← Book details Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 67

Sashe 66

Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'' dake ki kasance uwata...Gara na mutu tun ina ciki!" Maganar ta sauka kamar bomb sauran matan suka zaro ido amma babu wanda ya isa yace komai...yan aikin sukayi ƙasa da kansu

Fuskokin duka waya'nda ke wurin sukayi duhu... Seraphina take kallon mu cike da tsana ba ita kaÉ—ai ba harda yan uwanta...da gudu tabar wurin tana kuka...

Diyaam yadai?? 👀👀

+2349138091955

RU'UYAA…📖

₦500 ne idan ya kammala zai koma 800

Biya ta wannan account É—in 9138091955..Salma Aliyu opay

Shaidar biya ta +2349138091955

Autumn writes 📖🖋️

RU'UYAA
The dreams we never lived
By Autumn 17 🍁🍁

30. ...son shi nake...🖊️

'' Come kitten...'' ya riƙo hannuna muka bar wurin Diyaam biye damu... zuciya tana tsananin ciwo...

Jinginar da bayan shi akan seat ɗin shi farzan yayi yake binsu da kallo har suka ɓace

da murmushin nasara a fuskar shi yabar wurin. su Hajiya Momma kamar maƙoshi zai faɗi tsabar yanda take ihu...

Anan parlor'n shi Khalil ya zaunar dani Diyaam zaune a gefe na shi kuma ya zauna a kujerar dake kallon mu...su biyun sai lallashina suke da ƙyar na samu na dena kukan sai shaƙuwa...

Ruwa ya zuba min a cup ya bani na amsa na shanye duka Diyaam ta riƙe hannu na tana shafawa nayi ƙasa da fuskata suddenly naji duk kunya ta kamani

'' Are You blushing?" Ya tambaya sai ya zaro wayarshi daga aljihun shi

'' kalli nan..'' hannuna nasa na rufe fuska ta bai barni ba har saida nayi dariya Diyaam na tayani daga nan yake bamu labarin zaman su Chicago yanda Roman abu kaÉ—an yake kaiwa mutane duka kamar Jackie Chan..hakan yasa ya dinga zuwa detention every now and

'' ai yanzu yayi sanyi,da dane ko magana ba zai yiba...cikin mu zai yi da duka dukan mu!" Nida Diyaam mun sha dariya har sai da cikin mu yayi ciwo...

da ƙarfe goma muka bar sashen shi,Diyaam ta wuce ɗakinta ni kuma na wuce namu sashen..samun Hansa'u nayi tsaye daga wurin gado na ina shigowa tayo kaina ta shaƙe min wuya

''shegiya wane irin tsafi kikayi amfani dashi wurin kama maxan gidan nan a tafin hannun ki...''

ƙoƙarin cire hannun ta nake daga wuyana amma abu yaci tura,fim ɗin Chinese ɗin da muke kallo ya faɗo raina yanda suke shure mutum idan an musu irin haka,ƙafata na ɗaga na sauke mata a ciki...taja baya harda faɗuwa ƙasa tana mulmula...da ƙyar na samu numfashina...

Ta miƙe tsaye tana huci..nace '' idan kina neman tsafin da nake amfani dashi...''

idona na nuna mata ina juyasu

'' wannan ne,kuma ke baki dasu...kin gane? Duk wanda ya kalla dole yaji ya ƙyasa!"

Na bangaje ta daga gabana na haye gado na...bada daÉ—ewa ba Mama Asabe ta shigo ta samu Hansa'u na kuka data tambaye ta cewa tayi

'' ba ruwanki tsohuwa..'' baki Alaikum Mama Asabe ta haye nata gado ta kwanta tan sauke ajiyar zuciya sai kuma ta fara juye juye

'' Mama Asabe lafiya kuwa?" Na leƙo kaina

'' lafiya lau Abeedah ciki nane ba daidai ba''
'' oh... Allah ya kawo lafiya...''

'' Ameen...'' bayan wani lokaci nace '' abin nan naki yana aiki Mama Asabe na gode sosai Allah ya ƙaro arziƙi!"

'' Ameen Ameen Abeedahtu..''

***

Washegari a gaggauce na shirya cikin uniforms É—ina, tunda ance ba zamu dinga aiki ba sai kawai na É—auki littafina ina muraji'a...

Da ƙarfe bakwai muka sauko zuwa dining ɗin mu wurin kari...Su Fauziyya, Hansa'u da sauran wasu daga cikin masu aikin sai hararata suke kamar na tare masu wani abu..babu abinda ya shamin kai ko kaɗan...

'' Allah ya bada sa'a Abeedah yasa a rubuta a sa'a ba sai an maimaita ba!" Mama Asabe tayi min addu'ar.. waya'nda ba yan baƙin ciki ba suka amsa da Ameen Hansa'u taja tsuki tace

'' Allah yasa daga waec har neco ɗin kiyi ta maimaitawa har ƙarshen rayuwar ki!"

'' Ameen ya hayyu ya qayyum!" Su Fauziyya suka amsa da ƙarfi..

Naji ba daÉ—i amma sai na kauda kaina kawai...bada daÉ—ewa ba na gama breakfast É—in...Babban gida muka shiga tareda Mama Asabe dasu waleeda suka wuce wurin aiki Ni kuma na wuce sashen Khalil in duba shi...

Da farko ƙofar ɗakin Roman na fara isa kamar in shiga kamar in ƙwanƙwasa daga ƙarshe na juya na bar wurin raina ba daɗi ..

Sashen Khalil na tafi na ƙwanƙwasa ya bani izinin shiga...na ɗan waro ido ganin su biyun zaune a parlor...Roman saye da jajayen kaya..gashin shi ya pake sama da ƙasa..ba ƙaramin kyau yayi ba... hankalin shi a kan laptop yana aiki..

'' Oh kitten...'' murmushi nayi mashi yace in ƙaraso ciki...ya nuna min ɗayar kujerar dake daga gefen hagu shida Roman zaune a kujera ɗaya...na zauna ina satar kallon Roman da bai kalli inda nake ba...

'' how are you today?" ya tambaye ni '' lafiya Lau,ya jikinka?"

'' Alhmadulillah!" Na gyaɗa kaina...na ƙara satar kallon Roman...can ya ɗago ya kalli Khalil ya tura mashi laptop ɗin yace '' na gama yanzu zaka iya submitting ba dole sai kaje can ba!"

Duba laptop É—in Khalil yayi ya gyaÉ—a kanshi..Roman ya fita daga sashen..bai kalle niba...kenan yayi fushi dani...

Khalil ma ya shiga nashi ɗakin,ina nan zaune ya fito riƙe da chocolate irin wanda Diyaam ta taɓa bamu ya miƙa min na karɓa ina kallon shi '' good luck with your exams!" Murmushin shi yasa naji nauyin da zuciya ta tayi ya rage...'' na gode!"

Na amsa..sai na miƙe '' bari in tafi kada inyi latti!"

'' driver zai kai ki?" Ya tambaya na girgiza kai, naga ya ɗauki wayar shi dake saman table da sauri nace '' a'a nafi son tafiya da ƙafa ne...''

'' really?" Ya É—age min gira na gyaÉ—a kaina '' okay...''

Fitowa daga ɗakin shi nayi ina tafiya slow slow naci karo dasu Seraphina..wani tsinannen kallo suka wurga min su uku dayasa zuciya ta bugawa da ƙarfi...

'' manta da cewa Ya Rome yace a rabu daku, wallahi sai zama a gidan nan ya gagari ku biyun!" Khaleesat ta faÉ—i hakan sauran basu cemin komai ba sukayi gaba...gabana ya shiga faÉ—uwa.. addu'a nayi na wuce É—akin Diyaam itama ta shirya breakfast take yi ita kaÉ—ai a É—akinta

'' Toh ni zan tafi idan kin gama sai ki iske ni..'' da sauri ta tashi tasa hijabinta tace '' bari inzo mu tafi...''

'' ke da mota zaki ni kuma da ƙafa zani...''

'' zan faÉ—awa Hamma sai mu tafi taren...''

'' a ƙafa?" Ta gyaɗa kanta...

Jakarta ta É—auka ta fito...É—akin Roman muka tafi amma bai nan muka sake zuwa inda yake art..nan ma bai nan

Sai da muka fita muka hange shi a parking lot,Diyaam gaba ina biye da ita... fatan zai kalleni ko sau ɗaya ne amma da muka isa har sukayi magana suka gama bai kalli sashe naba...irin chocolate ɗin da Khalil ya bani ya miƙa mata tare da faɗin '' Ace your exams papillon (butterfly)'' ta amsa da '' insha Allah Hamma...'' ya gyaɗa kanshi sannan muka bar wurin.. zuciyata na ci da wuta..kamar inyi kuka sai Juyowa nake ina kallon shi...

Yau ko kyau'n anguwar ban gani ba...har muka iso makaranta raina ba daÉ—i kuma babu wanda yayi magana cikin mu...

Wurin ƙarfe takwas su Jadeedah suka iso muka haɗu cikin farin ciki muna yima juna Allah ya bada sa'a.. wannan lokacin har an canja mana lambobi...

Dukan mu ajujuwa daban daban muke...kafin mu shiga jarabawar sai dana raba mana chocolate É—in da Khalil ya bani '' ina kika samu wannan chocolate É—in Abeedah?" Jay d ta tambaya

'' Khalil ya bani...'' zaro ido Asma'u tayi '' ina kika ganshi?" yanda idonta ke sparkling naso in gano wani abu kafin in amsa malam Nura ya gargaÉ—a mu zuwa ajujuwan mu...

Tsaye mukayi a bakin ƙofa idan an kira mutum da number shi sai ya shiga aji...nice no 17... ana kira na faɗa ajin na samu wuri na zauna...kafin wani lokaci har kowa ya zauna...babu kowa a corridor'n...

Ajin duk wanda ka kalla zaka ga fuskar shi ɗauke da damuwa sai yan ƙalilan...ajiye pencil da biro da cleaner nayi saman table ina addu'a zuciya ta fal da tsoro
da ƙarfe goma za'a fara jarabawar,a tunani na kafin nan,fargaba da tsoro sun gama damu... Finally lokaci yayi aka shigo ana rarraba mana tambayoyin da amsa booklet bayan an gargaɗi masu ɗauke da takarda ko wani abu na satar amsa su fitar dashi...

da ƙarfe goma da rabi exam ta kama zamu gama huɗu da rabi... numfashi naja kafin na jawo pencil ɗina na fara rubuta amsa bayan na cika duk bayanan da aka buƙata

Malamai ne ke bi row by row suna karɓar kuɗin ɗalibai suna basu amsa...sanda naga hakan ba ƙaramin mamaki nayi ba sannan naji wani abu ya daki zuciya ta...idan anyi magana sai suce taimako suke bayan kuma babbar illa suke haifar wa na cin hanci da rashawa da kuma daƙile ɗalibai wurin karatun jarabawa...

sanda suka tambaye ni idan ina so in biya ɗari biyar na girgiza kaina wani irin kallo suke bina dashi,bani kaɗai ba harda sauran wa'yanda suka ƙi...

Da ƙarfe sha biyu da rabi muka gama objective aka bamu hutun awa ɗaya kafin a koma ayi essay...

Ƙarƙashin bishiya muka zauna mu biyar... Asma'u ta sake tambaya ta ina na haɗu da Khalil

'' wai ke ko son Khalil ɗin nan kike ne?" Anaam ta tambayi Asma'u tana riƙe haɓa... blushing Asma'u take kafin tace '' wai ma...ni nace ina son shi?"

Jay d tana dariya tace '' to bagashi ba duk kin bi kin isheta da ina suka haÉ—u....''

'' in sonshi kike Gara ki faÉ—a tunda wuri!" Anaam take tura kafaÉ—ar Asma'u da zolaya

'' ba so ba ƙauna... mtschewww!" Tashi tayi tabar wurin bayan ta faɗi hakan...

Sallah mukayi kafin muka sake komawa aji..nan ma an karɓi kuɗin mutane,nidai da kaina nayi wannan jarabawar kuma ina roƙon Allah yasa hakan ta kasance har ƙarshe...2:00 muka gaba paper essay aka zo oral test kuɗin wannan sashen yafi yawa har dubu ɗaya acewar malaman wai wannan yafi wahala...

Wani abun mamaki harda invigilators aka haɗa baki ana biyan su...faɗin yanda nake jin ƙunci a zuciya ta game da hakan ɓata baki ne ...
Chapter 66 · 0% Book details