← Book details Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 67

Sashe 32

Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'' ban shirya amsar bulala da safen nan ba''

na bata amsa nima murya ƙasa ina jin haushin Mutumin nan har cikin raina...yan matan suka nutsu na girgiza kaina

'' excuse me uncle saminu munyi sababbin baƙi''

Malam murtala ya faɗa tare da shigowa yayi ma baƙin alamun su shigo ciki,zamu sake tashi mu gaishe shi yace mu zauna macijin sari ka noƙe ya kafe baƙin da bamu san ko waye su ba da ido dan sun ɓoye bayan malam murtala

'' class monitor?"

Ya kira yana kalle kalle da sauri ta fito ta tsaya gaban shi

'' ga baƙi idan malamin ku yazo sai ki nuna mashi su a sa sunan su a rijista ''

ta gyaɗa kanta yayi ma macijin sari ka noƙe godiya sannan ya tafi

Sai lokacin naga ashe Anaam ce da wata bafilatana kai!! da duk ajujuwan dake makarantar sai ajinmu za'a kawo ta Innalillahi na ɗaure fuska ganin yanda yake binta da ido ƙasa ƙasa yana lasar baki, saye take da riga da skirt da suka kama ƙugunta da mazaunan ta.. dan tana dasu ma sha Allah amma itama ƙirjinta kamar nawa..nata ya ɗanfi nawa girma.. farar fata,ƙaramar fuska manyan idanu da dogon hanci ƙaramin baki wanda kalar take pink gashinta irin na Asma'u. doguwa ce itama bata da ƙiba... Hijabinta fari zuwa guiwa hannunta riƙe da jakar leda da littafai a ciki fuskarta kamar zatayi kuka Ɗayar kuma dogon hijabin ta ruwan ƙasa ya ɓoye kayan dake jikinta har ƙasa yake kanta ƙasa.amma dai fara ce sosai kamar zabiya...

'' zoku zauna!" Class monito ta faÉ—a tana nuna masu wuri....'' yarinyar can kyakkyawa'' Jay D ta faÉ—a a kunne na tana nufin Anaam '' sai shegen tsiwa '' na bata amsa

'' kin santa ne?" Kafin in bata amsa naji yana faÉ—in

'' baƙi su gabatar mana da kansu ko?" Anaam ta kalli macijin sari ka noƙe...sai ta ɗauke kanta da wata ƙaramar Muryar munafunci tace

'' Sunana Sha'awanatu Is'haq Anaam ''

Yan aji basu ce komai ba amma na tabbatar kowa da magana a bakin shi..ɗayar baƙuwar kuma da sanyayyar murya mai daɗin sauraro tace

'' Safiyya Muhammad Diyaam''.ya ɗauke kallon shi daga Anaam zuwa Diyaam data mayarda kanta ƙasa bayan ta gama gabatarda kanta,Ma sha Allah kyakkyawa ce sosai tana da gashin gira baƙi mai yawa..ga gashi kwance a goshinta....itama bakinta ƙarami laɓɓanta jajaye

'' Ma sha Allah Sha'awanatu da Safiyya..kuje ku zauna..''

yayi maganar yana nuna masu seat É—in mu nida Jay D,da kuma wanda ke gefen mu,dama mukaÉ—ai ne zaune mutum biyu.Anaam taci magani da idon mu ya haÉ—u..na É—auke idona daga kallonta

Seat ɗin gefenmu ta zauna hakan ba ƙaramin daɗi yayi min ba

,'' matsa mata ta zauna mana!" Inji macijin sari ka noƙe ni nayi nisa cikin tunani ita kuma yarinyar tayi min tsaye a kai maimakon tace in matsa wasu mutane dai...!!

Jay D ta fara matsawa sai nima na matsa ta zauna a hankali tana ajiye jakarta mai hoton yan matan nan masu dogon gashi

🍁: Disney princesses

Izini parinses...sosai jakar tayi min kyau amma ta Jay D da take baƙa tafi kyau

Bata ce mana komai ba muma ba muyi mata magana ba yana koyarwa idonshi na yawo tsakanin Anaam da Diyaam shiÉ—an abinda ban ceba...

'' na kawo mana abinci yau '' Jay D ta faÉ—a muna coper note daga allo '' har naji ina jin yunwa '' amsa mata... tayi murmushi '' ranar da kika tafi kamar inyi hauka...''

'' nima nayi kewarki s....''

'' Abeedah Abdul wahhab Jadeedah Ahmad ku tashi tsaye!"

Inji macijin sari ka noƙe yan aji suka bimu da ido kamar basu san muba tsabar gulma da tsegumi

Miƙewa mukayi muna cigaba da maganganun mu da rubutu a paper...

Ya juyo yana kallon yan aji yana musu bayani sai sintiri yake a layin mu...kai!! Allah ya wadan naka ya lalace...

Koda aka tashi break riƙe mu yayi wai zai mana test....sosai nake ji kamar in shaƙo mugu

'' ku zauna '' ya faÉ—a Jadeedah harda godiya
Bayan ya gama rubuta tambayoyin ya samu ya zauna saman desk ɗin wasu yan mata bayan ya Kore wacce bata da kyau a cikin su,ya ɗaura ƙafar shi inda ake zama ya wani buɗe ƙafafu zaman iskanci

Duk wanda yaga yanda yayi zaman zai É—auka nomal abune amma Ni Abeedahtuwo nasan akwai manufar hakan ...

'' malam zan iya shigowa?'' Asma'u da bata san kowane malami bane ta nemi izini.. batareda ya kalli ko wacece ba yace '' shigo ''

Anaam na ganin Asma'u ta wage baki tana murmushi Allah ya gani ita babu abinda ta gane ga yunwa dake cin hanjinta Asma'u na murmushi ta ƙarasa seat ɗin su Anaam

'' Allah ya kawo min É—auki.. dan Allah tayani rubutun nan dan ban gane ba kuma ban san amsar ba...''

sai ta matsa ma Asma'u ya kasance su huÉ—u ne a seat É—in dukansu babu wanda yasan komai...

'' ke kin matse mu!"

Wadda ke ƙurya ta faɗa tana ya mutse fuska.. sharply Anaam ta kalle ta '' nasan babu abinda kika sani dan kin samu za'a taimake mu shine kike yimana baƙin ciki ko?"

Ɗayar ta kalli yarinyar dake ƙurya fuska ba annuri tace '' kiyi shiru dalla...tana gamawa zata tafi ai...''

Asma'u ta fara rubuta amsar suna kwashewa...É—ago kanshi yayi daga wayarshi da yake latsawa suka sauka akan Asma'u...

'' ke me kike yi a nan?"

Ya tambaya da ƙarfi yana cin magani..sai lokacin Asma'u ta lura da shi

'' n..na..t..nemi izini...'' tayi maganar a rarrabe

'' zoki fita!" Ya faɗa a fusace yana hararar ta ta miƙe sum sum ta fita daga ajin ya fesar da numfashi mai zafi kafin ya koma ya zauna....

Na taɓe bak Juyowa inda sabuwar yarinyar nan take nayi naga rubutun mu iri ɗaya dukan mu a seat ɗin yanda take rubutun a nutse a kuma a hankali Na ɗauke idona na mayar akan nawa paper da Hausa nake rubuta amsoshin duk da kuwa zan iya kwafa wurin Jay D amma dai na fison inyi da kaina minti goma yaci cikin break ɗin mu sannan yace wai a zo a dinga submitting ɗaya bayan ɗaya

matan suka yi tururuwa a gaban shi suna botsare botsare gaskiya basu da kamun kai Anaam ce ta ƙarshen kaiwa yake binta da wani matsiyacin kallon ƙasan ido kamar in sa biro in tsikare shegun idon nan nashi ..

'' class monitor zoki taya ni É—aukar wa'yannan papers É—in''

yayi gaba yarinyar biye dashi '' ɗan iska '' na faɗa murya ƙasa.yana fita aka fara surut wasu suna gulmar Anaam akan yanda tayi magana da kuma yanda itace ta ƙarshe wurin kai paper ta ita kam ko ajikinta na kalli window naga ashe akwai hadari kaɗan sai kuma masu sayarda abubuwa mutane sun dabaibaye su Na juyo na kalli baƙuwa daidai itama ta juyo idon mu ya haɗu na zaro mata idona

'' Innalillahi!'' ta faɗa dafe da ƙirji nida Jay D muka yi dariya

'' Tuwo samin wannan a jakar ki dan Allah '' Anaam ta faÉ—a tana turo min littafanta

'' salan jakar ta katse ko? ban sawa!"

'' mtchewww... Matsala ta dake baki da mutunci..''

ta faɗa tana juya ido ta ƙara da faɗin '' ina ne ajin su Asma'u?" Share ta nayi...

'' kin santa ne?" Jay D ta tambaya '' ɗiyar ƙanwar Maman muce...''

'' cousin É—inki ce kenan?"

'' koma me hakan ke nufi, eh ''
Bata ce komai ba ta jawo wata jakata fito da babbar kula

'' su Jadeedah me aka kawo yau kuma?"

Habeeba ta tambaya miƙa masu kular tayi tace

'' gashi dukan ku kuje kuci ''

sai ga yan mata da yawa sun yo wurin seat ɗin mu,kafin habeeba ta karɓi kular wasu sun rigata a wani seat ɗin ƙarshen aji suka tafi duk mutanen dake ajin ƙalilan kaɗai ne basu tafi ba kan kasani sai gasu suna wasoso hannu baka hannu ƙwarya suna zage zage..wasu an ɓata masu hijabi

'' me kika kawo masu?" Na tambaye ta

'' kaza,zo muje wurin masallaci '' ta miƙe tare da ɗaukar jakar baƙuwar na ganin zamu wuce ta miƙe ta bamu hanya

'' zo mu tafi..'' tayi maganar tana kallon yarinyar sai da taÉ—an yi jim na yan sakanni kafin ta É—auki jakarta ta biyo mu

'' Anaam mu tafi '' na kira ta ganin tayi zaune

'' ai na É—auka kin manta dani!" Ta faÉ—a da gatse ban tanka ta ba...

''.mun gode Jadeedah.. Allah yabar ƙauna!!" Yan ajin suka faɗa ta window... cike da jin daɗi

'' Ameen '' Jay D ta amsa..hannunta riƙe da nawa..

Mu huÉ—u muka jero muna tafiya...'' ranar kina tafiya Deen ya dawo da daddare...''

''.yayan ki?" Na tambaya duk da nasan shiÉ—in take nufi

'' a'a ubana!" ta amsa dajin takaici kamar zata kaimin duka ''haha Jadeedahtu Jidderh ƙawar Bee...'' muka yi dariya nida ita Anaam taja tsaki

'' ashe kice Jadeedah?"

'' baki da kunnuwa ne? Baki ji abinda kowa yake kiranta ba?"

'' kewai tuwo naga sai wani zaƙewa kike daga kinje gidan su kin dawo ita ɗiyar masu kuɗi ce ke ko da kike ɗiyar talakawa wahala zaki sha in gaya maki toh yayi''

zan bata amsa Jay D ta hanani hakan yasa nayi shiru ina jin haushi sosai...

Yarinyar nan kuwa shiru tayi kamar babu ita a wurin..duk inda muka wuce sai ayita kallon har muka iso wurin masallacin ba kowa muka zauna saman dakali sai ga Asma'u tazo itama ta zauna tare da mu Anaam na ganinta ta fara zuba kamar pamfo

Kular ta ciro ta ajiye tsakiyar mu sannan ta ɗauko ruwan gora ta wanke hannunta ta miƙa min,na wanke na miƙa ma baƙuwar yarinyar..saita girgiza kanta alamun bazata ci abincin ba..na ƙanƙantar da idona

'' kina tsorata baiwar Allah '' Asma'u ta furta

'' ni ba mayya bace bafa... kuma idan naba mutum abu dole ya karɓa'' na riƙon hannun ta na wanke mata tayi tsuru da ido... hannunta da laushi kamar auduga

'' ji bala'i..ana dole ne?" Anaam tayi maganar share ta nayi na miƙa ma Asma'u ta wanke hannunta taba Anaam

Nina buɗe kular wani irin dadɗaɗan ƙamshi ya ziyarci hancin mu lafiyayyen farfesun kaza ne daya ji haɗi...
Chapter 32 · 0% Book details