← Book details Wata Kishiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 107

Sashe 25

Wata Kishiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

sannan se turaren jiki dozing daya, se panties dozing daya da pad din always itama dozing daya, se takalmi slifas irin na yan hudu guda biyu. A ka'ida abubuwan da AAsaraki yace a bawa ko wacce me aiki yafi haka amma ita Sauden ce ke bada san ranta sauran abubuwan tayita ajiyarasu saboda mugun hali da bakar zuciya kuma babu abinda zatayi dasu, har atamfofi guda ashirin ashirin ya dace a dinga bawa ko wacce me aiki in aka kawota gidan amma ina ita gimbiyar yan wadannan abubuwan kadai take bada izinin a bayar. Bayan larai ta gama nunawa yarinyar komi ta bata sabulu daya a cikin dozing biyun sabulun da aka bata da soson wanka tace taje tayi wanka, sauran kayayyakin ta kwashe tasa mata a Waldrop din. Yarinyar ta isa bakin kofar bathroom din se kuma ta dawo ta bude Waldrop dim da Larai ta ajiye kayayyakin ta dauki brush da Colgate din, ta zuge jakarta ta dauki dan zanin dazata daura in tayi wankan, kana ta nufa bandakin larai na kallonta a zuciyarta tace "Dagani yarinyarnan zatayi tsafta..." Mikewa laran tayi ta isa bakin kofar toilet din tace "Kiyi hanzari ki gama..." Yarinyar ta taba kofar alamar taji, larai ta fice a dakin tana mamakin yadda har zuwa lokacin yarinyar bata mata magana ba. Zama larai tayi a bakin kofar dakin tana me jirn fitowar yarinyar daman ta fito daga dakinne danta bata guri intayi wankan ta samu dmr kimtsawa....seda larai ta farajin motsi alamar yarinyar ta fito harma ze isa ta shirya kana ta shigo dakin, tasameta tsaf tana sanye da doguwar rigar material A-shape material din ya amsheta kwarai da Aniya, kasancewar color dinsa,Army green ne irin dark dinnan sosai me adon flowers light green ba karamin amsarta kalar yayiba, abinka da farin mutum kalarsa komi akasa mata kyau yake mata, se kamshin turarrukan da aka bata takeyi. Larai ta zubo mata ido kyar kirjinnan nata cike luntsum-luntsum da nonuwa tsayayyu wanda hatta da kan nonuwan duk ana gani kasancewar rigar taso ta dan kamata, dukda rigar taji jiki ammafa ta mata tsananin kyau. Kasancewar kanta ba dankwali hakan ya bawa larai damar ganin cukurkudadd'en sumar kanta wadda ta zubo mata har gadon bayanta zuwa duwawuknta mnya-manyannan wadanda suma suka cika rigar dake jikinta. "ya subhanallahi!'' larai ta fadi a bayyane yayin data karaso ta shafo sumar kn yarinyar matsalar gashin ba gyara, a farko larai tasha gashin doki ne seda ta taba ta tabbatar da gashin yarinyar ne, mamaki ya rufeta ta rike baki tana salallami hadi da salatuttuka "La'ilaha ilallahu ni Larai , oh muna ganin indian a TV yau ga Indian har gida Allah ya kawo mana ita..." Jin abinda larai tace yasa Yarinyar yin murmushi hadi da mikewa tsaye ta dukunkune sumar kan nata ta dauresa larai na tsaye tana kallonta se doko salallami takeyi hadi da hailala wasu tayisu completely wasu kuma ina, daman bata iya ba dan bashan inuwan Mkrntar allo tayi ba sbda kauyensu kauyene na karau, burin iyayensu in suka haifa yara mata sukai 10yrs su musu aure sam iyayen yara basa nemawa yaranasu cigaba dukda akwai makarantun gwabnati a garin, da isilamiyoyi amma sam su yan garin basa zuwa da Anga yarinya ma tana zuwa boko shikenan za a hau gulma ace tazama yar iska me bin maza(Allah ya rabamu da jahilci wanda yafi hauka wuyar magani) "ke yarnan ya sunanki ne dan Allah? Amma daga indian kikazo ko?'' Larai dake tsaye ta zubo ma yarinyar wadannan tambayoyin masu cike da sambatu hadi da dimauta, itafa tinda uwarta ta haifota bata taba ganin farar fata bama face to face kamar wannan yarinyar ba se yau shiyasa ta dimauce iya dimauta. Yarinyar data juyo ta kalli Larai ta sakar mata murmushi hadi da kokarin bude baki ta fara magana cikin karyewar harshe hade da bebanta, se a lokacin matar ta fuskanci ashe bebiya ce, wani irin ruwan maliyar tausayin yarinyar ne yayi tsalle ya wanke ma larai zuciyarta nan da nan se taji madarar tausayin yarinyar ya wanke mata makoshi, kawai se taji idanuwanta na cikowa da ruwan hawaye, ta girgiza kai hadi dacewa ''Oh duk wannan halittar da ubangiji ya zuba, ga baya ga tudu biyu luntsum-luntsum, ga madubi me kyau, mace iya mace, kaya iya kaya , Amma Allah ya tauyeta ta hanyar magana Allah sarki!'' Cewar larai murya cikeda tausayi, nan da nan hawayen tausayi hadi da imani suka wankewa laran fuska yarinyar takai hannu ta share mata hawayen sbda duk tanajin me laran ke cewa, hijjabin larai ta dauko ta bata black color cikin sabbin hijjabs din da aka bata, tasaka hijjabin yaxo mata har zuwa kasan kafafuwanta, sosai hijjabin ya amsheta ya mata kyau ainu. ganin time na tafiya yasasu ficewa a dakin, suka nufa kiching, da kiching din da dakin nata ba nisa ita dakinta ba kusa yake da dakunan masu Aiki ba, an wareshi ne daban kuma yafi ko wanni dakunan masu aiki kyau a ciki. Suna isa kiching din nan yarinyar ta saki ido tana kallon ikon Allah da zallar dukiyar da aka zubawa kiching din gashi wani irin fadede dashi danse mutum talatin su tsaya a cikinsa ba tare daya cika ba, an zuba komi na bukatuwa a kiching din, duk kayan furniture din kiching din dark green ne hkn ya kara daukar hankalinta a kyaun kiching din. Larai ta shiga nunna mata komi da komi, kama daga kn kiching har zuwa kan store da dakin da kulolin da ake zubawa gogan abinci suke, dakine guda wanda ke cike da manyan kuloli na Alfarma bawai na kananun alfarma ba guys i mean alfarma wadda ta amsa sunanta alfarma ba muna Alfarma ba Alaji, kyaun kulolin ya ratsa yarinyar tin a nan ta lura komi de na mutumin nan is perfect and nice, hakan ya bata tabbacin shi din special guy ne. A gaggauce larai ta fiddo mata da macaroni da kifinsa busashe da kayayyakin vegetables da komi dazata bukata har tagama fiddo mata da komi yarinyar idanuwanta na kan wasu kwalebaninndake cike da kayayyakin spaces irin wadanda ta saba gani tin a kasar ta, sede tayi mamakin ganin larai bata bata dasu ba. "Yawwa ba asa masa gishi a abinci knji kou?'' Cewar larai yarinyar ta daga mata kai alamar Eh, daman ita de larai ba gane maganar bebaye takeyi ba shiyasa tanaso ta tambayeta abubuwa da dama amma ta hadiye, kasancewar tambayar data mata a dakima data fara mata magana gaza gane me take nufi tayi, dan haka ta hakura ta hadiye tambayoyinta ta barwa cikinta Amma fa jikinta na bata yarinyar nan special ce ba local ba. Larai na gefe tana kallon yarinyar ta fara ayyuknta cikin natsuwa hadi da sassarfa hkn ya bata damar gano yarinyar nada zafin nama, a natse take aiki amma kuma saurin aiki ne da ita. Larai na kallon yarinyar ta hada komi ta daura a kn gass hadi da kunna fan din dake saman gass din wadda ke zuke kamshin tiririn abinci ta yadda kamshin baze taba fita waje ba. Larai tayi mamakin yadda komi da yarinyar ke amfani dashi a kiching din cikin kwarewa take amfani dasu, dagani de komi ba sabo bane a gareta, larai na gani ta isa ta dakko wadannan glasses bottle din robobin spaces din daba me amfani dasu se ita da aka kawo yau-yau, har laraba ta gama ayyukanta a gidan na tsawon shekaru bata taba amfani da wadannan spaces din ba, amma duk bayan wata daya za a zubar dasu asa wasu a nan gurin, se yau rana daya taga yarinyar ta dakko duka kwale banin spaces din ta bude hadi da duba rubutun kasan ko wanne, ta diba ta zuba kala biyar a girkin guda uku kuma a cikin farfesun busashen kifin, larai na kallonta bata dakatar da ita ba, tana gani ta bude frij ta dauko wani abu a cikin ledarda ta kamfani shima duk kayan vegetables ne, amma laran bata taba ganin anyi amfani dashi ba se yau, yarinyar ta wankesa tasa a cikin farfesun kifin, azabar kamshi ya kara rikirkid'a larai, se hadiyar miyau takeyi kwat-kwat. Yarinyar ta gama girkin tsaf cikin kwarewa, larai jiki na rawa tazo ta diba kowanne taci nan ta kara jinjinawa yarinyar domin bata taba cin abinci me dadin wannanba. Larai ta nunnuna ma yarinyar kulolin daza tasa farfesun da dafadukan macaroni. Yarinyar tazuba komi cikin tsari, kana ta hada masa Apple joice ta zuba a cikin hadadden jug dinsa me kama da danyan gold, larai de na tsaye tana kallon ikon Allah yarinyar ta gama komi ta hada a kn kayataccen trea hadi da plates da spon da de komi daza' abukata, ta hada masa, suka nufa side din nasa ta kofar baya, knocking sukayi a falon sukaji shiru dan haka suka shiga falon bakin larai dauke da sallama ba kowa a falon se azabar kamshi da sanyin dake aiki a falon, saboda tsabar sanyin dake falon kai kace inka taka kasa ruwa ne ze bulbulo. Kamshin falon daya daki yarinyar seda ta lumshe idanuwanta tana mejin wata iriyar nutsuwa na ratsata hadi da kwanciyar hnkli seda ta sauke ajiyar zuciya tana me bin falon da ido tsarin kujerun falon da shape dinsu hadi da color dinsu ya bala'in burgeta ga wasu kananun throw pillows milk a kn kujerun tsarin komi na falon is perfect ita nan yafi mata kyau a kn falon hajiya saude. Dinning room suka nufa inda aka killacesa da wani irin glass me duhun golden color, an masa zanen mnyan flowers milk color, suna isa bakin glass din ya bude se gasu a wata duniya me tsananin kyau hadi da tsari! Dinning table dinsa and chair's sun hadu iya haduwa, kalarsu milk ne masu ratsin golden , ga wani hadadden golden din carpet daya mamaye gun dinning din me tsananin kyau hadi da laushi. kujerun zaman dinning din kujeru ne guda biyu, wadanda sukaji laualshi iya laushi. ta cikin nanma akwai wani dining room din shii na zaman mutane dayawa ne sbda in case in yayi baki. tako ina a dining room din cike yake da flowers masu launika iri daban daban se uban kamshi na Alfarma flowers din ke fitarwa, ko ina de acan-acan kmr aljannarh duniya. ajiye
Chapter 25 · 0% Book details