← Book details Wata Kishiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 107

Sashe 104

Wata Kishiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dr yace "Wlhi bana kasar ne, Dana bar kasar duk se nasa wayoyina a yadda ni zan iya kiranka kawai...kuma na kira Abdoljalal lokuta da dama a kashe ka gayamin meke faruwa, jikina na bani akwai babbar matsala, ka gayamin meke faruwa dan Allah?..." Nan ahamad ya kwashe labarin komi dake gudana ya gayawa dr mus'ab kama daga kama Abdoljalal A kan Almuqri'ah da saude tayi har zuwa gudun Almuqri'ah a gidan, har de zuwa yanzu da halin da Abdoljalal yake ciki. Ahamad yaji kansa ya tsananin sara masa jin Ahamad yace masa wai Almuqri'ah ta gudu , seda dr ya koma ya jingina bayansa da bayan motarsa nan take yaji jiri na neman kwasarsa "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!'' Itace kalmar data fito daga bakin dr, nan take idanuwamsa suka shiga kokarin daukewa daga gani na wasu yan dakiku. "Ina ta shiga?'' Cewar Dr da yayi mgnr fuska da murya dauke da zallar tashin hankali. "Bamu sani ba, an kai cigiya kaf gidajen TV da gidajen redio duk bamu samu tadawo ba, duk inda nake inada tabbacin yanzu ta haihu gaskiya,,, wlhi Oga na cikin tsananin dmwa muje kaga halin da yaje ciki..." Cewar Ahamad. Ba bata lokaci dr yabi ahamad a baya zuwa dakin Almuqri'ah inda nan Abdoljalal ya koma rayuwa tinda ta bar gidan be leka ko kofar dakinsa ba, yazama kmr mahaukaci. dr nashigowa dakin idanuwansa suka sauka a kan Abdoljalal dake kwance kasan tiles din dakin duk yabi yayi karo-karo dashi se kasusuwa kawai a jikinsa, yayi bala'in baki, tako ina jikinsa gashine buzu buzu. Tsabar tsananin tausansa ya rufe dr nan da nan se hawaye ya fara zirya a kan kuncinsa, "mutum ba komi bane..." Dr ya fadi a bayyabe ganin yadda jalalu dan gayu kyakyawa ya koma bashi da maraba da kwarangwal. Abdoljalal na ganin dr ya taso a hnkli yana me binsa da ido kmr mahaukaci yace "Kaganta? Kaga yarinyar nan? Ta gudunmin da ciki wlhi... Kace tadawomin da cikina.." Dr ya karajin tausansa ya rufesa, seda ya mike tsaye ya kula da kayan Almuqri'ah dinne a jikinsa, tinda ta bar gidan kayanta yake sawa kullum sune suturarsa, duk yabi ya gigice ya koma mahaukacin karfi da yaji. "Why Abdoljalal....innalillahi wa'inna ilaihi!'' Cewar dr daya kara fashewa da kuka ya rungume Abdoljalal yana fadin "Kaine haka jalalu? Kaine anya jalaluna ne kuwa..innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!!' Dr ya dinga kuka tamkar ransa ze fita, tabbas ya tabbatar da mahaukacin so Abdoljalal keyima Almuqri'ah, gabaki daya dr ya rikice ya gigice, shima yashiga tashin hankali,,, yana rungume da Abdoljalal harna tsawon 10mnt yana kuka Abdoljalal dinma na kuka ahamad dake gefe shima yana kuka tamkar ransa ze fice daga jikinsa. Kana ya dago Abdoljalal daga jikinsa suka karasa bakin bed suka zauna, ahamad ya danne tashin hankalinsa ya shigama Abdoljalal natsiha kan ya dannewa ransa ya dauki kaddara, ya karashe da tausar masa zuciya kan za'aga Almuqri'ah din, Abdoljalal yajishi ne kawai amma ina be dauki natsiharsa ba ko kadan. Da kyar dr ya iya barin gidan karfe sha biyu na dare byn ya lallaba Abdoljalal yaci abinci da kyar. Da dr ya koma gidansa rnr sam beyi bacci ba, kwana yayi tsaye cikin tashin hankalin , Allah-Allah yadingayi gari ya waye. Yanayin asubahi ya hau motarsa ya nufa gidan malam nata'alah . tashin hankali, yana isa gidan yaga babu gidan babu dalilinsa kmr an shafe gidan se fili kawai ba gida. hnkalin dr ya kuma ninkuwa gun tashi, nan take ya tuna da wata kalma da malam ya taba gaya masa dajimawa, yace masa " akwai lokacin dazeso komi ze rincabe, to a lokacin ne ni bazaka ganni ba har abadan..." A lokacin dr besha da gaske bane yasha kawai ya fadi ne, ko yace be fahimci mgnrsa ba se yanzu ya fahimci kanun zancan nasa. Tashin hnklin dr ya ninku ji yakeyi kmr zeyi hauka, ya dinga zagaye turun wada ko zega malam amma ina begansa ba sbda shidin ba mutum bane aljani ne, daman danya temaki Almuqri'ah ya bayyana, yanzu kuma temako ya kare tinda ta dangana da inda ya dace ta dangana. Se dare dr ya dawo gida cikin tashin hnkli yayi tagumi kawai ya rasa ina zesa rayuwarsa yaji ddh, yakira Isma'il ya sanar dashi abinda ke faruwa. Hankalin isma'il dake kasa me tsarki ya tashi ainun, kusan 2month yayi a kasa me tsarki yanata ibada da Addu'ur'i kan Allah ya warwarewa me martaba da iyalinsa damuwarsa, Allah yasa Abdoljalal dansu ya dawo garesu. Dr na gaya masa wannan kaddarar data kuma kunno musu kai ya shiga dakin kabah yaci gaba da Addu'ur'i ga ubangijin da baya bacci, a kaf addu'ur'insa seyace Allah ya tarwatsa saude. Me martaba mutum be garesa, yana jibantarsa fin tunanin me tunani, in yace masa yana cikin damuwa to tabbas seya hau yafishi shiga damuwa me tsanani,, yana tausayawa ga kowa dake kasanshi, shiyasa waziri ke tsananin tausayawa garesa, rayuwa nan da waziri keyi da kodar me martaba daya yake rayuwa,, yayi ciwo me tsanani har kodarsa ta lalace aka cireta me martaba ya bashi tasa.. Ba duk d'a ze iya wannan shahadarba musammanma a matsayinsa na shugaba me mulki kuma shahararren me kudi. Dr ya kira mami ya sanar da ita halin da ake ciki , itama tashiga tsananin tashin hankali. IIsma'ildr mus'ab mami duk suka shiga tashin hankali mara misaltuwa,tako ina aka saka cigiyar neman Almuqri'ah sannan duka dukufa adduarh, duk abubuwannan dake wakana Ammah bata sani ba, sam ba a bari taji komi ba, sbda gudun tashin hankalinta. Dmwar da dr ya shiga tafi ta kowa ji yakeyi kmr zeyi hauka, zuwa yanzu ko miyaun bakinsa da kyar yake iya hadewa. Yau tinda Ya tashi yaketa bincike a dakin tako ina, besan dalilin bincikenba, yana binciken yaga kudinnan da dr ya bashi yabawa Almuqri'ah a drower ya dauko kudin ya rungume a kirjinsa yana hawaye hadi da tunano reaction dinta data amshi kudin. "Meyasa zaki tafi ki barni a matsifa irin wannan...ya rabbih menayi kayimin wannan jarabawar... Ina sanki wlhi, ya Allah kasa ba hakkin iyayena bane yake bibiyata..." Ya karashe yana me kara fashewa da kuka kmr ransa ze fita harda shasheka, a kwanakinnan ya fara tunanin anya ba hakkin iyayensa bane ke bibiyarsa yasa yashiga wannan mummunan halin, yanzu fa beda maraba da mahaukaci, dan duk wanda ze kallesa zesha ko mahaukaci ne. Hannu ya kai ya jawo drower din kasa , se kuma yaga wata takka fara a ciki harda baze dauki takaddarba se kuma yasa hannu ya dauka hannun nasa na rawa, ya bude takaddar yaga rubutu da blue din viro.. "Rubutun dr..." Ya fadi a bayyane ba tare daya karanta note din dake cikin takaddar ba. Yabi rubutun da ido ko a mafarki aka nuna masa hand writing din dr zesan cewa hand writing dinsa ne. Jikinsa na kakkarwa ya fara karanto note din kamar haka. "Ina fatan kina lafiya Almuqri'ah, wannan kudin naki ne nasan zakisan kona menene dakinga kudin,, ina fatan zaki tsaya ki nutsu kiyi aikin daya kawoki gidan Abdoljalal cikin Aminci...kakarki tana nan cikin aminci itama, Allah ya bada sa'arh ya dauramu a kan saarh Amin ya Allah..." Abdoljalal yaci gaba dabin rubutun da kallo yayinda zuciyarsa je tsuma, ya kasa fahimtar me rubutun ke nufi, tabbas de yasan rubutun dr ne, ,abu daya ya fahinta wato aikin da Almuqri'ah tazoyi gidan kenan dasa hannun dr.."to meyasa zeyimin haka?'' Cewar abdoljalal, nan take zuciyarsa ta chanza lamarirrika, ya mike a zabure yana fadin. "Munafukinka na gindinka..." Ya fice a dakin kafafuwanta ko takalmi babu, sanye yake da jallabiyar maroon ta Almuqri'ah Abdoljalal dinne yase mata.. Ahamad dake zaune bakin get yaga Abdoljalal ya tunkarosa gadan gadan seya shiga mamakn lafiya, ya mike tsaye zumbur, ya zubowa Abdoljalal ido, yau kusan 2weeks kenan ko masallaci Abdoljalal din be fito yaje ba, a daki yakeyin sallah. "Akwai matsala..." Ahamad ya fadi yayinda zuciyarsa ke dukan uku uku. "Dakko mota da hanzari kajani zuwa office din dr mus'ab..." Cewar Abdoljalal da takaddar ke hannunsa yanata kara karantawa. Ba tare da ahamad ya masa musu ba, sbda yadda yy mgnr ya tabbatarwa da ahamad wani bala'in ya kunno kai.ya nufa packing space kusan a tarema suka karaso packing space din abdoljalal yashiga gaban motar, ahamad yaja motar suka fice a gidan yana kallan rigar dake jikin Abdoljalal be dace ya fita da ita ba amma beda yadda zeyi, be isa yace masa ya koma ya cire ba. Paid book ne 08101626484 "Kai kayi maza maza kayi sauri da motar nan fa..." Cewar Abdoljalal, dayake ganin kmr ahamad baya sauri, shi kuma dukya kagu ya ganshi gashi ga dr mus'ab, kwata kwata beyi tsammanin abinda dr ya aikata garesa ze aikata din ba, ashe maciyinn amana yake tare dashi be sani ba.sune kalaman da Abdoljalal keta juyawa a cikin kansa yayinda yakejin zuciyarsa kmr zata fashe. Ahamad ya kara gudun motar sbda mgnr da Abdoljalal yayi. Tafiyar 15mnt ta kaisu office din dr, ko packing ahamad be gama yi ba Abdoljalal ya fito daga motar cikin sassarfa ya nufa cikin asibitin yayinda yazama abin kallo sbda rigar jikinsa, wasu suka hau kakkauce masa saboda a zatonsu mahaukaci ne. Direct office din dr mus'ab abdoljalal ya shiga, yaga baya office din. Dan hk ya fito yaga wata nurse ya tambayeta ina dr?, a tsorace ta bashi amsa da "Beso ba yau..." Tayi hanzarin barin gun sbda itama a zatonta mahaukaci ne. Abdoljalal ya fice a asibitin ya koma mota ya kalli ahamad yace "muje gidansa..." Ahamad ya tada motar hadi da tambayar Abdoljalal "Meke faruwa ne ranka ya dade.." Abdoljalal yayi banza dashi kmr beji shi ba sam ko mgna ma bayaso yayi sbda azabar turiri da tashin hankalin dake cikin zuciyarsa. Ahamad be kara cewa komi ba yaja motar suka fice a asibitin zuwa gidan Dr mus'ab. Ba jimawa suka isa sbda gidan da asibitin ba nisa. Ahamad nayin packing abdoljalal ya fito , direct ya nufa part din dr mus'ab zuciyarsa a zafafe. Bako sallama ya fada falon Dr din, ya taddashi zaune kan kujerarsa ta 3ct ya rafka uban tagumi yau ko office be fita ba, ya hana kuwa zuwa part dinsa sbda dmwar da yake ciki. Kwatsam yaga jalalu ya fado falon nasa, ya dago ya zuba
Chapter 104 · 0% Book details