Sashe 9
Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan barina restaurant É—in toilet na wuce na sha kuka sosai ina fitowa kuma akace manager na kirana..tsaye nake gaban shi yanata surfafa min bala'i akan abinda ya faru a restaurant yana magana akan wasu etik and etike (ethics and etiquette) '' taya za'ayi kima customer ir..."
'' uban etik and etike manager...taya za'a yi kafaɗi irin haka? kasan abunda yayi min ne? idan ƙanwarka ce wani ya riƙe mata hannu yana mata maganganun banza zaka ce haka?..." nan nashiga sauke mashi bala'i ta inda nake shiga bata nan nake fita ba,dafe kanshi yayi kafin ya fara bani haƙuri... dan kuka nake kamar raina zai fita ina sheshsheƙa, zaunar dani yayi a ɗaya daga cikin kujerun dake office ɗin shi ya ɗauko ruwa ya miƙa min ya tsuguna gabana yana bani baki...bayan nasha ruwan na ɗan rage sheshsheƙa ya ƙara bani haƙuri sannan yace intafi hotel inyi aiki in bar restaurant ɗin
gyaɗa kaina nayi na miƙe na fara tafiya '' na gode '' na faɗa sannan na iyarda fita, elevator na shiga ya ajiye ni a floor ɗin kitchen.. gani nayi chefs ɗin suna ta kai komo daga gani sauri suke suyi subawa kowa order shi
'' ke zo ki ɗauki wannan abincin ki kai ma room no 207 !" wani daya juyo ya ganni yayi maganar yana nuna min cart ɗin da aka shirya komai ciki.. yatsine fuska nayi kafin na ƙarasa naja cart ɗin na shiga elevator na danna 2nd floor kafin ƙofar ta rufe sai ga Abeed ya shigo yana min murmushin shi mai kyau har saida dimple ɗinsa ya fito tsayawa yayi kusa dani hannunsa ɗauke da wani rufaffen plate
'' yau ba magana name sake?" ƙin kallonshi nayi,yayi yar ƙaramar dariya, wani abu ya zaro daga aljihunshi ya miƙo min,saida na kalli abun dake ɗauke cikin ƙaramar kwalbar nace '' meye shi?" hannuna ya riƙe ya samun a tafi...yace '' sunan shi Usma grass root,ranar naji kina tambayar abinda zai sa gashin mutum ko girar mutum da eyelashes suyi tsawo su ciko da sauran su shine na kawo maki...amma kibi ahankali idan ya shiga ido akwai zafi sosai!" ya ƙarashe maganar yana kashe min ido, juya abun nayi a hannu na kafin na ƙara kallon shi nace '' ina ka samu?"
'' siya nayi " ya bani amsar '' nawa?" na sake tambaya '' dubu sittin!" zaro ido nayi wannan albashi nane na wata uku,kuma shima haka
'' ko baki so?" ya tambaya yana É—age min gira '' girgiza kai na nayi...sai kuma nace '' meyasa zaka kashe kuÉ—i masu yawa don ni bayan kai ma ji da kanka kake?" murmushin gefen baki yayi min wanda bansan ma'anar shiba '' kada ki damu,kedai kiyi amfani dashi kawai!"
'' meyasa kake kulani?" na tambaya hannu naɗe a ƙirji na juyo ina kallon shi,ya shafa ƙeyarshi'' son ki nake!" waro ido nayi da farko sai kuma na fara dariya kamar mahaukaciya harda ɗaura hannu akai...'' bana son wasa... me yasa kake kulani?" nayi tambayar fuska a tsuke, ajiyar zuciya ya sauke ya koma serious yace '' saboda kece the most authentic person Dana taɓa gani a rayuwa ta!" kallon shi nake cikin rashin fahimta bangane me yake nufi da wannan kalmar ba,gane hakan da yayi yasa ya fara min bayani,'' idan akace mutum authentic,ana nufin yana abu da gaske,baya ɓoye ɓoye,baya yin abu dan mutane su gani..da zuciya ɗaya yake abu!" yake juya ido kamar mace
'' Oh..'' na furta ahankali, na faÉ—awa duniyar tunani da gaske ni...mema nene kalmar? aidai kunji Abinda ya faÉ—a ko da gaske ni haka nake? '' keep being yourself,zaki gani wata rana akwai wanda zai soki dan hakan kawai..zai soki a yanda kike batareda ya nemi ki canja wani abu game da kanki ba!"
buÉ—ewar elevator yasa yayi gaba batareda ya sake cewa komai ba,sanin idan na cigaba da tsayuwa elevator zata rufe dani a ciki yasa na fito ina tafiya a hankali ina tura cart É—in da gaske akwai wanda zai soni a yanda nake batareda na zama mai kyau har na fitar hankali ba? naga yanzu mazan sun iskance idan har baki da wa'yannan kyaun zuciya bazai sa su kulaki ba!
Na sauke ido tare da danna ƙaraurawar ɗakin na ɗari biyu da bakwai...da turanci aka amsa '' come in..'' taɓe baki nayi ina faɗin ' yan wulaƙancin ' a raina
tura ƙofar nayi na shiga wani irin daddaɗan ƙamshi na dukar hancina da kuma sanyin Ac, ɗakin yayi min kyau sosai king size bed ne me ɗauke da jan zanen gado kamar wani ɗan tsafi sai dogon benci mai katifa..aidai kun gane shi irin wanda ake ajiye wa gaban gado ko? wanda masu kuɗi tsabar iyayi suke ajiyewa bayan bashida wani amfani
Sai jan carpet me ratsin fari a gaban gadon,daga gefen dama na É—akin idan an shigo TV ne sai wardrobe dake kallon É—ayan bangon daga Tsakiyar É—akin akwai kujera zaman mutum biyu da table a gaba sai labule masu nauyi suma jajaye
painting É—akin kamar fari kamar yellow bansani ba sai toilet...É—akin ya burgeni sosai duk da ba wannan ne karo na farko da nake shiga É—akin hotel ba
wani saurayi ne zaune a saman kujerar daga shi sai ƙaramin wandon da ko rabin cinyarsa bai kai ba,askin kanshi low cut kyakkyawa ne sosai ban taɓa ganin wani me kyau irin nashi ba duk rayuwata fuskar sa ɗauke take da manyan laɓɓa (full lips) hancinsa dogo mai kyau haka ma idanun shi farare masu ɗauke da ƙwaya hazel brown kamar zuma..yana da ƙaton jiki.. '' kutumelesi!" kalmar ta fito daga baki na batareda na shirya ba,amma wannan anyi babban ɗan iska! wane irin iskancine wannan? ji nayi na fara tafasa daga ciki ni kyaun shi bai wani burge Ni ba kokaɗan
gefen wando na na taɓa naji turaren yajina na nan.. gyaɗa kai nayi tsaye daga bakin ƙofa '' ga abincin na kawo'' na faɗa batareda motsawa ba daga inda nake ba... ɗagowa yayi ya kalleni tareda sakar min Murmushi mai kashe zuciya sai dai ni tawa zuciyar bata mutu ba!
ya tashi zaune yana shafa kuncin shi yace '' kece wacce ta cika ma wani baki da yaji ko?!" sai dana harare shi nace '' ko kaima kana so ayi maka fiye da nashi ne?" Naji kamar in share wannan banzan murmushin dake fuskar shi...taya ma ya sani? munafukai masu kwana da ido É—aya a ko ina...
'' to ƙaraso ciki mana...''ya share abinda na faɗa
dogon numfashi naja tare da juya idona a kaikaice jin yanda zuciya ta take ingizani da inyi mashi wanka da turaren yaji amma sai na dake na tura cart ɗin har zuwa gabanshi na fara sauke abincin duk abunda nake inajin yanda idonshi ke yawo a jikina hakan ya ƙara hasala ni miƙewa nayi tareda ɗaura hannuna a ƙugu a matuƙar tsiwace nace '' wai Malam kallon bai isa haka ba? ko kai maye ne aniyar moɗa tabi randa!" Takaici duk ya isheni...bai dena kallo na ba
sai ma kamar dariya nabashi '' meye sunan ki?" ya tambaya '' ba faÉ—in suna nazoyi anan ba!" na bashi amsa a zafafe
'' sunana Ibrahim ''
'' ban tambaye ka ba!" gyaɗa kanshi yayi yana riƙe dariyar shi, da alamu wannan ne karo na farko daya haɗu da masifaffiyar yarinyar da kyaun shi baisa ta rusuna ba lashe bakin shi yayi,'' zamu iya zama abokai?" yayi maganar yana miƙo hannu mugaisa
'' sunana ba chidera ba dakake miƙo min hannun ka,nan kano ne garin hausawa idan kana buƙatar abokai mata katafi Lagos! !" nayi maganar ina sauke abu na ƙarshe dake saman cart ɗin na miƙe zan tafi ya riƙe hannu na..shima ya miƙe,ji nayi zuciya ta tana bugu da mugun ƙarfi, jan hannu na nayi a tsiwace nace'' dalla sake min hannu dan niba yar iska bace!" amma ko gezau sai ma ƙara riƙe hannun da yayi yana murmushi, tsoro naji ya saukar min irin wanda ban taɓa ji ba...na kuma san saboda ba kayane a jikinshi
ƙwace hannu na nayi ina matsawa baya shima yana matsowa har muka dangane da window yayi min runfa da faffaɗan ƙirjinshi,naji numfashina nafita sama sama,ya saka idonshi cikin nawa Haryanzu da murmushi a fuskar shi '' ww...wai...mmm..meye..haka?" nayi maganar a tsorace ina damƙe turaren yaji na idan naga abu yaci tura in watsa masa inyi gaba, ahankali cikin raɗa ya matso da fuskar shi dab da tawa yana faɗin '' to waye ɗan iska?" Yawu na haɗiye ina nadamar abinda na faɗa..
'' banda amsa yanzu kam!" na kawar da fuskata gefe dan yanzu ba shine lokacin rashin kunya ba...yayi dariya daga ƙirjin shi tare da danne leɓenshi da fararen haƙoranshi...
Hakan ya ƙara tsorata ni sai ƙoƙarin basarwa nake kamar bana jin tsoro amma ƙafafuna rawa suke..harda ɗan ƙaramin fitsari nayi a wando...
murya na rawa nace '' nidai matsa min in wuce!" maƙe min kafaɗa yayi yana kallon idona.. pepper spray ɗina zan jawo yayi saurin ɗaura hannun shi mai bala'in laushi a nawa...ɗan ƙaramin sauti ya ƙwace min a razane nayi hiri hiri da ido...tawa ta same ni,yana kallon cikin idona da manyan nashi, da zurfaffar murya yace '' meye sunan ki?" zuciya ta kamar zata fita daga ƙirjina tsabar yanda take bugu...har so nayi in ture shi amma ina zan taɓa a jikin nashi daba kaya?
Runtse idona nayi na ɗaura hannayena a ƙirjinshi ina turawa da duk ƙarfin da Allah yayi min amma bai ko matsa ba sai dariya da naji yana yi '' wato abun ya kai har da cin zarafi ko?"
Ya tambaya murya ƙasan maƙoshi... buɗe idona nayi suka shige cikin nashi,da sauri na ɗauke su na mayar akan hannayena dake manne da ƙirjinshi...gefe da gefe...saman kan baƙin abun nan da maza da mata suna dashi...yawu na haɗiye zan janye hannu na ya riƙe....
saura kaɗan zuciyata ta fito ta baki ...murya na rawa nace '' n ...nifa...ka rabu..da..Ni...baka gani mayya bace...zan iya shanye maka..jini... ka barni in fita..toh!" wannan barazana ko ƙaramin yaro aka yiwa ita tsaf zai kwashe da dariya bare babban mutum...yake kallona kamar abinda na faɗa shine mafi girman wasa daya taɓa ji...