Sashe 97
Wata Kishiya Complete Hausa Novel · about 8 min read
yankan kai..."larai tayi maganar a zuciyarta. A kofar dakin Jimmalo larai taga jimmalon ta kalleta taga idanuwainta sunyi luhu luhu tayi kuka tagaji. Larai ta tabe baki tace "ohh aiki yasamu gwari...aise ki tashi kije oga na kira.." Jimmalo taji gabanta ya yanke ya fadi jin abinda larai tace a karshe, ta mike tsaye hadi da gyara zaninta wanda ke kokarin kubce mata, tashin hankalin datake ciki baze misaltuba, ko sadda ubanta ya mutu bata shiga tashin hankalin datake ciki ba a halin yanzu, tin tana ganin yarinyar zata dawo yanzu ta cire raima da yarinyar zata dawo gidan yau kimanin 2days kenan bata gidan, jimmalo kullum kwana da wuni takeyi tana kuka, tunaninta daya ne ina yarinyar taje?'' Ta tabbatar in Abdoljalal yaji bata gidan tsawon 2days seya fi jimmalo damuwa "wane itama...." A jere jimmalo da larai suka iso inda Abdoljalal yake, jalalu yabisu da ido yaga bega Almuqri'ah ba sede jimmalon, kallo daya ya mata yagane bata cikin hayya cinta kmr yadda shima baya cikin hayyacin nasa lips dinsa duk yabi ya bushe rakayau se faman jikashi yakeyi da yawon bakinsa.. "Ina Almuqri'ah na?'' Abdoljalal yayi tmbyr idanuwansa na kan jimmalo, larai taji kmr ta kashe knta dayace Almuqri'ah na. Jimmalo kam gabantane ya yanke ya fadi, ta daburce ta rasama mezatace masa, kawai se yaga hawaye sharr a idanuwan ta..hakan ya bala'in jefa Abdoljalal a tsananin tashin hankali mara misaltuwa , ya tabbar da akwai babbar matsala.."nace ina Almuqri'ah da d'an cikina? Ina take? Ina d'an cikina? Kiyimin magana, ina cikina danayi mata? Ina cikina dake jikinta?!!!'' Abdoljalal yayi mata tambayoyinnan cikin tsawar data kada hantar cikin jimmalo ta kalleshi tayi kasa da kanta, duk yabi ya haukace, a hakama dan beji komi ba kenan. "Ina take nace?!!!! Ina cikina?!!!!" Abdoljalal ya kara tmbya cikin tsananin tsawar da har securities seda sukaji, dukkaninsu suka hada baki gun cewa "Anxo wajen..." Kaf jikinsu ya dauki rawa, suka kira masu gadin get din tsakiya dana farko duk suka dawo cikin gida sukayi tsuru tsuru, tini wasunsu sun fara zawo. "Ta gudu,tin washe garin ranar dakuka je asibiti, na nemeta bangantaba wlhi..." Jimmalo ta fadi cikin kuka, ta zube kasan guiwowinta hadi da kara rushewa da kukan tashin hankli me tambarin matsifa da bala'in dake tattare da ita ko kwatan Abdoljalal bata kaiba. Larai de na gefe. Jin abinda jimmalo tace yasa kunnuwan Abdoljalal daukewa na wasu dakiku, idanuwansa suka lumshe da yana, yaji wani luuuu kmr ze fadi, se kuma ya rike jikinsa sbda shi namijin duniya be yayan namijim zaki ne,sam ba a ganin tashin hnklinsa duka, dan hk yanzuma rabi aka gani a zahiri. "Banji me kikace ba? Ta gudu? Ita wa ta gudu? Almuqri'ah ta gudu? Ta ina tabi ta gudu? Ina taje? Ina cikina na jikinta??'' abdoljalal yayi maganganun kamar ze haukace saboda rudu da gigita, idanuwansa se lumshewa sukeyi yana kara budesu, tashin hnklinsa baze misaltuba har abadan, kai kace cewa akayi masa Almuqri'ah din ta mutu. Jimmalo ta kasa amsa masa tambayoyinsa se faman rusar kuka takeyi. Larai tayi carab tace "ta gudu ranka ya dade, wallahi ta gudu yarinyar nan, ta bakin get tabi ta gudu, suma kansu securities basu san guduwa zatayiba suka barta ta fita , ..." "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!!'' Abdoljalal ya maimaita 3ryms hadi da dafe kansa,, idanuwansa suka kara lumshewa. "Ta gudun min da ciki? Ina tajemin da cikina? Ku fada mata ta dawo ta bani cikina dan Allah...innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!!''' Abdoljalal ya fadi kmr saban hauka so yakeyi yayi kuka amma ya kasa, tashin hankali mara misaltuwa ya shiga, zuciyarsa tashiga, fuskarta ta bayyana Dmwar zuciyarsa,. Larai tayi lakur, tana hango bala'in dake tattare ga Abdoljalal. Jimmalo kam se kuka takeyi. "Karya kuke min bata gudun min da ciki ba wlhi,,, se kun nemomin ita tabani cikina wlhi..." Ya fadi yana girgiza kai, ji yakeyi kmr a mafarki yake,. ya juya cikin hanzari ya nufo bakin get securities na ganinsa sukayi kasa da kansu, dmwa da tashin hankalin dake kan face dinsa basu taba ganin makamancinsa ba a tattare dashi se yau. "Da gaske ne Almuqri'ah ta gudu?'' Abdoljalal ya fadi a haukace byn ya iso inda suke kmr zararre , jijiyoyin knsa duk sun tashi . Duk suka kasa magana sede suka kara kasa da kansu. Abdoljalal ya daka musu tsawar dabe taba daka musu irintaba se yau "Nace da gaske ta gudun min da ciki?" Jikinsu na rawa suka amsa da "A, sir..tuba muke sir..." Suka hada baki gun fadar hakan. Idanuwan Abdoljalal suka kawo wasu zafafan kwallah, nan da nan suka karayin jajawur zuciyarsa kmr zata fito fili, jikinsa ya dauki rawa. kaf ma'aikatan suka karayin kasa da idanuwansu, zuciyarsu nata fatt fatt fatt, sun san karshen zamansu a gidan yazo, tini suka fara kokawa kansu. "Ku kuka barta ta fita daga bakin get?bayan ga cikina a jikinta?'' Abdoljalal ya fadi cikin kuka se yarfa hannu yakeyi sbda rad'adin da zuciyarsa keyi be tabajin irinsaba se yau.. Securities sukayi shiru suka kasa amsa wa.. "Badaku nake mgna ba dan kan babbar bura ubanku ku amsani, karku karamin shiru, in ba haka ba, wallahi zansa muku bom in kashemu baki daya nida ku, shegu tsinannu, yan iska, nace ku kuka barta ta fita a bakin get, gets hard guda uku ta fice a cikinsu ta gudunmin da cikina a jikinta, dan kutmar babbar bura ubanku?'' Abdoljalal ya fadi cikin fitar hayyaci da tsantsar tsagwaron ruwan wutar bala'i hadi da gobarar tashin hankali. Duk ma'aikatan suka kara shiga taitayinsu, sbda tashin hankalin dasuke tsammani zasu gansa a ciki se suka gansa a mafiyinsa. Duk suka amsa da yess hadi da ban hakuri. "Kuka barta ta gudun min da ciki, har tsawon 2days bata nan, ina taje? Da d'an cikina ta gudu kou? D'an cikina kou? Cikina na jikinta kou? Innalillahi wa'inna ilaihir...!!!''' Be samu dmr karasawa ba ya zube nan kasa sumamme tamkar an zare masa rai, idanuwansa suka lumshe dmn ba karfi a jikinsa. Hankalin securities din ya matukar tashi, yadda naga fuskokinsu dmwarsu suma bazata misaltuba. Gadan gadan sukayo kansa suka dagoshi, aka kawo ruwa aka yayyafa masa, amma sam be farfado ba ko ajiyar zuciya beyi ba, hankalin maza ya kara tashi wasu tini idanuwansu sun fara kawo kwallah, wadanda ba musulmai a cikinsu ba se kiran Jesus sukeyi suna ihu suna rawar diskon tashin hankali, tini suka tara kaf ma'aikata mata a gurin kukansu ya jawo hnklinsu. Tantiri kam si yafi kowa kuka da ihu harda daura hannu yayi a kai yana fadin "Wayyohhhhh mun shiga uku mun lalace !!''' Se rawar tashin hankali tumbinsa keyi.... Nan suka kwasheshi a haukace aka sashi a mota, Almustapha ya rikeshi, da salisu tantirin daketa kwallah Zuwa yanzu yayi ihun ya gaji har muryarsa ta dishe,, kaf ma'aikatan gidan sunyi nadamar barin Almuqri'ah ta fita a gidan, sbda hkn ya matukar jefasu a tashin hnkli seda kowa kowannensu yashiga tashin hankali. A guje Dreva ya shiga motar yaja suka fice a gidan, motar securities na biye dasu a baya. Insha Allahu zaku jini da daddare. Aski yazo gaban goshi azabar zafinsa nakeji *na gaya muku zan dinga hutun 2days a week kuma ban fadi ranaku ba, to hutuna nayi na 2days din,, kinganni nan nasaba da zagi duk wanda ya zageni ya ragemin kayan wahala.... A barni in bi book dina a sannu pls masu sona dan Allah...wadanda basu sona adeyi hkri...* Bata tsaya wata wata ba, Ta buge security din dake kofar get din wanda ya dakatar da Almuqri'ah daga karasowa cikin gidan, idanuwanta dana Almuqri'ah suka sarke cikin na juna. A lokaci guda dukkaninsu zuciyarsu ta buga da karfin, da basu san zuciyoyin nasu nada irin karfin ba. "Wacece ke?'" Hajiya ummu salma ta fadi out of control , wani abu taji a zuciyarta gami da yarinyar,.Almuqri'ah tabi Hajiya ummu salma da ido, da tayi mgna se taji zuciyarta ta buga da karfi fin a farko, voice dinta yayi kama da makusancinta amma ta rasa fahimtar wanene wannan din?" Kaf kallo ya dawo kan Hajiya ummusalma da Almuqri'ah , kama daga masu neman temako har zuwa kan securities duk suka tsuro musu ido. "Dan Allah wacece ke?'' Hajiya ummusalma ta kara tambaya hadi da dafe saitin zuciyarta sbda bugun da take mata kmr zata fashe, ta sauke idanuwanta a kan cikin jikin Almuqri'ah, hk kawai taji wani abu na fisgasta gami da cikin jikin nata. Wani irin murd'awa marar Almuqri'ah tayi ta cije, still kwayoyin idanuwanta na kan hajiya ummusalma, wadda sak kamanninta kema Almuqri'ah kama da wani data sani amma sam ta rasa tunano waneneshi wannan din. Hannu Hajiya ummusalma ta kai ta shafi cikin Almuqri'ah ba tare data sanma tayi hakan ba, Almuqri'ah ta zabura ta kalli matar, yadda ta shafar mata ciki sak haka Abdoljalal ke shafar mata ciki. "Dan Allah ki gayamin wacece ke?'' Hajiya ummusalma ta sale fadi a gigice, data shafi cikin Almuqri'ah se hankalinta ya kara gushewa, ta kasa dauke hannunta a kan cikin Almuqri'ah, ma'aikatanta da kaf da jakadiyarta suka matso kusa kusa,, mamaki ne ya rufesu musammanma jakadiyarta, nam take zuciyarta ta ayyana akwai wata a kasa. Wani irin ciwon mara ne ya turnike Almuqri'ah wanda ya wuce a daure masa nan ta durkushe kasan kafafuwanta hadi da cije lefe. Nan take hajiya ummusalma ta fahimci nakuda ce,, nan take ta gigice, tasa dreva ya dakko mota, ta umurci jakadiya data tayata suka kamo Almuqri'ah zuwa cikin gidan, da kyar take daga kafafuwanta, se azabar zufa kawai take karyo mata, suka dauketa da temakon sauran ma'aikatan aka sata a bayan mota, hajiya ummu salma ta shiga bayan motar ta jawota jikinta, ta kurawa cikin jikin yarinyar data rairaye yayi kasa sosai ido, ita kadai tasan me takeji a kan cikinnan na jikin yarinyar. "Kai yi sauri kaja motar muje asibiti..." Cewar hajiya ummu salma, datayi mgnr da dreva dinta, jakadiyya ta juyo ta zubo ma Almuqri'ah ido wadda keta faman yarfe hannu tana cije baki idanuwanta a kulle suke gam,, jakadiya ta kalli ummusalma taga cikin jikin yarinyar kawai take kallo, wani irin karatune a kan fuskar hajiya ummusalmar me wuyar karantuwa, nan take jakadiya ta shiga thinking din wacece wannan yarinyar ?'' Hajiya ummusalma tasaba temakon mata da dama, tanada tsananin imani