← Book details Wata Kishiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 107

Sashe 44

Wata Kishiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

dr mus'ab dake kallonsa yayi murmurshi dan yasan halin kayansa. "Bakada lafiya ne?'' Dr mus'ab ya jefo masa tambayar dan ganin ya zauna bece masa komi ba se mulkin kawai yake zubawa. Abdoljalal yace cikin isa da zallar mulki irin na jinin sarauta "zazzabi nakeyi sosai a kwanakinnan, ina ganin jiri sosai..." Dr mus'ab dayazuba masa ido hadi da nazartarsa yace "me kake tunani?" Abdoljalal ya dago ya kalles se kuma ya wani dauke idanuwansa yana fadin.''Daga zazzabi da ganin jiri se aka gaya maka tunani nakeyi ko uban yan iya!.."Abdoljalal ya Karashe maganar cikin zallar mulki. Dr yayi murmushin gefen kumatu .."wallahi tunani kakeyi malam,se wani ciccijewa kake kmr wani dan daba...'' A hasale Abdoljalal yace "Adda da gariyo ne suka bayyana dan knsu..." Dr mus'ab dariya tazo masa wuya amma ba damar yinta, dole ya gimtseta dan wallahi zuwa yanzu tsoron gogan yakeyi se yayita matseefa ba dalili, me neman kuka ne aka jefesa da kullin kashi. "Malam zaka dubani ne ko yaya?'' Abdoljalal ya fadi ba kwarin jiki. Ba tare da dr yace komi ba ya mike ya fara duba bp dinsa nan take yaga yayi wani irin hau sosai kuma yasan damuwa ce tasa jinin nasa hawa. "Saraki pls meke damunka haka ne dan Allah? Meke damunka da har jininka ya hau haka sosai?'' Cewar dr dake mamakin ganin yadda jinin saraki ya hau ya refesa.. "Tunaninta yasamin hawan jini nan gaba wallahi har ciwon zuciya zesamin, a hankali se kabari!..." Ya fadi a zuciyarsa ba tare dayasan maganar ta fito fili ba, domin yanzu be iya boye magana a zuciya saboda ya gaji da boyewar, yayi dauriyar harya gaji, kai shi bedama dauriya a kn yarinyar,. Dr yabishi da ido yana kara bude kunnuwansa kan abinda suka jiyo masa daga bakin Abdoljalal. "What?! Mekace saraki? Tunanin wa kakeyi dayake neman kaika kabari? Dan Allah yau kayi sharing problem dinka dani pls abokina, ni me rike maka sirrinka ne har abadan .'' dr ya fadi mamakin Abdoljalal na kara ninkuwa a ransa. Haka kawai Abdoljalal ya tsinci knsa dason gayawa dr abinda ke ransa game da yarinyar domin ya gaji da boyewa, yana ganin inya fadi masa ze samu sassauci. "Kullum tunaninta nakeyi...in ban ganta ba rayuwata batamin dadih, tsananin sha'awarta nakeyi, sha'awar daban tabawa wata ya mace irin taba se ita wallahi dr na rasa ya zanyi, kuma so nakeyi na rungumeta ko zanji sasauci amma na gaza yin hakan ,dr dan Allah in ana allurar chanzawa mutum tunani kayimin tunani na da lissafina ya chanza, in koma kmr da, wallahi haukacewa nakeso nayi...pls ko za a kaini asibitin mahaukata ne dan wallahi na haukace... Mutum daya ta hanani sukuni kwata-kwata dr..." Duk maganganun nan da yakeyi yinsu kawai yakeyi amma ji yakeyi kamar ya daura hannu a kai ya fasa ihu ko ze samu sassauci, idanuwansa tini suka ciko da kwallah tin sadda ya fara maganganun. Glasses din dake idon dr ya ciresa ya ajesa a gefe, a gefe, ganin lamarin bana wasa bane, jin maganganun dake fitowa daga bakin abokinsa, lumshe ido yayi saboda gani yakeyi mafarki yakeyi, wai yau saraki ne, wai AAsaraki ne ke maganar soyayya, abinda be taba yiba tin zamanshi dashi a rayuwarsa. Tagumi dr ya rafka da hannu biyu biyu yana kallon Abdoljalal dake zaune gabansa yayi kasa da idanuwansa yayin da tini hawaye suka fara zirya a kn fuskarsa, nan dr ya kara sarewa, dumbin mamaki ya kuma rufesa. "Saraki ne yau ke hawaye?'' Dr ya fadi a fili yayin da mamaki ke kara lullubesa, sannan ya shiga tunani tunani, kwakwalwarsa itama ta dauki zafi ta shiga thinking. "Saraki kasani a tunani, pls maganar nan da kake fadi saude kake nufi matarka ne , ko yaya ne ni wallahi ban gane ba?'' Dr ya fadi cikin rudu. Abdoljalal da idanuwansa keta ambaliyar ruwan kwalla har zuwa lokacin yace "Al-muqri'ah ce! Wallahi itace, watace ba kowa bace a duniya, amma ni a duniyata itace duniyar tawa ma gabaki daya, dr yarinyar nan ta chanzamin tunani da rayuwata duka...'' Ya fadi wasu hawayen na kara wanke masa fuska. Dr ya dakko glasses dinsa daya cire ya mayar a idanuwansa, danyafi kallon sarakin da kyau, damin ya fara tunanin kode da gaske ne asibitin mahaukatan za a kaisa dan bega alamar a zancensa akwai hankali ba. "Wacece kuma hakan saraki? Anya Jalalu ba gamo kayi ba wanda yasaka hauka? Ko kuma de ka fara shaye-shaye ne..." Dr ya fadi yana jin jina kai, dan baya tunanin a duniya AASaraki zeso wata mace kmr yadda yake cewa, domin Saude bazata barsa yaso wataba. "Wannan shed'aniyar..." Dr ya fadi a ransa. "Wallahi dr kullum da tunaninta nake kwana nake tashi wallahi nine Abdoljalal abokinka wanda kukayi karatu tare bude idanuwanka sosai ka ganni nine, wallahi ji nakeyi zan mutu a kn yarinyar nan dan Allah dr meke samuna ne pls ka gayamin?'' Abdoljalal ke maganar cikin rud'ani danshi besanma meke samunsa na,. "Zazzafan SO ne ke damunka saraki, duk wannan alamomin daka gayamin naso ne, sanma me zafi..." Dr ya bashi amsa direct danya fahimci shi be fahimci meke damunsa bama kwata kwata. "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!'' AASARAKI ya fadi hadi da cusa hannayensa na dama dana hagu cikin audigar sumar knsa, yana meci gaba da hawaye. Dr ya tsura masa ido zuciya cike da tausayawa, mamaki da alhini basu barshi ba har zuwa lokacin, ganin AASaraki gabansa yana riskar kuka kmr karamin yaro, hakan nasashi tunanin anya ba mafarki yakeyi ba. "SO?' Dr SO fa kace,,,'' Abdoljalal ya fadi still wasu hawayen masu rad'ad'i suna zirya a kan fuskarsa. Dr yace "Yeah zazzafar SO ka fada abokina me tsananin zafi amma dan Allah ka sassautawa kanka ka tsaya muyi magana ta fahimta, in kana kukannan bazan fahimceka ba, dan Allah saraki kaifa babban mutum ne, kaine fa next president dinmu, pls ka dinga dauriya..." Dr ya fadi cikin damuwa. Abdoljalal ya amshe da "wallahi dr bansan dauriya ba a kan wannan yanayin da nake ciki, dan Allah dama haka shi SO din yake?'' Dr mus'ab ma tini damuwa ta rufesa ganin abokinsa na kuka haka ba kakkautawa. "Saraki wallahi SO ka afka, amma ni ban fahimci me kake nufi ba at all ko ince na shiga rud'anu, dan Allah wacece wadda ka kamu da santa har haka Abdol a ina take pls?'' Nan Abdoljalal ya kwashe labarin al-muqri'ah ya bashi daga farkon fara ganinta har zuwa yanzu be boye masa komiba. Tini wata azababbiyar zufa ta rufe dr mus'ab, duk sanyin AC dake office din bejinsa, sema yaji AC din zafi take basa, saboda azabar tashin hankali, tinda saraki Ya fara basa labarin ba abinda yake tunanowa se saude, tausayin yarinyar ya kamashi, dukda be ganta ba,again gata bebiya gata me aiki, duk makirci da bala'i da matseefar saude babu wanda dr besani ba. "Ya Arrahamanirrahim! Ya Zaljalalu wal-ikram'!'' Dr mus'ab ya fadi, yayin da zuciyarsa tayi masa sanyi karai, tausayin yarinyar kawai ke yawaita a zuciyarsa kuma gata karamar yarinya dan duk saraki ya gaya masa. " Dan Allah dr ka gayamin yazanyi da abinda nakeji a kan yarinyar nan..." Cewar saraki da har zuwa lokacin yaketa kwallah, kai bakace babban mutum bane. "Saude..." Itace kalmar data fito daga bakin Dr. "Banjin tsoron kowa a kn yarinyar nan dr, in duk duniya zata taru nasan bazasu ciremin san yarinyar ba, haka in duniya duk zasu taru a kaina zasu kasheni bazan iya daure wannan abin da nakeji ba..." Abdoljalal ya fadi ba gudu ko ja da baya,. Dr mus'ab ya kara firgita da lamarin, Saboda yana hango bala'in dake kwance yana bacci tsawon shekaru amma yanzu ake neman tadasa. "Dr SO nakeyi na kusanci jikin yarinyar nan, abin ya min yawa ga Azabar SO, ga azabar sha'awah, wallahi so nakeyi na kusanceta, jiki da jiki...." Abdoljalal ya fadi babu alamar wasa. Dr ya zaro ido wato de dr ya fahinci lamarin ya wuce zurfi da tsawon tunaninsa. "Sex kenan fa kake nufi saraki?'' "Yeah so nakeyi nayi making love da ita ko zanji sauki a marata, wallahi dr babu wanda ze iya fahimtar me nakeji a zuciyata, innaga yarinyar nan bakuncin hauka ke ziyartata, bana iya controlling kwata -kwata a kan yarinyar dr..." Abdoljalal ya fadi yayinda fuskarsa ke bada tabbacin abinda yake fadi zuwa lokacin hawayen idanuwansa sun kafe sbda azabar ta shahara iya shahara. "No no no...saraki Pls karka ci yar mutane sede in zaka Aureta ne..." Cewar dr. Abdoljalal yace "Yeah zan Aureta wallahi dr, ban taba san wata halitta da tsananin sha'awartaba se yarinyar..." Dr mus'ab ya gama fahimtar da gaske Abdoljalal yakeyi son bebiya yakeyi, amma kuma sede in saraki yashiga rayuwar yarinyar to tabbas yarinyar zatasha wahala bashi sarakin ba ita zata wahala. "Frnd kode kaci yarinyar ne?'' Dr ya jefowa Abdoljalal tambayar. "Meyasa kace haka?'" Abdoljalal ya jefesa da tambaya ba tare daya bashi amsar tashi ba. "Saboda san da kake mata yayi yawa saraki, in ba de ka cita bane kaji band'ashenta da dadih taya zaka mata wannan san shiyasa na tambayeka kode ka riga ka hau kn yarinyar ne..."cewar dr. Abdoljalal dake kallon dr yace "Wallahi dr ban cita ba, ni tsoro take bani ko hugging dinta na kasa yi, amma wallahi yarinyar ta gama nakasamin rayuwa dr pls help me my Frnd!'' Ya karashe mgnr da magiya kai kace dr mus'ab ne ze cire masa abinda yakeji a kn yarinyar. "Pls ka fita a rayuwar yarinyar nan jalalu kafin itama a sabauta mata rayuwa a kanka,,dan muddin ka Aureta matarka tasani wallahi itace ajalin Yarinyar nan...so dan haka is better ka fitar mata a rayuwa dan Allah saraki ka duba nakasar yarinyar, pls kada asata a wahala kamar yadda akasa Aysha a wahala..." Girgiza kai Abdoljalal ya shigayi tin kafin dr ya dire maganarsa. "Dr ta ina zan cire abinda nakeji? Wallahi bani nasawa kaina ba...dani nasawa kaina da tini na cire sbda ta hanani sukuni..." Dr ya gyara zamansa a kan kujerar dayake yace "Kayi try pls...wallahi lamarin yarinyar kawai nake dubawa, kasan halin matarka ba mahalicci a zuciyarta..." Abdoljalal yayi shiru yana nazarin maganar dr mus'ab, tabbas yasan haka ne duk abubuwan da mus'ab din ke fadi, yauce rana ta farko da dr ya fadi aibun hajiya saude suka
Chapter 44 · 0% Book details