← Book details Wata Kishiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 107

Sashe 49

Wata Kishiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya dade...amma har fadawa ta danyi , ai danma yarinyar nada dauriya wallahi, ciwon kwana daya dukta zabge, inajin zazzabin cizon sauro ne, dan wannan dakin nata baze rasa sauraye ba..."cewar larai fadi ba a tambayeka ba. Ai nan hankalin Abdoljalal ya kuma tashi, kawai dannewa yayi yace "Allah ya kara sauki..." Abdoljalal ya fadi murya cikin tashin hankali. Larai ta kwashe kayan ta fice. Ya furzar da wata iska ta tashin hankali, daga bakinsa, kana ya mike ya fice, fitowa harabar gidan yayi, yana kallon larai ta gama gyara kiching din ta mayar ta kulle kiching din Ta nufa nasu bangaren. Abdoljalal bega yarinyar ba se hankalinsa ya kuma tashi, haka kawai yaji a jikinsa ciwon nata ba kadan bane. Seda ya tabbatar da larai ta kai side dinsu na masu aiki. kana ya nufa dakin nata, zuciyarsa nata tsananta bugu kmr zata fashe, ya isa kofar dakin ya taba handle yajishi a kulle jikinsa har yana rawa, ya shiga aikin knocking din dakin, al-muqri'ah dake kwance zazzabi ya Kuma lullubeta se rawar sanyi kawai takeyi, ta lulluba da bargo,, taji ana knocking, Mikewa tayi da kyar tasha ko larai ce ke buga dakin, ta karaso ta bude dakin ta koma ta zauna gefen bed din tana ganin jiri, tasan sanadin ganin jirin nata dan bata cin abinci ne, saboda kwata-kwata batajin dadin komi a duniya tasan saboda rashin ganinsa ne duk yasata a rashin jin dadin duniyarta ma baki daya,,, ga ciwo ga damuwarsa da batasanma tanayi ba.. Turo kofar dakin yayi ya shigo jikinsa har yana rawa ya kagara yasata a idanuwansa, ko ze samu kwanciyar hankali,. Kamshin turarensa ya doki hancinta yayinda tayi saurin dago idanuwansa ta zuba masa su, ji taji zuciyarta tayi mummunar harbawa, taga shi ma itan ya zubowa ido, daga jiya zuwa yau har ta rame, amma fa yafita rama,. Ganinta yasashi nan da nan yaji tausanta ya kuma lullubesa,, a bangaren al-muqri'ah kuwa ganinsa seya tunasar da ita abinda ya faru tsakaninsu na duwawuknta da yayita matsa mata su, gashinan har yanzu ciwo ma suke ta mata, saurin kauda fuskarta tayi gefe, tanajin kmr yanzu abinda ya faru tsakaninsu ya faru. "Yarinyata..." Abdoljalal ya fadi ba kunya ba tsoron Allahn duwawuknta daya gama mammatsawa amma wai yanzu yake cewa wani yarinyata. Ta dago ta sake kallonsa , seta dauke idanuwanta, Abdoljalal ya bita da kallon kewarta da yayi, yayin da the more yake kallonta the more zuciyarsa ke tsananta bugu a knta. Karasowa yayi hadi da sosa keya danya fuskamci har yanzu fushi takeyi dashi. Ya zauna kusa da ita gefen bed din yana zama tayi zumbur ta mike, ta koma can bedside ta zauna, se kumbura fuska takeyi.. Abdoljalal de ya bita da ido. "Ya jikinki yarinyata..." Ya tambaya fuska cike da damuwa. Tajisa amma ta masa banza, ya kureta da ido kmr maye duk tabi ta zurma kmr tayi 100days tana ciwo., dawo da idanuwa sa yayi yabi dakin da kallo, har zuwa kan bed dinta, idanuwansa suka sauka a kan wayarta da hajiya saude ta bata sanda aka kawota.. Hannunsa har yana rawa ya kai ya dauki wayar, direct contact ya shiga yaga number guda biyu ne kawai, da number dinsa dana hajiya saude, ya shiga miss call yaga ba a taba kiran wayar bama, ya sauke ajiyar zuciya da har kishi ya motsa masa, yasha ko waya take tayi da maza, se Allah ya rufa mata asiri. Cewarsa. Dealing number dinsa daya gani a wayar yayi yaji akwai card, kiran na shiga ya kashe wayar yayi message ta yadda ze gane lambarta ce, kana ya ajiye wayar inda ya dauketa duk tana kallonsa, yana ajiye wayar ya dago ya zubo mata ido, tayi hanzarin dauke idonta a knsa, ya karasa ya taba jikinta, yaji wani irin zafi rau, jin ya taba mata jiki tayi hanzarin mikewa ta nufa toilet ta kulle yabi duwawuknta da kallo, mikewa yayi ya nufo toilet din danya fahimci ma kamar duk ta tsaneshi ne ne ynzu. Tsayawa yayi a kofar toilet din yayi juyin duniya ta fito suje asibiti amma taki fitowa, har wuraren 2:am yana nan yana dakin amma taki fitowa dole ya fice ya bar mata dakin, tanajin ya fice ta fito ta kulle dakin ta koma ta kwanta tanajin kanta na mata azabar ciwo, dukda tanajin haushinsa amma ganinsa ya haifar mata dajin sanyi a ranta.... Haka ya jera 1week yana ziryar dakin, wani lokaci ya sameshi a bude wani lokaci a kulle, tinda ta gane ma, yana zuwa take rufe dakinta, inyazo yayita juyin duniya ta bude amma taki budewa har yanzu fushi takeyi dashi ga zazzabi tana fama dashi, duk tabi tasashi a usumar rayuwa, sati daya be gantaba ji yakeyi kmr ze haukace, kansa ya dauki zafi yana tafiya yana layi, kmr mahaukaci haka yake jinsa a kwanakinnan, ko abincima ya dena ci. Ya shiga damuwa harya gaji da damuwa... Ko abincinma ta dena fitowa dafa masa, yasan duk sanadin matsa duwawune da yayi, gashi ansashi ababbar bala'i kwata-kwata ko bacci beyi, kwana yakeyi yana kwallar tashin hankali, be taba tabbatar da meye matsifar duniya ba se akan yarinyar nan, sam shi besanma tashin hankali ba se a knta. 10;pm yazo ya tsaya a bakin kofar dakin nata, yaci saarh yana taba handle din dakin nan take dakin ya bude, seda ya sauke ajiyar zuciya ya sako kai cikin daki da sauri kmr an jefosa, idanuwansa suka sauka a kan larai dake zaune gefen bed din ita kuma al-muqri'ah tana kwance ta lullube rub, har kanta da bargo, ganinsa a dakin yasa larai a mamaki, ta tsugunna ta gaidasa ya amsa, amma hankalinsa na kan al-muqri'ah, karasowa yayi, ya yaye mata bargon data lullube dashi, wani irin zafi da tiririn dake jikinta ya dokeshi,. "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!'' Ya hau salallami cikin tsananin tashin hankalin dabe taba shiga kwatan kwacinsa ba se yau,, ya zuba ma kyakyawar fuskarta ido, duk tabi ta karayin haske amma ta rame sosai, idanuwanta a kulle suke amma taji shigowarsa har zuwansa kanta duk tanaji bata bude idontaba. Jikinsa har yana rawa ya fice a dakin ya nufa side dinsa cikin gudu gudu, ya dakko car key dinsa, ya isa packing space da knsa ya dakko mota zuwa kofar dakin yarinyar, duk ma'aikatan gidan sun shiga mamakin ganin saraki da kansa yau yake driving, abinda wasu basu taba gani ba se yau, shi sam baya tukin mota sede a tukashi. Yana ajiye motar a saitin kofar dakin ya fito cikin tashin hankali, Da knshi ya tasheta zaune ya bata takalmi tasa, ba tare data masa musu ba, larai dake tsaye tana kallon munafunci da kwa-kwaf ganin gogan na niyar ya kamota yasata Saurin kamota cikin hanzari dantaji yana cewa asibiti zasuje. Laraice ta kamo masa ita har cikin motar, ta shigar da ita mazaunin gaba, duk jikinta yayi lagwa lagwa zazzabi ya karar mata da karfin jikinta. Abdoljalal ya shiga yaja motar suka fice a gidan. Nan larai ta tsaya bakin kofar dakin, tana mamakin wai Saraki ne yau da daukar me aiki a motarsa. "Tabbas da wata a kasa..." Larai ta fadi a bayyane hadi da rike haba, tin a fuskar gogan ta fuskanci abubuwa dayawa a kan yarinyar ammafa sede maganar nan bazata fito fili ba, wane mutum wane aikinsa. Se hakuri da typing error ba editing. Vip 1k normal 500 0542703718 Saada tu Abdullahi gt bank shedar biya ta nan 08101626484 ko M.T.N card. SAADATU BINTU ABDULLAHI (writer of Kyautar Allah) Page15 Tirkashi! Nan fa Ma'aikatan gidan suka rikece da gulma ammafa gulma ta zuciya domin wannan magana bazata faso fili ba, kowa sede yasawa bakinsa linzami, laf ma'aikatan gidan na cike da alhini amma ga iya wada'da suka gani, ko labari kowa ya kasa bawa dan uwansa saboda kada kace kai nace, ammafa alhini be barsu ba, dan a tsawon shekarun aikinsu a gidan basu taba ganin saraki ya dauki me aiki ba a motarsa, sun kula asibiti ze kaita, domin tin bata da lafiya larai tazo ta shafa musu labarin bata da lafiyar, amma fa yanzu bataso tace dasu komi ba, sede tayi wucewarta ta koma bakin aikinta a zuciya kadai taketa juya lamarin amma harshenta baze iya tattauna maganar da kowa ba,. "Wace ni bakina kanin kafata..." Larai ta fadi a zuciyarta tana meci gaba da aikin gabanta. Yana driving yana kallonta cike da tausayawa, yayinda hankalinsa kwata-kwata Be jikinsa, zuciyarsa na kanta, se rawar sanyi takeyi har zuwa lokacin. Karatun alqur'ani yasa a cikin motar, saboda duk zafin ciwo inde za asa karatun alqur'ani me girma a kusa dame ciwon insha Allahi ze samu sassaucin ubangiji. Da temakon Allah kawai ya isa wani dankareren private hospital wanda yafi kusa dashi, ko kusa be tinkari zuwa asibitin dr mus'ab ba saboda yaanada nisa.. Packing kawai yayi ya fito ,ya bude mazaunin datake, yana niyar daukanta cik ta sakko da knta, cikin dakiya ya kamo mata hannu, ta kwace hannunta, asibitinma dabadan ciwo ya addabetaba da bazata zoba wallahi kawai bata da choice ne. Kaf mutane suka zubowa Al-muqri'ah ido dukda tana cikin ciwo amma se kallonta akeyi saboda tsananin kyaunta Abdoljalal se hade girar sama data kasa yakeyi, bakin ciki ya cikasa,. A jere suke tafiya shida ita Abdoljalal se kallonta yakeyi, yanata wani kakkareta, dukda darene amma asibitin nada yalwar haske kai kace rana ce, hakan ne ya bawa masu kallonta damar kallonta. "Sannu Allah baki lafiya..." Ya fadi kmr zeyi kuka yayin da yakeji kamar ya ciro ciwon yasa a jikinsa, jinyarta tafi masa zafi a zuciya a kan tasa jinyar, da ana cirewa daya ciro ya hada da nasa ciwon.. Ba bata lokaci sukaga dr a asibitin, Abdoljalal yace dr mace suke bukatar gani, dole kuwa dr macen al-muqri'ah tagani, ba wani lalata lokaci aka mata gwaje-gwaje nan ana gano maleria ce, da ulcer. Nan take aka basu gado, aka shiga bata temakon gaggawa, aka mata allurori ba jimawa bacci yayi awon gaba da ita akasa mata drib. Abdoljalal dake zaune kn kujera yana facing dinta, tausanta dukya rufesa, ansha gwagwarmaya da ita kafin ta tsaya aka mata allura besan matsoraciya bace se yau, da kyar ya riketa ta yadda aka mata allurorin, ance fararen mata basu da kwari, ita de kyakyau take
Chapter 49 · 0% Book details