Sashe 42
Wata Kishiya Complete Hausa Novel · about 8 min read
da dafa masa abincin, dan kar ki bari ya zama lefi,..." Al-muqri'ah ta daga mata kai alamar toh, amma zuciyarta ba ddh, sam bata maji gamsuwa da kalaman laran ba. Larai tayi murmushin shu'umanci kana ta fara magana cikin makirci "Yarnan kede Allah yasa kinzo da farin jini gidannan...har Wani ya ganki yace yana sanki, yasameni yace in gaya miki, a cikin masu gadin canne na kofar get yaje, baki gansa ba kamilalle salihin bawa..." Al-muqri'ah dake jinta, ta hade rai dan ita batason maganar maza, sam bata sakewa da d'ana miji, se Abdoljalal ne kadai take sakewa dashi har take masa murmushi, amma ita maza basa ganin fuska a gunta, komi takeyi tana taka tsantsan da d'ana miji, saboda kakarta ta taba gaya mata in mace ta sake da saurayi namiji in har yasan farjinta, to tabbas duk namijin daze aureta a banza ze dinga ganinta, kuma kakarta ta gaya mata duk maza mayaudara ne, basa sanka seda wata manufa, duk mesanka na Allah baze tunkareka ba, sede ya tunkari magabatanka musammanma ita al-muqri'ah datakeda karancin shekaru. Sannan kafin tazo gidan ma seda hajiya knde ta mata warning kn ba ruwanta da mazan gidan saboda yan iska ne, to ta rike hakan a knta gam, kunsan bebe da rike abu, dan haka ta girgizawa larai kai alamar aah ita bataso. Larai ta fahimci me take nufi da girgiza kan tace "kisoshi ze baki kudi masu yawa seki tafi gida ki dena bautar nan ta wahala..." Al-muqri'ah ta kara fahimtar wato san bana gaskiya bane, dan haka ta girgiza mata kai alamar aah, larai ta fuskanceta, nan take ta gano yarinyar nada wayau , ba irin wawayennan bane, kuma zatayi wuyar kai, balle ma bebaye nada wahalar sha'ani, kuma larai tayi alwashin insha Allahu seta shawo knta dan 50k ba wasa bace a gareta. Yarinyar ta juya ta fara aikinta, taki kara sauraren larai tanaji tana mata mgna duk a kan taso wanda ke sonta dinne, amma taki bi ta kn laran, da larai taga hakan ta fice a kiching din tana fadin "Ko uban waye ke sekin amince da salisu tantiri, in knsan wata baki san wata ba, dubu hansin dinnan bazata wuceni ba a banza a hofi duk bakin cikinta se tantiri yaciki ni kuma se naci 50k..." Tini larai ta gama lissafa abinda zatayi da 50k din da tantiri ze bata in bukatarsa ta biya a kn bebiya. Zuciya ba dadih ta shirya masa abincin rana ta kai dinning din ta fito daga side din jiki ba kwari, tana fitowa taci karo da usman me gyaran side di Abdoljalal. gaidasa tayi, usman ya washe baki hadi da amsawa tini shima ya fahimci bebiya ce sbda suna yawan haduwa shida ita, inta fito side din nasa, usman shine me kula da bangaren gogan duka. Da bebanci ta kuma tambayarshi megidannan ko yayi tafiya ne..." (Dan bata gamsu da abinda larai ta gaya mata ba Kwata-kwata, zuwa yanzu ta kara jin tsoron larai) usman yanada kani bebe, dan haka ya fahimci me take nufi. "Oga na nan a bedroom dinsa me kyau, amma sede beda lafiya jiya da daddare ya kirani na dakko masa drink a frij yasha paracetamol,..." Cewar usman. Al-muqri'ah data zuba masa ido tana saurarensa , daman tanaji a jikinta tabbas ba lafiya Ba, har zuciyarta, taji rashin lafiyar tasa. Allah ya sawake tace da bebanci, kana ta juya ta nufa kiching tana jiran usman ya wuce taje ta dubo gagon dan wallahi zuciyata bazata jure ba, kawai ji tayi so takeyi ta gansa, dan taga a wani hali yake ciki. Zaunawa tayi a kiching din tayi tagumi, kai kace mutuwa aka mata, se hadiyar miyaun damuwa takeyi da tashin hankali, lokaci zuwa lokaci seta tashi ta leka taga usman ya bar kofar side din nasa, amma se taga ma ya shige side din nasa, ta koma ta zauna tana jiran ya fito dan ita ma ta shiga taje ta gansa da jikin nasa, ko zuciyarta zata nutsu ta dena hadiyar yawunnan na zallar damuwa. Tinda usman ya shiga be Fito ba seda akayi magriba duk al-muqri'ah na nan zaune tana jiransa ya fito ko sallar la'asar da magriba a nan kiching din tayita, gani takeyi kamar in zata shiga side dinma usman ze hanata ne,dan kunya takeji ta shigo kuma ta nufa dakin Abban nata alhalin usman na nan, wallahi daba dan haka ba da tini taje ta gansa, dan zuciyarta se azabar zirya takeyi taki zama guri daya. Usman na fitowa daga side din ya nufo kiching din datake, ya sameta tsaye, ya kalleta ya sakar mata murmushi domin shima wai santa yakeyi tin randa ya fara ganinta ya kamu da zallar madarar zumar santa. "Oga yace ki kawo masa abinci dakinsa na sama..." Cewar usman. Seda ta sauke ajiyar zuciya saboda wani irin dadih daya ratsa mata zuciya, Kmr tana jira ya fadi hakan, ta fice a kiching din zuwa side din cikin sauri sauri, usman ya tsaya ya zuba mata ido seda ta shige ya dena ganinta, kana ya wuce hidimar gabansa se murmushi yakeyi a zuciyarsa yace. "Nasamu matar aure..." Danshi bada isknci yake sonta ba da aure yake sonta. Jiki na rawa, ta dauki abincin data kawo masa na rana a kn dinning, dan Tashin hankaki be batta ta dafa wani ba, ta nufa falonsa, direct ta nufa upstairs bata taba hayowa upstairs din nasa ba se yau, bin ko ina takeyi da ido, yayi kyau iya kyau amma tashin hankalin dake zuciyarta be bari ta fahimci kyaunba, tinda usman yace mata beda lafiya bata kara fahimtar jikinta ba har zuwa yanzu. Tsayawa tayi bayan ta gama hayowa saman, taga dakuma kusan hudu biyu na kallon biyu, daki na farko ta nufa nan zuciyarta ta sanar da ita yana ciki sbda a nan tafi jiyo kamshin turarensa. Knocking tayi a hnkli a bakin kofar dakin, cikin sanyin murya yace "Waye? Da bebanci tace masa "Ni ce..." Yayinda duk ta kosa tasata a ido. Jin maganarta tasashi saurin tashi zaune hadi da mata iso, yanajin wani kwari na ziyartarsa daga jiya zuwa yau duk yabi ya rame ainun kmr yayi ciwon 1week, ga ciwo nacinsa kuma yakishan maganin arziki se jiya dayaji wuta iya wuta shine usman ya kira usman ya bashi drink a frij yasha paracetamol. . Turo kofar dakin tayi ta shigo idanuwanta da nasa suka sarke da juna, nan take tausayinsa ya lullube zuciyarta, ta zubo masa ido kmr yadda shima ya zubo mata nasa sexy eyes din, yana mejin wani sanyi daya ganta, nan take 50% din ciwonsa tini duk ya ragu. Ganin yadda ya rame daga jiya zuwa yau yasata jin hawaye sun cika mata ido duk yabi ya chanza dagani yasha wahala,, cikin hanzari ta karaso ta ajiyr trea din a bedside, ta tsugunna ta gaidasa hadi da tambayarsa ya jiki..." Da sauki ya amsa...' idonsa na knta, tini ya hango taruwan kwallah a cikin idanuwan nata. "Tashi ki zauna gefen bed ki zuba min abinci inci.." Ya fadi da muryarsa a ta masu ciwo. Ba musu ta zauna Kn bed din , amma sede taki yadda ta kara kallonsa danta tabbatar inta matsa a kallonsa tana iya fashewa da kuka. Serving dinsa tayi da abinci mara nauyi (dafa dukan taliya wadda taji kayan lambu) da perper fishi din data dafa masa, ya amsa, ya ajiye a kan cinyoyinsa idanuwansa na knta, wallahi ganinta ba kamaramin haifar masa da karfi yayi a jikinsa ba, amma ya narke yace ''ki bani a baki...'' Dagowa tayi ta kallesa ta zaro ido,, dan ita seya koma mata kmr wani baby. ya kara marairaicewa dan gudun kada tace aah yace "Kinga fa banda lafiya tin jiya ban iya komi dan Allah knji yarinyata..." Se tausansa ya kara ratsata, sannan sunan daya kirata dashi na Yarinyata yayi tasiri a ranta. tasowa tayi ta matso kusa dashi ta zauna ta fara basa abinci a bakin, ya amshe, se bin fararen yatsunta yakeyi da ido, yanaji kmr ya kamosu ya hau tsotso, seda yaci abincin ya koshi duk tana bashi a baki yaci sosai, sbda rabonsa da abinci tin shekaran jiya, nan ya danji karfi ya fara zuwan masa, Dan tini yayi rabin warkewa da ganinta, sede fa akwai babbar jinya a zuciyarsa, wadda besan da ita ba. ta miko masa drink a hannunsa, yaki amsa yace shima sede ta bashi a baki, bashi tayi yasha ya koshi, ya koma ya jingina bayansa da fuskar gadon yana kallonta, jinsa yakeyi kmr wani baby yau,. Tashi tayi ta dauki trea din ta masa Allah ya kara sauki, sam beso ta tafi ba amma beda yadda zeyi dan haka yace "Ki kawomin furar rufaida a frij anjima zuwa 10:pm ..." Al-muqri'ah tace toh hadi da ficewa a dakin yabi bayanta da ido, dabadan dauriya ba wallahi da babu abinda ze hanashi rungumarta a dakinnan yau, dan wani abu ke jansa a kn yarinyar., tashi yayi ya dauro alwala domin zuwa lokacin anyi isha'i yayi sallar isha'in ya idar ya koma ya kwanta se kallon agogon dakin yakeyi, duk yabi ya kosa 10:pm tayi ya sake ganinta. 10:pm dai-dai ta iso kofar dakin tayi knocking yace ta shigo dan yasan ita ce, hannunta rike da trea tashigo dakin, ya zubo mata ido a wannan karan kai kace yau yasaba ganinta gaidasa tayi hadi da masa ya jiki ya amsa cikin murnan ganinta,. ta ajiye trea din hannunta a bedside inda ta ajiye na dazu, ta zauna kasan dakin yace "aah banso ki zauna a kasa ki dawo kan bed dina ki zauna..." Ta taso ta dawo gefen bed din ta zauna, tana kallon gefe, kyar ya kurawa gefen face dinta ido, dai-dai saitin dimple dinta yaji kmr yasa mata harshe ya tsotsi gurin amma ya danne, ya rasa meke dibarsa a kn yarinyar, yake irin wadannan tunani tunanin dabe saba irinsu ba.. Da bebanci tace masa yasha furar..." Yace "aah baze sha ba ya koshi amma zesha anjima..." Daman badan yasha furar yace ta kawo masa ba, kawai dan yanaso yayita ganinta ne,, ya zaunar da ita yanata kallo har 12:am kana ya batta ta tafi badan yaso ba, da tunanin rashin lafiyar tasa ta kwana a ranta, tasan yanajin jiki, kawai danta fuskanci yanada