Sashe 22
Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ina tsaka da wannan tunanin ta shigo riƙe da ruwan zafi...amma ban iyarda cire kayan ba,akwai yar ƙaramar singlet data tsaya rabin cikina da kuma pant
Sai nayi ƙasa da kaina ganin yanda ciki na yayi flat naji inama ace ya cigaba da zama a haka...
'' Mama dan Allah..babu abinda ya faru kuma zan iya yin wankan da kaina dan Allah!''
na roƙe ta da magiya...ta tsare ni da
Ido na tsawon lokaci kamar me lissafin wani abu kafin ta sauke ajiyar zuciya ta ajiye min ruwan ta fita
Asma'u tayi zaune tsakar gida zugum.. zuciyar tana kai kawo...waye gayen nan na É—azu? Taga alamar da yayi ma Abeedah yace
'' bye bye kitten ''
dama sun san juna ne? Ina tasan zazzafan gaye haka.. kyakkyawa dashi son kowa ƙin wanda ya rasa...ita ya dace ace sun fara haɗuwa ba Abeedah ba!
'' Me Asma'u ke tunani haka?"
Inji mama dake fitowa daga ɗaki ta ɗauko tabar ma,jin anfara kiraye kirayen salla kuma ƙasan ma ta bushe
'' babu komai...kawai ina tunanin...dabadan Allah ya kawo shi ba,da mai zai faru da tuwo!"
Tayi ƙarya lafiya lau duk da wani sashe na maganar ta gaskiya ne amma ita babban tunanin ta,ya zata haɗu da guy ɗin...wallahi ta kamu da sonshi...' Abeedah ta san shi'
Wani sashe na zuciyarta ya ayyana sai itama ta samu dabara,tasan yanda zatayi
Bayan ta samu mafita ta miƙe da murmushi a fuskar ta,ta ɗauki buta tayi alwala dan yin Sallah
Da ƙarfe bakwai mu duka muna zaune,kaina saman cinyar Mama dake shafa min ruwan shinkafa tana tambaya ta...kamar wata..uhmm...
ðŸðŸ: Detective
Yauwa kamar detective,har nayi wanka lokacin na sauya kaya zuwa farar riga doguwa... Asma'u daga gefe tana rubutu a littafin ta
'' Shi wannan waye shi? Wanda ya kawo ki gida!" Mama ta tambaya...sai Asma'u tayi cak da rubutun da take
'' Oh... Khalil...sunan shi Ibrahim,a maina hotel muka haɗu yana ta so mu zama ƙawaye amma nidai naƙi yarda...''
Mama ta É—anyi jim kafin tace
'' meyasa baki yarda ba? Yana da wani aibu ne?"
Girgiza kaina dake kan cinyarta nayi ina turo baki nace '' Mama fa suna da kuÉ—i..kuma nidai bana son masu kuÉ—i wallahi!"
Mama batace komai ba ta cigaba da yimin abinda take
'' kenan kun daÉ—e da sanin juna?" Asma'u ta tambaya daga gefe tana kallo na
'' ban sanshi ba...''
'' yake kiran ki kitten kuma baku san juna ba?"
Ta sake magana..na É—an É—ago idona na kalleta
" ya kira ni da kitten?taya ni banji ba sai ke mai kunne an uku ko?" sai tayi shiru
Bayan sallar isha'i sosai ake kwararo sanyi kuma babu nepa....amma akwai taurari da wata ga iska mai daɗi yake share mana saurayen dake gantsarar mutum daga zaran ya zauna...Mama take sanar dani wai wayanda suka bamu kyautar gida sunzo sun kawo takardun gidan duk da su hankalin su ma baya jikin su alokacin..nemana shine gaban su,ta ƙarashe da faɗin
'' na É—aga batun komawa sabon gida sai sati na sama!"
Idona har sun fara lumshewa nikam...cikin muryar bacci nace '' Allah ya kaimu!" Ta amsa da Ameen
'' Mama yace zai sake zuwa gobe ko?" Na tambaya ina nufin Ibrahim
'' haka yace!"
Inji mama... lumshe idonta Asma'u tayi dajin daÉ—i aranta gobe zatayi shiga ta musamman dan jan hankalin shi
Nidai daga Maganata ta ƙarshe ban sake cewa komai ba, da safe bayan munyi salla mun zauna har rana ta fito muka fito mama ta wuce kitchen ni kuma na fara sharar tsakar gida Asma'u tana wankin toilet
''.Mama naso ace gidan nan akwai bishiya cikin shi wallahi!"
Nayi maganar ina tattare sharar mama ta taɓe baki
'' dan ki dinga hawa ko?"
Na ƙyalƙyace da dariya jin abinda ta faɗa
Muka cigaba da hirar mu..nidai dama ba makaranta zanje ba...bayan munyi kari nayi wanka nasa riga da zane atamfa shuɗi..na ɗaura zanen wani gefe yafi wani tsawo..idan ina tafiya sai ƙafafuna su dinga kwarewa
'' ke dai Allah ya miki magani..zanen ma baki iya É—aurawa ba!"
Mama dake zaune kitchen tana rigar shinkafa ta faÉ—a da alhini..nikam dan mutum bai iya É—aura zane ba,a ganina ba wani abu bane amma mama ta dinga mita...
Kuɗi taba Asma'u dake saye da baƙin hijab tace taje ta siyo kayan miya..karɓar kuɗin tayi tana faɗin
'' ni zanyi miya!"
Zuwa nayi na zauna bakin ƙofar kitchen ɗin
'' Mama wai wannan abincin da ake faman yi na menene?"
Mama ta É—an kalleni
'' na tarbar yaron arxiƙi ne,dabadan Allah ya kawo shiba da bansan inda kike ba Abeedatu!"
Ta ƙarashe tana jinjina kai kamar tunanin rasa ni na haddasa ma zuciyarta babban ciwo
Nayi murmushi'' ashe kina sona? Ba kince kina da Asma'u ba?"
Na tambaya da hawaye a idona..duk da ba ciwo nake ji a zuciya ta ba
'' wasa nake..dukan ku inason ku,idan wani abu ya faru da ɗayan ku Bansan yanda zanyi ba... Kiyi haƙuri idan abinda na faɗa yasa kinji ba daɗi!"
Mama ta faÉ—a tana cigaba da aikinta
Sosai naji ta ban tausayi...sai na share hawaye na na gyaÉ—a kai
Har zanyi magana'' NEPA!!!" Na faɗa da ƙarfi tare da miƙewa daga bakin ƙofar kitchen ɗin ina taka rawa da maɗaukakin farin ciki a fuskata...Mama ta girgiza kanta da murmushi a tata fuskar itama
FaÉ—awa É—akin nayi na kunna tv nasa tashar yan china daidai ana fim É—in kashi of lof ...( Ashes of love)
Tun ina kallo har bacci ya ɗauke ni...da ƙarfe ɗaya mama ta tayardani inyi sallah,bayan na gama naci abinci Asma'u nake kallo data zage tana kwalliya tasa irin kaya na sosai tayi kyau kamar in sace ta in gudu...' idan fa yaga tafi ki kyau..ya Dena kula ki?' wannan tunanin yasa naji abincin da nake ci ya fita raina...ba lallai na faɗa ba..amma ina son shi..bawai sona soyayya ba a'a irin dai kamar idan kana da aboki...sai abokin ya haɗu da wani wanda yafika sai ya dena kula ka... irin ciwon da mutum zaiji a wannan lokacin shine nake ji a raina yanzu...
'' Asma'u kina da kyau meye na kwalliya kuma? Ina zaki haka...''
Tayi murmushi tana kallona ta cikin madubi tace
'' kishi kike ne? Babu inda zanje so calm your heart...''
jin amsarta ban sake cewa komai ba da gaskiyar ta,a karo na farko nayi kishi da ita. ba irin kishin dana kasa tantancewa akan ko ina jinshi ko bana jinshi ba.... wannan na tabbatar da kishin ta nake ji...kishin kyaun ta...inama ace nima ina da kyau har haka? Idan Khalil ya ganta zai dena kula ni? akwai lokuta da yawa da mutane suke Dena kula ni daga lokacin da suka ga Asma'u
Har yanzu ban dena jin tsoron sake faruwar hakan ba..wai yaushe ma shi Khalil É—in ya dame ni? Yaushe na damu dashi har haka? ' saboda shine namijin daya fara kulaki duk da munin ki!' zuciya ta tunatar dani
'' ya dai? Da gaskiya ta kenan? Kina gudun kada yaga yar kyakkyawa ya dena kula ki ko?"
Sai nayi ƙasa da kaina.. murmushi me kyau tayi kafin ta taso ta tsaya bayana.. numfashinta na dukan wuya na...muryarta da kaifi bakinta saitin kunne na tace
'' ki tafi ki ɓoye...wani wuri kafin ya iso...ki hutar da kanki daga zama ' invisible ' idan ina a wuri! Babu wanda zai taɓa lura dake Abeedah...ke ɗin..zaki cigaba da zama a inuwata!...''
ko wace kalma daga bakin Asma'u tana yanka zuciya ta kamar wuƙa mai kaifi ko fiye da haka.. hawaye suka fara ƙone idona... zuciyata tayi nauyi...abincin dana ɗiba cikin cokali na kasa kaiwa baki
ÆŠis! É—is! Hawayen suka fara sauka da mugun sauri...sai tasa hannun ta tana share min...da wani irin abu da bansan meye shi ba a muryar ta tace
'' ba ina cutata maki bane..kawai ina faɗa maki gaskiya ne! Ke akoda yaushe kina faɗin..Gara mutum ya faɗa maki gaskiya komai ɗacinta abinda nake kenan Abeedah!!kada ki riƙe ni a zuci!"
Ta ƙarashe maganar tana ja baya kamar batace komai ba
'' d..d..da gaskiyar ki...zai fi..idan na bar wurin!"
Na faÉ—a cike da rashin wayo..Ni Abeedahtuwo ban san sanda zan koyi tsaya ma kaina ba..kullum saidai inta yarda da abinda mutane suka faÉ—a min... ajiyar zuciya na sauke tareda ajiye abincin gefe na share hawaye na
Ina nan zaune ina tunane tunane har ƙarfe huɗu sai mukayi sallar la'asar tare..bayan mun gama azkaar Mama tace
'' har yanzu yaron nan bai zoba...kodai sun fasa xuwa ne?"
Da sauri Asma'u tace '' kai Mama..taya zai fasa zuwa bayan yace zai zo? Ƙila Saida yamma..''
'' Allah yasa! Wai ina zaki da kika sha wanka haka?"
Idon Asma'u suka fito jin tambayar mama
zuciyarta na bugu tace '' Uhmm...dama..uhmm yau naso inje gidan su ƙawata rakkiya amma sai na fasa yanzu...''
na ɗago idona ina kallon ta jin ƙaryar data shuta amma bance komai ba
Sai na miƙe
'' Mama ina zuwa zanje gidan su sale... Tun ranar da muka tafi tare ban sake zuwa duba shi ba...''
na faÉ—a.. gaskiyar shine kawai ina so in tsere kafin su iso kamar yanda Asma'u ta faÉ—a
Mama zatayi magana ta rigata faÉ—in '' gaskiya ya kamata ki tafi...kai zumunci baice haka ba Abeedatu...yaron nan abokin kine fa ''
tayi maganar tana girgiza kai..sai Mama bata ce komai ba.. hijabi na na canja zuwa baƙi sannan na fita
Ba gidan su sale na tafi ba...bayan gidan mu..inda gulbin nan mai koren ruwa na tafi na tsaya.. kamar hawaye na sun san cewa na kawo inda nake jin nafi samun sirri suka fara zuba ba ƙaƙƙautawa ban san dalilin da yasa kalaman Asma'u game da khalil suka yimin ciwo ba...
Ina kallon ruwan ina kuka.. fuskata ta ɗanyi ja kamar idona...na daɗe a wurin duk lokacin da nayi niyar komawa sai wata zuciya ta kwaɓe ni daga ƙarshe na duƙa wurin ina dambe da zuciya ta kafin na samu ƙwarin guiwar miƙewa na fara barin wurin
A hanya na gamu da sale dake tafiya da sandar guragu da guntun wando a jikinshi kamar zanyi dariya amma saina haÉ—e
'' ke bakida mutunci ai..yayi..''
'' yi haƙuri..rayuwa ta shamin kai wallahi..yanzu ma gidan ku nayi sai gashi mun haɗe..''