← Book details Wata Kishiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 107

Sashe 106

Wata Kishiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

datayi karaya, dr ya mata transfer zuwa asibitin mahaukata, ya kira motar asibitin suka dauketa zuwa can asibitin mahaukatan, sede doctor ya gayawa wadanda suka kawota inda zasuje su sameta. Suna airport ,suka shiga jirgi, cikin hikimar ubangiji jirginsu ya lula sama zuwa yola. Haka kawai jalalu kejinsa a farin ciki mara misaltuwa. Sefa hkri da typing error. Allah yasa mugama lafiya paid book ne 08101626484. Cikin cikon ubangiji suka isa yola,. Abdoljalal da Ahamad suka sakko daga cikin jirgin, abdoljalal ya kalli ahamad yace "Waze daukemu zuwa gida?'' Ahamad yace "A, sir na kira waziri isma'il na gaya mishi gamu a hanya ya turo a daukemu gasu nan ma sun iso..." Ahamad ya karasa mgnrsa hadi da nuna inda motoci guda biyu sukayi packing. Suka karasa ga motocin suka shiga suka nufa gidansu Abdoljalal se numfashi kawai jalalu yake saukewa, yana mamakin kansa wai yau shine zeje gidan iyayansa da kansa, ada baya tunaninma ze gane gidan iyayen nasa se yau yaji sun dawo zuciyarsa sabbi fil,yana tsananin san iyayensa amma besan meyasa ya banzatar dasu ba ada,. Suka isa gidan dreva yayi packing ya fito, ya shiga bin gidan da kallo kmr bakon duniya. ma'aikatan gidan seda sukayi da gaske suka gane Abdoljalal ne sbda lalacewar da yayi,ya kasa takawa daga inda ya fito daga motar, maaikatan gidan suka shiga karasowa suna zubewa hadi da kwasar gaisuwa, Amsawa abdoljalal yakeyi yana me binsu da ido... Tini labari ya isarma hajiya Salma wadda ke zaune a falonta bayanta goye da dan Almuqri'ah mesunan me martaba wanda akece masa nor, se macen wanda akecewa Aflah datake hannunta. Mamaki ya rufe ummusalma da labarin da jakadiya ta kawo mata na Abdoljalal yau a gidan. Kasa daurewa tayi ya karaso ta fito zuwa inda yake still Norr na bayanta Aflah na hannunta, ta nufo inda Abdoljalal yake gadan gadan. Tin daga nesa taga ya lalace ya rame tamkar bashi ba kawai seta fashe da kuka, Abdoljalal shima yana ganinta ya fasheda matsanancin kuka yana mebin yarinyar hannunta da ita da kallo, besan meyasa ba yana ganin yarinyar yaji gabansa ya yanke ya fadi. Karasawa yayi ya rungume Ummihnsa yana kuka tana kuka jakadiya ta amshi yarinyar hannun ummusalma da norr dake bayanta.. Sosai jalalu ya rungumeta jikinsa yana kuka me tsuma zuciyar me saurare, kaf maaikatan gidan suka zagayesu suma duk suna kuka, banda Almuqri'ah wadda batasanma me akeyi ba tanacan part dinta tana fama da Isma'il da Abdoljalal yau rigima suketayi mata, da ita da nanny dinsu se fama sukeyi dasu. "Alhamdulillahi yau jalaluna yadawo gareni ubangini ya Amsa Adduarh ta...ya ilahi na gode maka..."ummusalma ta fadi still tana kuka,,yayinda me martaba ya karaso inda suke shima yanzu labari ya taddashi har part dinsa, ya zubo musu ido bayanta. Shima ya fasheda kuka ganin lalacewar da Abdoljalal yayi, ya karaso ya rungumesu su duka da jalalun da ummusalma, ya rungumesu sosai shima martaba yana hawaye.... Seda sukayi 30mnt a haka kana suka dunguma zuwa part din me-martaba hajiya salma ta kasa raba jikinta dana Abdoljalal, shima hakan, yau farin ciki mara misaltuwa iyalan ne martaba suke ciki. "Meya sameka babana dukka lalace haka?'' Ummusalma ta fadi cikin damuwa da zallar soyayyar danta. Abdoljalal ya fashe da kuka sosai hadi da zamewa kasa ya shiga rokon mahaifiyarsa da mahaifinsa yafiya, nan kaf duk sukace sun yafe masa. Ya kara fashewa da kuka sosai ya shiga gayawa iyayensa irin kaddarar da yake ciki ,da duk abubuwan daya wakana tsakaninsu da isma'il da dr mus'ab, duk haduwarsu Da Almuqri'ah seda ya fadima iyayensa komi be boye musu ba. Me martaba yaji dadin hakan sosai, ummusalma ma taji dadin hakan, suka dinga sawa isma'il da mus'ab da Ahamad da nurse mami, and kande albarka domin jalalu be boye musu komi ba, sunji ddh sosai domin dasa hannunsu ne da kuma temakon Adduarh jalalunsu ya dawo garesu yanzu sede suyi fatan Allah ya bayyana matar Abdoljalal din. Me martaba ya kira jsma'il ya masa godiya harda kuka, kana ya kira Mus'ab ya masa godiya yama ahamad dake kusa dashi godiya sosai tamkar ze tsugunna masa, har nurse mami seda me martaba ya amshi lambarta ya kirata da kansa ya mata godiya nan take ya mata kyautar manyan kudaden data fita a talauci na har abadan. Me martaba ya saje kiran mus'ab yace yanzu yanada bukatar Ammah taxo yola ta zauna dasu.. Mus'ab yace toh..nan take yase mata jirgi ya kawota kasar yola dmn tini mys'ab ya sanar da ita ba a ga Almuqri'ah ba sbda beda choice fole seda ya gaya mata ammah tashiga dmwa sosai amma ta dauki kaddara. Ammah ta iso duk suka taru a falon me martaba anata jajantawa juna, se yanzu Abdoljalal yaga Ammah ya miko gaisuwa cikin girmamawa.... Nan de suka shagala a murna har tare suna tareda juna, se 12:am suka rabu, Ammah ta nufa part dinta da ummusalma ta ware mata akwai komi na bukatuwa a ciki. se girmamawa hajiya Ammah akeyi wato fatima tako ina. Duk abunnan da akeyi Almuqri'ah bata sani ba, seda jakadiya tazo ta shaida mata itama tashiga murna sosai, domin tasan labarin dan Ummihn a gurin ummihn ta sanar da ita komi.... Jalalu yayi kwanan farin ciki a ranar , yasamu ya danci wani abun yau sbda Ammah data matsa masa sosai. yanzu dmwarsa daya Almuqri'ah da cikinsa. Seda saude tayi 1week asibitin mahauka anata zabga mata Allurori , kana aka gane ba mahaukaciya bace aka batta ta koma gidanta. Tana cike da haushin hajiya Abulle sbda ta kirata yafi sau goma amma sam taki xuwa tasa a fitar da ita daga asibitin mahaukatan. Saude dukta lalace ta zabge , amma bata daddaraba taci gaba da neman maganin tsafin dazata kara mallake Abdoljalal, taje wani guri akace seta bada jinin mahaifitarta ba bata lokaci tace ta bada itade burinta ta kara malleke Abdoljalal,, . washegarin rabar da saude taje gun bokan ta bada mahaifiyar aka kirata akace uwarta ta rasu, saude ko hawaye batayi ba itade burinta Abdoljalal yadawo gareta ta rama wulakancin dayayi mata. Tini hajiya saude ta fahimci wacece Abulle yanzu, ta fahimci ashe munafukartace, ta fahimci duk wani plan da Abulle aka hada aka cuceta, bokanta da kansa ya gaya mata sbda ta babe musu da Abulle bata bashi kudin aikinsa ba. Saude tayi kuka kmr ranta ze fita daga jikinta nan take ta zage bokan tass ta uwa ta uba, kana ta dawo taje gidan Abulle ta dinga zaginta sukayima juna tonon asiri a ti-ti har tsirara saude da Abulle sukayi suna fad'a a ti-tin Allah ta'alah. Washegarin dasukayi fad'an mijin Abulle ya saketa saki uku, sbda fadannan da tone tonen dasukayi duk yana nan yaji komi, ya kwace kaf dukiyarsa dake gurin Abulke, dole Abulle takoma gheton gidansu bata tsinanawa iyayenta komi ba datanada kudi,, Abulle tashiga tashin hankali kara misaltuwa ta dauki aniyar ko zata mutu seta zama ajalin saude, kisan rai takeso ta mata, sbda ta rabata da mijinta kuma ta rabata da kudadenta da kayan jikinta kawai ta fita a gidan Alhaji. Saude kuwa taci gaba dabin bokaye kan kace kwabo kaf kudadenta sun kare bata da komi , shagunantama da gwala gwalenta dukta sayar tabawa bokaye kuma ba biyan bukata,, saude ta zama tamkar mahaukaciya ga wata uwar rama tayi, wanda yasanta adama bazece itace yanzu ba, babban bala'in gashi gabanta nata fidda wasu irin manyan tsutsotsi.... Saude tazama mahaukaciya tuburan ganin hakan yasa sojojin dake aiki a gidan suka sata a daki suka kulle, sbda wari takeyi kuma gashi tsirara take yawo ko ansa mata kaya seta cire, se zonawa kanta asiri kawai takeyi , haukan nata ma mara kyau na dariya, duk abubuwan data yima Abdoljalal se tonawa kanta asiri takeyi tana ihu tana dariya. A haka kande tazo ta ganta ta dinga salatittuka, dmn tazo gun Almuqri'ah ne domin ta rasa wayarta Kuma tayi jinya ne bataji dadih ba kwata kwata, ganin ba kowa a gidan yasa kande juyawa ta koma inda ta fito tana mamakin lalacewar da saude tayi. "Duk abinda ka shuka wlhi shi zaka girba, yanzu tin a duniya hakki ke tambayarka base ka mutuba...kadanma kk gani saude..." Cewar kande da hakan ya tsananin mata dadih. "Karahen tika tiki tikkk,,yanzu meye ribarki kinzo a zero zaki koma a zero,, ya Allah ka rabamu da tabewa, duk wanda yazo duniya ya mutu yashiga wuta yayi asara babba, sbda Allah ya gama mana sitira, inma ta yaye mu muka yayewa kanmu .." Kande ta kuma fadi tana kuka, tana tausayawa kanta, itama nan data tuba wuyace tasata tuba, domin HIV saurayinta ya kwaso yasa mata, bata saniba seda ciwon yaci jikinta yanzu haka magani kawai taketa amsa tanasha shine ta fara gane ganta. "Yola** Kusan satinsa daya yau a garin yola ba karamin kulawa ummih ke basa ba, sam basu hadu da Almuqri'ah ba, hidimar yaranta tasha mata kai, sbda zazzabi sukeyi again, ummih ce tace ta bari ta natsa kana sesu hadu da d'an nata su gaisa. Wani irin so Abdoljalal kema yaran , kullum yanzu suna hannunsa Abdoljalal da isma'il sbda sune masu yar lafiya,,, sosai ya kamu da sansu sosai, ummih ta bashi labarin yadda suka hadu da Almuqri'ah yana tsananin bukatuwa dason yaga mahaifiyar yaran, shima da kansa yaga kamanninsa da yaran ya baci, 4tyms yana tambayar ummih yanaso yaga uwar yaran se tace masa gobe tace masa jibi, . yau ya gaji dan haka ya matsa ma ummih ta Masa jagora zuwa part din Almuqri'ah tin daga bakin kofa yaji gabansa na faduwa. Suna shigowa ya ganta zaune a falo hannunta rike da Aflah yana ganinta ya zaro ido yana fadin "Ummih itace..." Almuqri'ah ma dagowar dazatawa kanta taga Abdoljalal ne, zumbur ta mike tana nunasa tace "Jalalu..." Nan take ummih tashiga rudu. "Kunsan juna ne .." Cewar ummib da mamaki ya kulle mata kai. Ba tareda Abdoljalal yace komi ba ya karasa ya rungume Almuqri'ah yana godiya ga ubangiji. "Ummih itace fa matata ce ....wlhi itace ummih bakinta ya bude , Alhamdulillahi..." Abdoljalal keta fadi a gigice,yayinda yadda tace masa jalalu yashiga amsa kuwwa a cikin kunnuwansa zakin muryarsa ya wuce tunanin ne kwratu. Ummih tashiga farin ciki mara misaltuwa ta dingawa ubangiji godiya domin ta fahimci komi, nan itama tashiga ma ubangiji godiya da
Chapter 106 · 0% Book details