← Book details Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 67

Sashe 58

Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mukhtar da Farzan ban san wanda yafi Zama shocked cikinsu ba...

''No way!!"

''Impossible''

'' wannan mummunar yarinyar ce budurwar ya Rom?''

Muryoyin suka faÉ—a a lokaci É—aya... Seraphina,Huriyya... Jameelah da Khadeejah ne suka faÉ—i a dukan su sun tashi tsaye daga wurin zaman su

Khalil yayi ƙasa da kanshi yana murmushi

'' Ya Rome,da gaske wannan itace budurwarka?" Khadeejah tayi tambayar cautiously cike da tsoron amsar da zata biyo baya ..kowa ma amsar shi yake jira har dani

'' Ask Google!" Batareda ya ɗago daga abincin shiba garmahon muryarshi ta amsa kuwwa a kunne na a karo na biyu,ƙafafuna kamar zasu zubar dani

Damƙe tiren dake hannu na nayi..cikina ya ɗaure..zufar da ba'a gani ta wanke goshina mutumin nan zai sani a matsala dama can ba wani sona mutan gidan suke ba yanzu kuma wannan...

Miƙewa yayi babu wani sauran bayani ya nemi fita daga wurin

Alhaji Hussein da tunda yayi magana Roman bai ce ko ehm ba ya paka abincin shi gefe ya kalli ɗan nashi dake barin wurin ya miƙe '' Romano!"

Kamar Romo bazai tsaya ba can kuma sai ya tsaya batareda ya juyo ba ... Alhaji Hussein kamar zai yi aman wuta ya nuna shi yace '' kai bazaka zama ɗa na gari ba? A matsayina na ubanka ba zaka girmama niba? Kaje wata ƙasa ka dawo bazaka iya gaishe niba... I'm your father!'' wurin yayi tsit kamar babu mai rai a wurin, mu masu aiki kan mu a ƙasa sai rarrabar ido muke

'' My father....'' ya furta slowly kamar abun na bashi mamaki,sai ya juyo ta kafaÉ—arshi

'' didn't see you there...PADRE!''... Voice cold as ice, idonshi da tsananin duhu ya cigaba da tafiyar shi

+2349138091955

RU'UYAA…📖

₦500 ne idan ya kammala zai koma 800

Biya ta wannan account É—in 9138091955..Salma Aliyu opay

Shaidar biya ta +2349138091955

Autumn writes 📖🖋️

RU'UYAA
The dreams we never lived
By Autumn 17 🍁🍁

25. ...yar aiki ce...🖊️

Kamar anyi ruwa an ɗauke bayan tafiyar Romo daga wurin...ƙila kowa ya shiga shock da abinda ya faɗa....

'' kun gani ko..Allah ya wadan naka ya lalace!" Hajiya Momma ce ta faÉ—i hakan

Hajiya Ruƙayyah ta taya ta da faɗin '' ai kam dai,bawai bana son yaro bane...amma gaba ɗaya hallayarsa abun tambaya ce!"

'' Gaskiya Alhaji ya kamata ka ƙara sa ke...yaro yana nema ya gagareka...'' Inji Hajiya Wareesha

'' nidai fatana wannan lokacin bazai dinga kwasowa mutane abun magana ba''

'' once a trouble maker always a trouble maker!" Farzan ya miƙe daga wurin zamanshi bayan ya faɗi hakan...

'' kuyi mashi uzuri...rayuwa babu uwa akwai wahala sosai!" Hajiya Hafsah ta faɗa daga ƙarshe...Hajiya Momma na hura hanci tace '' Koda Fateemah aw Cora ɗin tana nan ai ba wani abun kirki zata aiwatar ba? Kai haɗa zuri'a da irin wa'yannan mutane dai masifa ne wallahi!"

Miƙewa Hajjo tayi cikin shiru tabar wurin sauran manyan matan suka cigaba da magana akan wacce suke kira Cora ko Fateemah duk sunanta ne,kamar basuga cewa Hajjo tabar wurin ba,suma mazan suka bar wurin kusan a tare...amma Cora bai yi kama da sunan musulmai bako?

Sai lokacin da suka bar wurin na lura cewa yan matan kamar zasu kashe ni da kallon da suke min...nayi ƙasa da kaina...Khalil ma yayi shiru kafin ya miƙe yabar wurin...

'' Mtchewww! aikin banza...this guy is a bad luck! daga dawowar shi har gida yayi tsami!" Jawaad da bai cika magana ba idan ana cin abinci ya faÉ—a tareda dukan table É—in kafin yabar wurin

suma sauran suka zare jiki ɗaya bayan ɗaya sai da ya rage yan matan da mu masu aiki harda Diyaam Seraphina tayo kan DIYAAM '' Tass!" Ta ɗauketa da marin daya amsa ƙara a gaba ɗaya dining ɗin ƙirjinta na sama da ƙasa

Ɗan kwalin Diyaam ya faɗi doguwar sumarta baƙa ta warware ta rufe rabin fuskarta.. hannun ta dafe da kuncinta...

sakin baki nayi idona na kallon tsakanin su biyun... sauran suka sadda kansu,yan matan suke kallon mu kamar zasu kashe mu '' ba saida nace kada inga ƙafar ki a parlorn nan ba?"

Murya na rawa Diyaam tace '' K...kit...haƙ..hamm..'' damƙo gashin Diyaam Seraphina tayi

Heedayah tace '' ki haÉ—a min da shegiyar nan mai idon Mayu!" Kallonq Seraphina tayi kafin tace '' ki bari in gama da wannan annobar...''

Idon Diyaam suka fito.. jijiyoyin goshinta sukayi ruɗu ruɗu hannunta riƙe dana Seraphina '' Bana ce kada ki sake kiranshi da Hamma ba? Dan ubanki yaushe ya zama Hamman ki?''

''.kiyi haƙuri dan Allah!" Diyaam ta faɗa tana kuka sosai.. idonta kamar jini..da ƙarfi Seraphina ta tureta ta faɗi goshinta ya haɗu da table take wurin yayi ja kasancewar ta fara...

Tana huci ta juyo kaina..sauran yan matan suka miƙe kamar cin mutuncina yafi ƙayatarwa sama da Diyaam

'' Ji nayi ya I.B ya kira ki budurwar ya Rome?" Matsawa na shiga yi tana matso Ni...'' hala baki ji bane da kyau kike tambayarta?"

Jameelah ta ɗauki gorar ruwa ta harbo sashena..da sauri na duƙe gorar ta sauka akan Seraphina...

'' Ahhh!!!!" Ta saki ƙara...ta juyo tana kallon Jameelah da fushi...

'' what the hell!"

'' oh bake nayi niyar jifa ba!"

'' amma ni kika sama!"

'' Duh! Ba laifina bane idan kin shigo tsakani....'' a fusace itama Seraphina ta É—auki gorar ta jefawa Jameelah..ta sameta a goshi

'' yanzu kema kin san yanda ake ji ai!"

'' Guys calm down!"

'' taya zanyi calming down wannan ugly duckling ɗin na ƙoƙarin shiga tsakanina da Ya Rome..bayan ni yake so!" Tayi maganar tana kallona

'' excuse me...wane irin ke yake so? Huriyya take hararar Seraphina kamar idonta zai faÉ—i

'' wasn't it obvious?'' Seraphina ta bata amsa

'' delude yourself girl!"

Faɗa ya koma tsakaninsu akan wake ƙoƙarin ƙwace Romo daga wa...ganin hankalin su baya kan mu na isa wurin Diyaam na taimaka mata ta miƙe salin alun muka bar dining

hawayen da suka zuba daga idonta sun isa cika murfin hira koma abinda yafi hakan girma...katin ma'aikatan tayi swiping elevator ta buɗe muka shiga ciki..nesa na tsaya da ita ..ƙila bata so asan munsan juna...ina satar Kallon ta daga lokaci zuwa lokaci yarinyar fara ce sosai...yanzu ta dena kuka kanta a ƙasa...

Sautin buɗewar elevator yasa ta ɗago ta fita ina biye da ita kuma ban san dalilin bibiyarta ɗin ba...ƙofar ɗakinta muka tsaya ta buɗe ƙofar na samu kaina da juyawa zan tafi '' Abeedah...'' ta kira sunan muryarta da taushi..Juyowa nayi ina rarrabar ido..ta nuna ɗakin '' mu shiga ciki...'' tayi gaba ina biye da ita abun ya ɗaure min kwanya...idan ita yar aikice meyasa take da ɗaki a cikin babban gida?

Meyasa kuma Seraphina tayi mata yanda tayi mata...gefen gadonta ta zauna ta nuna min kusa da ita...nake jin ɗar ɗar..kafin daga ƙarshe na zauna ɗin

ƙaramin locker dake gefenta ta buɗe ta ɗauko magani tana lura da ciwon data ji '' kawo in yimiki...'' na karɓa daga hannunta...bayan shuɗewar lokaci tace '' ashe kina ɗaya daga cikin sabbabin ma'aikatan da aka ɗauko...'' gyaɗa kaina kawai nayi..ban manta yanda ta share niba ɗazu da nayi mata magana

'' oh...nima aiki nake a nan gidan..nasan kina tunanin yanda akai nake da É—aki anan a maimakon sashen ma'aikata ko?" Jinjina kaina nayi tareda ajiye almakashi bayan na samata plaster a ciwon

'' Hamma Roman ne ya kawo ni shekarun baya...ya ganni ne a gefen hanya bani da inda zani...ni na zaɓi in zama mai aiki a nan a maimakon in zauna ana ciyar dani kyauta...'' nayi mamakin jin wannan.. kuma na rasa abun faɗa gane hakan tace

'' kin tafi makaranta jiya? Yasu Anaam da Jadeedah?" Murmushi nayi kafin na bata labarin abinda ya faru a jiya É—in duk da ba wani abu mai yawa ne ya faru É—in ba...

Mun daɗe muna hira kafin na tashi na wuce sashen ma'aikata inda ake magana akaina...da gaskiya ta..abinda Khalil ya faɗa baƙin jini ya ƙara min..ina tafiya ana bina da baƙin ido kamar zasu sa in faɗi...

Washegari da safe ban samu damar zuwa dining ba saboda wannan Hajiya Momma data tsare ni a ɗakinta da wanki kuma fa akwai laundry room wai ita bata so ana sama ta kaya a mashin kuma bata ga wanda ya dace data ba wannan aikin ba sai ni koda na gama ƙarfe sha ɗaya bazan iya zuwa makaranta ba...haushi kamar in cinna mata wuta..dataga alamun na ƙufula wani shegen murmushi ne maƙale a fuskarta..nakai bakin ƙofa na juyo na kalleta nace '' aljannu na suna tashi su daki wanda ya ɓata min rai...ko su haukatar da mutum... Hajiya gwaggo kibi a hankali...'' expression ɗin dake fuskarta was priceless

Da sauri na fita daga É—akin ina dariya... kitchen na tafi na iske sun haÉ—a wani abu a tray kamar biscuit da juice..da sauran abubuwa..kusan plate biyar ne... Hansa'u ceta shigo ta kwashi guda uku saura biyu Leonardo yace in bita dasu zuwa Movie room...

Badan naso ba nabi bayan ta.. yarinyar is self absurd ...ji take kamar tafi kowa kyau da komai a gidan saboda kawai uniforms ɗin ta sun matse ta sun fito da surar jikin ta take ji kamar maxan gidan ba zasu iya haƙura ba harda su Romo da Khalil tana tafe tana juya mazaunai...

abinda ya faru a Movie room ya ƙayatar dani fiye da komai a ranar...

sanda muka shiga wurin da duhu amma ba mazan kaɗai bane yau harda matan...layi layi take bi tana miƙa masu suna ɗauka kowa hankalin shina akan TV nidai ina tsaye daga gefe...

Bayan ta gama dana hannunta tazo ta karɓi nawa na juya Zan bar wurin saboda yanda Mukhtar ya dawo da hankalin shi akaina naji an bada tass

Juyowa nayi da sauri naga Hansa'u riƙe da kuncinta Armani tsaye a gabanta

'' BABBAR BALA'I!!! Ni kika mara?'' Hansa'u tayi maganar kamar zatayi kuka...'' ko zaki rama ne?'' Armani ta tambaya
'' dalla fita kiba mutane wuri shegiya me kama da aljannu..''
Chapter 58 · 0% Book details