← Book details Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 67

Sashe 21

Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ina Magana hawayen takaici na zuba kamar pamfo na tsani wannan abun da masu mota suke su wani su dinga damun mutum da odar mota...

...'' amma yarinyar nan...''

Kallon da Khalil ya jefa mashi yasa driver Habu yayi shiru...buÉ—e motar yayi ya fito ya tsaya yana kallona da tambaya a fuskar shi

'' Kitten!!" Ya kira da mamaki,nima ƙifta idona da suka yi ja kamar gauta nayi dan in tabbatar shine..shi ɗin ne amma me yake anan?

'' what happened?" ya tambaya tsaye dab dani,share hawaye na nayi da magiya nace

'' dan Allah ka kaini gida!" da sauri na tura hannu na cikin hijabina tare da matsar dashi daga jikina kunya ( shame and embarrassment) ya rufe ni..ya gani? meyake tunani? ko in tambaye shi? Nayi wannan tunani tare da ɗago idona dake ƙasa suka shige cikin nashi dake kallona kamar yana ƙoƙarin fahimtar abinda ya faru..ko dai yana duba wani abu daban ba😡

wannan tunanin yasa naji haushin sa ya cika ni

'' toh ko a kawo maka kujera sai ka zauna ka kalle ni da kyau?"

Nayi maganar a fusace,dan nidai a ƙwaƙwalwata ƙirjina yake kallo eh...

🍁🍁: ke Abeedah mutumin dake shirin taimakon ki?

Abeedah: dan zai taimake ni sai ya gama kalle ni?

🍁🍁: bafa abunda yake kallo ba kenan

Abeedah: toh nidai abunda raina ya ayyana min kenan

🍁🍁: your insecurities really run deep

Abeedah:🙄🙄 koma me hakan ke nufi to gaskiya ne..ba zaki gane ba Autumn sai idan ke ce a wannan yanayin...

juyawa nayi na fara tafiya bayan na faɗi hakan haushinsa na ƙara hauhawa a raina manta kawai dama koda yaushe ni ina sama ma kaina maslaha batareda kowa ya taimake ni ba,yanzu ma zan koma gida..Ni ɗin mai dogaro da kai ce yanzu ma zan dogara...

jin an riƙo hannu na yasa na tsaya na juyo

'' You have a fiery temper,yi haƙuri muje in kai ki gida!" zare hannu na nayi daga nashi ganin yana murmushin nashi sai kuma na wuce shi kamar motar mu ce
da kanshi ya buɗe min ƙofar har zan shiga naji Muryar me fes mas yana faɗi cikin wata ƙatuwar murya mai cike da ban tsoro duk da muryarshi ba ɗaga ta yayi ba

'' Are You kidding me? Does this look like a dumpster?"

'' Rom,have some humanity in you...'' Khalil ya faɗa da rashin jin daɗi a murya shi,ni kam sai rarrabar ido nake tsakanin su, ƙwaƙwalwata na loading a 360 ina ƙoƙarin fahimtar mai suke cewa amma dai wannan mai fes mas ɗin na fahimci cewa mugun bawa ne wallahi,sai gardama suke, hankali na ya ƙara tashi ganin dare na yi

'' idan taimako take buƙata,ka tarar mata abun hawa mana yakai ta har gida...akan me zata shigo tayi contaminating iskan cikin motar... ''

aha! an faɗi magana da yaren da nake ji..wai kuma mugun bawa ne ya faɗa..dama yana jin Hausa? hausar ma irin ta kanawa..taɓ ɗi jam amma anyi ɗan gulma kuma sai na gano ma'anar wannan kalmar kntamineyt daya faɗa..kuma Oti kada kiyi ƙoƙarin gyaramin yanda ya faɗa na faɗa ehe

ƙafafuna suka fara rawa da naga rana ta faɗi duka, hawaye suka fara sauka daga idona,na juyo na kalli Khalil,tattausan hannun shi ya kawo a fuskata yana share min hawaye,na daskare dan banyi tsammanin hakan ba

'' don't worry kitten,zan kai ki gida yanzun nan!" gyaÉ—a kai nayi jiki a sanyaye

'' pls Roman!" Khalil ya roƙa,wai ashe sunan mugun bawa Romo..Romon kaza?

Romo bai sake cewa komai ba..hakan yasa Khalil sakin lallausan murmushi kafin ya taimaka min na shiga cikin motar sai shima ya shigo...kafin in zauna yayi saurin ɗaukar rigar dake wurin ya shimfiɗa min sosai yake kusa dani kamar zai rungume ni,ba ƙaramin takura nayi ba

'' zauna!''

Ya matsa daga kusa dani sai lokacin na samu na saki numfashin da bansan na riƙe ba amma kafin in zauna direban ya figi motar da ƙarfi...sai gani daɓas akan cinyar khalil hannun shi a ƙirjina 😳😳...irin daga ni harshi ɗin ba muyi tsammanin abunda ya faru ba,saura kaɗan numfashi na yabar gangar jikina

🍁🍁: what the freaking pregnant duck!!!!

Abeedah: ke dai tayani jimami ɗazu ina ƙorafin yana Kallona sai kuma ga hannunshi daɓe daɓe a wurin wayyo kunya!!!

a bazata na faɗo saman shi.... Kai!!!..wani irin kunya ne ya dabaibaye ni irin wanda ban taɓa ji ba,naji kukana na shirin dawowa sabo..da sauri na miƙe daga jikinshi na zauna inda yayi min shimfiɗa hawaye na sauka a hankali ta coner idona naji inama ace ban shigo motar ba,har lokacin ina jin hannunsa a wurin duk dana sauka daga jikin shi,na kasa yarda da abinda ya faru,ya taɓani fa...

'' ka dinga abu a hankali mana!" Yayi maganar wa driver '' yi haƙuri yallaɓai!" Ya furta

'' kada ki damu bada daÉ—ewa ba zaki koma gida!" jinjina kaina nayi ban yarda na kalle shi ba,ko me yake tunani a ranshi?

'' me kike yi anan?" Ya sake tambaya,ko kaÉ—an bana son magana dashi da alamu shi bai ma san abinda yayi ba,sai dana É—ago na zabga mashi harara ina turo baki nace

'' Mama tace in tafi..in ɗauko mata niƙa shine wani mutum me shan taba ya biyoni da gudu... Yasa na ɓace!'' na ƙarashe da goge fuskata da hijabi na

Sosai fuskar Khalil ta nuna baiji daɗin abinda ya faru da niba,kawai sai naji hannun mutum a kafaɗa ta yana shafawa alamun lallashi '' it's okay...'' yafara da turanci..wani irin ɗagowa nayi na harare shi da jajayen ido na sai kuma na kaɓe hannun shi ina ji kamar zuciyata na kamawa da wuta,ai tunda ya taɓa ni duk da nasan bada gangan bane na dinga jin haushin sa kenan

🍁🍁: ai shine,akan me zai taɓa forbidden fruit 🍓 🤣

Abeedah: ni dai kada ki kaini inda ban jeba toh!

🍁🍁: 🤣🤣

'' lallashin ki nake fa!" ya rausayar da kanshi gefe,ji nayi kamar in make shi da shegun idon nan nashi kamar na akuya

'' toh idan ana lallashin mutum sai akace a dinga taɓa shi?"

duk da nayi ƙoƙarin kada in nuna fushi na kasa dannewa,ji nake kamar ana yayyafawa zuciyata fetur

'' yeah.. that's how it's done!"

yayi maganar murya ƙasa,bakin shi a washe dan ya fahimci ya ƙular dani sosai ɗauke kaina gefe nayi ban sake cewa komai ba shima sai yayi shiru

Duk wannan maganganun da muke Romo fa yana jin mu amma kamar babu shi a wurin ko juyowa baiyi ba shi uban jiji da kai zan koya mashi hankali kuwa

Da misalin ƙarfe shida da rabi muka iso anguwar mu, ganin mutane da yawa tsaye bakin ƙofar gida da Mama da Asma'u yasa gabana ya faɗi...

Ina gani daga inda nake zaune Mama tasa ƙarshen hijabinta tana goge hawaye...Malam Hassan maƙobcin mu da maman Amal na bata haƙuri... Asma'u daga gefen ta itama dai alamun tayi kuka...

'' inda mutane zaka tsaya!" Na faɗa cike da damuwa,motar na tsayawa na shiga ƙoƙarin buɗewa in fita amma na kasa,dole Khalil ne ya miƙo hannu ya buɗe min,da sauri na tare ƙirjina kada ya sake taɓawa bada gangan ba,tunda dai na dawo gida bazamu wanye lafiya ba

Na fita da gudu kamar zan kife ina kiran

'' Mama!! Mama!!"

Mutanen suka fara rabewa suna bani hanya Mama ta miƙe da jajayen ido

'' Abeedah..''

ta kira itama tana zuwa inda nake Asma'u biye da ita,muna cimma juna na faÉ—a jikinta tare da sakin kuka itako sai hamdala take

Mutanen wurin na tayata...duk da wasu yan gulmar kayan jikina suke kallo da kuma motar dana fito daga ciki

'' ina kika tafi Abeedah? Kin samu a damuwa!"

Mama ta tambaya tana É—agoni daga jikin ta..ina kuka na shiga faÉ—in abinda ya faru... saboda bana so mutane su fara cece kuce da yamaÉ—i É—i anga Abeedah ta fito babbar mota

Sai mutanen suka mayarda kallon su wurin Khalil dayayi tsaye wurin batareda sanin abinyi ba...ya sakar musu murmushi yana shafa kanshi

'' ina yini...!!" Ya faɗa da murmushin kunya..sai suka fara amsawa suna sake yimashi godiya..matan kuwa duk da akwai masu aure sai duba shi suke dan da gaske ba ƙarya gayen ya haɗu nima na sani

sakina Mama tayi sai Asma'u ta riƙe ni itama tana kallon Khalil

Har ƙasa Mama ta kai tana kwararomashi godiya da ruwan addu'oi...ɗan zaro idonshi yayi awkwardly kafin shima yakai ƙasa yana amsa addu'oin ta yana sosa kai....

Slowly ya É—ago hunter eyes É—inshi da suke blank babu wani expression a fuskar shi datake cikin mask... blankly yake kallon taron jama'ar wurin, idonshi akan Mama dake yi kamar zata mayarda Abeedah cikin cikinta

''Perché una madre ama sempre il proprio figlio,E ti amo allo stesso modo E ti amo allo stesso modo, qualunque tu sia Romano.(saboda uwa tana son ɗan ta,kuma nima ina sonka a duk yanda kake Romano)" maganar ta fara amsa kuwwa akanshi kamar alarm ɗin daya ƙi mutuwa...

Driver ya jinginar da kanshi a glass Yana kallo shima,sosai abin ya ƙayatar dashi,a hankali mutane suka fara raguwa

Sai Mama ta miƙe shima ya miƙe ya kalle ni

'' Toh Mama sai gobe zan zo insha Allah!"

Ya faÉ—a yana kallo na

'' Allah ya kawo ka lafiya!"

Mama ta bashi amsa da farin ciki

Ya jinjina kanshi tare da kallo na da murmushi a fuskar shi

'' Bye kitten!"

Yayi min alama da bakin shi ..a karo na farko nima sai na sakar mashi murmushi ina mashi bye bye haushinsa ya É—an ragu a raina ganin yanda ya girmama Mama

Ya juya ya shige motar su har lokacin muna kallon juna sai da motar tabar wurin... mutanen suka watse muma muka shige gidan mu

'' Asma'u É—aura min ruwa a wuta in ma Abeedah wanka!"

Zaro ido nayi jin abinda Mama ta faɗa ina kallon ta...sai na shagwaɓe fuska

'' Mama kimin wanka kuma?"

Nayi maganar rai ba daÉ—i

'' Yoh ko kin wuce in maki wankan ne?''

'' gaskiya kam! Gabjejiya da ita zaki mata wanka?"

Asma'u dake shigewa kitchen ta faÉ—a...Mama bata saurare muba,ta fara cire min hijabina da lakar ta bushe akai

Sai tace inje baye in jirata..kaini Abeedahtuwo yaushe Mama zata dena wannan al'adar Tata?ƙila ma tunani take wani abu ya faru!
Chapter 21 · 0% Book details