← Book details Wata Kishiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 107

Sashe 21

Wata Kishiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

uban kowa yasan sirrinsa dake boye tin tini, dan hk ya koma ya zauna hadi da basarwa danma Allah yasoshi basu san kn zancen ba yan uwan aikin nasa sundeji kande na masa tsawa. Kande tayi kwafa kawai taci gaba da tafiya yarinyar na biye da ita a baya, har suka isa kiching din ma'aikatan na nan inda ta barsu sukayi mamakin ganin dawowarta, ta kara binsu ta wankesu da zagi tass-tass, kana suka nufa cikin falon hajiya saude, a falon suka tadda hajiya sauden zaune ta daura kafa daya kan daya table din gabanta cike da kayan marmari na motsa baki. "Barka da hutawa ranki ya dade..." Hajiya kande ta fadi murya cike da maula. A takaice saude ta amsa da "yawwah...ku karaso..." Ta musu iso zuwa gabanta. Suka karaso suka zazzauna a kasan carpet din, kallo daya yarinyar tama hajiya saude tayi kasa da knta haka kawai taji kiyayyar matar a zuciyarta tin sadda ta daura idanuwanta a kan picture din matar. Hajiya saude ido tabi yarinyar dashi still se take tajin bugun zuciya amma ta dage tunawa datayi da maganganun hajiya Abulle itama da knta tasan ko tsirara mijinta zega mace baze taba ko kallontaba, dan tasan kishi ne kesata jin bugun zuciya a kn yarinyar. "Toh hajjaju gamunan mun dawo..." Cewar kande ganin saude ta tasasu a gaba ba tare datace komi ba. Hajiya saude takai apple bakinta ta gutsira ta jijjiga kafarta dake kan daya cikin isa kana ta fara magana. "Zan dauki yarinyarnan kafin de zuwa ki samar min wata, nan bada jimawa ba..." Kande tace "toh hajjaju..." Hajiya saude taci gaba da magana "Amma sede akwai sharruddan dazan kafa mata ai kince tana jin magana kou?'' Kande tahi wankan tsarki tayi carab ta amshe da "Eh tanajinki hajjaju gimbiyar mata..." Hajiya saude ta kara gyara zama tana fuskantar yarinyar cikin kallon tsana hadi da bakin cikin kyaun da Allah ya tara ma yarinyar. tace "Ke kina jina Kou?'' Yarinyar ta dago ta kalli hajiya Saude hadi da daga mata kai alamar ehh. Hajiya sauden taci gaba da magana "Zaki dinga dafawa mijina abinci ai kn iya girki sosai kin iya farfesun busashen kifi hkou?'' Yarinyar ta daga mata kai alamar eh. Saude tayi jimm idanuwanta na kn yarinyar tunani takeyi ta ina za ayi aiki da bebiya wadda bata magana sekace de duk duniya an rasa masu aiki, ita da gogan ze Amince dame aikin kamfani ma aka daukar masa wadda ta iya girki sosai ba wadannan locals din ba, amma ina shi locals din yakeso. dan guntun tsuki taja kana taci gaba da magana idanuwanta na kan yarinyar "Kin iya karatu da rubutu na hausa?" Yarinyar ta daga mata kai alamar ehh hajiya saude ta dawo da dubanta kan kande tace "Wai haka ta iya karatu da rubutu? Ko karyarsu ce dasuka saba dan masu aikinnan duk makarya tane'' Kande ta amshe da "Kwarai ma kuwa hajiya...ai tayi makaranta fa ta gwabnati irin ta bebaye tayi makaranta sosai nan har rubutu da karatun turancin dana hausa kakarta tace ta sosai, tafa gama sacandari, sannan uwa uba tayi karatun Allo saukarta biyu na alqur'ani ne girma, bakin talauci nefa yasata fitowa aikinnan hajiya,..." Cewar kande data kara da fadi ba a tambayekaba. Hajiya saude tace "okay to abin zezo da sauki tinda ta iya karatu da rubutu,,, za a baki komi na abinda zaki dinga dafawa mijina a rubuce kama daga kan abinda zeci dasafe zuwa kan abinda zeci da rana da daddare da time din da ake ajiye masa komi da komi a kn dinning, ki tabbatar da kinyi komi in time banasan abinda ze batawa mijina rai sannan becin gishiri a abinci duk de za a baki a rubuce ki tabbatar kinyi komi a kn ka'ida kinajina kou?" Yarinyar ta daga mata kai alamar Toh.. Hajiya saude dake kallonta har zuwa lokacin kiyayyar yarinyar nata yawaita a zuciyarta, taci gaba da magana "Ka'idojina sune na farko karki kuskura wata magana ta shiga tsakaninki da mijina bayan gaisuwa, kin ganni nan dago ki kalleni da kyau!'' Yarinyar ta dago ta kalleta hajiya saude ta nuna knta da yatsanta hadi daci gaba da mana "Kin ganni ko banda mutumci inde a kan mijinane babu irin abinda bazan iya aikatawa ba a kan mijina, dan wallahi har kisan kai zan iyayi a kan mijina..." Yarinyar ta kure hajiya saude da ido sosai zuciyarta cike da firgici yayin da idanuwanta suka bayyana abinda ke zuciyarta wato tsoro da firgici. Hajiya saude ta daga mata kai alamar tabbatarwa. Hajiya kande ma seda ta firgita dajin furucin hajiya sauden batasha halin nata ya wice inda take tunani ba se yau. Saude taci gaba da magana cikin isa " banda kirki a kan mijina amma in kika kiyayemin mijina zakiyi aikinki ba ruwana dake saboda bani kikewa aiki ba mijina kike yimawa sede a karkashina kike, amma ko haduwa ba kullum zamu dinga yiba, sede kullum a ka'ida se duk ma'aikata sunzo sun gaisheni dasafe da daddare, kinji ni da kyau kou?'' Yarinyar dake kallonta da saurarenta ta daga mata kai alamar "eh.." Har zuwa lokacin firgici da razana basu barta ba. Hajiya saude ta kara ballar apple din dake hannunta tana masa wata iriyar tauna ta rashin mutumci a cikin bakinta kana taci gaba da magana. "Sannan Kullum ki kasance cikin tsafta, duk sanda zaki shiga kiching yima mijina girki ki tabbatar dakinyi wanka kinga sau uku zaki dinga wanka a rana kenan kou?'' Yarinyar ta daga mata kai alamar eh. Hajiya saude ta mata wani kallon dayasa yarinyar yin kasa da knta ganin zallar rashin mutumci a cikin kwayar idonta. "Banasan kiyi kwalliya ko kadan a wannan fuskar taki, kullum ki kasance cikin hijjabi dare da rana da safiya, ki dinga sa hijjabi har kasa kinadasu ko a tsiyace kikazo kema?'' Yarinyar ta dago ta kalleta zata girgiza kai hajiya kande tayi saurin cewa "Ai a tsiyacen tazo hajjaju sede in a bata hijjaban ade temaka kmr yadda aka saba..." Saude ta taba baki tace "Okay zansa laraba ta bata, sannan za a nuna mata dakinta na kwana,..ki kara ja mata kunne a kan mijina kafin ni na mata babban jan kulle, Dan banda mutumci hanyarma da mutumci yabi ni ban bi ba, karta kuskura ta dinga jimawa a side din mijina, inta kai masa abinci fita zatayi inya gama zuwa kmr 3h se taje ta kwashe komi ta gyara inda ya bata domin besan kazanta haka itama ta tabbatar da tana tsaftace knta, tanasa turare kwalliya ce kadai baza tayi ba, sannan a dinga brush dan bamusan kazanta nida mijinnawa,, in bnda ma kaddara dashi abinda yakeso megidan ai wannan yafi karfin ta dafa masa abinci.. " saude ta karashe maganar tana yatsina fuska. Hajiya kande ta amshe da "Dama mana hajiya yo Allah na tuba Ai mijinki babban mutum ne yau ko yan indian yakeso su dafa masa abinci ai ze samu, Allah na tuba kudi nefa tako ina Allah ya baku.." Saude ta yamutsa fuska tace "kundeji sharuddana kou?" Kande ta amsa "Anji ranki ya dade kuma dole abi ko ince anbi ma tini..." Hajiya saude tace "Yafi de...ynzu ku tashi kuje side din masu aiki kice larai tazo inasan ganinta dan dole wannan dund'um din seda waya sbda ta nan za a dinga mata messages din abinda zata dingama mijin nawa..." Kande ta karbe da "Dundum ma haka take wannan ai tafi dundum..." Saude ta yatsina fuska kana tace " nan zaki kwana ke kande ?'' Hajiya kande tace "Aah hajiya tafiya zanyi me napep ma na can yana jirana..." Saude tace "Okay ba dmwa ku tafi ki turomin laran de inajin yau yarinyar zata fara Aikinta mugani ya nata hannun yake..." Kande da tini suka mike tsaye ita da yarinyar ta kara amshewa da "Dama mana ta fara hajiya to meye amfaninta ai daman aikin tazoyi ba hutu ba, hutu aise ku dakukaci kuka tara..." Hajiya kande ta fadi zuciya cike da rashin imani. Saude ta tabe baki hadi da lalubar Aljihunta ta lalubo kudi yan dubu dubu kusan dubu talatin ta mikawa kande, kande ta tsugunna ta amshe jiki na rawa ta shiga antayo mata godiya ruwa ruwa, hajiya saude bata bi ta kanta ba tace "Sannan kudin aikin yarinyar nawa za a bata?'' Kande da bakinta yaki rufuwa saboda farin cikin kudin da saude ta bata tace "toh hajiya a bata abinda kikaga ya dace..." Hajiya saude tace "Okay...ya sunan yarinyar ne?" Kande tayi jim tace kai na mnta sunanta da wahala gaskiya. Saude ta daga kafada irin ko a jikintannan daman ita ko tasan sunanta ba amfani ze mata ba dan sunan duk ma'aikatanta daya ne a gunta Wato Ke\kai. Hjya Kande ta karama hjya saude godiya kana suka fice a falon, ta kai yarinyar gun sauran masu aikin nan wajen kiching sannan ta gayawa larai hajiya saude nason ganinta cikin hanzari larai ta tafi amsa kiran madam dinta. kande ta tafi cikin murnar abinda take bukata ya tafi dai-dai ko tace abinda aka sata,se hamdala takeyi a zuciyarta tana tafe tana waiwayon yarinyar , haka kawai kuma taji zuciyarta na cike da tausayin yarinyar, bata taba kawo me aiki taji tausayintaba kmr yadda taji tausayin wannan yarinyar har zuwa kasan zuciyarta, a hk ta fice a gidan zuciya cike da murna data fito tasha bazataga me napep din ba se kuma akaci sa'ah taga be tafi ba ashe yana nan yana jiranta hakuri ta bashi na barinsa datayi yanata jiranta, bakomai yace yana me jiran fitowar yarinyar danshi sbda ita ya tsaya jira da baze ma jirataba a wannan uban dadewar datayi, ganin hajiya kande ta shiga bega yarinyar ta fito ba. yasashi tambayar ina dayar dasuke tare. Hajiya kande tace " daman ai aiki na kawo ta tana cikin gidannan..." "Allah sarki..." Cewar me napep din, a zahirin gaskiya Sam me napep din ba haka yaso ba, yaso ya sake ganin yarinyar haka kawai yakejin san yarinyar na ratsashi. Wayarta dake cikin jaka ta dauko tayi dealing wata number wadda bata da suna se J kawai aka rubuta a kn sunan, hajiya kande tayi dealing number din bugu daya aka dauki wayar, hajiya kande tace "wasikarnan a gayawa me aikenta ta isa inda akeso ta isa
Chapter 21 · 0% Book details