← Book details Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 67

Sashe 37

Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babu wanda ya ƙara magana suka fara cin abincin su ni na kasa cin abincin a gaban mutane da yawa.. musamman kuma da wannan ɗan rainin wayon da duk abinda ake bai ce ko ƙala ba...Anaam hannu baka hannu ƙwarya zar ban takaici kamar bata taɓa cin abinci ba... Jay d tana ci kamar irin na yan gayu... Asma'u kuwa wasa take da abincin ba wani ci take ba Baturiya da Khalil wani abinci sukayi oda..ni wallahi ƙyama abun yake ban kamar zanyi amai da sauri na ɗauke kaina kada suce nayi musu rashin mutunci...

Bamu bar wurin ba sai wurin ƙarfe huɗu da rabi,Khalil yasa aka samin nawa abincin a take away dukan mu harda romo muka fito har hadari ya taru kamar ruwa zasu iya tsugewa a koda yaushe,shuke shike nan sai rawa suke da iska..ƙamshin ƙasa ya fara tashi wurin yayi duhu mutane wasu na shiga wasu na fita..naji wani irin mutuwar jiki ya ziyarce ni saboda wannan hadarin muka haɗa ido da Asma'u itama dai abinda ke raina shine a nata bamu taɓa daɗewa har haka bamu koma gida ba na juyo na kalli baturiya laƙame da Khalil kamar zata koma cikin shi suna magana suna dariya Romo yana tafiyar shi da ɗaiɗai hannu cikin aljihu duk shine a baya,juyawa Khalil yayi yana mashi magana da wani yaren daban fahimta ba

'' ni na kawo sune da zan mayar dasu?" Ƙatuwar Muryar shi ta karaɗe wurin duk da bada hayani ta fito ba..gabana ya faɗi Ko kaɗan bana son zama inuwa ɗaya dashi taya zai mayar damu kuma?...

'' Capri pls we have some catching up to do okay '' baturiyar ce ta faÉ—i hakan muka koma rarrabar ido dasu Jay d Anaam dake kusa da Asma'u tace

'' Allah dai yasa ba wannan mai takunkumin'' ban iyarda jin abinda zata faÉ—a ba nayi gaba iska na kaÉ—a hijabina da sauri na tare jikina ta gaba da baya na tafi na tsaya wurin motar shi...

a maimakon su iso sai naga ya tsaya ya nuna musu wata baƙar mota irin tashi mai baƙin glass duk da a ɗan kwai tazara tsakanin mu,naga yanda fuskokinsu suka canja da alamu suma basu so Jiki a saɓe sukayi mashi godiya, baturiyar tana yi musu bai bai suma sunayi mata suka wuce biye da Romo a baya

Asma'u take ji kamar tayi kuka ko kaɗan bata so haɗa su da Roman da Khalil yayi ba,a nata lissafin da zatayi duk yanda zatayi ta zauna a gaba kusa da khalil amma yanzu duk wannan ya rushe taji hawaye sun cika idonta musamman data ga yanda Leona ta kanainaye Khalil wani irin pang of jealousy ke sukar zuciyar ta at the same time tana ji inama ace itace in place of Leona take bin bayan su da kallo iskan daya ɗan fara tasowa sai kaɗa gashin Leona yake, Khalil ya share mata gashin zuwa bayan kunnen ta suna murmushi kamar masoya ɗauke idonta Asma'u tayi ƙololon abinda ya tsaya mata a maƙoshi sai ƙara girma yake ta juya ta isa motar Roman

suna isowa Khalil ya buÉ—e mata motar ta shiga tana dariya akan wani abu daya faÉ—a da alama basu ma lura Dani ba...

sai daya rufe motar sannan idonshi ya sauka akaina ji nake kamar zanyi kuka

'' kitten...'' turo baki nayi idona suka ciko da hawaye sai ya zagayo sashen da nake yana kallo na..ɗauke idona nayi ina ƙoƙarin danne kukan dake taso min

'' kina buƙatar wani abu ne?" Ya tambaya bayan ya gama kallona sama da ƙasa '' m..meyasa kace ya mayar damu gida? Dama ka bari mun hau abun hawa da zai fi idan fa ya sauke mu a tsakiyar hanya..?"

Nayi maganar ina kallon fuskar shi idona suna ƙyallin hawayen matsowa ya ƙarayi da murmushi a fuskar shi yace '' shine yasa zakiyi kuka?" Kwaɓe fuska nayi tare da kallon gefe '' akan me zanyi kuka?"

'' that you're missing me already...'' ya bani amsa na taɓe baki wai kewar shi taɓ ɗi jam

'' anyways kada ki damu Rome zai kai ku gida lafiya lau trust me yana da mutunci idan kin sanshi...''

wai yana da mutunci idan na san shi bai yi kama da masu mutunci ba wallahi buɗe motar yayi ya ɗauko jakunkunan mu ya riƙe '' mu tafi in raka ki''

badan naso ba muka jera muna tafiya nake ji kamar kada mu rabu nidai ko kaɗan wancan Romo'n bai yimin ba wallahi... mun kusa isa na miƙa hannu

'' kawo jakunkunan budurwarka na jiranka...'' miƙo min jakunkunan yayi da murmushin zolaya

'' ko kema kina so ki zama budurwata ne?" girgiza kaina nayi ina kallon jakunkunan naso in rataya jakar Jay D da Asma'u amma hakan na nufin hijabina zai mannu da jiki na za'a ga abinda nake ƙoƙarin ɓoye rashin shi sai kawai na riƙe jakunkunan a hannun haguna jakata data Anaam ana dama na ɗago fuskata a marairaice nace '' toh kazo muje sai idan ya sauke mu sai ku dawo ku ɗauki ɗayar motar dan Allah''

nan ma hawaye suka ƙara cika min ido na rasa dalilin hakan amma dai sahihin bayani shine bana son kasancewa inuwa ɗaya da Romo....

Shafa gefen fuskarshi yayi ya ranƙwafo murya ƙasa yace '' oh kitten..ki dai ce bakyason rabuwa dani...ko?" zaro idona dake cikin nashi nayi hawayen sai suka kwanta a ƙasa suna sheƙi amma basu zubo ba..baki na ya buɗe amma na kasa cewa komai... murmushi yayi ya ware hannayen shi tare da faɗin

'' let me hug you goodbye...'' ya fara ƙoƙarin rungume ni kuwa da sauri naja baya kumatuna sukayi ja na kasa cewa komai na juya na bar wurin harda ɗan guduna ina jiyo dariyar shi mai daɗin sauraro daga baya na yana faɗar abinda banji da kyau ba sai da nakai wurin motar Romo sannan na juya na kalle shi har lokacin yana tsaye a wurin hadari ya ƙara tasowa farfajiyar restaurant ɗin ta ƙara duhu sassanyan iska na busowa bishiyoyin sai rausayawa suke da iskan dake kaɗa su yayyafi aka fara kaɗan kaɗan Rungume hannayeneshi yayi murmushin shi yaƙi ɓacewa sai kuma ya ɗaga min hannu na turo baki Ina ji kamar in bishi yana da kirki sosai...

Ɗauke idona nayi na mayar akan motar da zan shiga baya na buɗe na same su zaune a takure wuri guda kamar waya'nda ke zaune saman garwashi kowa dai ya kama kanshi so nayi in zauna a baya amma duk sun mahe wurin Anaam harda faɗi ƙasa ƙasa

'' ke kije ki zauna gaba kada ki takura mana anan...'' Asma'u ta gyaɗa kai alamun gamsuwa tana harara ta kamar na tare mata wani abu bana son rigima yasa na ajiye musu jakunkunan su..nabar ƙofar buɗe idan sunji haushi su rufe jiki a sanyaye na buɗe gaban na shiga shegen turaren nan nashi mai ƙarfi da wari kamar kashi ya cika min hanci ko kallona bai yiba sai ma wayar shi da yake daddannawa shiɗan rainin wando da Khalil ne da bazai yi mana haka ba...

Rufe ƙofar nayi na takure waje ɗaya sai daya gama ɓata lokaci sannan ya miƙa farin hannun shi ya kunna motar ya gyara zaman shi ya fito da motar daga inda take pake dukan mu muka yi shiru da ƙyar muke numfashi kamar muna gudun ɓata mashi rai gaba ɗaya yanayin motar Ba rayuwa a ciki ba kamar ta Khalil ba dogon tsuki naja batareda na ankare ba amma duk da haka bai kalle ni ba Tsayawa yayi daidai inda Khalil ashe har lokacin yana tsaye a wurin na ɗauka ya koma motarsu...

Sai daya gama shan ƙamshi sannan yayi ƙasa da glass ɗin fuska sake yace '' Rome dan Allah ka kaisu har ƙofar gida...Kitten tace wai sauke su zakayi a tsakiyar hanya.. don't do that...''

yayi maganar yana min murmushi nikam na turo baki batareda nasan nayi hakan ba murmushin shi ya faÉ—aÉ—a

'' hmm sauke su tsakiyar hanya sounds epic''

dariya Khalil yayi yace '' ayi haƙuri...'' baice komai ba ya kalli bayan motar yana yi masu Jay D bye bye sannan ya ƙara kallona nima shi nake kallo

'' ka fita daga cikin ruwa kada ka kamu da mura'' inji Asma'u sai ya gyaɗa kai batareda ya cire idonshi a nawa ba yaja baya sannu sannu glass ɗin ya fara yin sama tun ina hango shi har glass ɗin ya rufe duka naji kamar ina zaune a keji na ɗauke idona inajin wani abu a zuciya ta daban taɓa sanin meye shiba...

Da ƙarfi ya figi motar muka fita daga wurin amma wani sashe na zuciya ta har lokacin bai dena son kasancewa tareda Khalil ba bata dena burin ina ma ace shine a maimakon wannan..ugh!! ƙara shigewa nayi cikin kujerar ganin uban gudun da yake shararawa kamar zai aika mu lahira

suma a can baya sun ƙanƙame juna ido waje suna shinshino ƙamshin mutuwa..shi mugun hankalin shi kwance zuciyar shi zaune...runtse idona nayi ina karanto addu'oi ƙasa ƙasa wani irin wawan burki ya taka dayasa nayo gaba kaina ya haɗu da gaban motar naji zafi sosai suma daga baya goshin Anaam ya bugi bayan kujerar da nake zaune badan taso ba tayi gum da bakinta da jin zafi na ɗago ina kallon shi idona cike da hawaye ina murza wurin amma bai ko kalle inda nake ba bare ya bani haƙuri sai ma gabanshi da yake kallo hankali kwance kamar bai san abinda yayi ba 'Mugu kawai..' na faɗa ƙasan maƙoshi..gani nayi yana shafa sumar shi kamar yanda cikakkun mugayen mutane suke yi a cikin fim sai yayi baya ya jingina da kujerar ƙila yaji abinda na faɗa,hararar shi nayi kafin na kalli gaban mu ashe wurin tirafic muka kawo motoci da mashuna sun cika wurin..ruwa ake kamar da bakin ƙwarya...nake kallon wannan baƙin abun dake faman share ruwan dake zuba a gaban motar tashi

Hannun rigar shi yaja...agogo mai bala'in kyau ya bayyana...yayi ƙasa da kanshi yana duba lokaci na lura da R-MAN da aka rubuta a farar fatarsa da wani handwriting mai bala'in kyau da baƙin bairo ƙila..daga gefe kuma hoton ƙwarangal irin na kai da ƙasusuwa ☠️

🍁: Tattoo ne
Chapter 37 · 0% Book details