← Book details Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 67

Sashe 59

Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya aka saka... Fuuu Hansa'u tazo ta wuce ni tana cika tana batsewa..sanda muka fito kasa haƙura nayi na kwashe da dariya... Juyowa tayi da jajayen ido tayo kaina..na kwasawa da gudu da ita biye dani...ina gudu dariya na cina...ban tsaya ba sai dana kawo gaban wata ƙofa...koda na ɗago bayan na gama kama numfashi ganina nayi gaban ƙofar nan mai XXX..

na juyo naga babu Hansa'u...ni kullum idan ana bina sai na kai wani wuri idan na juya sai inga wa'yanda ke bina É—in har sun daina...

Miƙewa tsaye nayi da kyau na sake tabbatar da babu wanda ke ganina na matsa gaba na ɗaura hannu na akai zan tura...

'' kina da ajiya a ciki ne?" Maganar ta sauka cikin kunne na a bazata yasa na juyo da ƙarfi losing balance nayi na faɗa jikinshi..yayi tsaye ƙiƙam kamar bishiya hannayen shi cikin aljihu...da sauri naja baya kamar na ɗosanu da wuta ido waje na kalli fuskar shi da take a matuƙar ɗaure...

'' Uhmm...na manta da soso ne a ciki jiya dana gyara wurin...'' ƙaryar ta gamsar dani don haka shima dole ta gamsar dashi ko? amma ko kaɗan babu alamun hakan sai ɗauke idonshi da yayi daga kaina '' bar wurin nan!'' muryarshi ba wasa a ciki yasa na kama gabana

Sai kuma na tsaya '' soson fa?" wai kada ya ɗauka ƙarya nake...bai ko kalle niba naga ya ciro mukulli daga aljihun shi...gwalalo ido nayi kenan shine da ɗakin..kuma na zage ina makaka ƙarya...

Da sauri nabar wurin na tafi ɗakin Diyaam na ganta tana karatun jarabawa..zama nayi muka cigaba tare tana nunamin abinda ban sani ba....tana da ƙoƙari sosai...

Washegari muka tafi makaranta amma ba tare ba...su Jay d suke tambayarta me yasa bata zoba ranar farko.. murmushi kawai tayi bata ce komai ba...nima ban faÉ—a masu cewa a gida guda muke aiki ba...

Rayuwa ta cigaba da tafiya...har exam time table É—in mu ya fito..a nan gidan su Khalil kuma dayawa daga mutanen gidan sunyi tafiya...harda Hajjo data tafi Makka...
cikin Alhazozan daga Alhaji Hussein sai Alhaji Mansir suka rage

Yan matan Seraphina, Heedayah Khadeejah da wasu da bansan sunan suba da kuma ya'yan Hajiya Momma kaɗai suka rage...suma samarin tsiraran su kawai ne a gidan duk sun tafi ƙasar waje karatu...

Yau Alhamis ina zagaye ƙaton gidan dan babu aiki da yawa saboda raguwar mutanen gidan... kitchen na shiga na buɗe ƙofar bayan nan da koda yaushe take a rufe.. nayi mamakin ganin dogon swimming pool da bishiyoyi hagu da dama da kujeru farare masu taushi...daga can gaba green grass mai laushi...

Iska da yanayin wurin na daban ne,kallon ruwan nayi da murmushi a fuska ta kafin nabar wurin na koma ciki na fara zagyena daga first floor... gidan kamar bada gaske ba saboda haɗuwarshi....daga first floor zuwa second floor har zuwa fifth floor...harda ɗakin motsa jiki na shiga na fito na duba sauran wurare a can ƙarshe naga wani ƙaramin matattakala,

Da nahau matattakalar ya kawo ni a roof top dake kewaye da glasses harda wani swimming pool...da kujeru masu taushi da lema kamar dai Beach...gaban wurin na isa ina kallon ƙasa jiri naji yana ɗiba ta da sauri naja baya tare da dafe ƙirji...

Zagaye wurin nayi ya tsaru sosai...zan bar wurin idona ya sauka akan Romo dake saye da rigar sanyin saƙa da baƙin jeans rigar tayi mashi yawa, ƙamshin shi ya mamaye wurin... hannun shi riƙe da plate ɗin katako da ake zuba paint 🎨 sama...ɗayan riƙe da brush...gaban shi allo da paper yana zane...

Matsawa kusa nayi na tsaya daga ɗan nesa kaɗan dashi ina kallon painting ɗin ƙaramin yaro da bazai wuce shekaru biyar ba yana bibiyar bilbilaye a wurin dake kewaye da bishiyoyi da haki mai taushi..komai na wurin green ne,sai wata mata biye da yaron su biyun farin cikinsu a bayyane yake...daga yanayin zanen zaka gane da safe ne wurin ƙarfe tara ko makamancin haka rana ta fito amma bada ƙarfi ba...

Daga ƙasa ya rubuta wani abun da ban san ma'anar shiba **(La cosa che ho perso**) abunda na rasa)

Painting É—in yayi min kyau sosai...'' idan kin gama kallo zaki iya tafiya!" Muryar shi ta sauka a kunne na,...Hausar shi idan dai mutum ba saurara yayi da kyau ba,zai É—auka da yaren Italiya yake magana...abu na chakwakiya

'' waya ce zanen ka nake kallo? ni aiki nazo yi... zanen ko kyau beyi ba... yaron daga gani bai jin magana...da nice Mamar dana kamashi na zane mashi jiki gobe bazai sake ba....fuskarshi kamar an taɓe alala kan titi kaɗan goge wannan abun..'' na ɗan matso gaba kaɗan amma cikin rashin Sa'a i tripped on absolute nothing, tafin hannayena suka damɓaru akan painting ɗin

A wani irin slow na fara juyo da kaina ido waje na kalle shi,if looks could kill da ban zo ina baku labari ba,ƙasan idon shi har wani ja yayi tsabar takaici

Da sauri na cire hannu na, zan matsa kuma na sake cin tuntuɓe da akwatin kalolin shi na damɓara hannayena a ƙirjinsa, ya wani irin zabura kafin plate ɗin painting ɗin ya sulɓuce daga hannun shi ya sauka saman yatsun ƙafafunshi dake saye cikin baƙaƙen slippers

Da sauri yaja baya yana tsalle akan ƙafa guda yana faɗin '' LORD GIVE ME THE PATIENCE '' idon shi kafe a kaina,ni kam nayi tsaye baki sagam ina kallon shi,mutum kamar ba namiji ba

ganin ya dena wannan tsalle tsallen yana takowa inda nake kamar dutse mai aman wuta,yasa na fara ja baya idona kamar zasu faÉ—o

'' ehhmm..naji kamar ana kirana bari in tafi...'' a gaggauce nabar wurin gabana na faÉ—uwa kuma babu wanda ke kirana fa...
__

Yau da wuri dukan mu muka gama aiki yasa mun taru a parlor muna kallon fim É—in indiya kafin wata mai suna Nana ta canja tashar zuwa ta yan Italiya wai tana so ta koya don ta burge Romo...aiko sauran kamar mahaukata suma wai suna so su koya É—in...aka bi aka ishemu da shegen Yaren mara daÉ—in sauraro...

amma fim ɗin yayi kyau..kuma naji daɗin kasancewar mu tare ba tare da anyi faɗa da hantara ba... na kuma riƙe kalma ɗaya take..wai ragazze..nifa ina ganin so suke suce ragadada,wannan abun da ake haɗawa da nama ko?

Oho..nidai idan na haÉ—u da Romo nan gaba zance mashi ragadada ake cewa ba ragazze ba..ehe!

+2349138091955

RU'UYAA…📖

₦500 ne idan ya kammala zai koma 800

Biya ta wannan account É—in 9138091955..Salma Aliyu opay

Shaidar biya ta +2349138091955

Autumn writes 📖🖋️

RU'UYAA
The dreams we never lived
By Autumn 17 🍁🍁

26. ... Maraya ne...🖊️

Washegari da sassafe ina kitchen...coffee Leonardo ya miƙo min yace '' ki kai room no 207''

'' Kai bazata yi hausa ba wai?" Nayi maganar da hausa,tsare ni yayi da ido ƙwaƙwalwarsa na aiki a 360..karɓar coffee ɗin nayi ina tunanin yanda zan fara hawa stairs tunda sassafe naga Farzan ya shigo
Parlorn ya nufi elevator da sauri na faÉ—a ciki tare dashi bayan elevator ta buÉ—e...saura kaÉ—an in mashi wanka da coffee É—in yayi saurin kaucewa

'' baki da nutsuwa!" na zaro ido nace '' ban taɓa jin wannan kalmar ba,akwai a dictionary?"

ya ƙanƙantar da idon shi akai na can yace '' of course you're dumb bazaki San me hakan ke nufi ba!" turo baki nayi fuska a ɓace kafin in bashi amsa elevator ta buɗe yayi gaba yabar ni tsaye a wurin sai dana ga ƙofar zata sake rufewa nayi saurin fita

samun Khalil nayi kwance saman blue carpet dake gaban gadon shi yana excercise...nuna min table yayi na ajiye coffee É—in anan zan tafi naji yace

'' zoki dafe min ƙafafuna kada ki bari suyi sama...'' Juyowa nayi idon mu ya haɗu...nake ji kamar in kwarara mashi coffee ɗin dana kawo...'' Uhmm..'' ya nuna min ƙafafun shi yana murmushin gefen baki

Dawowa nayi na dafe mashi ƙafafun yana tashi daga kwance ya zauna sai ya koma..kuma baiyi zufa ba..ɗauke fuska ta nayi gefe dan idan ya ɗago fuskokin mu zasu kasance kusa kusa,hucin shi na sauka a gefen fuska ta...

'' wai har yanzu baka gama ba?" Na tambaya bayan shuÉ—ewar lokaci zuciya tana tafasa

Rashin amsa daga gareshi yasa na juyo daidai ya taso fuskokin mu were inches a part...idon mu ya shige cikin na juna ..bugun zuciya ta ya sauya... lumshe idonshi yayi tare da karkatar da kanshi yana matso da fuskar shi saura kaɗan bakin mu ya haɗu nayi saurin miƙewa

Dariya yayi yana kawarda kanshi gefe '' such a buzz kill...da kin tsaya mana...''

Hanyar fita nayi..wannan Khalil É—in is a bad influence...'' oh haka fa...baka yi brush ba shine yasa!"

ina jiyo dariyar shi na riƙa handle ɗin zan fita naji yace '' zoki jira inyi brush sai mu sake gwadawa...''

na buɗe ƙofar na juyo akan kafaɗuna nace '' Too bad..you missed!"

Na fice da sauri, kumatuna suka yi ja..tunowa da haÉ—uwar mu ta farko yasa murmushi ya wanzu a fuskata

Wurin tagar dake corridor na tafi na tsaya ina kallon tsakar gida,idona ya sauka akan Romo dake zaune saman wani baƙin mashin ƙato irin wanda masu gudun tsere suke hawa...shima yasa baƙaƙen kaya daga sama har ƙasa... hannunshi riƙe da helmet baƙi...ƙila yaji a jikin shi a na kallonshi ya juyo da baƙaƙen idonshi saitin da nake tsaye...duk da nisan da muke dashi sai da zuciya ta ta buga da ƙarfi...kallon shi bai daɗe ba ya ɗauke yasa helmet ɗin ya fice da gudu daga gidan kamar zai tafi lahira...

Zan bar wurin ɗakin ƙofar Seraphina ya buɗe tana ganina fuskarta ta sauya '' ke zonan!'' ƙarasawa nayi gabanta ɗin ta nuna min ɗakinta '' wuce ki gyara min ɗaki...'' tana faɗar haka tayi gaba ta barni tsaye

'' wuce ki gyara min ɗaki... ba'a gyarawa!" Na kwaikwaye ta amma dai daga ƙarshe banida zaɓi dole na shiga na gyara...

Da ƙarfe goma duka yan gidan ne zaune a parlor harda su hajiyoyi,samari da yan matan da suka rage a gidan...

Wasu mutane suka zo daga company'n kaya daban daban suna nunawa yan gidan kowa ya zaɓa...nake ji yan gidan na faɗin kayan designer ne limited edition...

Kowa darjewa yake ya zaɓa...mu masu aiki ba'a barmu mun huta da guje guje zuwa nan da can ba...
Chapter 59 · 0% Book details