← Book details Wata Kishiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 107

Sashe 102

Wata Kishiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

Se yanzu t take nadamar daukar yarinyar aiki a gidanta sauba adadi. Lalubo wayar hajiya Abulle tayi, ta kirata bugu biyu ta daga, saude ta fasheda wani irin kuka kmr ranta ze fita. "Hajiya jalalu ya cuceni..." Saude ta fadi yynda kmr ranta ze fita. Abulle taji wani farin ciki ya rufeta ruf, dukda batasan meya faru ba a bayya ne abulle tace "Meke faruwa hajjaju?'' Cikin muryar dmwa a zahiri. Nan saude ta kwashe labarin komi ta shaidawa Hajiya Abulle,. Nan farin ciki ya lullube abulle a zuciya tace "Komi ka shuka aishi zaka girba...Allah ya ninka miki bala'i..." abulle ta fadi a ranta, amma a zahiri tashiga jimami mara misaltuwa."kai wannan Abu ya tsananin dagamin hankali hajjaju,,,innalillahi wa'inna ilaihirraju'un! Shin yanzu yaza muyi? Ina boka yake har hakan ya faru...kai wlhi har zazzabi ya rufeni hajiya wannan bala'i dame yayi kama..." Cewar Abulle, da iya harshe tayi maganar. Saude ta kara rushewa da kuka tace "Wlhi bansan mani ta ina zan bullowa wannan matsifar ba Abulle, ji nakeyi daman mutuwata nagani da wannan tashin hankalin, yanzu haka gani a hanyar zuwa gun boka ..." "Okay karki damu kawata ki kwantarda hankalinki, tinda ma zakije gun boka ai magana ta kare...yanzu wai ina ita yarinyar?''cewar Abulle. Saude ta kara jin wani bakin ciki kmr ze kasheta , ta tsani yarinyar nan , bata taba tsanar wata halitta ba kamar yadda ta tsani yarinyar nan ba. "Kamar ta gudu a gidan yarinyar ,,, haka Abdoljalal ya nunamin,,, wlhi Abulle wannan lamarin yamin shigar bazata ko a mafarki ban taba tsammanin hakan ba, ji nakeyi kmr na kashe Abdoljalal dinma kowa ya huta....." Abulle tace "aah karki kasheshi ai shine ke din, yanzu de ki karasa gun boka muji yadda zata kaya..gobe zan dawo nima, wannan tashin hnkli ai dole in dawo..." Saude tace toh, daga hk sukayi sallahma ta ajiye wayar, yayinda kunci be bar ranta ba, data tuna Almuqri'ah se taji gabaki daya ta tsani kanta,. Se tsakar dare suka isa garin sakwato. Dreva ya ajiyeta a bakin wani daji, dmn yasaba kawota. Hajiya saude ta daba tafiya a kafa, ko tsoron dajin bataji, abinda ya tinkarota yafi komi ban tsoro a rayuwarta, babban tashin hankalinta ace wai yau itace Abdoljalal ke kora a gidansa saboda wata can banza yar aiki, ita ko a banza bata dauki Almuqri'ah ba. Seda tayi tafiyar 1h a dajin kana ta isa inda bokan yake, ta fashe da kuka, kmr mahaukaciya, ta shaidawa boka abinda ke faruwa a gidanta tass, tana kuka. Ta tuhumu bokan dayasan halin da take ciki, boka yace aah sam domin asirin da Almuqri'ah tama Abdoljalal me karfi ne, kosu basu san faruwar hakan ba. Saude ta sauke ajiyar zuciyar tashin hankali tace "Ka temakeni boka Wlhi ji nakeyi kmr zan haukace...so nakeyi kawai a kashe yarinyar da d'an cikinta, sannan a dawomin da hnklin mijina kaina,, boka karkayi wasa da Aikinnan nawa ina cikin tashin hnkli, yau waini Abdoljalal ke kora a gidansa a kn wannan karamar tsinanniyar yarinyar, sbda ta mishi asiri tasa yaci gindinta ya gigice,,,..." Saude ta karashe tana me kara fashewa da kuka. Boka ya kwashe da dariyarsu ta marasa imani kana ya fara mgna yayinda dajin ke amsawa. "Hahahaha...ki iwantarda hankalinki, ai yanzu tinda ta bar gidan to tabbas yanzu zamu kasheta da d'an cikin...hahahaha...ki kwantarda hankalinki, tinda kikace mu din, to tabbas mudin zamuyi miki komi....hahahahaha..." Ya karashe da fashewa da dariya. "A kasheta kisan wulakanci boka,,a dawomin da mijina dai-dai boka...boka kacikamin aikinnan ina cikin dkwa, in har kayimin aikinnan babu abinda bazan iya maka ba,,karka karamin sakaci wannan tashin hankalin yazo gidana, boka,,ni in zeyu ma kaf dangin yarinyar nan a kashesu..." Saude ta fadi cikin rashin imani. Boka ya fasheda dariya, yace "Angama!!!''' Ya kara kyalkyalewa da dariya. nan gun bokan ta kwana yana sukuwa a kanta, se asubahi ta dawo inda ta bar dreva dinta nan ta taddashi, tashiga suka dakko hanyar dawowa kaduna,sam zuciyar saude bata nutsu ba, dukda bokan ya bata tabbacin yau yau dinnan ze kashe Almuqri'ah da abinda ke cikinta. *Adamawa Yola* wani babban private hospital hajiya ummusalma ta umurci dreva dinta ya nufa dasu. Suna isa aka shiga da ita dakin haihuwa cikin gaggawa, ummusalma ta tsaya a wajen dakin tanata zagaye zuciyarta na kan yarinyar, haka kawai takeji a jinin jikinta yarinyar nan akwai wani abu me karfi tsakaninta da ita, ita de kawai taji ta kamu da tsananin san yarinyar da abinda ke cikinta. Kusan 1h suna tsaye bakin kofar dakin haihuwa hajiya salma da jakadiya, amma sukaji shiru, hankalin ummusalma yaki kwanciya se zagaye kawai takeyi a kofar dakin, zuciyarta nata bugawa da tsananin karfi. Awa daya da minti goma sha biyar suka shude kana dr ya fito ya kalli hajiya ummu salma yace ta biyoshi office, ba musu ta bishi ya kalleta ya cire glass din idanuwansa kana ya fara magana cikin harshen turanci. "Hajiya bazata iya haihuwa da kanta ba sede a mata CS din gaggawa..." Nan take ummusalma tace "Inde ba damuwa a mata CS din..." Cikin harshen turanci. Nan dr ya tambayeta wacece dinta? Hajiya salma tayi jim ta rasa yazatace se kuma ta tsinci bakinta dacewa "Ni uwar mijintace..."dr yace okay..ya bata wata takadda tasa hannu,. Dr suka dukufa a kan Almuqri'ah aka mata CS ,ba bata lokaci aka ciro mata yaranta guda hudu uku maza daya mace. Dr ya fito ya samu hajiya salma inda take tsaye sam ta kasa zama jakadiya na zaune. Tana ganin dr ta nuf osa kafin ya karaso inda take. "Ya ake ciki?'' Ta tambayesa cikin harshen turanci, yayinda take cikin tashin hnkli, gabaki daya tunaninta na kan yarinyar da yayan dazata haifa. Dr yayi murmushi kana ya cire face marks din fuskarsa cikin ladabi ya fara mgna cikin harshen nasara "ina tayaki murna ranki ya dade, anyi CS lafiya an samu nasarar ciro mata yara hudu uku maza se mace daya..." Hajiya salma taji wani irin sanyi da ddh sun ratsata a lokaci kankani. "Alhamdulillahi..." Ta fadi hadi da dukawa nan tayi sujjadar godiyar ubangiji, ta dago ta kalli Dr din bakinta har kunne, yayinda tini itama jakadiya ta taso ganin hajiya salma na sujjada. "Ta haihu ta haifa yara hudu uku maza daya mace..."hajiya salma ta fadima jakadiya bakinta kmr gonar audiga..haka kawai itama jakadiya seta tsinci kanta a zallar farin ciki. "Alhamdulillahi Allah ya rayasu dan Annabi SAW..." Duk suka amsa da Amin. Nan take salma tama dr din daya mata albishir dinnan gagarumar kyautar kujeru guda hudu na hajji , se guda hudu na umrah..dr ya dinga dogiya domin musulmi ne, ya dinga godiya kmr ze tsugunna mata. "Aje a siyo kayayyakin jarirai maza na Alfarma..." Ummusalma tayi mgnr da jakadiya fuskarta nata kara fadada da murna da zallar farin ciki, batasan meyasa ta tsinci kanta a farin ciki mara misaltuwa ba. Jakadiya tace angama, ta fice a asibitin domin gudanar da umarnin hajiyarta. Ummsalma ta dawo da dubanta kan dr muhammad tace "Dr a kaini inga babys dinnan dan Allah..." Da turanci tayi mgnr. Dr yace "Angama ranki ya dade .." Suka juya zasu nufa dakin da yaran suke, ganin me martaba ya nufo inda take yasata dakatawa, ya kureta da ido yana me mamakin ganin farin ciki da Annashuwar dazece be taba ganin irinsaba a tattare da ita se yau, tsawon shekaru suna tare. "Waya gaya maka ina asibitin me martaba?'' Ta jefo masa tambayar yayinda bakinta ke a bude dan dariya. Me martaba ya karaso hadi dacewa "Ai duk abinda ya faru a kan idonane,,, matata sarkin temako, tin dazu nake jira inga kun dawo naji shiru shiyasa na kira drevanki ya gayamin inda kuke shine nasa a kawoni..."ummu salma tace "To barka da zuwa..wannan karan temakon da nayi yasani a nishadi mijina, wlhi ji nakeyi kmr anmin bushara da Aljannarh..." Me martaba ma ya shiga annashuwa ganin farin cikinsa a annashuwa yace " ai naga Alama farin cikina meke faruwa?'' Ummusalma ta kara fadada murmushinta tace "Wadda na kawo asibitin CS aka mata ta haifi yan hudu uku maza daya mace,,kaji kyautar Allah ko mijina, muje muga yaran wallahi dukna kagu in gansu,,,dr yimana jagora.." Ta karashe mgnrta da dr muhammad. "Masha Allahu..." Me martaba ya fadi cikin zallar nishadin da shima besan kona menene ba. Dr ya gaidasa Cikin girmamawa domin ya ganeshi. Kana ya musu jagora zuwa dakin da yaran suke kwance a kan wani kyakyawan mayen bed. Hajiya salma da me martaba sukabi fararen yaran da ido yayinda duk yaranma suka idanuwansu a bude yake an killacesu cikin kayan yaran da asibitin kesawa yara in an haifesu, in mace zata haihu a asibitin sam bata bktr zuwa da kaya sede in ita tazo, macen sanye take da peach din kayan jarirai masu azabar kyau an lullube mata kai da hula peach abin lullubintama peach ne ta bude idanuwanta tarr ga idanuwan nata manya manya,,su kuma sauran mazan sanye suke sa kaya sky blue towel din lullubinduma sky blue ne. Me martaba da ummusalma suka tsinci kansu dajin faduwar gaba ne tsanani dasuka daura idanuwansu a kan kyawawan yaran, gani yadda yara mazan suke kama sak da Abdoljalal ya tsananin sasu a wani irin yanayi, dukkaninsu duk sunga kamannin, macen kuma sak kamanninta da hajiya salma, har wani digon baki gareta irin na jikin ummusalma. "Kinga abinda nagani kuwa?'' Me martaba ya dago ya fadi yana kallan salma wadda ko kyaftawa batayi a kallon yaran, ba tare data dago ba tace "meka gani?'' Me martaba yace "Yarannan sak kamar su daya da Abdoljalal mazan, abin mamaki, har idanuwansu da komima irin na Abdoljalal, macen kuma wallahi sak kamanninki ne da ita.." Me martaba ya karashe mgnrsa yana kallan macen yana kallan salma. "Nagani wlhi, yadda mazannan suke sak haka Abdoljalal yake da yana jariri, me martaba kamannin ya baci..." Salma ta fadi tanasa hannu ta dauki yaron namijin guda daya ji takeji kmr yaran jininta ne, tamkar zata maidasu ciki haka takeji. "Allah me iko..." Cewar me martaba shima yasa hannu ya dakko macen da maza biyun duka, ya rungumesu jikinsa, ummusalma ta tsurawa yaran data dauka a hannunta ido, haka kawai taji hawaye na zirya a kan kuncinta itade tasan bana bakin ciki bane na zallar farin cikine.
Chapter 102 · 0% Book details