← Book details Wata Kishiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 107

Sashe 51

Wata Kishiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

barin dakin yace ta huta kuma karta ci gaba da dafa masa abinci ta bari se ta kara samun sauki..... Yace kuma ta dinga fesa maganin sauro na fesawar daya siyo... Al-muqri'ah tace toh ta kuma masa godiya, Abdoljalal yace "Zaki biya ai...." Al-muqri'ah ta daga masa kai alamar toh... Abdoljalal ya fice a dakin zuwa side dinsa samshi ko abinci beci dukya rame inyana ganinta sam bejin yunwa. A zamansu a asibitin al-muqri'ah ta fahimci Abdoljalal mutumin kirki ne kuma shakuwa ta kara shiga tsakaninsu me tsanani , ta faraji a zuciyarta zuwa yanzu ba abinda bazata iya ma Abban nata ba, danta faranta masa, kome ma zatayi masa tasan bazata biyashi ba, dawainiyar daya dingayi da ita a asibitin har kayanta ya dinga wanke mata abinda be tabayi ba, ko kayansa be taba wankewa ba tinda yazo dunita sede boxes kadai yake wankewa kansa, amma ita kullum data cire kaya ze wanke a zamansu a asibitin.. Al-muqri'ah ta kuma fadawa kogin soyayyar Abdoljalal ba tare data sani ba, amma ita knta ta afka kogin da yake ciki tsundum ya koyar da ita sanshi kuma tini ta dauka. 8:am da talatainin safiya saude zaune a falonta, Yayinda larai ke tsugunne a kasa, fuska dauke da tsoro, hajiya saude ta zuba mata ido se faman girgiza kafafuwa takeyi, sanye take da wata buhun rigar atamfa abuja bubu, a kalla yanzu turmin atamfa biyu hajiya saude keci, ta kara tafka wata uwar rusheshiyar kiba, ta kuma dunkulewa rigijiji, ga uwar uban dukiyar kumatunan nan nata sun kara subutu subutu kamar fanje yaji yis, bakinnan nata ya kara zungurere dashi, kamar na biri gashi baki kirin kmr na yan shaye shaye,, hankalin hajiya saude kwance se kara rushewa takeyi tana tarwatsewa kamar chin-chin yaji kayan hadi. "Ina shi usman din danace ki kirawoshi ku taho tare..." Cewar gimbiya madam Hajiya saude, tana magana kumatunan nata na motsi, yayin da nonuwannan nata suka kara uban tsawo har sun wuce cikinta sun kai cibiyarta, kmr de sideden silifan, tumbinnan nata ya kuma kara uban fadi da tsawo, data zauna tumbin ze zauna shima a kn cinyoyinta rigijib. Jikin laure ya kara daukar rawa daman ita tinda akace mata wai hajiya na kira yau da sanyin safiyarnan ita da bata tashi da wuri amma yau ta tashi da sanyin safiya. larai ta gama yadda da yau akwai tashin hankali ta riga ta sadakarma kwan baya gurbi ne ze fashe, in ko ya fashe seya addabi uban kowa da wari har wadda ta fasashi. "Eh yacemin ynzu zezo saboda oga yasashi wani aiki ne shine yake dan karisawa..." Cewar larai, Hajiya saude ta bude baki zatayi magana usman ya iso yayi sallama ta masa iso ya shigo shi knsa gabansa faduwa yakeyi saboda kiran saude ba Alkhairi bane. Zubewa usman yayi ya fara koro mata gaisuwa ba tare data amsaba ta gyara xama, hadi da gyara zaman dankwalin dake knta ta turo shege gaba, ta chuno dogon bakin bakinta kana ta fara magana cikin ruwan wutar bala'i. "Kai dan bura ubanka har wuyanka yayi kaurin dani zanyi kira kazo kace wai, kana karasa aikin Abdoljalal ne... nan take usman ya shiga bata hakuri daman yasan za ayi haka, domin ya lafiyar kura balle tayi hauka, inda sabo kowa ya saba da zagin hajiya saude. Kwafa saude tayi hadi dacewa ina dai-dai da zamanin ko wani dan tsinannan me aiki a gidannan..." Duk suka hada baki gun Cewa "Allah ya huci zuciyarki..." Ta kuma yin kwafa, hadi da gyara zama irin na masu isa da duniya wadanda basu san akwai mutuwa ba. "Daman na kiraku ne in tambayeku, amma inaso duk ku gayamin gaskiya, domin in har kukamin karya na gano hakan a karshe wanda yake lahira ma seya fiku jin dadih,, kundesan wacece sauden saraki ba imani bane ya yawaita a zuciyata..." Usman da larai suka hadiye wani mugun yawu na tashin hankali suka juyo suka kalli juna, kana duk suka amsa da zasu fadi gaskiya, zuciyarsu se dukan dari uku uku takeyi, saboda basu san mezata tambayesuba. Saude taci gaba da magana, tana karkata akalarta ga usman. "Zan fara ta kanka kai usman kana jina kou...." Usman ya amsa da "A, ranki ya dade..." Har jikin usman din na rawa. Hajiya saude taci gaba da magana tana tsaresa da yan mitsilayen idanuwanta na harijai. "Kai usman kafi kusanci da bangaren mijina, ya kake ganin mu'amalarsa da wannan me dafa masa abincin, aikinta takeyi ko kuma de tana shigarmin harka mijina saraki? Dannasan de shi mijina ko kallon bnza bata isheshi ba,ni nasan mena taka a kanshi.... usman ya hadiye wani yawu kana ya saita kansa ya fara magana cikin kwarewa, "Ai ranki ya dade knsan de waye Alhaji saraki, ina .e tabbatar miki dako kallo ma wannan yarinyar bata isheshi ba, zan iya ce miki ma basu cika wani haduwa dashiba, shi yamafi zama a saman benensa, in kinga ya sakko abinci zeci, kuma daya Ci abinci shikenan seya koma sama..." Usman ya fadi ne kawai dan gaskiyar bazata fadu ba, amma shima ya fara fahimtar abubuwa, yana gani oga na shishigewa yarinyar.."wawuya jaka in banda wawanci ke kya dauko wannan dankwalin kice mijinki baze kalletaba..." Usman ya fadi hakan amma fa a can kasan ransa. hajiya saude ta sauke ajiyar zuciyar maganganun usman danta kula shi ustazi ne baze mata karyaba, nan da nan ta fara aminta da kalamansa, mummunar mafark tayi yau taga mijinta tsaye da wannan yarinya me aiki sunawa juna kallon So da kauna shine hankalinta ya tashi ta gaza komawa baccin ma yau gabaki daya, amma fa tasan kawai sherin shedan ne ke bibiyarta koda yake itama da knta tasan tafi shedan sharri. "Ka tabbata usman? Dan wallahi inna fahimci wani abu akasin abinda ka gayamin wallahi gidan nan ya mana kadan nida kai..." Cewar saude. Usman da gabansa ke dukan uku uku ya juya ya kalli larai ta daga masa kai cikin kissa alamar yace ehh ba tare da burunguzuma ta fahimtaba.. "Tabbas ranki ya dade duk cikin kalamaina babu karya, wannan magana gaskiya ce, shi yallabai fa ranki ya dade be ganin kowa a duniya seke,..." Usman ya karisa maganar hadi da zuzuta ta, danso yakeyi su gama lafiya shi da ita, dan kowa yasanta da shegen kishin bala'i. Hajiya saude tayi murmushi jin abinda usman yace kana tace "Ko ya akayi kasan haka usman?'' Usman ya tunano wata karya kana yace "Ai ranki ya dade knsan na hannun damansa, Ahamad dinnan aminina ne, shiya gayamin yacemin wallahi duk kamfanonin oga ko sakatariya beda ita mace, saboda kawai matan ma duka basa gabansa, to yanada kema mezeyi da wata mace a duniya, ubangiji fa shi kadai yasan halittar daya maka miki, ai yanayinki ya wuce misali ranki ya dade, surarki ta wuce me hankali..." Larai ta kalli usman danta fahimci magana yama sauden cikin magana amma Hajiya saude bata fahimtaba sema ta shiga nishadi mara misaltuwa. "Alhamdulillahi,,, toh yanzu zan baka wani aiki na kulamin da yarinyarnan a kn mijina, insha Allahu ni nasan mezan maka..."cewar hajiya saude. Usman yace "an gama ranki ya dade..." Hajiya saude tace "yawwah jeka tokai na gana da kai, duk abinda ka gani ko ake ciki ka dinga sanar da larai tana gayamin ko kazo ka sameni...da kaga akasin abinda nakeso kazo ka gayamin..." Usman yace "toh angama ranki ya dade..." Ya mike ya bar falon yana godiya ga Allah dasuka rabu lafiya, seda yayi nisa da side din kana yace "wawuya duk wayanki kinyi ya ubangijinmu ne... Insha Allahu se munga karshenki, bi izinillahi se oga ya auro mace, danke ba mace bace, baki da maraba da botoramin film muguwa kalarki kalar zuciyarki, in ba ma kaddaraba me oga zeyi dake... Dan dagani ke bakar kaddarace a gurin oga ...." Usman ya kyakyale da dariya shifa gabaki daya halittar matarma dariya take bashi. "Burunguzuma kenan....wai!!'' Usman ya kara fadi yana tafe yana dariya. Usman na fita hajiya saude ta dawo da dubanta da hnklinta kn larai tace "Toke ina jinki, ki gayamin gaskiya ya aikin dana saki, ya rayuwar mijina da yarinyarnan?'' Larai ta gyara zama hadi da gyaran murya tace "Yawwah hajiya knsan de gaskiya dayace kou, toh ita zan gaya miki, in kn amince..." Seda gaban hajiya saude ya fadi jin abinda larai tace. "Eh na amince ki gayamin...Ai gaskiyar nakeso ki gayamin larai...." hajiya saude ta fadi yayinda zuciyarta ke tsananta bugun da batasan na meneneba, ta kara kure larai da ido.... Har larai zata bude baki tayi magana hajiya saude ta dakatar da ita dacewa "Ki fito fili pls ki gayamin gaskiya larai dan Allah, ni knsan inde a kan mijina ne banda hankali, kawai ki gayamin gaskiyar meke faruwa da mijina da yarinyar nan..." Saude tayi maganar da kwantacciyar murya yauce rana ta farko da larai taji saude tayi magana da kwantacciyar murya batasan tanada kwantacciyar murya ba se yau. *pls a bar fitarmin da littafi dan Allah...* Vip 1k normal 500 0542703718 Saadatu Abdullahi gt bank shedar biya ta nan 08101626484 ko M.T.N card. SAADATU BINTU ABDULLAHI (writer of Kyautar Allah) Page 16 Larai tayi kasa-kasa da murya irin ta gulma da munafunci kana ta fara zayyano zance. "Yooo ranki ya dade yallabai mezeyi da wannan yarinya me siffar jinnu wal-insu, ai ranki ya dade ki tsoma ranki a ruwan sanyi kawai, ki maya wankan tsarki da ruwan kankara, kiyi bacci ki huta, yar hutu jikar hutu, babu wani abu ko makamancin abu a tsakaninsu da wannan me aikin, in takaice miki ma hajjaju ikon Allah ai shi Yallabai ma kyamar yarinyar yakeyi....." Hajiya saude tayi bending a kn kujera hadi da sauke nannauyar ajiyar zuciya, tasha wata matseefar larai zata gaya mata akasin abinda usman ya gaya mata. "Amma larai har kinsa gabana faduwa nasha akasin kalaman dasuka fito a bakinki zaki gayamin, wallahi har zazzabi ya fara rufeni..." Cewar hajiya saude da zuciyarta, ta kuma kwanciya saboda kalama larai dana usman data hada a kanta. Larai ta watsa hannu hadi dacewa "Ah'ah ranki ya dade, ai wannan magana da usman ya gaya miki kaf gaskiya ce, ko digo daya na karya babu, shiyasa nima na kara tabbatar miki da gaskiyarnan bisa gaskiya,,, ranki ya dade kmr fa cewar usman ne ke kadaice a
Chapter 51 · 0% Book details