← Book details Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 67

Sashe 6

Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

hira mukeyi har muka isa makaranta daidai an gama assembly class muka wuce,nida su Aleeyah ajin mu ɗaya SS3D Asma'u kuma science take... Muna shiga mathematics na shigowa ji nayi kamar in fasa ihu,bani son makaranta amma kuma naƙi jinin mathematics da malamin da kuma mai koyar da subject ɗin

'' Gooooood mooooooining sir!" muka gaidar dashi, kallon mu yayi cike da jin haushi kafin ya bamu izinin zama batareda ya amsa gaisuwar muba '' ku fito da mathematics note book É—in ku,ku buÉ—e zuwa inda muka tsaya!" yayi maganar yana jinginar da zabgegiyar bulalar shi

kusan rabi da kwata na aji sai rarrabar ido muke kuma nima ina cikin su... a inda nake zaune daga baya dan back bencher ce duk wuya duk runtsi babu Ni a gaba

aji ya É—au surutu tsawa ya daka mana tare da faÉ—in '' ba surutu nace kuyi ba ku nunamin littafin ku..'' kafin ya gama wayarshi tayi ringing

kallon kallo muka shiga yi wasu na shewa wayanda keda note kenan,wasu sun fara sun shiga uku wasu kuma suna faÉ—in in ma kashe su za'a yi saidai akashe su...wasu har sunfara kuka suna yarfar da hannu,oh...ashe ban faÉ—a muku cewa makarantar mu makarantar mata bace? makarantar mata ce toh

nidai daga inda nake zaune babu abinda ya dame ni nama ga nawar azo ayi dukan kowa yakama gabanshi bawai dan inason duka bane sai dai saboda bani kaÉ—ai za'a daka ba, sannan wani irin daÉ—i nake ji ajiki na me haÉ—e da tsoro...

'' Operation show me your note!" wata mai suna Hameeda ta faɗa tana sheƙewa da dariya itama fa bawai dan tanada note ɗin ba,ga hadari daya taru aji yayi duhu da haske

da sauri muka fara yan dabaru masu ƙananan jakunkuna suka rage littafan su,sai su tusa jakar a bayan su idan malami na duka bazasu ji zafi ba..nima dai haka nayi

Bayan wani lokaci sai gashi ya dawo da discipline master Wanda kafiri ne sunan shima gunta..amma tunda mu Hausawa ne kuma yan makaranta Mr Mugunta muke kiran shi, musamman ni...da muguwar fuskar shi da akoda yaushe murtuke take da kuma buɗaɗdiyar muryar shi yace '' idan kasan baka da note ka fito '' sai ga rabi da ƙwatar aji sun fito wasu harda hawayen su

zan iya rantsewa naga lokacin da ya lashe bakinshi tsabar mugunta kafin yayo cikin mu bulala biyar biyar,duk inda ya samu zunta ma mutum ita yake, hankali na ya tashi amma kuma wannan daɗin ƙara ratsani yake

musamman wasu idan aka dake su naga yanda suke faɗuwa ƙasa suna billiƙe billiƙe kamar tanar da aka zuba ma gishiri abun dariya yake bani wasu harda yar drama '' wayyo Mallam tsaya kar ka karye Ni....na bani na shiga uku.... wallahi Ni kaɗai mamata take dani.....dan Allah kayi haƙuri...mamata ki taimake ni.....'' haka dai

lokacin da aka kawo kaina ba ƙarya nima bulalar ta shige ni wallahi ba ƙarya amma sai na dake
lokacin da yagama zane mu wasu harda kukan su,shiko sai huci yake harda zufa yana cigaba da murmushi

Bayan ya tafi kowa ya koma seat É—inshi aka fara wani banzan ni nama manta sunan topic É—in amma dai nasan akwai logic ciki...oh na tuna logarithm...har da wani graph Wai sai mu gano wata banzar X da Y can...har yayi ya gama wallahi komai ban gane ba

yana fita aji ya kacame da surutu '' kai amma mutumin nan anyi tsinanne... wallahi bulalar da yayi min babu wadda ta shige ni sai ta ƙarshe dan ga ɗuwawu ya zunta min ita da ƙyar nake iya zama!" inji A'ishah class Captain,muka kwashe da dariya suma wasu sai ƙara tsine ma mr mugunta suke

wani Malami ne ya leƙo '' wane subject kuke dashi yanzu?"
'' I.R. S'' suka amsa tare gyaÉ—a kai yayi yana faÉ—in '' ku fito da littafin ku kafin yazo!" muka amsa da '' Yes sir '' amma babu wanda yayi hakan

'' Macijin sari ka noƙe muke dashi fa!" Muneeba ta faɗa tana kallona, wannan sunan nice dakai na na raɗa masa shi me yasa? mutumin tsohon munafuki ne kuma na tsane shi...tantagaryar ɗan iska ne,na rantse ba sau ɗaya ina ganin shi a hotel ɗin danake aiki ba da yan mata daban daban suna iskancin su

amma idan yazo gaban mu sai yayi tayi kamar na Allah yana jawo ayoyin Alkur'ani da hadisi yana fassarawa, yan mata da yawa harda ni ada yana burge su..sai da na gano waye shi Sannan nagane cewa kuskure ne...yan mata da yawa suna matuƙar macewa akan mutumin nan musamman saboda kyakkyawa ne gaskiya,ga ilimin addini ɗalibai sun yarda dashi basu kaɗai ba harda iyayen su,na rasa dalilin dayasa mutane irinshi ke ɓoyewa bayan addini suna cin amanar ɗalibai da iyayen su da kuma addini duka...

ina tsaka da tunani ya shigo ajin yan mata suka fara gyare gyare, yanda ya tsuke fuska zakayi tsammanin mutumin kirki ne...naji daɗi sosai da Asma'u ta rabu dashi,nasan lokacin dayake magana da ita da zummar yana sonta sai ya dinga kiranta office ɗin shi... Allah yasa na gano hakan da wuri na kuma taka musu burki na rabasu kuma tayi min alƙawarin bazata sake ba,bansan ya zanyi ba idan wani abu ya faru da ita wani banza ballagazan namiji ya lalata rayuwar ta... lokacin harda zuge ta yake akan ni ina kishi da ita ne don tafini komai...abun ya baƙantamin rai sosai

ya sani nima kuma nasani nidashi maƙiya ne na har abada bazamu taɓa shiryawa ba!

'' me kike tunani?" naji muryarshi kusa dani dab da kunne na,da sauri na juya na kafe shi da idona da launin suke ƙara rinewa idan na tsani mutum,idan kuma inason mutum idona har wani ƙyalli suke idan nayi fushi ko kuma bana son in nuna emotions idona size ɗinsu ragewa yake

kallon shi nake cike da tsanar data kasa ɓoyuwa a idona '' meye damuwarka?" na mayar mashi da tambayar

haÉ—iye fushin shi yayi tare da faÉ—in ki maida hankali,komawa yayi gaban allo kowane sakan biyar sai ya kalle ni har yayi ya gama bance komai ba..yan matan ajinmu kuwa sai biloshing suke...bafa haka kalmar take ba amma aidai kungane ko?

Bayan ya fita sai ga Civic ta shigo,nifa bana maida hankali idan ana karatu dan ba ganewa nake ba,amma yau topic É—in da aka koyar damu yaja hankali na sosai,da farko waje nake kallo kamar koda yaushe ina tsarawa acikin raina yanda zanyi kyau idan inada wannan da wancan idan fuska ta babu pimples idan... idan...

'' Our topic for today is SELF ESTEEM!!". Muryar malamar ta dawo dani daga tunani na, duk da bansan mai hakan ke nufi ba jinayi ina so insan ma'anar hakan yasa na mayarda hankali

'' wa zai faɗa min me ake nufi da SELF ESTEEM?" ta tambaya tana kallon mu, mutane dayawa sun ɗaga hannu amma babu wanda ya cinki ansar da kyau..nuna ni tayi tareda faɗin '' meye ma'anar SELF ESTEEM?" kallon mutane nake ido waje kamar yanda suke kallo na,sun sani na sani bansan amsar ba,wasu har sun fara dariya, yawu na haɗiye kafin na miƙe ina kallon malamar da itama nitake kallo batareda tunani ba nace '' sef istim na nufin sanin darajar kai da kuma samun ƙwarin guiwa a duk abinda mutum yake...kamar dai ace yaƙini.. mutum yazama mai yaƙini akan kanshi!" na amsa da ina ina,ina shafa kunne na inda ake sa ɗan kunne idona ƙasa..duk sanda nake jin tsoro kaɗan haka nake

ji nayi yan aji suna dariya,banji ba daɗi ba don abune dana saba dashi malamar ta kalle ni tareda ƙara faɗin '' shine amsar ki?" ta tambaya,gyaɗa kaina nayi alamar eh

'' CLAP FOR HER!!!" ta faɗa da ƙarfi,sai kawai suka faramin tafi sakin baki nayi kafin na zauna na kasa yarda wai yau ni ake tafa mawa abinda bai taɓa faruwa ba tsawon shekaru goma sha bakwai na rayuwa ta, suma yan ajin mu sunyi mamaki don dai sun sani niɗin daƙiƙiya ce lambar ƙarshe ban taɓa daga hannu don amsa tambaya ba ban kuma taɓa amsawa daidai ba koda kuwa amsar a bayyane yake

bayan wani lokaci malamar ta fara bayani da turanci

- Self-esteem: It's how you feel about yourself, your worth, and your abilities. It's your internal evaluation of yourself.( self esteem shine yanda kake ji game da kanka da kuma yanda, amfanin ka,da kuma abunda zaka iya yi... yanda kake ji azuciyar ka dakuma yanda kake É—aukar kanka... Sai kuma akwai low self esteem da high self esteem
- Low self-esteem: You're kinda down on yourself, doubt your abilities, and might feel unworthy or not good enough. 😔( Shine tsaurarawa Kai, kokonton abinda zaka iyayi da wanda bazaka iya ba, sannan kake ji kamar baka cancanta ba ko bakada amfani ko baka kai ba....
- High self-esteem: You feel confident, capable, and worthy. You like who you are and trust your abilities. 💪 ( high self esteem,kanajin ƙwarin guiwa, zaka iya, ka cancanta...kana son kanka kamar yanda Allah yayi ka,baka neman wani ya yabe ka ko ya soka sannan kayarda da abinda zaka iyayi...

misalin low self esteem=

😔

- Constantly comparing themselves to others ( haÉ—a kanka da Wasu)
- Saying "I'm not good enough" or "I'm a failure" ( cewa ni ban isa ba kuma ban kai ba ta hanyar raina kai)
- Avoiding challenges or new experiences due to fear of failure ( gujewa ƙalubale da sabon abu gudun kada a faɗi)
- Needing constant validation from peers ( buƙatar mutane su yabe ka ko abokai)
- Negative self-talk or self-criticism (Maganar da bata dace ba ko mara daÉ—i wa karan kanka)
- Difficulty accepting compliments or praise ( wahalar yarda idan an yabe mutum)
- Feeling like they're not worthy of love or respect ( ji kamar basu cancanci a girmama su ba ko a sosu..) tunda malamar tafara magana na nitsu bani kaɗai ba ma harda sauran yan aji... bamu taɓa bada hankali ga wani subject ko topic ba kamar yanda muka bada a wannan topic
Chapter 6 · 0% Book details