← Book details Wata Kishiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 107

Sashe 88

Wata Kishiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

ba a cikin masu mata bangajiyar za a samu matsala kuma inta gantama matsala ce, domin ta tsaneta Fin kaf ma'aikatan gidan ...jimmalo na zaune tana wadannan Tunani tunani Almuqri'ah ta fito daga dakinta cikin hanzari sanye da rigar material har kasa mara nauyi duk tabi ta jike da zufa sumar knta har diga takeyi da zufa hijjabi ne a hannunta tama kasa tsayawa tasa hijjabin a dakin itade tinda tasamu ya sauka a kn durinta da wuri shikenan ta godewa Allah tayi hamdala, ta fito waje sbda azabar zafin da takeji shi kuma Abdoljalal ya shiga toilet wankan tsarki, dmn hk sukeyi inde yaci ita seta fito waje tasha iskar wajen ta huta, dan batajin ma iskar AC na shigarta itade kawai tafisan iskar waje, A kn ta AC kota fanka . idanuwanta suka sauka a kn jimmalo Wadda itama itan take kallo nan take Almuqri'ah ta gano jimmalo na cikin damuwa. Nan tashiga tambayarta meya sameta hadi da karasawa inda take zaune. Batare da Jimmalo tace komi ba, ta cire hijjabin jikinta ta mikawa muqri'ah sbda yafi girma. Muqri'ah ta amsa fuskarta dauke da ayar tambaya, jimmalo ta amshi hijjabin hannun Almuqri'ah din tasaka, kana ta kalli muqri'ah din tace "kisa hijjabin dana baki, yafi girma nasan ze rufe cikin jikinki yadda baza a gansa ba...zamuje muma hajiya saude barka da zuwa ne tadawo dazu..." Nan take cikin Almuqri'ah ya juya jin abinda jimmalo tace, knta ya dauka, wato motar data gani dazu kenan itace tadawo amma shine ta tambayi Abdoljalal yace ba ita bace, alhalin yasan itace din.. Ganin tashin hankali da firgici hadi da tsoro sun bayyana a kn fuskar muqri'ah yasa jimmalo sassauta nata tashin hankalin tace "Ki kwantarda hankalinki ba abinda ze faru, insha Allahu Allah na tare da bayinsa masu gaskiya, ubangiji baya jarabtar bawa da Abinda yafi karfinsa, tinda kika Allah ya miki jarabar nan, kuma baki cikinnan to tabbas akwai yadda zeyi dake da cikin baki daya ..." Kalaman jimmalo yasa zuciyar muqri'ah sassauta tashin hnklinta, tasan ubangiji shi ze mata sutura kmar yadda yasabawa bayinsa salihai. Tasaka hijjabin da jummalon ta bata, dayake yanada fadi sosai nan ya boye cikin jikinta se kayi da gaske ka gane. Jimmalo ta kalleta byn tasa hijjabin tace "yawwah ki dinga wasa da hannunki a cikin hijjabin ta yadda cikinki ze kara rufuwa, har mu shiga mu fito lafiya, kiyita adduarh, nima zantayi, Allah yasa mu shiga lafiya mu fito lafiya..." Almuqri'ah ta amsa da amin. Suka fara tafiya, Almuqri'ah taji kmr ta koma dakinta taje ta gayawa Abdoljalal se kuma ta fasa, saboda haushinsa ma takeji, yasan matarsa tadawo ta tambayeshi amma yaki gaya mata, sbda ita ba komi bace garesa,.. Suka nufa part din Hajiya saude kowaccensu zuciyarta ta na dukan uku uku, sede sukasa ubangiji gaba, kuma sunsan ya isar musu komi. WATA KISHIYA LITTAFIN KUDI NE 08101626484 *na cire friday da saturday a ranakun hutuna, kawai zanyi hutun 2days a sati Ba rana, zandeyi hutun 2days kawai ngde fans da love* Dai-dai suna isowa alon hajiya saude kaf ma'aikatan mata sun gama mika gaisuwar su, sun fice, kana jimmalo da Almuqri'ah suka sako kai falon . hajiya sauden ma na shirin mikewa ta hau sama ta huta, to ba gajiya ma a jikinta sam sbda a yawon nasu sunyi hutu ita hutu, ita a jirgin natama na dawowa Nigerian hutunta ta dinga yi. Idanuwan Almuqri'ah suka sauka a kn hajiya saude wadda ke tsaye, byn sun shigo falan, nan take Almuqri'ah taji jikinta na neman fara rawa saboda tsoro da firgicin inta gane tanada cikin mijinta yazatayi, nan take tayi controlling kanta gudun tonuwar asirinta, tasan innasirin ya tonu har jimmalo se tasha azaba.nan ta nutsu se wasa takeyi da hannunta a cikin hijjabin jikinta, tayi kasa da knta daga kallan hajiya sauden.tana shigowa falon itama hajiya sauden ta bi Almuqri'ar da ido, Nan take seda gabanta ya yanke ya fadi, taji wani yanayi a zuciyarta tamkar taga abin tsoro, wato do-do, itafa sam tama mance da yarinyar a yan kwanakinnan, koda ma'aikata matan gidan sukaxo suka gaidata sam bata kula ma ba yarinyar ba, amma ta kula babu jimmalo. ta manceta a kwanakinnan sam, a farkon barinta kasar ne ta kwallafawa ranta tunanin yarinyar jefi jefi. Dawowa hajiya saude tayi ta zauna kan kujerar data tashi, sbda jiri taji yana neman kwasarta, idanuwanta sam basu kauce akan almuqri'ah, sam ko kallan jimmalo ma batayi ba. Jimmalo da Almuqri'ah suka zube kasan carpet din falon hajiya saude, jimmalo ta fara gaidata ta amsa, sama sama, jimmalo ta kara da mata ya gajiyar hanya, sam bata amsaba a wannan karan,,,, ,Almuqri'ah ta gaidata sam bata amsa ba, kuma taji bawai bata jiba, idanuwanta na kan Almuqri'ar, kyaun da yarinyar ta kara ya firgitata Ainun. "Wato anzo gidan kudi an kara gogewa ba shakka madallah!..." Hajiya saude ta fadi a bayyane, zuciyarta fal tsoron da batasan kona menene ba, itade kawai tasan mijinta ne ya fado mata rai. Jimmalo da Almuqri'ah suka kalleta datayi mgnr, sukaga tasaki baki tanata kallan Almuqri'ah, kallo daya suka mata suka sauke knsu kasa, zuciyarsu se mugun bugu takeyi dan gani sukeyi asiri ma ya gama tonuwa a yau, musamman ma jimmalo hnklinta yafi na Almuqri'ah tashi, sbda ita tafi Almuqri'ah sanin wacece saude, a duniya komi akace saude ta xata aikata jimmalo zatace ta Aikata ma kawai, saboda Saude ta wuce tunanin duk me tunani, bata dauki ran kowa a bakin komi ba, ranta ne kawai ta daukeshi rai, sena jalalu, shima san bnza take masa, san da yakeda dalilin yinsa (kudi). Sosai hajiya saude ta gigice da ganin k'aruwar kyaun yarinyar ta kuma kyau, kyaun ma na fitina,. "Ba shakka..."saude ta fadi tanajin zuciyarta na harbawa da mugun matsiyacin karfi, ta rasa dalilin hkn, a yau bugawar zuciyarta daban ne a kn ada intaga yarinyar, tini taji kanta ma harya buga ya fara mata ciwo,ta lumshe Chinese eyes dinta ta kara budesu a kn Almuqri'ar wadda tashin hnklin datake ciki kadan ya rage ya taddo yanayin da Saude take ciki. Jimmalo ta taba Almuqri'ah alamar su tashi su fita, sbda kallan da saude kema Almuqri'ah yana tsorata jimmalo, tasan de ko Asiri ya rufu yau dole ne ze bayyana, sbda me fallasa asiri ne a jikin Almuqri'ah (wato ciki dan fallasa) jimmalo da Almuqri'ah suka mike tsaye a tare da niyar barin falan nata jimmalo tace "Allah ya huta gajiya ranki ya dade...." Almuqri'ah de kasa cewa komi tayi sbda dukta kagara su bar part dinma baki daya,jikinta har yana rawa, babyn cikinta ma se harbawa yakeyi da karfi da karfi kmr fad'a, ko a hk tasan bbyn jikinnan nata me lafiya ne. Sam hajiya saude bata amsa jimmalo ba , idanuwanta na kn Almuqri'ah ,haka kawai take ganin wani yanayi a tattare da jikin yarinyar dukta chanza, ita sam ba hk ta ganta ba a farko, yanzu se tagama duk tabi ta chnza yanayin siffa gabaki daya,, fuskarta tayi mata wani iri. Suka juya zasu bar falon cikin sauri musamman Almuqri'ah wadda taketa sauri su fita. "Keeeeeeeeeeeeeeeeeeeeeeeeeee!!!''' Hajiya saude ta fadi cikin daga murya da kaskanci, kai kasha ko mutumin dake wajen falon take kira da kee din. Gabaki dayansu seda hantar cikinsu ta kada, suka tsaya cak daga tafiya. "Shikenan ta gane..." Jimmalo ta fadi a ranta, zuciyarta kmr ta fado kasa sbda bugu. Almuqri'ah kam tini zufa ta karyo mata.."keeeeeeeeeeeeee yar talakawa!!!! Jikar jikokin matsiyata!!!!'' Hajiya saude ta sake fadi a wannan karan cikim tsawa da daga murya.. Sam Almuqri'ah bataji zafinn sunayen da saude ta kirata dasu ba, sema Jikinta ya hau rawa, a razane Almuqri'ar ta juyo sbda tasan da ita hajiya sauden take, jimmalo ta juyo itama a zuciya se Adduarh takeyi kan Allah ya rufa musu Asiri. Hajiya saude ta kalli face din Almuqri'ah cikin kallan wulakanci kana tace "Matsiyaciya kinsamu dadih kinyi qiba kou, har wani tumbi kika ajiye kou? Toh ki kwana ki tashi da shirin kwanan nan zaki barmin gida na, kinji kou?!!'' Cikin tsiwa tayi mgnr. Almuqri'ah ta kara kasa da kanta, yayin da take godewa Allah da hajiya saude bata gano cikin jikintaba. Jimmalo seda ta sauke ajiyar zuciya, a ranta murmushi tayi, bata taba ganin sauna irin saude ba, wato taga cikin amma setasha ko tumbi ne "lallai me hankalin Mutane ke gani,bame hankalin jaki ba..." Jimmalo ta fadi a ranta. "Kinjini ko baki jini ba? Hajiya saude ta fadi da dakawa Almuqri'ah tsawa, hk kawai taji a ranta kmr ma ta tashi ta danne yarinyar ta kasheta a falon kowa ya huta, bata taba tsanar wata halitta kmr yadda ta tsani yarinyar nan ba. Almuqri'ah ta daga mata kai alamar eh taji. "Ku ficemin a falo tsinannu ..." Hajiya saude ta fadi cikin gigitar hnkli hk kawai taji hnklinta ya gushe. Cikin hanzari suka fice a falon, hjya saude ta sauke nishin Ajiyar zuciya hadi dacewa "Inaji a jikina nice Ajalin yarinyar nan saboda na tsaneta wlhi, tsansr daxan iya kasheta inna ci gaba da ganinta a rayuwata..." Hajiya saude ta fadi a ranta, hadi da lumshe idanuwanta, haka kawai taji zuciyarta ta cike da damuwa, sam kuma batasan meye dmwar ba, tadesam ganin yarinyar nan ne ya haifar mata da damuwa. Almuqri'ah da jimmalo suna ficewa a parrt din nata suka ma Allah godiya sbda hajiya saude bata gano cikin ba, sunsan Allah ne kawai ya rufe wannan sirrin, suka iso kofar dakin Almuqri'ah Jimmalo ta kalli Almuqri'ah tace "Mungodewa Allah, muna rokon Allah yaci gaba da rufa mana wannan asirin..." Almuqri'ah ta amsa da amin a zuciyarta tana tunano klmn hajiya saude, datace ta kwana da shirin zata bar gidannan. Sam ita jimmalo bata damu da wadannan kalama na saude ba, sbda tasan abu ne me wuyar gaske a yanzu Almuqri'ah ta bar gidan, sbda Abdoljalal ya riga daya kamu da mummunan dafin da maganinsa na gurin Almuqri'ar,jimmalo tasan sede ayi bala'in daxa ayi amma rabuwar Abdoljalal da Almuqri'ah zeyi whla, sede inda karfin sihiri domin kuwa shi asiri gaskiyane nameshi. "Ki shiga dakinki ki huta da fargabar nan " cewar jimmalo, Almuqri'ah tace toh "Nagode..." Ta cire hijjabin jimmalon ta bata, itama jimmalon ta bata nata, Almuqri'ah ta kara mata godiyar hijjabin da jimmalon ta bata domin shiya
Chapter 88 · 0% Book details