Sashe 11
Wata Kishiya Complete Hausa Novel · about 8 min read
shine abinda aka rubuta yakai 5mnt nan tsaye yana kallon sunan nasa, kana ya karasa jikin kofar tanajin duminsa ta bude hadi da miko masa gaisuwa cikin harshen turanci dayake kofar na'ura ce wadda nasara ya kerata, shi kadai ke iya budeta, duk wanda ya biyo ta kofar bazata bude ba sede inta baya zaka shigo. Takawa yashigayi a hnkli byn ya shigo kofar ta mayar ta rufe ya zubawa kasan tiles din ido kai kace yau ya warke makanta shi knsa tiles din side din nasa ban taba Ganin irin saba , butter milk ne me tamburan heart heart kalar red da sky blue, inka tsaya tsaf zakaga knka a kn tiles din domin yafi madubi haske, wani irin kamshi se tashi yakeyi, direct falonsa ya nufa, wow! A nan kyaun yake alaji! falon ya hadu iya hadu ya kayatu harya gaji da kayatuwa sam babu hayaniya a falon, amma fa nan kyau ya tare a falon, kujerune kalar 2color a falon, 3ct da 2ct duk blue ne se 1ct butter milk dayar 1ctr dinma butter milk ce,, se wasu kujeru daga gefe na shan coffe guda biyu su kuma bakake ne masu rodi rodin golden color da dan table dinsu a tsakiyarsu golden neshi yana dauke da flowers a tsakiyarsa, gabaki daya tsarin falon tsarin tuwarawa ne ga rest chair a gefe butter milk ta hadu iya haduwa se wani kyalli takeyi na gold gold gashinan de, kaff fitilun kwan falon abin kallo ne danni ban taba ma ganin irinsu ba. Kallon falon yakeyi kmr yau Allah ya jefoshi cikinsa hk yakeyi wasu lokutan se yadinga ganinsa kmr shidin bakon duniya ne. Komi na falon is so cute and perfect komi fa ya hadu tsakiyar kujerun falon an mamayesa da wani carpet butter milk masu digo digon sky blue, ga wani dan karamin table a tsakiya wanda aka ajiye masa wata dankarereiyar flower milk color me ratsin sky blue da red red a jiki, ko wani gefe na kujerun akwai side table. Sanyin AC kawai ke tashi a falon tasama takasa na'urorin sanyi kawai ke Aiki, tamfatsetsen TV din falon se Magana yakeyi shi kadai ba dan tayi. Kyar ya tsayar da idanuwansa a kan TV na bangon daketa zubo kimtsatstsun bayanai ba kakkautawa ta cikin tashar sunnah TV ita kadai yake kallo Se BBC da tashar Aljazeera. Karasawa yayi ya daura kafarsa ta dama a kn carpet din dake tsakiyar kujerun nan da nan sekou kafarsa ta lotse luf a cikin carpet din laushi da laushi sun hadu, seya bashi wani irin lallausar laushi a tafin kafar tasa me ratsa gangar jiki da jijiyoyi, seda ya dan sauke ajiyar zuciya me fidda sarewar ni'imomi. kara daura kafarsa ta hagu kn carpet din yayi ya fara takawa a hnkli ya karasa kn kujerar 2st ya zauna seta lotsa itama tayi wani kasa dashi ta kuma ta dawo dashi sama luuuuuuuu ni'imar duniya me kwantar da hnklin bayin Allah kenan, bending din bynsa yy a kn kujerar yana me zuqo numfashinsa daddad'an kamshin dake falon ya bugesa ya kuma ya bugesa 100x, seda ya lumshe idanuwa tsawon 30second ya budesu a kan agogon bangon dake falon yaga karfe biyu ake nema zuwa yanzu,, mikewa yayi ya nufa kiching dinsa wanda kofarsa ke manne da falon. Wow! Kiching din ya hadu ya kayatu yayi wani irin luntsumemen kyau me razanarwa, color din kiching din blue ne light da butter milk, hatta da duk tiles din kiching din butter milk ne da sky blue light sosai. Se sanyin AC kawai ke aiki a kiching din kai kace kankarewa zakayi, ka koma kankara, wanda be saba da AC bama tini ze kankare ya koma kankara shikam gogan da sanyi da zafi duk be iya rayuwa seda sanyin AC sbda sabo. Komi na aiki a kiching din na'ura ce hatta da pot din girki na'ura ce,. Ma'ajin Kettle ya nufa ya latsa wasu malatsai nan da nan ruwa ya bulbulo a cikin kettle din ya kunna, ya nufa ma'ajin glasses cups dinsa dayake shan coffee dasu ya gansu jere reres a cikin glass ya danna password, nan da nan glass din ya bude, ya dauko cup din golden color da dan karamin trea din mahalin cup din ya saki famfo ya dauraye cup din da trea din, ya nufa inda kayan coffee din nasa suke ya zuzzubo komi mizanin dayakeso zuwa lokacin tini ruwan kettle din ya tafasa dan 10second yakeyi ya tafasa kara kunnawa yayi ya tafasa again kana ya zuba a cup din mizanin dayakeso ya nufo hayar dawowa falon ya zauna kan kujerar shan coffee dinsa, ya kai glass cup din bakinsa ya fara sha cikin salo a hnkli a hnkli har wani lumshe ido yakeyi dan dadin coffee din, girki ne kawai dabe iya ba da dakansa ze dinga yi shi mutum ne dabe jira a masa kwata kwata beda son jiki dan ko sadda Baba ladidi ke kawo masa abinci side dinsa daya gama ci ze kwashe komi yakai kiching ya gyara inda ya bata intazo kawai kiching take nufa ta kwashe ta fice dasu, shi be sakin jiki yace komi se an masa aah sam beda lalaci. yanashan coffee din yana kallon agogon bangon dake manne a bangon falon, 2:30am dai dai ya gamashan coffee din ya kai cup din kiching ya wanke da knsa ya mayar inda ya daukesa, ya juya ya fice daga kiching din direct matattakala ya nufa ya haye yana danjin dadin jikinsa daman dayaji bejin dadih dayasha coffee se yadanji sanyi sanyi bakomi bane sabo ne da yayi dashan coffee din, yanzu de shine ma abinsa ya manta When last yasawa cikinsa abincin kwarai. Direct bedroom dinsa ya nufa ya bude kofar bedroom din ya shigo bakinsa dauke da sallahma. Wow! So so cute ashe nan bedroom dinsa kyau yayi Aure ya tare.! Komi na bedroom din milk ne and golden light hatta furniture din kaf milk ne da cotton din dakin duk milk and light golden ne, ko ina tsaf tsaf danshi beson kazanta da tarkace shiyasa hatta bedroom din nasama beda wani uban tarkace beson haya-haya , shi sam ma baya bata wuri, bathroom dinsa ya fada, wayyoh kyau! Kyaun bathroom din ya fita yadda yafi tunanin me lissafi, duk na 'urorine a toilet din, an killace gefen wanka daban, da toilet seat, duk an wawwaresu daban daban ansa musu wani irin kayataccen labule a tsakiya, komi na bathroom din butter milk ne hatta da tiles din dake bango dako ina duk butter milk ne, se uban kamshi ke tashi a bandakin ko ina tal tal kmr a lashe. Kama ruwa yayi dan already yayi wanka dazu ya dauro alwala ya fito yadawo dakin nasa ya nufa ya nufa gaban mirror dinsa wanda Yake cike taf da turarruka kmr gaban mirro din mace, ya dauki hadadden perfume dinsa wanda ko kwalbarma abin kallo ce ya feshe jikinsa dashi, ya mayar ya ajiye ya nufa inda aka tanada dan ibada a dakin ya tada sallar kmr yadda ya saba duk daren duniya...bashi ya idar ba seda aka fara kiraye kirayen sallar asubahi! Kana ya dakata yayi addu'ur'insa ya mike ya Nufa bathroom dinsa ya cire kayansa ya shiga na'urarsa tayin wanka , yana daga tsaye nan ya danna wani malatsali sega ruwa me dumi yadda yakeso ya zubo batare dayayi komi ba na'ura ta masa wanka tas da nau'ikan sabulai iri iri na kamshi, ya fito hadi da jawo towel ya goge jikinsa ya dawo dakin a gaggauce ya shirya cikin jallabiya butter milk ya feshe jikinsa da turare, ya fice zuwa masallacin dake cikin gidan, bashi ya dawo cikin gidan ba se 6:30am. Ya nufa kiching ya hada mutumin nasa wato coffee yasha 7:am yabi lafiyar gadonsa yana mejin ni'imomi na sakkowa ga jikinsa, dabadan karfin ibada ba shi knsa yasan dabesanma a yaya yake ba. 3:am a bakin get din gidan AASARAKi ta bugawa hajiya kande da wata yarinya fara Sol kmr Aljana wadda a kalla shekarunta bazasu yawai taba, yarinyar sanye take da hijjabi blue black dark sosai dukda hijjabin ya kode iya kodewa musammanma daga saman kai Amma ya amsheta Ainun ya fito da kyakyawar fuskarta zuwaiiitt doguwace fuskar tata me cikar kumatu kubul-kubul lugub-lugub, dukda akwai alamun wahala a jikinta amma hkn be hana kyaunta bayyana ba, tanada dara daran idanuwa kmr zasu fado kasa dan girmansu ta cikin idanuwan nata dan tsakan brown ne sosai ba baki ba, farin kwayar idon nata fari ne soll kar-kar tas-tas, tanada yalwar gashin ido zara-zara, tanada cikar gashin gira harsun hade da juna, tanada dogon hanci gashi siriri har baka, bakinta dan mitsitsi kmr gidan tsutsa duk wani mumini inya kalleta seyaji sanyi kuma seya firgita da kyaun nata, a ido kawai zaka fahimci ita din ba yar nigeria bace gaskiya launin fatarta shi ze kaya tabbatar maka da hakan, hijjabin jikinta ya dan zame ta baya gaban sumar knta ya kwanta luf-luf, takalmin kafarta wani irin lasashen slifas ne wanda ya gaki da duniya launin blue,, a mizanin incin tsawonta zata kai 57 dole ne asata a jerin dogaye duba da yanayin shekarunta, sannan siririya ce sam bata da jiki, dagani hakan baze hana a gane albarkatun jikinta ba , ta rungume jakarta ta cikin hijjabin dake jikinta. hajiya kande kuma sanye take da mayafi green tasha dankareriyar atamfarta me launin koriya wato green,bag dinta ma green ce, black ce ita amma taci bleaching dan haka tayi wani red red da ita kallo daya zaka mata ka tabbatar data taba bariki, to ba karya bane dan seda tayi 20yrs a saudiya tin lokacinma tana 18yrs tanaji da danyen yarintar budulci, sede tin tana 10yrs ta zubar da budulcin a gantalin tsiya,. Aiki tajeyi saudiyar amma ta tubure ta balle bin maza, nan wani balarabe yasamu damar narka mata sperm a mahaifa tasamu ciki, hkn ne yasa dole aka dawo da ita nigerian ba tare datayi Aune ba, gaskiya ta gwabza bariki tin bariki tana bariki ba barikin yanzu ba ta wahalar rayuwa in kayi wasa ma se Abincin dazakaci ya gagareka bariki ba riba koda ita datayi me ribar bata kare lafiya da duniya ba dan har yanzu bin mazan takeyi tsofe tsofe da ita ta ajiye