Sashe 41
Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Koda muka shiga aji sai alhini suke wasu suna faɗin baza su rubuta jarabawar ba dasu biya dubu saba'in da biyar Gara sun kama sana'a...ni kuwa nawa tunanin shine dole in ƙara ƙoƙari wurin neman aiki zama nayi ina cigaba da tunani naji wasu daga gefe na suna faɗin '' wai fa ba'a haɗa da kuɗin lesson ba...in an haɗa dasu dubu tamanin da biyu ne...'' da ƙarfi na juyo
Wacce ke shan ruwa kusa da wacce tayi maganar ta fesar da ruwan ta window ido zare '' dubu tamanin da biyu? Kam bala'i da yake dai Allah yasa ba lesson ɗin nake ba...'' wacce ta fara magana da farko ta sheƙe da dariya '' dey play..yarinya ko kinyi lesson ɗin ko bakiyi ba dole sai kin biya...''
Ajin ya kacame da surutu kowa yana ƙorafin kuɗin sunyi yawa...ina zan sama mana kusan dubu ɗari biyu da arba'in da wani abu? ɗauke kaina nayi na koma kallon window..ina hango bishiyoyin da ganyayyakin su suke Kore shar...hasken rana na ƙarama kalar su haske,ga yara can ƙila yan SS 1 da 2 suna kai kawo wasu na shiga aji wasu na fita babu ruwansu da abinda ya shafe mu..mu yan SS 3...haka zalika babu wanda yasan abinda ke raina babu wanda yasan matsalolin dake damuna... Bana tunanin akwai abinda za'a faɗa idan dai ba kuɗin za'a kawo ba da zai canja min yanda nake ji a raina...oh Allah ni Abeedahtu tako wace fuska ina da matsala...
'' Bee...'' Jay d ta jijjigani tana yaƙune fuska ta kasa fahimtar me nake tunani da har banji taba...'' me kike tunani haka?" Matsa mata nayi ta shiga ta zauna ƙamshin turaren ta yaɗan sa naji yar ƙaramar nutsuwa.. Diyaam ma ta zauna a nata gefen sai lokacin naga ashe Itama tasa uniform sosai tayi kyau farar fatar ta ko mutum bai taɓa ba zai san tana da laushi
'' lesson É—in da akace wai ko mutum bai yiba zai biya sannan ni ban san cewa ana biya ba wallahi..'' na faÉ—i rabin gaskiyar abinda nake tunani...juya idonta Jay d tayi '' dama suna abu kyautane?" Na girgiza kaina...na juyo gefen Diyaam
'' Ma sha Allah Sofia Diyaam tayi kyau'' tayi murmushi batace komai ba... Daga nan malamin literature ya shigo ajin.. mayarda hankali mukayi akan abinda yake koyarwa musamman ni..a da bantaɓa jin ina buƙatar in mayarda hankali ba domin in fahimci karatu ba saboda na riga da na yarda cewa bazan gane ba..amma yau daban ne,ina so in fahimci abinda ake koyar damu...kuma ƙwaƙwalwa ta taƙi bani haɗin kai..amma na tilasta kaina..bayan ya tafi nasa Jay d da Diyaam suka ƙara yimin bayani...
''.you know what? Idan an tashi ki biyo ni gida mu dinga study session akan English da math.. kin ji?" Jay d tayi maganar tana kallo na...'' idan na biki,wazai nema min aiki?" Dogon numfashi taja.. Diyaam tabi mu da ido...'' zamu iya duk lokaci guda...ina nufin,idan mun fara mock,wasu ranaku zamu tafi gida da wuri sannan jarabawar Bama dole bace.. idan mun gama study session sai ki tafi neman aikin...'' gyaÉ—a kaina nayi da gamsuwa da abinda ta faÉ—a....
'' zamu iya farawa yau?idan an tashi tara''
'' idan kina so...'' murmushin jin daÉ—i nayi...daga nan muka cigaba da hira.. Diyaam ta bamu wani cakulet da muka tambaya ina ta samu saboda daÉ—in cakulet É—in
'' hamma na ya kawo Mani daya tafi ƙasar su...'' kallon ta mukayi dan bamu fahimci abinda take nufi da 'ƙasar su'' ba amma bamu yawaita tambaya ba Anaam itama ta shigo cikin hirar...bayan an tashi tara bamu fita ba,maka Jay d ta ɗauka tayi rubutu a gaban allo..sannan ta juyo ga sauran dake cikin ajin tace
'' ina bada study session kyauta ga duk mai so zai iya shigowa... subjects ɗin da nake koyarwa math da English da literature..'' rabi da kwatan yan aji duk sukace suna so yan kaɗan kawai ne suka tafi wasa...Jay d ta tsaya gaban allo tana mana bayani da ƙwarewa da kuma haƙuri...yanda take bayanin ko wani malamin albarka.... Kuma ina fahimta dama tun farko matsalata ba rashin fahimta bane sai na fahimta na gane sosai amma kuma nan da ƙanƙanin lokaci sai in daburce idan an tambaye ni...
Bayan an tashi makaranta mu yan SS 3 muka tsaya domin lesson ɗin....sai ƙarfe huɗu muka gama.. sallah muka fara yi sannan kowa ya kama gabanshi...yan ajin mu sai godiya suke ma Jay d..nida kaina naji ina alfahari da ita
Wurin famfo muka tsaya mu biyar ɗin,muna wanke ƙafafun mu da suka ɓaci da ƙasa..nake kallon ranar data zama ja ta fara tafiya gida sai kuma makarantar mu data zama empty ba mutane da yawa duk sun fita...ajujuwan mu da wasu tagogi suke buɗe...ƙaraurawar dake maƙale da bishiya bata da mai bugata...da yan tsiraran mutane da suka rage...wasu suna wasa a hanyar su ta fita..wasu suna da yawa..wasu su kaɗai suke tafiya..ba kowa tare dasu...
Wasu da murna da farin ciki a fuskokinsu wasu kuma... fuskokinsu ba walwala naji abu ya tsaya min a ƙasan ciki..kamar kada mu tafi...kamar mu koma aji...bana so in rabu dasu..na gode Allah daya sa bani kaɗai ce zanbi hanya ba da irin fanƙon (emptiness) da zanji sai ya ninka wanda nake ji a yanzu...
'' mu tafi...'' Diyaam data gama wanke fuskarta ta faɗa...a tare muka jero muna tafiya suna hira nidai nayi shiru ina sauraren su... A bakin gate muka samu motocin su Jay d da Diyaam sun iso kafin muyi wata tafiya mai nisa... dolen mu muka yi musu bankwana suka shige motocin su,mu kuma muka cigaba da tafiya a ƙasa... Na juyo ina kallon wa'yanda ke bin hanyar nan da mutane da yawa ke bi...rana ta haska bayan su,mu kuma muna fuskantar ranar...ina cikin yanayi...ban san abinda kemin daɗi ba...har ji nake kamar in jawo gobe... Jay d..da Diyaam..su nake kewa duk da bamu daɗe da rabuwa ba...sai kuma damuwar data maƙale min a zuciya kamar baƙar tsutsa... (leech)
Da muka koma gida babu wanda yayi maganar kuɗin makaranta...kawai muka yi wanka muka ci abinci..na fito bakin ƙofar gidan mu domin wasa da sauran dake wurin..abubuwa suna tafiya dai dai da farko su Asma'u ma suka fito suma..bada daɗewa ba mutane suka soma taruwa...
Ina tsaka da lilo naji wata mai suna A'e tana faɗin '' fuskar ki Abeedah kamar anyi ƙunar baƙin wake...duk ta gwalje ta lalace...'' wa'yanda ke kewaye damu suka fashe da dariya...lilon dake shilla wa da ƙarfi... Ya rage tashi kamar farko...naji kamar an soki zuciyata da mashin da aka ɗosana cikin wuta....
'' wallahi kuwa da gaskiyar ki..da nice da irin fuskarta,da bana tunanin zan iya fitowa cikin mutane...'' inji Sumayya...sauka nayi daga lilon... Wata yarinya ta hawo..na ƙaraso inda suke
'' cin fuska har a gabana baxaku iya bari in bar wurin ba?" Nayi maganar da ɗacin rai...da farko zaune suke sai suka miƙe '' wasa muke fa..ke baki iya ɗaukar wasa bane?" Haleema ɗaya daga cikinsu take min kallon rainin wayo...
Haɗiye abinda ya tsaya min a wuya nayi...na kalli A'e '' Fuskata bata gwalje ta lalace ba A'e,ƙila rashin idon ne yasa kike ganin haka...ina nufin,mutum mai ido biyu yafi mai ido ɗaya...ki kalli kanki a madubi A'e...ƙila shima ɗayan idon naki ya fara samun matsala...'' sakin baki A'e tayi tana kallona suma sauran sukayi shiru Anaam ta matso kusa tana hararar su, wurin yayi tsit da wani iska mai nauyi na juyo na kalli Sumayya
'' da yake ni bana kunyar fitowa da yanda fuskata take..ba sai nayi kwalliya mai yawa ba don ɓoye Fuskata da yake Allah ya rabani da yawo da fuskar da gefe guda fari gefe guda baƙi kamar anyi gobara tsabar bleaching...'' Sumayya ta zaro ido...da alamu mamaki take ya akayi na sani...
'' haba Abeedah akan me zaki dinga zaginsu har haka ke baki san wasa ba..?" Aliya da batayi magana ba tuni ta furta..ganin yanda suka yi shiru kamar ruwa ya cinye su... dariyar da bata kai zuci ba nayi..ina danne baƙin ciki na...'' wasa?"
na É—ago idona ina kallon su duka
'' lokacin da suke wasar sun yi tunanin yanda zanji? Sunyi tunanin wani irin yanayi hakan zai jefa Ni? Sunyi tunanin wane irin tasiri hakan zai haifar a zuciya ta da rayuwa ta?..."
Na dakata ina share hawayen da suka sauko min dukan su jikinsu yayi sanyi na cigaba da faÉ—in
'' mafiyawancin mutane suna faÉ—in abinda yazo kansu ne batareda tunanin yanda wanda aka faÉ—awa maganar zaiji ba...a wurin su wasa ne..abin ayi dariya...amma wanda aka faÉ—a mawa? Baya mantawa! Wasu har su mutu wannan maganar tana kasancewa dasu ta rayu dasu....wasu maganar tana gina su wasu kuma ta rusa su... Akan mai zasuyi wasa da abinda bani na É—aurawa kaina ba? Ita A'e da take da ido É—aya,ita ta halicce kanta a haka? Meyasa bazatayi tunanin yanda zata jiba idan wani ya faÉ—i magana akan yanayin halittar ta? Bana son irin wannan wasannin!"
Na ƙarashe maganar da gargaɗi ban jira cewar kowa ba na wuce ciki...kallo ya koma akan su A'e..da yawan su sun gamsu da abinda na faɗa...ai babu wanda zaice ba'a taɓa faɗa mashi wata maganar data tsaya mashi a rai ba ko?
'' ku iya bakin ku idan ba haka ba wata rana zai saku a matsala...'' cewar Asma'u kafin ta wuce ciki...da nadama a muryarta A'e tace '' dan Allah Anaam ki bawa Abeedah haƙuri...'' suma sauran abinda suka faɗawa Anaam kenan....
+2349138091955
RU'UYAA…📖
₦500 ne idan ya kammala zai koma 800
Biya ta wannan account É—in 9138091955..Salma Aliyu opay
Shaidar biya ta +2349138091955
Autumn writes 📖🖋ï¸
RU'UYAA
The dreams we never lived
By Autumn 17 ðŸðŸ
18. ... tawakkalin da nake so...🖊ï¸
Da na shiga gidan,daurewa nayi na hana kaina kuka na danne baƙin cikina kuma na hana zuciya ta..tambayoyin da take rattafo min a duk sanda abubuwa suka kasance kamar haka...
Dogon numfashi naja sannan na shige cikin gidan ina kallon tsakar gidan da ba kowa sai na wuce É—akin Mama