← Book details Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 67

Sashe 31

Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ban kalle ta ba..na isa wurin Asma'u dake kusa da ita na rungumeta '' nayi kewarki Asma'u ''

'' nima '' ta bani amsa da jin daÉ—in daba ta nuna shi ba da daÉ—ewa....

Bayan nan Mama taje ta zauna a baranda..Ni kuma na jawo akwatin da sauran abubuwan da Maman su Jay D ta bani na nuna mata..sai albarka take sawa...sai da na buÉ—e akwatin naga bandir É—in dubu dubu guda biyu nayi mamaki sosai gashi niba waya ba balle in kira in yimata godiya dan nasan ita tasa su....

Asma'u da Anaam suna ta kallo baki sake dan komai dake cikin akwatin duk da sauƙin su a ido,kuɗin su idan mutum yaji sai ya riƙe baki nan nake ta basu labarin gidan girman shi da kuma kayan more rayuwar dake ciki da kuma yanda mamansu take kyautata min...

'' kuma a haka yarinyar bata da girman kai ko nuna ita wata ce'' mama ta faÉ—a

'' ai nima nayi mamaki ba kaÉ—an ba Allah dai ya barni da Jay D...''

'' Ameen...''

suka amsa... Anaam tabar wurin ta shige ciki tana kallo...tashi nayi nima na wuce kitchen na É—aura ruwan zafi... sannan na dawo nace ma Asma'u ta É—auki abinda take so....naba mama kuÉ—in...

Da Isha'i ina ɗakin Mama kwance a cinyarta bayan na gama sallah nan take faɗa min ashe ranar dana tafi ranar suka zo da ƙarfe taran dare...auren Inna sarai ya mutu da mugun mijinta kuma yace shi bazai riƙe Anaam ba sai dai ta tafi da ita dama Mama ita kaɗaice dangin data rage mata shine yasa suka rankayo nan nidai naji daɗin kasancewar su damu duk da waccan Anaam ɗin yar rainin hankali ce kuma shekarun mu guda da ita mata kamar tabi iska amma sai shegen tsiwa...

'' yanzu kenan mun dena kwana tare?"

Na tambaya ina tashi zaune

'' toh ko saman wani daga cikin mu zaki dinga kwantawa?"

Inna sarai dake shigowa cikin É—akin ta tambaya tare da zama bakin gado tana harara ta

'' nidai da Mama ta na saba kwana!"nayi maganar ina turo baki

'' TOH ai sai kixo ki ture ni daga saman gadon ki kwanta ko kuma ki shige cikin cikinta...''

Na miƙe tsaye ina buga ƙafafuna nayi ƙofa ina faɗin

'' toh ki buÉ—emin cikinta ki gani in ban koma ba!"

Ta ɗauki pillow ta jefe ni dashi nayi saurin kaucewa ina ƙunƙuni...Mama dai bata tanka mana ba...na wuce ɗakin mu, iske su nayi suna magana, suna gani na suka yi shiru kamar sunga munafuka..ban bi takansu ba na wuce na kwanta ina jin kewar Jay D..gashi banida waya da number ta dana kira ta

'' Ibrahim yazo sanda baki nan..''

Naji muryar Asma'u banyi niyar tanka ta ba nayi shiru na cigaba da tunani na

'' daga zuwa gidan masu kuÉ—i zaki ari halinsu ki yafe,wahala zaki sha wallahi..''

inji Anaam itama banyi niyar amsa mata ba amma kafin in iya hana kaina nace

'' muryar ki tana jima kunnuwa na ciwo..shirun ki shine alkhairi pls''

Asma'u ta juyo dan kawai nace pls murmushin gefen baki nayi da basu gani ba...Anaam kuwa kamar zata kama da wuta... Asma'u ta É—aura hannun ta a kafaÉ—ar ta tana tausar ta can suji dashi

'' nace Khalil yazo '' ta maimaita ganin na farko ban amsa ba

'' ba kurma bace Ni!" Daga nan ban sake tanka masu ba tun ina jinsu sama sama har bacci ya É—auke ni washegari Litinin bayan mun karya wanka nayi na fito É—aure da zane saye da hijabi na shigo É—aki nabar su zaune a baranda banda Anaam dake cikin É—aki itama tana shiri share ta nayi na jawo uniform É—ina ina sawa na saka wando da singlet zan saka riga naji tana faÉ—in

'' mace kamar na miji ba gaba ba baya tabɗi jam ni da ace na miji ce ko kyauta baxan karɓa ba!"

Sosai maganarta ta dake ni amma nayi kamar ban jiba ita da Asma'u haka suke idan suka haɗu suyi ta yimin wulaƙanci suna ƙuntata ni dan kawai sun ga ina biye su ina nuna baƙin ciki na banda yanzu zama gidan su Jay D ya canja ni koda kaɗan ne

'' ke idan ana harka da muta ne..ki dena shigowa...babban zagi ne ga jinsin mutane...''

ta tashi zaune daga kwancen da take

'' kina nufin niba mutum bace? To wacece ni?"

Na saka farar rigata da hula na fesa turare mai daɗin ƙamshi na juyo ina kallonta da idona dake a ƙanƙance na yan sakanni kafin na sauke ajiyar zuciya na zauna bakin gado ina sa safa nace

'' yanzu ma da nake ƙoƙarin gano a wane sahu kike..idona har sun fara ciwo..dan ke dai ba mutum bace..sannan kiranki dabba..babban cin zarafi ne ga dabbobi!"

Na miƙe nabar ɗakin da murmushi ganin fuskarta tabini da ido cikin rashin gasgata abinda kunnuwanta yaji ta saba yaɓa min magana sai dai inyi shiru ina kuka amma wai yau shine na bata amsa mai zafi...lallai

'' Ke Anaam ki tashi ki shirya mu tafi makarantar su a miki rijistreshon!''

inna sarai ta leƙo ta faɗa ma Anaam dake kwance zuciyarta a maƙoshi saboda abinda Abeedah tayi Mata

''ni sai wani tam (term) zan shiga makaranta!"

Tayi maganar tana juya baya kamar an jefo inna sarai ta wani irin tiƙe ta a baya da tafin hannu Anaam ta zabura kamar akuyar da aka zuba ma ruwan zafi tana soshe soshe fuska a kwaɓe

'' idan ina magana kina magana sai na dinga saɓa maki dalla jeki yi wanka In ma haka zaki tafi da warin jiki ke kika sani!"

Tana kaiwa nan tabar wurin..Anaam ta fara kuka ƙasa ƙasa kafin ta fito daga ɗakin sum sum ta wuce bayi

'' Mama xan fara neman aiki fa...daga yau ''

na faɗa ina karɓar kuɗin break '' aikin me kuma? Kuɗin da muke dasu sun isa ba saikin nemi aiki ba...''

Na girgiza kaina nace '' kuɗin zasu ƙare musamman yanzu da muka ƙaru sannan kuma ni bana son zama haka kawai..nafison ace ina da aiki...''

'' ke uwar son aiki...ai saiki tayi...Uhmm na manta ban faÉ—a maki ba...yaron nan.. Ibrahimu yazo...'' har zan fita na juyo

'' waya kawo shi? Mema yazo yi?"

'' wani yaro daga tsohuwar unguwar mu ya kawo shi...harda jikunkunan shinkafa dasu mai ya kawo mana..ya bada kuɗi duk da banso karɓa ba...''

na sosa gefen fuska ta ina tunani sai kuma na juya nace

'' an gode amma Mama in faÉ—a min kike Dan kada in nemi aiki..gaskiya dai...''

'' wane mutum? ai tunda kika ce zaki nemi aiki ban isa in hanaki ba...''nayi dariya tare da fita daga É—akin

Na samu inna sarai zaune tare da Asma'u tana kama mata gashinta na zauna daga gefe ina kallonsu

'' Nasan Tuwo ji take ina ma ace itace da wannan gashin ko?" Asma'u tayi maganar tana É—age min gira da murmushin gefen baki

'' wai ku har yanzu baku canja da wannan halin nason ƙuntata ma baiwar Allah bako?" Inna sarai ta dakata kaɗan

'' ita dai take son ƙuntatawa kanta ba kowa ba...''Asma'u ta amsa ta..ina murmushi nace

'' dana ga gashin Jay D na tabbatar da naki ashe sheƙar tsuntsaye ne,inna sarai gashin Jadeedah har mazaunai kuma baƙi wulik ga laushi ga ƙanshi mai daɗi ba irin na Asma'u ba da ake wata da watanni bai ga ruwa ba duk wari yabi ya ishe mutane''

Asma'u ta ƙwace kanta daga inna sarai tana kallona baki sake inna sarai tana ta dariya

''.kice kema kin koyo yaɓawa mutane magana''

Asma'u ta katse tada faÉ—i '' amma ai nan kike kina santi...''

'' dane kai bai waye ba amma yanzu da kaina ya waye ji nake kamar in ranƙwashi kaina dayake dai rashin sani yafi dare duhu...''

Asma'u take harara ta kamar idonta zai faɗi ta miƙe tabar wurin fuuu tare da jan tsaki na ɗauke kaina

Ƙarfe bakwai da arba'in muka bar gidan mu huɗu harda Inna sarai da Anaam dake ta cin magani mu uku muna ta hira har muka kawo makaranta har anfara tare latti daƙyar aka bar mu muka wuce bayan inna sarai ta roƙa mana gafara kamar wasu fursunoni (prisoners) aji muka wuce su kuma suka tafi ofishin pirinsipal

Math ne cikin ajin hakan yasa ko ina ya É—au shiru kamar sunga mala'ikan mutuwa nima kaina dai tsoron mutumin nake nayi tsaye a wurin ina kallon Jay D da ita bata ma lura dani ba badaÉ—ewa yan ajinmu suka taru da yawa a waje

'' ehen meye ne?" Ya tambaya da ƙatuwar muryar shi yana kallon mu da jajayen idonshi

'' anan ajin muke''

Hameeda ta faÉ—a cikin rashin damuwa dan ita dama bata tsoron duka ko kaÉ—an

'' in roƙe ku ku shigo ne?"

Ya tambaya da É—aga murya da sauri sauri aka fara shiga aji Ni ban ankara ba jin tambayar da yayi yasa nace

'' hakan ma dai dai ne!" Maganar ta sauka a kunnen shi yan aji ma sunji

'' dan Ubanki zo nan!"

Ya faɗa yana jawo hijabina ta baya saura kaɗan in faɗi na tashi tsaye da kyau ina ƙwalalo ido

''.maimaita abinda kika faÉ—a'' nayi tsuru da ido tsoro ya cika ni yan aji suka bimu da ido '' b...ba..n..ce komai ba...''

sai da yayi min kallon sama da ƙasa kafin idonshi ya sauka cikin nawa ya ja baya

''ke mayya ce?"

Ya tambaya da rainin wayo

'' a'a sunana Abeedah ba sumayya ba''

na bashi amsa nima da rainin wayo kafin yayi magana sai ga exam master ya faso kai aka tashi wurin gaishe shi hakan ya bani damar tserewa ya bamu izinin zama kafin ya shiga dogon zance akan waec dake ƙaratowa bayan ko rabin term ba'a kai ba yana ta zance har piriyod ɗin mas ya ƙare na gode mashi sosai...IRS...macijin sari ka noƙe ne ya shigo gaba... '' goooood morrrrrrni saaaa '' yan aji suka gaishe shi nidai miƙewa kaɗai nayi da wata yar iskar murya yace '' morning how' you?"

'' fayyyn tank yuuu saaaa'' abu kamar suna waƙa zab ban takaici '' ku zauna '' ya faɗa da rubuta kwanan wata da sunan subject ɗin

'' ba magana Bee?"

Jay D ta faɗa murya ƙasa bayan mun zauna
Chapter 31 · 0% Book details