← Book details Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 67

Sashe 39

Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da jin haushi na mijin ya bar wurin nima na koma ciki...can wurin sha ɗaya gaban gidan mu ya cika da masu sonyin lilo manya da yara mafi yawancin su yan mata ne da ƙananan yara...

Fitowa mukayi muma tunda bamu da aikin yi muka bi ayarin masu son yin lilon,ganin akwai layi yasa wasu daga cikin yan matan suka ja gefe wasu suna yar carafke dan ƙasar wurin mai laushi ce sosai wasu kuma suna a yu redi (are you ready)

Masu carafke nabi..Jay d da Anaam kuma yan Are you ready.. Asma'u lilo...wurin ya zama wurin wasa nan da nan muka ƙara sanin mutane suma suka san mu,wasu ma maƙotan mune...sai suyita kallo na saboda kalar idona..nidai ban damu ba

A karo na farko ina ƙare ma unguwar tamu kallo..unguwa ce mai kyau... akwai gidaje uku manne da namu daga gefen dama da hagu...a gidan ƙarshe can gefe akwai wata bishiyar dalbejiya inda masu saide saide ke yaɗa zango..sai nan gaban gidan mu kaɗan filin ƙwallo ne daga can gaba sosai akwai borehol da sauran su..

Kamar kada ranar ta ƙare saboda yanda muke nishaɗi...daga ƙarshe mun samu damar hawa lilon sai kuma muka taru duka mu manyan muna Are you ready...bakin Jay D ya kasa rufuwa

Da ƙarfe ɗaya muka watse kowa ya tafi wurin salla

'' to tunda kun dawo sai kuzo ku ɗaura abinda zakuci ko?" Turo baki Anaam tayi tana ƙunƙuni wai ba'a dafa abinci ba.babu wanda yabi ta kanta,Saida muka yi salla sannan muka dinga tunanin mai za'a dafa daga ƙarshe dai muka dafa taliya Jay d ta kira mamanta muka gaisa harda su Mama...

Da yamma muka koma wurin wasa mutane kamar ɗazu yanzu ma sun taru..wata wasa daban mai nishaɗantarwa muka yi...filin ƙwallon nan duk yan maza masu guntun wando...sai ƙarƙashin bishiyar dalbejiyan nan mutane sun taru sun rufa akan masu sayar da abubuwa...

Wurin magrib muka koma gida...nishaɗin da muka kwaso daga waje har lokacin yana tattare damu,yau akwai wuta hakan yasa bamuyi kallo da laptop ɗin Jay d ba...sauran ranakun da suka biyo baya farin cikin da muka tsinci kanmu a ciki baya misaltuwa da sauri ranakun suka wuce kamar basu taɓa kasancewa ba... Jay d ta koma gidan su muka dawo daga mu sai mu...wasannin da ake gaban gidan mu ba'a dena ba....

A nawa ɓangaren kuma na cigaba da neman aiki na, makaranta anyi sanarwa cewa wani sati zamu fara jarabawar wai mok (mock) kafin jarabawar ta gaskiya harda lesson akeyi...nima kuma na shiga musamman ajin da ake koyar da turanci...su Asma'u dasu Diyaam ma duk suna ciki...

+2349138091955

RU'UYAA…📖

₦500 ne idan ya kammala zai koma 800

Biya ta wannan account É—in 9138091955..Salma Aliyu opay

Shaidar biya ta +2349138091955

Autumn writes 📖🖋️

RU'UYAA
The dreams we never lived
By Autumn 17 🍁🍁

17. ...Matsaloli...🖊️

Yau weekend,wurin ƙarfe goma Asma'u na zaune saman lilo ita kaɗai ba kamar sauran ranaku ba da mutane ke tururuwa yau daban ne ... saye da wandon jeans da riga sai hijabi peach color fuskarta fayau amma kyaunta bai ɓoyu ba..a hankali take shilla lilon tayi nisa cikin tunanin Khalil tana tsara an impossible future with him murmushi tayi tana lumshe ido ta fara shilla lilon da ƙarfi da nishaɗi tana sama da ƙasa ko tsoro bataji

Da sassarfa yake tafiya hannunshi riƙe da baƙar leda,kayan jikinshi yadi baƙi yasha ruwa ya gaji takalmin ƙafarshi ma sun siɗe bai ankara da mutum a saman lilon ba...GBAM!! Ƙafafun Asma'u suka sauka a fuskar shi da ƙarfi har Saida yayi baya baya ya faɗi baƙar ledar hannun shi ta faɗi duk abubuwan dake ciki suka zube ya dafe gefen idonshi daya fashe yana zubar jini... Asma'u ta ƙanƙame lilon that was spiralling out of control a mugun tsorace ..sai jujjuyawa yake da ita yana haɗa tada bishiyar ta bugu ba kaɗan ba ihu kawai take...

'' kamar Asma'u ce ke ihu ko?" Cewar inna sarai data fito daga ɗaki a gaggauce hannunta riƙe da hijabi, Anaam ma ta fito saye da gyale suka fita daga gidan a tare...nidai ina kwance a ɗakin mu..yau ranar tazo min a wani irin yanayin ƙunci da har bana son ko motsawa,kamar inyita kwanciya kada in tashi...bawai dan na mutu ba... jan bargo nayi na lulluɓe har zuwa kaina...

Da ƙyar Mama sarai ta tsayar da lilon daga juyawa Asma'u ta ƙanƙame ta kamar tana gudun idan ta saki zata faɗi idonta a matuƙar firgice tana numfashi sama sama tambayar ta inna sarai take Meya faru amma ta kasa Magana sai juyawa tayi inda mutumin nan yake zaune..gaban rigar shi ya ɓaci da jini hannun shi ɗaya rufe da idonshi..su Inna sarai suka kalli inda take kallo

'' Innalillahi wa inna ilaihi raji'una meya faru?" Anaam ta kafe gayen da ido inna sarai take sallallami,wurin shi suka isa Anaam ta duƙa tana tattaro mashi abubuwan shi.. Asma'u ta duƙa gaban shi fuskar ta ɗauke da rashin jin daɗi.. batare da tunanin komai ba ta kai hannun ta,ta cire nashi dake rufe da idon...har wurin ya kunbura idon ma yayi ja

'' laahaula wala ƙuwwata illa billa...wai Meya faru ne?''

Murya na rawa Asma'u tace '' buge shi nayi ban san yana zuwa ba kayi haƙuri dan Allah...'' naɗan lokaci baice komai ba sai ƙoƙarin buɗe idon yake amma ya kasa..da sanyayyar murya yace

'' ba komai...'' hakan yasa Asma'u ta ƙara jin bata kyauta ba..she felt guilty..'' tunda kina da fes ait bos ki kular mashi da ciwon mana...'' da sauri ya girgiza kanshi '' ki bar shi kawai sauri nake..''

'' A'a bawan Allah tunda ita tayi maka wannan ta'asar kabari ta gyara dama nos (nurse)take so ta zama...''

bai sake cewa komai ba cire hannun ta Asma'u tayi daga fuskarshi ya miƙe da ƙyar suka nufi cikin gidan sai da suka fara shiga sannan ya bisu..kujera Anaam ta ɗauko daga kitchen ta ajiye mashi a tsakar gida.. Asma'u ta shiga ɗaki ta ɗauko first aid box a gaggauce ta fara wanke mashi ciwon bayan ta share jinin da auduga kamar yanda aka koya musu a practical.. sannu Inna sarai da Anaam suke mashi every now and then

Daga cikin ɗakin ina jin yanda suke ta yi mashi sannu suna ƙara bashi haƙuri harda Mama amma ban fita ba na cigaba da kwanciya ta...zuciya ta a ƙuntace na rasa inda zan sa kaina ji nake kamar in aske fatar jikina in sauya zuciya ta da komai nawa ko zan samu sauƙin abinda ke damu na...yaushe zan samu abin da na roƙa? Yaushe rayuwa ta zata sauya? Wayyo Allah na! siririn hawaye ne ya sauka daga idona nayi saurin share shi jin an ɗaga labule

'' wai Abeedah yau lafiya kuwa?" Inna sarai ce take tambayar yi nayi kamar ina bacci ban tanka taba...a can tsakar gida Asma'u ta gama addressing ciwon ta manna mashi auduga da plaster with expertise...ta sauke ajiyar zuciya tana kallon fuskar shi,samu tayi shima ita yake kallo ta ɗauke idon ta tareda miƙewa ta kwashe abubuwan da tayi amfani dasu tana faɗin

'' kabi a hankali kada ruwa ya taɓa wurin kaji...'' sai kawai ya gyaɗa kanshi ya nemi tafiya..inna sarai da Mama suka hanashi wai ya ɗan jira kaɗan..bai so yayi musu kawai sai ya zauna ɗin...Anaam ta jawo kujera ta zauna kusa dashi ta fara zuba kamar pamfo...shidai daga uhm sai uh uhm da murmushi a fuskar shi

Daga lokaci zuwa lokaci idonshi ke kaiwa gefen da Asma'u take duk tayi sanyi..bayan wani lokaci ya miƙe cike da girmamawa yayi ma su Mama sallama..sosai suka ƙara bashi haƙuri akan abinda ya faru yace ba komai ya ɗauki ledar magungunan shi ya ƙara kallon Asma'u one last time da murmushi kafin ya fice...

'' kamar in bishi...''

'' daga ganin mutum kamar ki bishi to ki bishi É—in...'' turo baki Anaam tayi da abinda inna sarai ta faÉ—a...

Ji nayi fuskata ta fara ƙaiƙayi ban wani damu ba na cigaba da kwanciya ta amma ƙaiƙayin ya cigaba...tashi zaune nayi na fara sosawa ƙaiƙayin ya ɗan rage na ƙara yin kwance ina kallon ceiling...nan bacci ya kwashe ni...

'' Innalillahi Asma'u zoki ga fuskar Abeedah sama sama nake jiyo hayaniyar su hakan yasa na buÉ—e idona''

'' taɓ ɗi jam...'' Asma'u ta rufe baki tana jinjina kai faɗuwa gabana yayi da sauri na tafi gaban madubi take zuciyata ta tsuke kamar ana matse min ita da ƙarfi ƙirjina ya fara sama da ƙasa na kasa kuka sai raɗaɗin da zuciya ta take yi wasu manya manyan pimples ne suka ƙara fito min da yawa kamar an watso su a ƙarƙashin haɓa da goshi da hanci...

'' wani abu kika sha hala?" Anaam ta tambaya tana duba ni nan da can. lumshe idona nayi hawaye suka fara silala kafin jikina ya fara rawa kuka na ya fara fita da sauri ...sukayi tsaye suna kallo na babu wanda ya lallashe ni

'' wai Meye nake jin tashin kuka?" Inna sarai ta shigo cikin É—akin..nuna mata ni Anaam tayi

'' ƙuraje ne suka fito mata a fuska shine take kuka...'' inda nake inna sarai ta iso

'' na gani...'' itama ta shiga duba fuskata daga gefe da gefe

'' ƙila wani abu tasha ko ta shafa..'' ina ji suna cinke cinken abinda nayi dayasa fuskata ta lalace har haka ban buɗe idona ba ƙuncin dake raina baya misaltuwa meyasa ni kaɗaice ta daban? Meyasa kowa yana rayuwa cikin sauƙi da jin daɗi banda ni?

Ƙara rushewa da kuka nayi inna Sarai take lallashina har da cewa zata taya ni tafiyar dasu hakan yaɗan rage min wani abu kaɗan ba mai yawa ba Asma'u da Anaam kallo kawai suka bini dashi

'' ke baga jiki ba ke baga kyau ba..oh ni tuwo..wannan abu haka? gaki da shegen tsawo mutum tsaf zai É—auka ke namiji ne..''
Chapter 39 · 0% Book details