Sashe 38
Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ɗauke idona nayi ina cigaba da jin haushin shi..a can baya suma sunyi tsit nasan sun ga nawar ya sauke mu mufara nunfashi...wayar sace ta hau ringin daidai saura second talatin a bada hannu...sai da wayar ya kusa katsewa sannan ya ɗauka da wani yare aka rubuta sunan dake yawo a screen ɗin...da ƙatuwar muryar shi yace '' Halo...'' abinda kaɗai na iya fahimta kenan...daga nan ban sake jin komai ba dan ƙasa ƙasa yake maganar kamar munafuki...
Ana bada hannu ya sake fisgar motar su Jay D da suka saki juna suka ƙara ƙanƙamewa...cire hannun shi yayi daga abun tuƙin ya ƙara ƙarfi AC'n bayan ya ga ina luƙunƙume kaina cikin hijabi tsabar mugunta... Bada jimawa ba ya kawo tsohuwar anguwar mu, lokacin har ya gama wayar...naɗan zaro ido amma nakasa cewa komai har ya paka ƙofar tsohon gidan mu da yanzu wasu ke haya ciki... batareda ya kalle niba yayi baya tare da faɗin '' come on Chop! chop! ...''
Yawu Anaam ta haɗiye ta buɗe baki tace '' b..ba na..nn ba..ane...'' bai motsa ba..nima ƙarfin hali nayi duk da so nake in sauka daga motar amma dai albarkacin littafan mu da zasu jiƙe nace '' mun can ja unguwa fa...''
Wayarshi ya kalla..bai kalli inda nake ba yace '' in fitar daku ne?'' wato shidai ala dole sai ya tabbatar min dashi Mugu ne ko? In ba mugunta ba taya zai sauke mu cikin ruwan nan?
Tura ƙofar Asma'u tayi ta sauka suma su Jay d suka sauka sai dana gama hararar shi na buɗe ƙofar na sauke ƙafa guda na juyo '' Amma baka da mutunci wallahi ga motar nan an sauka ka cinye tayi maka maganin yunwar dare!'' na sauka tare da buga murfin motar da ƙarfi take ruwa suka fara jiƙani amma hakan bai kashe wutar dake cikin zuciya taba tada motarshi yayi yabar mu tsaye a wurin Anaam ta jefo min jakata '' yaron nan baida mutunci Saida ya Khalil yace ya kaimu har gida amma ji inda ya sauke mu'' babu yanda muka iya muka fara tafiya dan ko kuɗi bamu da bare mu samu abun hawa Allah ya taimake mu wani mai adaidaita sahu yayi mana lift har zuwa gida...muka rakashi da addu'oi...duk da dai mun ɗan jiƙe amma ba sosai ba...
sallama mukayi muka shigo ciki inna sarai ta ɗage labulen ɗakin su saye da hijabi tana kallon mu cike da tuhuma gaisheta mukayi bata amsa ba ta shiga tambayar daga ina muke da sauri Asma'u da Anaam suka samu ƙarya suka faɗa..bata yarda damu ba amma bata musa ba ɗakin mu muka wuce zane na ɗauka na fito daga ɗakin zuwa baye bayan na gama wanka nayi alwala nazo nayi salla suma haka sukayi sai da muka zauna na tuna da abincin da Khalil yayi min take away '' hah ai sai dai ki hari gaba..ko in zaki iya kibi bayan wannan marar mutuncin dan dai abincin yana cikin motarshi a baya...'' inji Anaam
'' kuma idan mun shigo dashi ai daya tona mana asiri..ina muka samu?" Asma'u ta ƙara... naji haushi sosai...
'' ɗazu da kika rugo da gudu me yake faɗa maki hala?" Jay d tayi tambayar kowa ya tsare ni da ido '' cewa nayi dan Allah ya kaimu gida ko ya biyo kada wannan mara mutuncin ya mana ta'asa shine yace wai kawai bana son rabuwa dashi ne.'' na ƙarashe ina dariya...itama Jay d ta tayani '' ai dai abinda ake gudu ya faru kam...'' Anaam dake gaban madubi ta faɗa... Asma'u bata ce komai ba sai assignment ɗinta da take...
Dawowa Anaam tayi ta zauna tare da mu,muna hira mu uku jefi jefi Asma'u ke sako baki...da ƙarfe bakwai da rabi ruwan saman suka tsaya... Bayan Isha'i na zubo mana shinkafa da miyar da aka dafa..Anaam tana ci tana yamutsar fuska ita ala dole abincin da Khalil ya siya mana yafi daɗi '' toh ko zaki nemo shi ya ƙara siya maki ne?" Asma'u tayi maganar tana ɗage gira '' kema kin san da ace nasan gidan su,da tuni na mayarda shi wurin zuwa na..''
'' uhm tsabar rashin kamun kai...'' hararata tayi tare da jan tsuki...Jay D ko Magana batayi sai lodawa take...
Bayan mun gama cin abincin muka fito zuwa baranda,samun Mama mukayi da inna sarai zaune suna magana akan koma Meye fitowar mu ta katse musu zance kamar basa so muji abinda suke magana akai..zama nayi kusa da Mama Jay D ta zauna gefe na...Anaam ta wuce ta kai plate kitchen Asma'u a ɗayan gefen Mama..babu wuta amma...Jay d ta kunna laptop ɗinta..na lankaye jikina dana Mama ina rawar sanyi '' kuje kusa kayan sanyi mana..'' Mama ta faɗa...a tare muka girgiza kan mu alamun a'a...ta taɓe baki '' toh ai shikenan...''
'' Jadeedahtu ya kika ji da zama a gidan namu?" Mama ta mayar da hankalinta akan Jay d.. murmushi tayi da gaskiya tace '' ji nake kamar in cigaba da zama anan!"
'' Allah ko?" Inna sarai furta...gyaÉ—a kanta Jay D tayi su Mama sukayi dariya '' yarinya baki da wayo bakisan daÉ—i ba...'' inji Anaam
'' sannu ke mai wayo..'' inna sarai ta harare ta...nida Asma'u bamuce komai ba sai ƙara shigewa nake jikin Mama '' wai dai Abeedah ko ciki za'a mayar dake ne? Wannan abu haka..ko Asma'u bata da son jiki kamar ke!"
'' Nima dai abinda na gani kenan mata kamar kyanwa...'' juya ido na nayi '' idan kashi banza ne kaza tayi mugani ma..''
'' idan fitsari banzane ake cewa...shima karin maganar sai an ciki gyara...'' tashi zaune nayi na jefa ma Anaam wani kallo'' eh sai an cini gyara...aini ba kamar wasu bane komai sai dai ayi irin na wasu...ni nawa daban nake dan haka ina sane nace kashi ehe!"
'' hum! Abeedahtu kenan!" Inji Mama..tana shafa kai na...Anaam ta taɓe baki... laptop ɗin Jay D data fara magana ta katse mana ɗan cecekucen da mukeyi,wani fim ɗin Hausa tasa saboda su Mama '' dama kin sa mana fim ɗin chana...''
''.ba'a sawa...'' Inji Anaam
'' ke kiyi ma mutane shiru kinji ko!" Inna sarai ta tiƙi Anaam a tsakiyar baya...Anaam kamar zata haukace sai soshe soshe take bakin nan a gaba kamar daɓurin saniya...rufe bakina nayi ina dariya
Daga nan muka yi shiru muna kallon fim É—in,kallo da inna sarai da kwai takaici bata iyay' yin shiru daga ta dame mu da tambaya sai ta dinga faÉ—ar abinda zai faru koda kowa ya sani...duk sanda ta faÉ—i wani abu ko tayi tambaya Anaam tafara sallallami kenan kamar ita tafi kowa jin haushi amma ina son yanda Jay D take mata bayanin komai dan dai da nice bazan iya ba wallahi...
Bayan fim ɗin ya ƙare muka koma kallon fim ɗin China... Allah yasa bata dame mu da tambaye tambaye ba sosai sanyi ya sauko yana shiga cikin ƙasusuwan mu amma babu wanda ya shirya miƙewa..dukan mu mun bada hankali muna kallo...da ƙarfe goma muka yi ma su Mama sai da safe muka shige ciki... Hasken wayarta Jay d ta kunna muka gyara shimfiɗar mu kafin muka kwanta a tare...kowa da abun lulluɓinshi
Nake jin annashuwa na ratsani saboda kasancewar mu a tare...Jay ma bata ɓoye jin daɗinta ba...hira muka shiga yi kafin da guda guda bacci yayi gaba damu...
Da safe bayan munyi sallar asuba bamu tafi makaranta ba kamar yanda muka yi a gidan su Jay d sai da rana ta fito sannan muka tashi daga wurin da mukayi Sallah...a tare muka tafi ɗakin su Mama muka gaishe su..suka fi mayar da hankalinsu akan Jay d..bayan gaisuwa Mama tace kunu da ƙosai za'a yi
Da sauri Asma'u ta ɗauki tsintsiya ta fara share tsakar gida..na faɗa kitchen na aza ruwan dama kunu...taune leɓenta Anaam tayi ganin mun barta da wankin wake '' yayi '' ta furta daga ƙarshe..wake ta auno ta zauna ta fara wanki tana gunguni '' bari in taya ki..'' Jay d tasa hannun ta su biyun suka cigaba da wanki suna hira kamar ƙawaye kamar babu rashin jituwa tsakanin su...
Bayan sun gama tare suka kai niƙan,dama ƙullu nayi na sauke ruwan na juye sannan na ɗaura mai... Asma'u ta wuce ɗakin mu ta gyara ta share harda kunna tsintsiyar ƙamshi, a ɗakin su Mama ma tayi haka...ta share baranda sannan ta shimfiɗa tabarma...na ɗauka rana bazata fito ba amma sai naga ta ƙwalle kamar ƙarfe goma tayi lokacin...
shigowa su Anaam sukayi suna dariya...ta kawo min ƙullun,albasa na fara yankawa na zuba sannan nasa magunguna da sauran su..bayan man yayi zafi na fara soyawa...bada daɗewa ba na gama na ɗauki kular ƙosan na ajiye inda zamu zauna na dawo na ɗauki kunun da kofuka...
Su Mama suka fito suma,kowa ya zuba kunu da ƙosai daidai wanda zai iya ci...har Saida ma suka rage..dole aka bawa almajirai dake ta Bara... Kayan datti inna sarai ta kwaso ta watso mana mu wanke bamu da zaɓi dole muka haɗo da namu duka muka wanke...sannan muka yi wanke wanke..aikin tare mukeyi...da nishaɗi da annashuwa...wurin ƙarfe goma na fito ɗaki zan sha ruwa naji hayaniya a ƙofar gida..hijabina brown na jawo nasa sannan na leƙa,wasu yan mata ne su uku da duka duka bazasu wuce shekarun muba suke roƙon wani dogon yaro akan ya tayasu ɗaura lilo ga bishiyar kaiwar dake gaban gidan mu..shiko sai ƙamshi yake sha musu..ƙarasowa wurin nayi..suka kafe ni da ido saboda ƙwayar idona.. murmushi nayi musu sai muka gaisa...nake kallon igiyar dake riƙe da hannun ɗaya daga cikin yaran tace '' wai lilo muke son ɗaurawa a nan dafatan ba matsala?" Karɓar igiyar nayi daga hannun ta '' ba matsala bari in taya ku ɗaurawa...''
Wata daban ta riƙe baki ta kalli doguwar bishiyar sannan ta kalleni '' kin tabbata zaki iya kuwa?" Har nayi gaba nake faɗin '' ki kalle ni...'' namijin yayi tsaye daga gefe hannu naɗe a ƙirji irin yana jira yaga na kasa...na basu mamaki sanda na haye saman bishiyar batareda na sha wahala ba... ɗaura igiyar nayi a reshe mafi tsawo..na tabbatar ya ɗauru da kyau sannan na biyo igiyar na sauko dan tabbatar da ingancin ɗaurin...
Suna tayi min godiya '' sunana Maryam..wannan Hibbatullah..sai Amatur Rahman..'' wacce na karɓi igiyar daga hannunta ta gabatar min da kansu...'' suna na Abeedah...''