← Book details Wata Kishiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 107

Sashe 69

Wata Kishiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

kuma duk a kan yarinyar, kalaman dayake gaya masa a kan san yarinyar dayakeyi ba karamin dimautasa sukeyi ba , be tabajin irin makamancin kalaman na so ba a bakin wani tinda uwarsa ta haifesa ko a labari be taba ji da gani ba se a kan jalalu, zuciyar Dr ta narke sosai. "Wallahi Ina cikin azabar so ,,, dr a kanta ne kawai nake gane fari da baki, amma da ina rayuwa ne, tamkar gunki, bansan ciwon kainaba seda na fara santa..." Abdoljalal ya kuma fadi still yana ci gaba da hawaye zuciyarsa na harbawa da karfi tamkar zata fashe. Dr mus'ab ya gyara zamansa sosai a kan kujerar da yake kai , ya fukanci in abu ya wuce haka Abdoljalal na iya haukacewa ma gabaki daya. Cikin sanyin murya dr yace "Dan AllAll ka dinga sassautawa kanka, in har SO yazama CUTA, Tabbas yanada magani, domin Allah be sauke cutaba seda ya sauke maganinsa, naganin CUTAR SO shine hakur..." Tin kafin ya karasa Abdoljalal ya girgiza masa kai hadi dacewa "nawa SON wallahi ba HAKURI bane maganinsa, nifa sam nawa CUTAR SON beda magani....'' Ya karashe yana share hawayen dake kan fuskarsa. "To na gaya maka zan sake gaya maka a karo na biyu, kayi Adduarh,,," Abdoljalal yace "Shine kawai..." "Insha Allahu yarinyarnan kaddararta seta zamar maka Abin alfahari.." Cewar dr mus'ab. Abdoljalal yaji dadin wannan maganar na dr, tinda suke tare be taba gaya masa kalmar data faranta masaba kmr wannan ta yau, murmushi yayi nan da nan kwallan da yakeyi ya dauke karkaf yace "Insha Allahu kuwa...ngde frnd ..." Dr murmushi yayi , shi kadai yasan meke zuciyarsa, yanada tabbacin bayan iyayen Abdoljalal seshi ze zamo na biyu a san ganin Abdoljalal a farin ciki, ya matsu ya fita a wannan rayuwar ya koma rayuwa irin tako wanni d'ana miji isashen wanda ya isa da mace....seda dr yakai 12:am a gidan suna hira kana ya mike, Abdoljalal ya rakosa har bakin mota, bayan sun iso bakin motar dr ya zaro kudade yan dubu dubu rafa uku ya mikawa Abdoljalal yabi kudin da kallo fuska dauke da mamakin ganin dr na basa kudi,.."dubu dari uku na menene?'' Saraki ya tambayesa fuska daukeda rashin fahimta. Dr yace "ka amsa tukunna se in fada maka ko na menene..." Saraki ya mika hannu ya amshi kudaden, hadi dacewa "Inajinka..." Dr yace "Na abinda kakeso ne a fadin duniyarnan...". "Al-muqri'ah..." Abdoljalal ya fadi direct yana murmushi, saboda duk dumiya ita yakeso a halin ynzu. Dr yace "A, nata ne, ka bata kuma ka hada mata da gaisuwa, domin tini ta jima dazama sarauniya a fadarka..." Abdoljalal yaji dadin kudaden da Dr ya bawa Al-muqri'ah , uwa uba kuma kalamansa sun masa dadih, yasa kudin a aljihun jallabiyar jikinsa, yana mejin wani irin sanyin dadih na ratsashi gami da kudaden besan meyasaba. "Ah wannan babbar kyauta, har haka muna godiya Allah ya kara arziki.. " Abdoljalal ya kwaroro masa godiya yayinda bakinsa yaki rufuwa, shifa yanzu inhar kanasan Al-muqri'ah to ka gama masa komi a duniya. Dr yace "Bakomai yima kaine..ai ka cancanci abinda yafi haka jalalu, kaidin mutum ne ba butulu ba, ina fatan Allah ya hadamu a aljannarh kmr yadda ya hadani dakai tin muna yara..." Abdoljalal ya amsa da "Amin Ya Ilahil Alameen.. '' sukayi sallahma ya shiga motarsa dreva yaja suka fice a gidan, Abdoljalal ya juya, ya nufa Dakinta se faman murmushi yakeyi haka kawai ya tsinci knsa dasan bata kudaden yanzu-yanzu. Yana zuwa dakinta yajishi a kulle ruf, yasan daman da wuya yasameshi a bude, zagayawa yayi ta window din dakin, ya hangeta zaune tana bisa dadduma hannunta rikeda alqur'ani me girma, se karatu takeyi tana motsa baki ba tareda fitar sound ba. Wani irin sanyi yaji yana kara ratsashi a kan yarinyar, gata yarinya karama amma akwai addini sam bata wasa da ibadarta, kwata-kwata bata shagala da duniyaba, hakan ke kara sa masa Tsananin kaunarta a birni da kauyen zuciyarsa. Har wuraren 1:am yana nan yana kallanta zuwa lokacin ta mike ta fara nafilfili kwata-kwata batasanma yana kallantaba. "Alhamdulillahi..." Kawai ya tsinci knsa dayin hamdala ba tare dayasan dalilin hakan ba , shide kawai yanaji a jikinsa zuwan yarinyar rayuwarsa Alkhairi ne, yanasa ran kada Alkhairin ya yanke na har abadan. Komawa side dinsa yayi shima ya dauro alwala ya fara nafilfili , dukkkanin sujjadarsa adduarh ce yake isarwa a gareta zuwa ga ubangiji mamallakin zukatan kaf mutane da Aljanu. Washe gari 9:am ta shigo aje masa breakfast dinsa, ta taddashi zaune kan kujerar dinning da counter me kamar azirfa a hannunsa yanata lazimi, gaidasa tayi sama sama ya amsa se murmushi yakeyi shi kadai, tinda ya fahimci kishi ne ke dawainiya da ita ya mata uzuri danyasan dole fa yayi kishi. Ta juya zata fita, Abdoljalal ya dakatar da ita, ta juyo ya mika mata kudin da Dr ya bata jiya yace ya bata, tana daura idanuwanta a kan kudaden kawai taji zuciyarta ta yanke ta fadi, ta dago ta kalleshi tana ne neman karin bayani a kan kudin na menene. Abdoljalal ya fahimci hkn dan haka yace "Abokina ne wanda muka taso tin muna kanana, dr mus'ab ya bani yace in baki..." Tace "Aah nagode..." Da bebanci. "Ba kyau maida hannun kyauta baya..." Cewar Abdoljalal. Bata saurareshiba Ta juya taci gaba da tafiya harta isa kofar fita ta juyo taga ya tsurawa bynta ido dagani saitin hips dinta yake kallo,se hadiyar tsinkakken yawo yakeyi. kudin hannunsa tabi da kallo, kawai seta tsinci kanta dasan dawowa ta amshi kudin, tace "Nagode..." Da bebanci, ta juya ta fice zuwa dakinta, ta zauna gefen bed dinta ta tsurawa kudaden ido kusan na 20mnt haka kawai takeji a zuciyarta kudadennan masu muhimmanci ne gareta, Abdoljalal yasha bata kudade masu yawa amma taki amsa, haka kawai yau taji bazata iya kin amsar wadannan kudaden ba, bude bedside drawer tayi zata saka kudaden wata takadda ta fado, zuciyarta kawai seta tafi ga tunanin Abdoljalal, tana bala'in kewarsa kawai dannewa takeyi ko ranar da abubuwannan suka faru tsakaninsu a mota data dawo dakin tashiga toilet , taga wani abu me yauki dukya jika mata pant, tinda ta fara wankesa seda tayi 15mnt tana wankesa amma yaki fita da kyar tasamu ya fita, ita de tasan tana jin kewarsa a duk jikinta, kuma tanaso ya tabata amma batasan wani jin dadih na, tasan de tana shiga yanayi inya tabata, amma ita kuma tanasan yanayin da take shiga din. Hannu takai ta dauki takaddar data fado a cikin kudaden a zatonta ko takaddar kudince domin hankalinta na kn tunanin jalaludden kawai ta jawo drower din kasa tasaka takaddar a ciki ta maidata ta rufe, kana ta maida ta sama da kudin ke ciki ta rufe. Sati daya ya shude hajiya saude tini suka lula jirhin sama itada kawarta hajiya Abulle zuwa kasahen wajen nigeria amma fa kafin tayi tafiyar seda sukaje sakkwato gun bokansu ya basu sa'ar tafiyar dasukayi, sannan Hajiya saude ta narka ma boka kudade kan ya kula mata da mijinta kada a barshi ya kalli kowa, ta barwa boka amanar Abdoljalal baki daya,. Gogan besanma tayi tafiya ba, saboda bata sanar dashi ba tinde ranar datace ya tura mata kudadennan yasan tace zatayi tafiya amma sam batazo sunyi sallama ba, ya saba da hakan, bebi ma ta kantaba, shi Batama gabansa a halin yanzu be damuwa da lamarinta, tunaninsa da lissafinsa na kan Al-muqri'ah. A bangaren al-muqri'ah kullum seta bude drawer dinnan ta kalli kudadennan da dr yabawa Abdoljalal ya kawo mata. safe rana dare kawai tasamu aikinyi kallan kudadennan kawai, batada abinda zatayi dasu, itade kawai kallansu takeyi, kuma tanajin dadin kallon da takewa kudaden. a kullum tunanin kakarta da mafarke mafarke masu kyau da marasa kyau yawaita sukeyi a gareta, fatanta da Addu'ur'inta Allah yasa zuwa yanzu tasamu lafiya, kawai tana kwantarda hankalinta ne saboda yazama dole, in har ta daga hankalinta tasan lafiyar kakar tatama bazata samu ba, shiyasa take hadiyar damuwa, sam bame iya fahimtar damuwarta, se mahaliccinta. Har yanzu haushinsa takeji, data ganshi seta tuna kisses din da matarsa ta masa ba karamin bakin mugun dashen furen shukar bakin ciki bane Kisses din data masa a kumatu ya barwa Al-muqri'ah ba. Abdoljalal ya bata hakuri yayi-yayi amma taki hakura, ya riga ya sadakar zesha wahala, saboda ya fahimci bata da saukin lallashi tin sadda ya taba duwawuka for the first time ya fahimci hakan, gabaki daya ta damula masa lissafi ayyukansa ma ya kasa yinsu a natse, kawai de yana yin wasu ne saboda sun zamar masa dole beda yadda zeyi, dan haka yake zuwa office ya danyi ayyukansa befin awa uku ya dawo gida, so yakeyi su dawo kmr da ta dinga rakashi office amma ina ba fuska, ashema wargi guri yake samu, wato ya fahinci face yake gani har yake taba mata jiki gashi yanzu de kiri kiri yana ganinta amma yadda take shan murr ma baze barshi ko kallanta ya faye yiba balle a kaiga maganar taba jiki.. So yakeyi yaje abuja saboda tafiyar tazo masa a dole a yau, tin tini ya dace ya tafi amma saboda ita be tafi ba, yasan in har beyi tafiyar da ita ba abinda akeso ya aiwatarma ko yaje baze iya ba, yau ya tashi ya shirya tsaf da shirin barin garin zuwa abuja ya riga yase musu jirgin sama zuwa abuja na 11:am se adduarh yakeyi Allah ya dorashi a kanta. 8:30am yau ta kawo masa breakfast ta taddashi zaune kan dinning chair yasha danyar shadda coffee brown me haske ta amsheshi ainun kannan nasa sanye da hular king die, ta matujar amsheshi, a kallo daya biyu uku ta fahimci yayi tsananin kyau. Ta gaidasa ya amsa kana ta ajiye masa masa trea din breakfast dinsa a kan dinning table ya kalli kyakyawar fuskarta sanye takeda hijjabi zumbulele har yana sharar kasa dark blue ya amsheta ainun. Ta juya ta bar dinning room din ya bita da ido hadi da murmushi saboda ya tunano abinda zece mata tabishi salin alin cikin kwanciyar hankali. Dan tsakurar abincin breakfast din data ajiye masa yayi, tinda ta fara fushinnan dashi dan dole kawai yakejin abinci dan kada ya mutu beci gindi ba . 10:27am ta dawo a tunaninta koya gama ma harya fita, tana shigowa ta
Chapter 69 · 0% Book details