lambar Dr, bugu daya dr rabi'u ya dauka zuciya fal mamakin yau Sarki ne da knsa ke kiransa, be taba kiransa da knsa ba, sede yasa na hannun damansa wazo Zakinsa wanda shine aminin sarki kuma me masa hidima Umar sunansa,. Yana daga kiran Me martaba yace "kazo gida ynzu,.." Yana fadar hkn ya katse wayar. Yadda yayi maganar ya kara tabbatarwa da rabi'u ba lafiya. Ba bata lokaci ya iso gidan, direct part din me martaba ya iso, ya nemi iso aka masa iso, ya shigo bakinsa dauke da sallahma yana me karewa aljannarh duniyar falon kallo, an narka dukiya ainun a falon. Karasowa dr rabi'u yayi cikin hanzari ganin hajiya salma kwance kan cinyar me martaba kallo daya ya mata ya fahimci itace ba lafiya. Ba bata lokaci dr ya dubata kasancewar akwai kebantancen asibiti da komi na bukatuwa a cikin gidan, dr yayi mata allurori nan da nan tasamu bacci. Dr ya juyo ya kalli Me martaba wanda ke zaune gadon da hajiya salma ke kwance, yayinda dr ke zaune bisa kujera. "Dr meke damunta?'' Itace Kalmar data fito daga bakin Me martaba zuwa ga dr, cikin tsananin tashin hankali me martaban yayi tambayar. Dr ya fara da kwantar masa da hankali, dukda be fahimci meke damuntaba saboda ba fanninsa bane amma ya tabbayarda akwai matsala. Me martaba yace "rabi'u, kanata kwantarmin da hnkali dan Allah ka gayamin meke damun matata.." Me martaba ya fadi cikin zallar damuwar tashin hankali, yayi mgnr tmkr ba babban mutum ba,. Dr rabi"u ya fara magana cikin muryar kwantarda hankali me dauke da tambarin girmamawa. "Insha Allahu ba wani babban abu bane, ranka ya dade, ku kwantarda hankalinku ynzu zan kira wani dr ya kara dubata,..." Hnkalin me martaba ya kara tashi yace "Kana nufin baka fahimci meke damuntaba..." Dr rabi'u yace "Ba fanni na bane, amma insha Allahu ba wata matsala bace bari in kira dr hassan yazo ya dubata inkun bada permission ranka ya dade.." Ya karashe mgnr cikin girmamawa. Ba bata lokaci me martaba ya bashi izinin kiran dr hassan. Dr rabi'u ya kira dr hassan, ba jimawa yazo ya dubata sosai, kasancewar sunada kayan aiki kwararru be wani bata lokaci ba gun gano meke damunta, zuciyartace ta kumbura,. Cikin dabara dr hassan da rabisu suka gayama me martaba, ba karamin tashin hankali me martaba ya shiga ba, dr rabi'u da dr hassan suka shiga kwantar masa da hankali, hadi dace masa ai warke insha Allahu inde aka daurata a kn magani da temakon Allah.... Haka akayi aka dorata a kn magunguna, yayinda Me martaba yake kwantar mata da hankali akoda yaushe, amma ina taki ta kwantar da hankalinta, seda aka hada da Addu'ur'i hadi da amsar mata rubutun ayoyin ubangiji kana jikin nata ya farayin sauki amma ta gaza komawa dai-dai, tunaninta da zancenta a halin ynzu duk na jalalu ne,...temakon ubangijine yayi tasiri a knta tasamu ta mike amma badan ta cire tunanin Jalalu ba, yana nan ga ranta, tasan har ta komawa mahaliccinta , jalalu shine kaf tattalinta da tunaninta a halin yanzu. USA..... Babbar asibiti ne, wanda su knsu turawan kasar keji dashi fiyeda kowanni asibiti a kasar, har zuwa kasashen dake makwabtaka dasu, duk sunaji da wannan asibitin. asibiti ne wanda sukeda kwararrun likitoci masu aiki kmr yankan wuka da temakon ubangiji,, wannan asibitin duk wanda kagani a cikinsa ba karamin miliyoyin kudade ya sauke ba, domin kuwa zuwan asibitinma bako wanni me kudi ba na kasar balle na kasashen nigeria, duk wani me karamin karfi yayi kuskura yazo asibitin nan kaf kudadensa zasu kare ba tare dayaga Koda dr ba. 10:pm Wata dattijuwa nagani kwance bisa gadon majinyata, hannunta makale da drib hancinta makale da na'u'rar zuko mumfashi wato oxygen, gabaki daya gadon da take kaima na'ura ce ke aiki a jikinta, tako ina a lullube take fuskarta ce kawai a bude, kanta sanyeda hula blue. Fans Gadon majinyatan dakin ma kawai abin kallo ne, ko ina so perfect, akwai komi na bukatuwa a dakin tamkar kana gida. Wata mace nagani zaune bisa kujerar dake facing gadon da matar ke kwance wadda a kalla zatakai 50yrs, black beauty ce, tanada kyau dukda ta manyanta, tanada matsakaicin tsayi a kallah bazatafi 56 ba lent dinta. Ita kuma wadda ke kwance gadon majinyatan a kalla zatakai 55yrs wato mara lafiyar tanada tsayin da a kallah lent dinta zekai 60, kaf tsawon nan nata ta mikeshi a kan gadan da take kwance, kai ka rantseda Allah matacciya ce. alamomin wahalar jinya dukya bayyana a tattare da jikin wadda ke kwance a kn gadon majinyatan, farace dattijuwar matar sosai tamkar a tabata jini ya bullo, gabaki daya zubin kalarta ba irin na yan nigeria bane. Matar dake zaune tana facing wadda ke kwance kan gadon asibitin, ta Tsureta da ido sosai fuska ba walwala, a kallah yau kusan watanninsu biyu kenan, anata mata aiki kusan karo na uku kenan, an mata juyan jini amma har rana me kamar ta yau bata farka ba, tana nan kwance tamkar matacciya, Kullum jiya iyau, abin de sede du'a'i. Ajiyar zuciya matar ta sauke, zuciyarta cike da tausayi da tausayawa wannan baiwar Allah. "Allah ya tashi kafadunki dan martabar Annabi SAW..." Cewar dattijuwar matar datayi adduarh fuska dauke da dumbin damuwa. Wayarta dake kan jikinta ce tayi vibrating, dubata tayi, taga Sunan Director ya bayyana wato me bada umarni, hanzari tayi gun daga wayar, hadi da mikewa ta nufa can cikin wani daki, saboda ba asan ayi hayaniya a kusa da ita kwata-kwata. Tana shiga ta daga wayar ta kara a kunne hadi da rage volume din wayar kasa sosai, ta yadda ita kadai ce zata iya jin me yake cewa. "Barka da dare ranka ya dade..." Cewar dattijuyar se tayi shiru batare danaji mena cikin wayar kecewa ba, zuwa can dattijuwar matar ta karbeda "eh toh dasauki de saukin musulunci,,,doctor's de sunce zasu shiga wani aikin a kanta, shine last and last in bata mike ba toh sede fa ayi hkri... ta karashe maganar murya cike da sarewa hadi da fargaba,, tayi shiru tana sauraren na cikin wayar kana daga bisani ta amshe da "Amin ya rabbil izzati..." Tayi shiru again tana sauraren na cikin wayar kana tace "Alhamdulillahi bama bukatar komi kayi hidima iyakar hidima ranka ya dade, Allah yasa Aljannarh tazamar maka makoma kuma, Allah ya tabbatar da Alkhairi a kan wannan babban sako dake kwance yana dabo, Allah yasa muji kyakyawan result..." Daga cikin wayar akayi magana ba tare danaji ba, matar tace "Toh shikenan ranka ya dade bari in kirata yanzu ma kuwa..." Ta katse wayar,, kana ta shiga calls dinta nan da nan ta nemo number me Alamar K, wato da dukkanin alamu suna yawan waya dame wannan number din, dealing number din tayi bugu daya zuwa biyu aka daga, ta kara Volume din kiran a wannan karan. "Allah ya temakeki jarida..." Daga cikin wayar wannan kalaman suka fito. Wadda aka kira da jariya wato dattijuwar matar nan ta amshe da "tare da ke Hajiya kande...to ya maganar wasika?'' Hajiya kande tayi murmushi tace "ina me tabbatar miki