← Book details Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 67

Sashe 8

Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama a ruɗe take tambaya ta cigaba da tambaya ta da ƙarfin hali irin na uwar data ga yarta cikin damuwa '' hum...dama wasu ne suka yi mata abinda suka saba!" da sauri Asma'u ta faɗa kanta tsaye hakan yasa na ƙara ɓoye fuskata a ƙirjinta, rungume ni tayi tana lallashina Muryar ta na rawa na tsani inji muryar Mama a irin haka, zuciya ta karaya take..duk da akwai sauran kuka cikina sai na haɗiye kawai

Mama ta ɗagoni tana share min hawaye tace '' Abeeda dan Allah ki dena saka kanki a damuwa ki tuna cewa duk wannan abun lokaci ne sannan kyaun jiki dana sura suna ƙarewa banda na hali...ki zama mace me kyakkyawar zuciya shine Abu mafi muhimmanci!" gyaɗa kaina nayi kawai babu wanda ke ganewa ko kuma zai gane sai wanda ke cikin yanayin..... Asma'u daga gefe tayi tsaye bata ce komai ba yanayin ta ya nuna bata ji daɗin abinda ya faru ba mema ake kiran kalmar da turanci....uhmm..

Autumn: guilty

ta kasa cewa komai..

riƙe hannayen mu Mama tayi ta shigar damu ɗakin mu dake ƙamshin tsintsiyar ƙamshi ta zaunar damu sannan ta fita

matsowa tayi da niyar magana sai kuma me ta tuna oho ta matsa baya nasan maganganun macijin sari ka noƙe ke yawo a kanta...

cire hijabina nayi tareda rigar uniform ɗin na ɗaura zane na zauna ƙasa bayana jingine da bango ido lumshe...bina da ido tayi,tasan maganganun ta ba ƙaramin...uhm..mema ake cema kalmar da turanci? yawwa...

Autumn: emotional breakdown

...eh.. kalaman ta sun ruguza ɗan sef istim ɗin dana samu daga malama Hafsah..da ina da low sef istim...amma yanzu shima low ɗin ƙila ya koma kwata ko babu ma duka

Kayan ta itama ta cire ta ɗaura zane ta zauna nesa dani tana wasa da yatsunta saboda wannan gilti ɗin datake ji..Mama ce ta shigo da plate ɗin shinkafa da miya ta ajiye.. da lafiya lafiya tashi zanyi inyita tsalle tsalle amma banda yau...baƙin ciki ne fal a raina abincin ma ya fita daga raina...

'' matso ga shinkafar nadafa tuwo!" Mama ta faÉ—a itama dai har yanzu bata wartsake ba,na tsani inga Mama cikin damuwa badan naso ba na matso mu duka muka fara cin abincin
bawai dan inajin daÉ—in abincin abakina ba nake ci...

Bayan mungama miƙewa nayi na fita ruwan sanyi na ɗiba daga drum na shige bayi nayi wanka minti talatin na fito na wuce ɗaki Vaseline na ɗauka ina shafawa ahankali a hankali ina kallon kaina ta madubi

Mama da Asma'u suka bini da ido, bayan na gama da wannan tsohuwar wardrobe ɗin mu na buɗe na ɗauki uniforms ɗin wurin aikin mu, baƙaƙen riga da wando da hijabi half sunna nidai nawa ya wuce ƙirji... ƙaramar singlet irin ta yara da pant pink color na ɗauka na matsa can gefe na saka kayan sannan na dawo na ɗauki hula fara itama na saka

yau shiru nayi babu mita babu kompilen,kwalli na shafa a idona dayasa suka ƙara fitowa da kyau naɗan shafa man baki wanda ni gaba ɗaya kwalliya bata dame ni ba,a ganina ni ba mace bace ban kaiba shine yasa banayi ko lip gloss ɗin bana shafawa...

duk da yanda nakeji na juyo da murmushi na kalli Mama nace '' Naga kinsa hijabi akwai inda zaki ne?" ajiyar zuciya ta sauke tace '' gidan Haule zanje ɗanta sale ne ya goce a ƙafa..''

'' subhanallahi! Garin yaya?" nida Asma'u muka tambaya '' wai an aikeshi shine kiken shi ya samu matsala wurin taka birki suka game da me mashin " ta bamu amsa cike da alhini '' bari idan anyi Sallah sai mu tafi tare daga nan in wuce wurin aiki!" na faɗa mata gyaɗa kai tayi nikuma na shiga neman wannan abun da ake laƙa ma mutum da suna a uniform mema ake kiranshi da turanci..uhmm... yawwa nem tag ( name tag) ganin shi nayi a ƙasan wardrobe na zuƙuna na ɗauka na kakkaɓe kafin na maƙala shi a gaban riga ta sunan dake jiki ' A.Tuwo' wato Abeeda tuwo juyowa nayi naga Asma'u ta kafe ni da ido rage girman idona nayi zuwa rabi...hakan yasa zuciyar Asma'u tsinkewa...tunda muke Abu irin wannan bai taɓa haɗamu ba...bana saurin warkewa daga gori...idan har aka goranta min akan abu ko kuma akayi anfani da ammm...mema ake kiranshi da turanci idan mutum na tsoron Abu...yawwa..insikiuritis (insecurities) toh yana matuƙar wahala in manta kuma bama dawowa daidai da koma wane ne yayi min hakan...

Bayan la'asar tare muka fito mu duka muna tafiya muna hira hakan ba ƙaramin rage min abinda ke zuciya ta yayi ba..ina matuƙar son Mamar mu ita kaɗai Banda Asma'u...uhh... shike nan dai.. itama ina sonta amma yanzu nayi fushi da ita

koda muka isa gidan Haule akwai mutane da yawa ga Saleh nan zaune da ɗauri a ƙafar shi,shima shekarun mu ɗaya,ana kiran hakan da turanci...?age mates!

nida shi bamu shiri ko kaɗan duk dashi bai taɓa kushe niba amma yana hararata gaisuwa aka fara tsakanin manya kafin aka fara magana akan Asma'u don ita duk wanda yaganta saiya maganta,tayi ƙasa da kanta tana murmushi jin ana yaba kyaunta'' oh harda ke aka zo kenan?" ya buɗe idonshi daga jin murya ta,kuma fa bacci yake..zama nayi gefen mama nace '' daga jin murya ta sai ka buɗe ido?" gyara zaman shi yayi yace '' yo na sani ko zuwa kikayi ki ƙarasani?" murmushi nayi nace '' ai saida daddare zaka ga wata mage me irin idona to nice!" tuf tuf yayi tareda faɗin '' li'ilafi ƙuraysh,aniyar moɗa tabi randa!" mutanen dake sauraren mu sunata dariya banda Asma'u...nima dai dariyar nayi

Mama ta miƙa gaisuwa nima na miƙa tawa da sauri yace '' ankarɓi ta Mama, ba'a karɓi ta Tuwo ba!" miƙewa nayi na taɓe baki tare da faɗin '' kadai ji dashi nan..ƙafarka ta karye kowa ya miƙo gaisuwa karɓa ake don ayi saurin tashi kai kana dawo ma mutane da gaisuwar su... toh nitawa karɓaɓɓace ehe!" nakai zauren gidan naji yana faɗin '' gocewa nayi fa ba karyewa ba!" aka saka dariya nima sai na murmusa... duk da bamu shiri da Saleh wallahi ina matuƙar ƙaunar shi fisabilillah
Kuma shima yana ƙaunata idan muka samu Abu sai mun bawa juna.. kuma bama rabuwa da cacar baki sai dai idan bamu ga juna

da sauri sauri na kawo bakin gate ɗin Maina granda hotel... gaidar da masu gadin nayi kamar koda yaushe sannan na shiga daga ciki,ƙaton hotel ne mai haɗe da restaurant,hotel ɗin ya haɗu ya gaji da haɗuwa dan 7 star hotel ne babba kenan

ta ƙofar baya na shiga na gaida head chief ɗin mu ko hakane sunan ta koba haka ba oho... faɗa ta balbale nidashi wai nayi latti... tafiya ta nayi nabarta da ɓaɓatu

cikin restaurant ɗin na shiga na samu abokan aiki na suna aiki nima sai na bisu ina karɓar order,Ina matuƙar son aiki na mafiyawanci duk ɓacin ran dana kwaso anan yake kwaranyewa idan na haɗu da abokan aiki... wurin a raye da surutun mutane ƙasa ƙasa ga hasken wannan globe ɗin me kama da sarƙa da ake kira da turanci uhmm.....candaliya ( Chandelier) ga sanyin ac da kuma Ƙamshin turaruka daban daban..duk da yau akwai sanyi dan Haryanzu rana bata fito ba,hakan bai hana a kunna ac ba

tuntuni na lura da yanda wasu dake zaune a table No. 6 suke kallo na suna lasar baki suna maganganu amma ban bi takansu ba...kirana suke zasu bada order naƙi zuwa na jawo zainab nace '' ga wasu can kije ki karɓa '' tafiya tayi ni kuma na matsa zuwa ɗayan table ɗin

Bayan mun gama karɓar order kowa yaje ya amso wanda ya karɓa, saboda zainab ta tafi toilet dole ni na karɓi order no.6...tura baron abincin nayi wanda ake kira da turance 🛒 cart... wannan na riƙe ba sai nayi tunani ba.. abubuwan da suka yi order shinkafa da mai da yaji,yajin cikin wata ƙaramar roba fara,sai salads da lemu, boza (burger)da tabarma (shawarma)da sauran su..

fuska a matuƙar ɗaure na isa gabansu na fara sauke musu abincin '' ji mana yan mata!" wani farin saurayi daka ganshi kaga bafulatani yayi maganar,sauran suna kallon kallo suna magana da ido,banza nayi dashi ina cigaba da sauke abincin '' kayan jikin ki sun burgeni! musamman daga ƙirji'' yayi maganar da shaƙiyanci, abokansa na taya shi

ji nayi kunya ta fara rufe ni jikina yayi sanyi musamman danaga kamar mu ake kallo, naji kamar insa hannu in kare ƙirjina amma konayi hakan abanza hijabin ƙarami ne

'' faɗa min bra size ɗinki in siya maki." plate ɗin dake hannuna na dire da ƙarfi jikina ya fara rawa kaɗan idona sukayi ja,na ɗago nakejin fushi na tasomin na kalleshi, sun ɗan tsorata kaɗan'' warin bakinka na damuna ko zaka iyayin shiru?" galala sukayi su dukan su.... mutanen wurin suka kwashe da dariya..wai an kunyata ɗan gaye

a fusace ya riƙe hannu na '' dan ma kin samu a na maki magana? me zanyi da flat board like you? da mumm....'' kafin ya ƙarasa maganar na ɗauki cokali na cika shi da yaji na tura masa a baki...

mutane suka hangame baki suna kallona shiko nan take idonshi suka yi jawur jijiyoyin wuyan shi suka miƙe...abokanshi suka kasa motsi

salad plate na ɗauka na kife masa akai na kalli cikin idonshi'' Flat board? a haka sheɗaniyar zuciyar ka take ƙawata maka ni...kuma kake yimin magana! nafi ƙarfin ka!" na faɗa ina warce hannu na nabar wurin.. tari yafara da ƙarfi ,da sauri ƙawayenshi suka dinga bashi ruwa yana haɗiye wa saboda azaba... idonshi sunyi ja dayaga abun bazai ƙare ba ya wani kwasa da gudu kamar mahaukaci salad na reto akanshi

mutane sai dariya suke ƙawayenshi suka ajiye mana kuɗin mu a table suka bar restaurant ɗin...

+2349138091955

RU'UYAA…📖
₦500 ne idan ya kammala zai koma ₦800
Biya ta wannan account É—in 9138091955..Salma Aliyu opay
Shaidar biya ta +2349138091955
Autumn writes 📖🖋️

RU'UYAA
The dreams we never lived
By Autumn 17 🍁🍁

5. ...
Chapter 8 · 0% Book details