← Book details Wata Kishiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 107

Sashe 4

Wata Kishiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abdoljalal bata period shiyasa bazata taba haihuwa ba, da jinin jikinta Aljanu ke Amfani ana mata tsafi dashi a kan Abdoljalal ita sam rashin haihuwar baya wani damunta abinda take nema kaf babu wanda bata samu ba a rayuwarta ta duniya, ba kasar da basujeba ita da Abdoljalal duk wata kasa dake fadin duniya sunjeta ita dashi, sannan itama data bushi iska take tafiyarta ita da kawarta hajiya Abulle wadda suka hadu a kaduna tin farkon Auranta da Abdoljalal itama yar hannushi wato zani ce ta tadda muje se hali yazo daya ake abota, duk sun tare ko ina sun hana mazajansu kara Aure bayan ba komi suke iya musu ba, hasalima duk basu iya daukar dawainiyar Mazajan nasu na Auratayya, zallar hutu kawai suka iya, musammanma ita Saudat,Bahaushen mutum yace dan talaka be iya samun guri ba, to hakanne ya kasance da saudat da Abdoljalal tayi kane kane ta rabashi da iyayensa. 7yrs da Auran Abdoljalal da Hajiya chef madam Saudat iyayen Abdoljalal sukaga shirun yayi yawa ba haihuwa su kuma babban burinsu be wuce suga jikokinsu ba. Dan haka suka daurawa Abdoljalal Aure da wata yarinya yar mutumci yar gidan dattako Aysha wadda batafi 24yrs ba, kwata kwata me martaba be nemi shawara da Abdoljalal ba kawai ya masa Auren ne danya isa,ya kirasa yace yana nemansa ya hanzarta zuwa yanason ganinsa, a ranar ya isa yolar shima saboda Saudat bata sani bane, data sani dabe isa yaje ba saboda ita ke hanasa zuwa ga iyayensa daman, shi kuma ko kara tasa masa be iya ketarawa ko ganinta yayi se gabansa yayita faduwa shiyasa in ya tafi abuja se yayi 3month ma be dawoba saboda kawai be buktr ko jin duminta kusa dashi, amma beda yadda zeyi, gashi be iya rabuwa da ita koda ze mutu, kuma be sha'awar wata diya mace inba ita ba, sam ma matan duniya baya ganinsu mata se ita kadai yanzu ba siririya doguwa ba ko wace mace ze gani kallon Arziki be mata duk ko musulkinta ko kyaunta, infect ma be ganin mata a mata kwata kwata a idanuwansa ganinsu yakeyi kmr maza..Koda Abdoljalal ya isa Yola me martaba Abdullahi ya masa naseeha Ainun a kn Auran daya masa ba tare da saninsa ba, seda gaban abdoljalal ya fadi jin abinda me martaba ya fadi, shi matsalarsa saudat amma dabadan ita ba shi yana bukatar auren a zuciyarta saboda yaba cike da bukatuwa da da mace, uwa uba kuma yanason d'a saboda shekarunsa kullum tafiya sukeyi dole yana bukatar yaga kwansa ko daya ne, Amma sam be sha'awar ko wacce mace se ita kadai. Yaso yama me martaba musu kan besan Auran Amma sede ba fuskar yin hakan me martaba ya bishi da ido duk ya koma kmr wata mace, shida dansa ya taso da jajircewa cikakken namijine Amma yanzu ya koma kmr wata mace ko magana ma be cika yiba, koda damanshi bame yawan magana bane, to abin ya ninku ya zama kamar wani kurma in yana tare da mus'ab ne kawai yake bude baki yayi magana shima bawai wata magana sosaiba hirar kasuwanci kawai sukeyi se kuma jefi jefi suna hirar mus'ab a kan matansa shi mata biyu ne dashi, da yaransa shida maza hudu mata biyu., shi kam Abdoljalal be iya cewa komi a kan tasa matar, dukda yanada abubuwan fadi dayawa amma be iyawa, yanada damuwa da ita Amma be iya fayyacewa kowa tsakaninsa da Saudat, sede ya barwa Allahnsa kawai, danmashi ma'abocin ibada ne, shiyasa wasu abubuwan Allah ke sassauta masa, dan ba haka akaso ganinsa ba, koda yake Shide asiri gaskiyar meshine. A ranar Abdoljalal ya koma kaduna ko amaryar be tsayama yaga kalartaba, jiki a sanyaye ya isa gida saboda me martaba yace masa washe gari Amarya zata tare a gidansa. Abdoljalal ya gaza gayawa Hajiya saudat rnr beyi bacci ba sbda fargaba. Washe gari saudat taga anata shigowa da kaya ana guda ayiriiiriii!!, ta shiga tashin hnkli fin tunanin me tunani, dukda a lokacin tasha ko batan kai yan kawo amaryar sukayi amma seda hnklinta ya tashi , bata tabbatarba seda da aka kawo mata amarya gunta Aka musu natsiha ta tabbatar da dagaskene Mijinta Aure yayi, ta kalli Aysha kyakyawace Sosai a ranta tayi murmushi mugunta, A zuciyarta tace "da Kinsan wacece ni dako za a Kasheki bazaki shigo gidan Aurenaba..." A ranar Saudat gidan bokanta ta kwana dake garin sakkwato daman a nan matsafin nata yake, wanda suke tare tin sadda Abdoljalal ke nemanta har zuwa yanzu. A ranar Amarya Aysha bata kwana gidanba kwacewa tayi ta fita tsakar dare wuraren 2:am ta balle tabi duniya ta haukace hauka tuburan, Abdoljalal ya shiga tashin hnkli me tsanani, haka iyayen Aysharma suka shiga, me martaba yafi kowa shiga tashin hankali, danma mahaifinta dame martaba sunada fahimtar juna daba karamin dauki ba dadih za ayi ba, seda akayi 1yrs ana rokon Allah kana akaga Aysha a can birnin sinnn wato china, me martaba yasa Abdoljalal ya aiko mata da takaddarta ta saki, dan abin ya girgiza me Martaba Ainun, ranar da Aka ganta ranar Abdoljalal ya Aiko mata takaddarta saki uku rerass. Wannan kadanne daga Aikin hajiya Saudat a kn mijinta ba wanda bazata iya kaudawa ba in har ze kawo mata cikas koda kuwa uwarda ta haifeta ne Saudat inde a kn kudine ba abinda bazata iya ba, zaman kudi takeyi da Abdoljalal dan ita be mata wani amfani a halin yanzu se kuma sanshi dake ranta, ba karamar sheke aya takeyiba da wannan bokan nata ko ince tantirin matsafi, Jinnu su cita, shima yacita ga uban kudi tana bashi ga kuma cinta yanayi tin tini har zuwa rana me kamar ta yau, ita kuwa burinta biyan bukatarta, inde a kan bukatarta ne a kn Abdoljalal ba abinda bazata iya ba kaf zuciyarta ta bushe rakayau, ba alamar imani a zuciyarta. Tindaga Auran Abdoljalal da Aysha, saudat ta kara nisanta Abdoljalal da iyayensa tazara me nisa, sam be zuwa inda suke sede su in sunada bukatar ganinsa suzo su gansa a office dinsa ko suje Abuja su ganshi, dukda manyantarsu Amma sam basa gazawa gun zuwa ganinsa musammanma mahaifiyarsa wadda ta kwallafawa ranta shi daya tall, sam bata gazawa gun masa adduarh kullum cikin ma dannata Addarh take , iyayen Abdoljalal suna fatan Dansu ya dawo da hankalinsa kansu kafin su koma ga ubangijinsu, sam Iyayen Abdoljalal basa zargin Saudat a kan lamarin Abdoljalal din saboda sun san girman lefin zato a musulunci sede kawai sun fawwalawa Allah lamarinsu suna fatan ya jibancesu Ya kawo karshen wannan lamarin. A bangaren Saudat bata taba takawa taje gun iyayen nasa ba, tin farko har zuwa yanzu dasukeda 20yrs dayin Aure ita da Abdoljalal hidimar gabanta kawai takeyi tana fantamawa da kudinsa yadda taso. taci tasha ta cika fam ta kara zama wargatsetse da ita a fari ba haka take ba dukda daman de tin can bata da shape me kyau, data samu guri taci dadih wahalar datasha ta duniya ta goge ta kara rusa wata kiba mara asali, bata da wata matsala, ta riga ta gama sakin jiki tasamu duniya 100% yadda takesonta, shiyasa bata da fargaba duk inda Abdoljalal ze shiga, dukda hnklinta be kwanciya inde yana abuja tana kaduna amma inta tuna irin Tsafin dake dawainiya dashi seta sassautawa knta bakin kishinsa da damuwa, ta riga ta tabbatar da ko mace be iya kalla a wannan sihirin dake binsa duk inda yake. *Back to story* Bayan ta gama wannan tunanin ta sheke da wata iriyar dariya ta nishadi, ta lunshe ido sau biyu a lokaci guda, ta kara Beading A kan kujerar lukutar fuskarta na fidda dariyar nishadi. ''Bade mutum ba...nikadai ce mata daya tal a gurin Alhaji Abdoljalal Saraki..." Ta fadi tana kara shekewa da dariya kmr wadda akawa bushara da Jannatul-firdausi. "Hmmm nasamu duniya wai nice kuwa mary ada..." Ta kara fadi tana bin kaf jikinta da kallo se nishadinta ya yawaita ta fiddo harshenta waje ta lashi saman lips dinta ta kuma cizasa a lokaci guda tace "Hajiya Saudat Mrs Saraki!" Ta fadi tana jijjiga kafafuwa cikin takama da zallar isa hadi da dumbin kasaita, tafi karfin 20mnt a zaune tana nishadi kana ta mike ta Nufa dining Area se uban girgiza takeyi tana juya plat bom-bom dinta. Ta isa ga dinning din ta jawo daya daga kujerun dining din ta zauna tana karewa warmers din dake can table din kusan guda goma, daman ita a ka idarta abinci kala goma sha ake mata nasafe batacin na rana domin se 2:pm ko after 2 dinma take cin abincin safe, sena dare datakeci wuraren 12:am ake sauke mata shi a dining ko 1mnt masu Aikin abincin nata suka kara ranar se an musu wulaknci na innalillahi kuma a hada musu da korar innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!. Wani malatsi ta danna a kn dining din nan da nan wani shirgegen katon igala ya fado a falon daga kiching , shine kukunta, sanye yake da uniform dinsu na ma'aikatan gidan kalar launin blue black. Zubewa yayi kasa ya fara kwararo mata gaisuwa cikin harshen turanci kai kace ze mata sujjada dan tsanar zallar ladabi da biyayya,..ko samun damar amsashi batai ba daman beyi tsammanin hakan daga garetaba, mikewa yayi ya fara gudanar da abinda ya kawosa wato yayi serving dinta dan ita ko cokali bata iya matsoshi gabanta saboda tsabar lalaci da samun guridan duk wanda kaji yace baze iya abu ba wallahi bata kamashi bane. Serving dinta yayi da tuwan Alabo miyar kubewa busashiya wanda yaci uban gandoji, tana kaunar Tuwan Alabo domin shine best food dinta saboda dashi ta ginu duk rnr duniya seta cishi, kafin ta kwanta bacci take fadin abubuwan dazataci da safe da daddare gata da shegen ci kmr gara, duk irin abubuwan dadih datake ci har yanzu cikinta be cunkushe ba, sbda ita din horon yunwa, shiyasa ynzu data samu abinci ba dama. Seda ta gama cinye tuwan alaban malmala biyar duk ma'aikacin nata na tsaye daman inde za ayi serving dinta tsayawa akeyi harse ta gama sannan a tafi. Byn ta gama ya kara zuba mata farfesun naman kai, nanma ta cinyeshi tass ya kara zuba mata farfesun naman Sa nanma ta cinyeshi tass, ya kara zuba mata farfesun naman rago nanma ta lamusheshi tass ga kunun
Chapter 4 · 0% Book details