Sashe 105
Wata Kishiya Complete Hausa Novel · about 8 min read
masa ido,cikin zallar mamaki, yaga yanayin dabe saba ganinsa a ciki ba a kan fuskarsa, kallon bnza kawai yake binsa dashi da kallan kaskanci. "Maciyin amana kawai.." Jalalu ya fadi hadi da karaso ya cukumo wuyan dr mus'ab ya dago takaddar dake hannunsa ya nunawa dr din,dr ya kalli takaddar, nan take ya tuna da Sadda ya rubutata da hannunsa yasata a tsakiyar sadakin Almuqri'ah. "Asirinka ya tonu maciyin amana kawai,,ace dakai za a hada baki anaso a cuceni ..mugu azzalumi,seda na fara zafafa a soyayyar yarinyar kuma seku hada baki kasata ta gudun min da ciki...wallahi ka gaya mata ta dawomin da cikina ko yau -yau dinnan insa a rufeka,, mugu azzalumi ni na daukeka da zuciya daya ashe kai ba hakan bane azzalumi mugu makiri, aniyarka ta sharri seta bika, nayi nadamar saninka a rayuwata, wlhi da zuciya data nake zaune dakai ashe kai akasin hakan ne..." Ya karashe mgnrsa hadi da fashewa da kukan takaici da zallar bakin ciki, wato besan da makiyinsa yake zaune ba se yau. Dr mus'ab ya bishi da ido cikin zallar dmwa da tashin hankali, yadda abdoljalal ke jefo masa kalamannan cin amana ba karamin dmwa ya jefa dr a ciki ba amma sede yamasa uzuri sbda rashin sani ne ke dawainiya dashi wanda yafi dare duhu. "Maciyin amana, Azzalumi insha Allahu se ubangiji yayi kaca-kaca da rayuwarka, kuma wlhi wlhi in baka fito min da yarinyarnan ba, kun bani ciki na ba, wlhi se nayi sharaarh dakai in zanyi yawo tsirara sena wulakantaka mugu azzalumi kawai..." Abdoljalal ya fadi still yana kukan bakin ciki. dr ya bude baki domin yama jalalu bayani amma yaki bashi daman hakan gashi ya shakure masa wuya sosai, yana kokarin ya kwace amma sam ya gaza sbda karfinma ba daya ba, kalan yadin ba kalan zaren bane, koda goma ta lalace dole ne tafi biyar albarka, zaki zaki koda kuwa gawarsa ce, in namin daji duka gani se hantar cikinsu ta kad'a. Jalalu ya dinga ma Dr maganganu masu zafi ya hanashi mgna kana a karshe ya fice ya bar falon nasa, byn ya kankara masa warning din in har gobe be fito masa da Almuqri'ah ba an bashi cikinsa ba wlhi sede Kawai dr yaji sammaci. Yashiga mota ahamad daketa kallansa yynda yaketa huci,ahamad ya kara tabbatar da babu lafiya. Yaja motar suka fice a gidan, har suka isa gida jalalu na kukan bakin cikin abinda dr ya masa. Ahamad nayin packing jalalu ya fito a daddafe yana mejin jiri ya nufa dakin Almuqri'ah yana shiga yaga dr zaune a gefen bed din Almuqri'ah ,abdoljalal na fita a gidansa shima ya hayo mota ya nufo gidan nasa cikin gudu, shiyasa ya rigasu karasowa gidan. "Dan Allah ka saurare ni frnd pls, wlhi bazan iya cin amanarka ba, duk inda naga wanda zeci amanarka ko ze cuceka wlhi se inda karfina ya kare, har raina zan iya badawa a kanka jalalu, kai mutum ne kmr yadda mahaifinka yake mutum pls ka saurareni..." Dr ya fadi yana kuka shima yayinda idanuwansa sukayi ja-ja-jawur kmr gauta be taba shiga tashij hnkli irin na yau ba. "Baka da abinda zaka gayamin.." Jalalu ya fadi shima yana kara kwallah kmr ze haukace yakeji, duniya ta masa zafi, ya zauna kasan dakin ya dafe kansa da hannayensa yana kuka fin tunanin me karatu kmr karamin yaro... Dr ya dinga masa magiya kan ya tsaya ya sauraresa,,da kyar jalalu ya yadda ya tsaya ya saurari me Dr zece masa.dr ya leka ya kira ahamad suka dawo dakin tare, kana dr ya fara zayyanowa jalalu labarin komi daga farko hatta labarin su Almuqri'ah da ammah (fatima) ta bashi be boyewa jalalu ba, ya kira isma'il a waya, domin shida ahamad ne shedarsa se nurse mami a duniya. Jalalu ya kara fashewa da kuka amma na farin ciki. "Ashe da Aure a tsakanina da Almuqri'ah,,gaskiya kai aboki ne na amana, kai abokine da babu irinsa a yanzu , ka gamamin komi mus'ab..." Jalalu ya fadi yana kuka hadi da nadamar maganganun daya gayawa mus'ab,ya rungume mus'ab din a jikinsa sosai, dukkaninsu suka fashe da kukan soyayyar junansu. Abdoljalal yadingama dr godiya mara iyaka, ya dinga rungumarsa kmr ze maidasa ciki seda Ahamad ya koka shima, baya tunanin a duniya akwai mutane irin dr mys'ab a halin yanzu, abokan yanzu duk munafukai,kai inka samu me sanka duniya ka riga dakai saarh, me sanka daya yafi makiyi dubban dubbai, (Ya ilahi dan Annabi SAW ka barni da hubb har abadan Abidina Amin ya ilahi) Ranar nan gidan dr ya kwana yanata kara bawa jalalu labarin komi yadda ya gudana. Abdoljalal yaji kmr ansashi a aljannah yaji ddh daya zamana Akwai aure a tsakaninsa da Almuqri'ah, dayasan cewa an biya mishi sadaki ai da bugun dazema durinta seyafi haka,,abdoljalal ya dingama dr mus'ab da isma"il da ahamad godiya dasa Albarka mara iyaka, a duniya byn iyayensa beda kmr mys'ab da Isma'il da ahamad, da hajiya kande ma, shi kadai yasan meze nusu na Alkhairi, Amma fa adduarsa garesu bazata yanke ba. Adduarhsu daya yanzu Allah ya bayyana Almuqri'ah. *Adamawa yola* Yau kimanin watanta biyu da kwana goma a gidan hajiya Ummusalma, ba karamin kulawa suke bata ita da yayantaba, yaran sun Fara wayau sosai zuwa yanzu, kasancewar duk sunada girman jiki gasu yan lukataye gwanin ban sha'awah, yara hudu reras lafiyayyu, kamannin yaran maza da Abdoljalal ya kara fitowa rass, sannan itama macen kamanninta da ummusalma ya kara fitowa sosai, a kullum yaran na gurin me martaba da ummusalma suke jigilar yaran,yaran dun zame musu farin ciki sun wanye musu kewar jalalu dake ransu, har ummusalma tayi yar kiba sbda zuwan yaran gidan. Yau ta kasance juma'ah ce, ta tashi sallar asubahi taji wani abu ya fita a jikinta da tsananin karfin tsiya, tayi wata iriyar atishawa, ta duba gabas ta duba yamma bataga kowa ba a dakin, daman yaranta badasu take kwana ba a gun ummusalma suke kwana dame martaba. Ta nufa bandaki a tsorace, ta kara kiba tayi bul-bul da ita tayi fresh ainun ummusalma na bata kulawa ta musamman tako ina ta kara cika, duk wata gaba ta jikinta ta bude ta kara kyau surarta ta kara bayyana kmr zata fashe. Tashiga bandaki tana brush, brush din yazo faduwa a hannunta zuwa kasa, tace subhanallahi, mamaki ya cikata jin subhanallahin datace ya fito ba gargada, ta kara fsdi kusan 7tyms, nan take taji alamar bakinta yakoma dai-dai yanzu ita ba bebiya bace, ta rasa ina zatasa rayuwarta dan farin ciki, a guje ta fice a toilet din, ta dice a bangaren nata yayinda tsoro da firgici suka rufeta, ta nufa pat din su me martaba, tana shiga ta taddasu har daki suna sallah, yaranta kuma nata bacci a gadansu. Su me martaba suka idar da sallar shida ummusalma, ta dago ta kalleta cikin tsoro tasha wani abin be yasameta,. Nan Almuqri'ah ta bude baki tayi magana, kaf suk farin ciki ya rufesu suka dinga godiya ga mahalli. Nan Almuqri'ah ta zube tayi sujjadar godiya ga Allah , bata taba tsammanin bakinta ze bude ba, ai rnr baki har baka dan murna, ga muryarta me azabar zakin tsiya. Mommy ummusalma ranar sadakar datayi dabance, Almuqri'ah kam wuni tayi tana ibada ta godiya ga ubangijin sammai da kasai. *Kaduna* Yau kimanin watansa daya da sanin labarin komi nasa da Almuqri'ah,. Tinda ya tashi yau yaji iyayensa kawai yakeson gani sbda su masa adduarh ya fita a matsifar nan da yake ciki, tayuma ko fushin rashinsa garesu ne ke dawainiya dashi. Dan haka da wuri ya shirya yasaka jallabiyarsa, ya kira ahamad yace yase musu jirgi zuwa adamawa yola. Ahamad yashiga mamaki mara misaltuwa hadi dajin dadih kuma, domin ba a mamaki da ikon Allah komi yayi farko zeyi karshe. Ba bata lokaci yase musu jirgi zuwa adamawa yola. Abdoljalal ya fito ze shiga mota saude ta fito ta watsa masa wani banzan kallo ta amso asirinta boka ya tabbatar mata da zuwa yanxu jalalunta ya koma yadda takesonshi. "Maci amana, dan iska mazinaci, zanga ai yanzu nida kai waye ze bar gidannan,, seka tsugunna ka rokeni gafarar cin amanata dakayi kana zakaci gaba da zama a gidannan.." Cewar saude datake tunanin jalalun da ne. Daman Abdoljalal yana ciki da haushinta yanzu duk yabi ya tsaneta sbda sanadinta ne Almuqri'ah ta bar gidan, shi a halin yanzu beda abarda ya tsana kamar hajiya saude, ya rasa ma meyasa tashigo masa rayuwa a matsayin mata, shide yasan bashi ya aureta da hayyacinsa ba. "Ke ni kk zagi..." Ya fadi a hasale, kawai ya rufeta da duka harda nauyi a bainar nasi, ya danneta ya dinga nauyi tana kukan neman agaji, ahamad na gani yaki dakatar dashi,sbda shima yana ciki da haushinta se ci masa mutumci takeyi kullum sbda ta koresa yaki tafiya. Securities na kallo amma basu iya su hana ba, .... Seda ahamad yaga jalalu na niyar kashe saude dan har ihunma gagar yinsa tayi kana ya kira wasu daga securities suka dagashi a kanta da kyar, ya barta a sume ya shiga mota yanata bambamin matsifa yana durawa sauden ashar, yace ta bar masa gidansa karya bari yadawo yasameta. Ahamad yace securities su zuba mata ruwa inta farfado s u gaya mata sakon oga in kuma bata farfado ba su kaita asibiti. Yashiga mota ya bar saude nan yashe da rabe-raben nonuwanta na guguna, duk tabi ta zabge kibar asarar nan yanzu babu se uban baki datayi, domin yanzu maima yadena amsarta, hatta da gawayin girki yafita kyaun gani da harke. Ahamad yaja mota suka fice a gidan zuwa Airport. Securities suka zubawa saude ruwa ta farfado da kyar byn an antaya mata robar bottles water guda ashirin da tara. Data farfado ta kasa tashi ko ina a jikinta karaya ce ga uban jini nata zuba a goshinta, , ta daku iya dakuwa a gun jalalu. Securities suka kwashi saude daketa kuka tana kiran ohhh yesuuu,,,!! Tana ihu irin na radhin tawakkali , securities suka nufa asibiti da ita. Suna kaita aka amsheta a zaton doctor din daya dubata ma Assident ne, se tambayarta yakeyi babbar mota xe tifa ta bigeta,,,saude ta dinga dura masa ashar,,, dr yaja baki yayi shiru a zatonta ko ta bugu ne a kwakwalwa, dan haka aka mata dauri tako ina