← Book details Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 67

Sashe 26

Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan an tashi break muna zaune nida Jay D ƙarƙashin bishiyar umbrella Jadeedah sai kallona take tana murmushi '' Meya faru?" Na tambaye ta ina juya idona...sai tayi murmushi tana kallon ɗan sululun dake riƙe a hannu na ta ɗauke idonta tana kallon nesa damu inda katangar take guntuwa muna hango mutanen dake wajen makarantar mu... masu aikin gyara hanya '' Faɗa min,ya kika ji sanda bama tare?" Ɗan sululun dake bakina na haɗe sannan nace daga ƙasan zuciya ta ina kallon ta '' ji nayi...kamar ni marainiya ce Jay D...ban san yanda rayuwa ta zata kasance ba idan babuke...'' taɓe baki tayi hmm.. Allah ko?" Alamun bata yarda ba...dukar wasa nayi mata a kafaɗa mu biyun muna dariya '' kin dai san ni abinda ke zuciya ta kaɗai nake faɗa Jay D bana ƙaryar abinda nake ji...''

'' Tuwo masu faɗar gaskiya sannun ki!" Wata mai suna Fadeelah daga C class ta katse ni tana zama kusa dani ta wani tsoma hannu cikin ɗan sululun...kuma sai da idon mu ya haɗu ta tura har guda biyar cikin baki....take na haɗe fuska tareda jaye kwano na...Jadeedah ta rufe baki tana danne dariya '' kinci rabon ki wallahi!" Na faɗa ina ƙoƙarin miƙewa

'' Matsala ta da Abeedah rowa!" Hafsah daga SS2 ta furta itama ta kwashe fiye da rabin abunda ya rage '' kambuuu!!!!" Na zaro ido kafin in sani sauran wasu dake kusa sun zo sun warce kwanon daga hannu na suka daka wasoso kamar zanyi kuka ganin yanda suke tumurmusar juna yasa mu dake kallo muna ta dariya...duk sun ɓata hijaban su da manja kafin suka fara guje guje'' zo muje in siya maki wani!" Jadeedah ta riƙo hannu na muka bar wurin...'' ke baki faɗa min yanda kika ji...''

'' Oh Ni I felt empty ban san yanda zan iya fasaltawa ba su ɗin da nake tare dasu ko kaɗan bamu dace da juna ba,ba kamar ke ba Abeedah... I love you so much!" Ta ƙarashe tana jan kumatuna

'' Innalillahi duk sai kin ƙara sa pimples sun fito min!" Na kaɓe hannunta daga fuskata...dariya tayi sai kuma ta shafa hannun a fuskar ta '' idan kina da pimples nima ya kamata ace ina dasu. ..''

'' pfft!! Akan me zaki so ki samu pimples akan kyakkyawar fuskar ki?" nayi tambaya ina kallon hannunta dake riƙe da nawa... zuciya ta na ƙara son Jadeedah sosai

'' saboda ina so inyi kama dake...sosai! Ji nake inama ace gidan mu ɗaya..ke Bee kwanakin nan da nayi babu ke wata irin ƙaunar ki ke ɗawainiya dani!"

'' wai ke sai kita magana kamar na miji...''

'' waya ce namiji kaɗai zai iya bayyana ƙauna Abeedah? Bawai ina ƙaunar ki..irin na banza ba...kawai ƙaunar ki daga Allah ne kin gane?"

'' na gane!" Haka muka cigaba da hira...har aka koma aji ranar naci ɗan sululu har nayi rarraba dashi nida Jay D har aka tashi muna maƙale da juna,ban wani cika shiga motarsu ba amma ranar har gida aka sauke mu nida Asma'u..

Ban taɓa sanin ƙaunar da nake ma Jadeedah tana da yawa ba sai da mukayi faɗan nan kamar zuciya ta zata buga bana fatan ƙara kasancewa nesa da ita...

Kamar yanda Mama ta faÉ—a ranar Lahadi muka koma sabon gidan mu,sosai muka share ko ina muka gyara...wasu Mutanen anguwar mu suka biyo suna tayamu gyara gidan,farin cikina baya misaltuwa a wannan ranar mama É—akinta ita kaÉ—ai,nida Asma'u É—akin mu É—aya sai wurin magrib gidan yayi shiru ya dawo daga mu sai mu...bayan Isha'i muna zaune a inda mukayi sallah nake kallon Mama data kafe wuri guda da ido...

'' Mama ko bakison gidan nan ne?" Asma'u ta riga ni tambaya '' kawai dai...nayi kewar gidan mu ne!" Ta amsa a sauƙaƙe '' zaki saba ai!" Asma'u ta amsa mata..sai kuma ta matsa ta kwantar da kanta saman cinyar ta'' Mama tare zamu kwana anan ɗakin...'' na faɗa ina kwantawa a inda nake

'' É—akin kufa?"

'' kin dai san bamu saba kwana daban daban bako?" Asma'u ta rigani faÉ—a.. girgiza kanta Mama tayi...mukayi shiru...

A raina ina mamakin meyasa Jadeedah bata zoba?

Daga ƙarshe dai tare da Mama muka kwana ranar Monday Jadeedah bata zo makaranta ba.hankali na ya tashi haka ma ranar talata Naji na ƙara shiga ƙunci... Ranar laraba ina zaune ƙarƙashin bishiyar da muke zama tare ina saƙe saƙe a raina 'idan fa kamar yanda yake faruwa a fim sai ka nemi abokin ka karasa ya tafi wani wuri bayan kunyi faɗa kun shirya nima abinda zai faru dani kenan?idan fa...

'' BEEEE!!!! Wai Meye kike tunani haka?" Jadeedah dake zauna gefe na tana magana tuni amma banjiba ta jijjigani tana kiran sunana da ƙarfi na juyo na kalle ta kamar na kasa yarda da ita ce a gefe na..sai da na taɓa fuskar ta '' kece?"

'' fatalwa ce!" Sai na saki dariya..inajin sanyi a raina...muka rungume juna '' ina kika shiga kwana biyu?" Sakin juna mukayi ta gyara zamanta ta riƙo hannuna '' wai Abba...haka kawai muna zaune zaman zaman mu wai...yayi mana visa zamu bar Nigeria!" faɗuwa gabana yayi..

'' ku bar Najeriya ku tafi ina?" Tana girgiza kai tace '' wai New Zealand! ''

''.oh...'' na faɗa inayin ƙasa da idona ta cigaba da faɗin '' amma kada ki damu,yanzu mu duka muka yi mashi yaji...muka dena mashi Magana daga ƙarshe dai ya yarda zamu cigaba da zama Nigeria amma shi zai tafi...nan gaba kaɗan wai muma zamu bishi!"

'' nan gaba kaÉ—an zaku bar Nigeria...hakan bai sa naji hankali na ya kwanta ba Jay D..idan fa kuka tafi? Ya zanyi?"

'' abu mai sauƙi zan saka ki a akwatina!"

'' kina da Iskan bani ke nan?"

'' ai ke babbar yarinya ce bakya buƙatar oxygen!"

'' idan na margaya barzahu kenan!" Mukayi dariya '' hankali na ya tashi sosai...''

''.nima inata kuka a ɗakina jin wai zamu bar tuwo a Nigeria!" Ta ƙarashe tana jan kumatuna....

+2349138091955

RU'UYAA…📖

₦500 ne idan ya kammala zai koma ₦800

Biya ta wannan account É—in 9138091955..Salma Aliyu opay

Shaidar biya ta +2349138091955

Autumn writes 📖🖋️

RU'UYAA
The dreams we never lived
By Autumn 17 🍁🍁

13. ...let me help you...🖊️

'' yaushe zaki zo gidan mu?"

Na tambaya ina kopar mata notes É—in da bata yiba,É—auke kanta tayi daga kallon window ta dawo dashi a kaina

'' kin san abinda nake tunani?

Ta tambaya da murna a muryarta,na girgiza kaina batare da na ɗago daga littafin ba gyara zama tayi taɗan duƙo da fuskarta kusa da tawa tace

'' idan fa kika zo gidan mu kikayi kwana biyu,nima inyi kwana biyu a gidan ku kamar sleep over?"

sai da na gama rubuta layin da nake kafin na É—ago na kalleta

'' ban fahimta ba"

'' ina nufin Mu kwana a gidan mu yau da gobe da jibi wani sati sai mu kwana a gidan ku irin haka! shi ake kira sleepover!"

Na bita da ido har tagama

'' slif kobar?"

Na tambaya ina ƙoƙarin rubutawa a bayan littafina tayi yar dariya tace

'' sleep over ba koba ba,kuma kina nufin duk abinda na faÉ—a abinda kaÉ—ai kika ji kenan!"

ta É—aure fuska

'' a'a..ban taɓa zuwa gidan kuba..idan fa innarki bata so ana kawo mata mutane? Kuma bansan me zance ma Mama ba ''

'' ba sai kin ƙara cewa komai ba!"

Ta É—aura yatsanta a bakina

'' Indai Ummi kike magana akai well,bata da matsala kullum sai ta tambaye ni ina ƙawarki Abeedah? Yaushe zata kawo mana ziyara? Yau ma faɗa mata nayi ta shirya abinci na musamman dan dake zan dawo gida kuma zamu fara biyawa gidan ku ai ni zanyi wa Mama magana kin san ni da iya zuba zance!"

ta gyara zama da Murmushi a fuskar ta kamar har tayi nasara ina son yanda Jadeedah take da ƙwarin guiwa da yarda da kai duk tace zata yi abu komai wahalar shi sai tayi duk yanda abu ya ɓaci tana da yanda zata ga abun cikin haske mai kyau Ita ɗin Uhmm

🍁: Optimist

Jadeedah ofitamus (optimist)ce,bazata taɓa yarda taga baƙin abu ba sai dai farin shi acewarta abinda kake tunani kodai ya gina ka koya rusa ka... ma'ana idan tunanin ka mai kyau ne to abubuwa masu kyau zasu dinga faruwa dakai haka zalika idan gurɓataccen tunani kake dashi abubuwa marasa kyau kaɗai zasu dinga faruwa dakai tunanin ka kai yake cutarwa ba kowa ba kai zaka kasance a yanda ka ɗauki kanka

'' kina jin abinda nake faÉ—a kuwa?"

Jijjiganin datayi ya dawo dani

'' eh inaji!"

Na amsa duk da banji komai data faÉ—a ba kallon data yimin ya tabbatar da bata gamsu ba

'' ina matuƙar ƙaunar ki Jadeedah Ahmad!"

Ta sakar min Murmushi mai sanyaya rai '' ba kamar yanda nake ƙaunar kiba Abeedah Abdul wahhab...''

'' dan na kira sunan babanki kema sai kin kira nawa ko?" Na tambaya ina murmushi ''

duk cikin son ne!" Ta bani amsa...

'' har da wani littafin Hausa na siyo maki..''

Idona suna ƙyalli nace '' dan Allah?"

'' sosai ma kuwa..kuma kin san abin burgewa?" Ta tambaya tana É—aura hannunta a table '' sai kin faÉ—a!"

'' jarumar baƙa ce...kuma bata da kyau, bata gane abubuwa bata da dogon gashi a taƙaice dai mummuna ce!"

Sosai nayi dariya dayasa yan ajinmu kallo na,na tsani ina karatun littafi inji ance jaruma fara ce ga kyau kamar ita tayi kanta raina mummunan ɓaci yake! Kullum sai ata zuzuta kyaun jaruman da har za'a sa mai karatu tambayar kanshi mai yasa baya da irin abun da suke dashi

Na fiso ace jarumar tana da wani abun da zai haɗa mu kamar dai ita baƙa nima baƙa

babu malamin daya shigo yan aji aka taru.ana wasar police kama ɓarawo wasu kuma sunyi gungu suna hira wasu suna carafke idan munji malami na zuwa kowa ya dawo wurin shi a guje,ranar tayi daɗi kamar kada a tashi

Sanda aka tashi,a mamakina sai ga Asma'u ta rugo ta rungume ni,na ƙame ƙam Jay D ta tsaya gefe jakar goyonta a hannu tana kallon mu Asma'u ta ɗago kanta ta kalle ni sai ta sake ni batareda tace komai ba Da murmushi a fuskar ta

'' sannu Jadeedah '' ta gaishe ta
Chapter 26 · 0% Book details