Sashe 19
Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nan da nan tayi ƙasa da kanta hawaye suka dinga fita da sauri da sauri kuma tayi tsaye wuri ɗaya ta kasa cigaba da tafiya yan aji sai kallo suke kowa ya nutsu
'' ke zoki sa ƙafar ki a ƙasa!"
Ya bata umarni yana nuna mata bakin ƙofa, yarinyar ta kasa motsi sai kukan ta daya ƙara ƙarfi tana sheshsheƙa tana sa hijabinta ta goge hawaye fuskarta tayi jawur Saboda fara ce bafulatana
'' dan ubanki bakiji ko..idan na same ki wurin sai kin yaba ma aya zaƙinta!"
Ya faɗa a harzuƙe tareda ɗaukar wata zungureriyar bulala ya ƙaraso inda take ji kake sha! sha! sha!
Yana ta auna mata buloli ta ko ina yarinyar takai ƙasa tana shille shille kamar kifin da aka fitar daga ruwa tana faɗin
'' dan Allah malam kayi haƙuri''
shiko kamar mara imani Saida taba kowa dake ajin tausayi wallahi
'' tashi ki wuce ki zauna banza jaka!!"
Ya faÉ—a yana huci harda share zufa..dukan sauran yan aji sun tsorata sanda ya É—ago da jajayen idonshi yana kallon su..sai kuma idonshi suka sauka akan Tuwo data ajiye kanta akan desk
'' wacece ke mun kwana a aji?!" Ya tambaya yana huci kamar wannan shine mafi girman laifin da akayi mashi
Da sauri na tashi zaune..idona sunyi ja dan dama duk wannan dramar da ake ni kuka na nake sharɓa...
Hijabina nasa ina goge fuskata...
'' Ke zonan!"
Muryar shi kamar ana surhen ƙanzo ba daɗin ji ko kaɗan...
Ahankali na tashi kaina ƙasa ina zuwa inda yake..sai bina suke da ido kamar na basu tausayi
'' Gani!" Na faɗa tsaye a gabanshi..hararata yayi daga sama har ƙasa sannan ya miƙa min littafin
'' karanta mana wannan shafin!"
Zaro ido nayi bakina na motsi hakama jikina na ƙyarma...yanda yan ajinmu suke kallon kallo na tabbatar sun hangoni a ƙasa kamar yarinyar nan...
'' Amsa mana!"
Ya daka min tsawa..hawaye suka shiga rige rigen sauka a fuskata
Karɓar littafin nayi sannan na juyo ina kallon su,shi kuma ya tsaya baya na..murya na rawa na shiga karatun da hausa '' Comfri henshon... T-hey..le'a' der and t- le'ad..
On' ce uupon a ti me,t..here was...''
''.innalillahi wa inna ilaihi raji'una...ke dan ubanki turanci kike karantawa ko Hausa!!!"
Yanda yayi maganar ba ƙaramin razana nayi ba..da sauri na juyo hakan yasa nidashi mun game dan kusa kusa dani yake... Da sauri nayi saurin matsawa baya suko yan aji suka yi wani '' Hah!!" Dan kawai jikin mu ya haɗu..toh ai dai bada gangan bane..sai ƙus ƙus suke
'' laa wallahi Abeedah ta rungume malamin nan!
'' É—an iska laifin shine shifa ya wani tsaya bayanta..dama abinda yake son yi kenan!
Nidai jikina babu abinda yake sai rawa ganin banzan kallon da yake jifa ta dashi sai kuma ya daka ma ajin tsawa '' Silence!!"
Sukayi tsit...a fusace ya zari bulala yayo kaina na fara ja baya kuka na,na ƙara ƙarfi indai ni kaɗai za'a daka wallahi bana so ko kaɗan
'' zonan!"
Ya furta yana matsowa
'' dan Allah kayi haƙuri...''
nidai sai jin saukar buloli na fara daga kowane sashe..sai ihu nake... Ina murje murje dan bulolin ba wasa...
Sai da yayi min ligya kamar Jameelah sannan ya daka min tsawa yana faÉ—in
'' tashi ki bar wurin nan sakarya daƙiƙiya!"
Jiki ba daɗi na miƙe ina tafiya ina sharar hawaye.. Allah yasa matane mu babu namiji ko ɗaya bayan malamin
Jay D na kalla kafin in isa seat ɗina ta ɗauke kanta... Ina zama aka fara ruwan sama da ƙarfi, huci mugun Mutumin ya saki kafin ya kwashe kayan shi yabar ajin mu
'' a gaskiya mutumin nan É—an iska ne,Ni dama tunda na fara ganin shi bai min ba wallahi!"
Hameeda ta faÉ—a tana harare harare
Sauran yan aji suka biye ta murya sama saboda ruwan basa bari aji abinda ake faÉ—a...nidai na cigaba da kuka na ,nayi tunanin Jay d zata zo ta lallashe Ni amma babu ita babu alamun ta
Har sanda aka tashi break kuka nake sannan kuma ruwa basu dena sauka ba
Masu sayar da abubuwan ciye ciye suka dawo barandar ajujuwan mu dan babu wanda yayi yunƙurin fita, idan malamai suka kama mutum ribiti suke mashi kamar sun samu jaki....
'' tuwo bani kuÉ—in tara na!"
Naji Muryar Asma'u akai na..na ɗago kaina naja hijabi na zuwa gaba sannan na ciro kuɗin cikin Safa na miƙa mata..ta karɓa ta fita batareda tace komai ba...
'' Abeedah kiyi haƙuri, wallahi sai Allah ya isar maki!" Inji A'ishah tana shafa baya na...
'' Ni wallahi yanda malaman nan suke dukan mu ba imani kada suje su mana illa '' wata mai suna Afrah ta faÉ—a tana gyara glasses É—inta
Sai mutane suka fara bamu haƙuri nida Jameelah..nayi mamakin yanda basu zauna suna mana dariya ba,dan dai abin dariya wurin yan ajinmu baya kaɗan
Da ƙyar na iya dena kukan.. sai kuma na kalli sashen Jay D na ganta tana ta raha da yan uwanta masu kuɗi sanda muka haɗa ido wani kallo tayi min kamar nida ita bamusan juna ba...naji kamar zuciyata tabar ƙirjina..sai nayi ƙoƙarin basarwa amma na kasa jiki ba ƙwari na miƙe na isa inda take
'' Jay D...ina so muyi magana...dan Allah!"
Sai sauran yara masu kuɗin suka kalle ni cike da rainin wayo amma banda ita,kawai ina son ƙawata ne... Ganin bata juyo ba kuma batace komai ba..ga mutane sai kallon mu suke yasa na fara jin kunya na kamani...
Gani nayi ta miƙe ta fita waje sai nabi bayanta sauran kuma suka cigaba da harkokinsu wasu na gulmar mu
'' Jay D...''
'' babu abinda ya rage da zamuyi magana akai Abeedah...kin ban kunya kin watsamin ƙasa a ido...nida nake ƙoƙarin yi maki faɗa tunda ke baki iyawa da kanki shine zaki dakamin tsawa a gaban mutane kina shatamin layi ko? Akan yarinyar da nake ƙoƙarin nuna maki ita wacece nake ƙoƙarin kare ki...ba matsala na fahimta jini yafi ruwa kauri kije keda ƙanwarki kawai nima sai in kama kaina...nasan matsayina yanzu ai!"
Tayi maganar cike da ƙunar rai... Tana ƙifta ido kada ta fashe da kuka,ni na kasa riƙe nawa
Kafin in yi magana
'' me kuke anan shegu cikin ruwan nan salon ciwo ya kama yarinya taja ma iyayen ta bala'i zaku wuce ku koma aji koko?"
Wani malami ne wanda ake kira da ƙashin miya yayi maganar.. mutumin sai tsawo kamar zanƙalalo ba ƙiba
Shigewa Jay D tayi ina biye da ita kaina a ƙasa, ta koma ta cigaba da zama da group ɗin masu kuɗi tabarni ni kaɗai...sai naji kaɗaici ya dabaibaye ni da ƙunci da raɗaɗin zuciya musamman idan na juyo naga kowa tare da abokin shi....Ni kaɗaice zaune a nawa seat ɗin kamar wata dodo ashe ban san nan gaba wanda zan ɗanɗana sai yafi haka ba
Ba'a Dena ruwa ba sai lokacin sallah, nan ma nayi ƙoƙarin yima Jay d magana amma sai ƙawayenta suka tafi da ita bansamu dama ba... kuma itama da kanta bata so tayi min magana...nasan abinda nayi mata ba ƙaramin jin zafi tayi ba kuma zata daɗe kafin ta sauko...amma dan Allah bazata iya dawowa mu cigaba da zama a seat ɗin mu ba? meyasa zata barni? dafe ƙirjina dake motsi da kuka nayi,tare da ɗauke idona gefe kada aga hawaye na
Sai kawai nayi alwala na shige masallaci..bayan antashi makaranta ma tafiyar ta tayi tabarni, Asma'u kuma wai sun shiga wani debate da za'ayi tsakanin makarantar mu da wata private school...wata yar ajinsu ta faÉ—a min
Sai kawai na tafi gida ni kaɗai duk ƙunci ya kamani... Sanda na shiga na iske Mama tana tuƙa tuwon masara... Tana ganin fuskata ta gimtse dariya
'' A'a tuwo yau babu sallama? Baki ga takwaranki nake ba...?"
Turo baki nayi inaji kamar in jefar da wani abu ko in gwara kaina da bango... Sai kawai na haɗiye ɗacin danake ji na shagwaɓe fuska nace '' Ni bazanci ba!"
ÆŠage kafaÉ—a tayi
'' tuwo dai nan nayi meci yaci wanda bai ci ya bari....''
Innalillahi..duk sanda Mama ta faɗi wannan haushi nake ji kamar kamar.... Idona suka ciko da hawaye ƙirjina na sama da ƙasa...ina hura hanci...
Fitowa tayi daga kitchen É—in tana share gumi tace
'' ina Asma'u?"
Na hankaÉ—a labule na shige É—aki ina faÉ—in
'' wai debate suke a makaranta"
'' toh niƙan data kai wa zai ɗauko?"
Mama ta tambaya tana biyo bayana
'' inta dawo sai taje ta É—auko ai..''
'' a'a wallahi baza'a bar min niƙa awaki suyi wasa dashi ba maza canja kaya kije ki ɗauko min niƙa na!"
Mama ta faɗa da bada umarni..hawaye na farayi zuciya a ƙuntace...nayi faɗa da Jay d, Asma'u bamu shiri..mama tayi tuwo....yanzu kuma inje in ɗauko niƙa ciki empty..kai! gaskiya ranar yau baƙinta yayi yawa
Mama tatafi tabarni,zane na ɗaura na fito na ɗebi ruwa cikin bokiti na faɗa toilet nayi wanka... Bayan na fito nasa doguwar riga green color da hijabi ruwan toka da hula ita ma haka sai nasa takalmi nazo wurinta karɓar kuɗin niƙa
Ɗari biyu mama ta miƙo min inata ture turen baki...bata kula niba
'' ƙila ma in ɓace!"
Na faɗa ina karɓar kuɗin
'' Yoh in kin ɓace ai inada Asma'u tuwo..sai muyi addu'a Allah yasa duk inda kike kina lafiya!"
Ta faɗa cikin halin ko in kula,maganarta tasa naji numfashina ya ɗauke,dama na sani babu wanda ke sona..toh mai zai sa a soni? me nake dashi? dariyar ƙunci na saki tare da sa ƙarshen hijabina ina goge hawayen da suka fara sauka
'' dama nasan ba'a so na,amma fadar hakan a fili ya ƙara tsaurara ciwon a zuciya ta!"
Mama ta kalle ni ido waje ganin ina hawaye sai kuma ta matso da nadama a fuskarta kafin tace wani abu nayi gaba ina faÉ—in
'' kada ki jirani Mama dan baxan dawo ba!"
ta biyo bayana tana lallashina amma bana ko jinta har na fita, mutane irin mu ba'a masu magana irin haka koda da wasa ne zamu iya jin ciwo mai tsanani,(could hurt harder than intended)kuma wannan maganar zata cigaba da zama damu,dama can bama kallon kanmu da ido mai kyau,wannan maganar sai ta ƙara ƙarfafa wancan zargin namu kawai