← Book details Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 67

Sashe 52

Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

''.gashi tana da wanda ke ɗaure mata ƙugu a gidan nan...'' wacce batayi magana ba ta faɗa tare da tattare hannun rigar ta muka cigaba da wanke wanken suna hira akan samari da yan matan gidan...

Sai wurin sha É—aya muka gama wanke wanken...na gaji iya kar gajiya...fita sukayi daga kitchen É—in na samu wuri na zauna saman É—aya daga cikin kujerun dake kitchen ...ruwan goran dake gabana na shanye ina tunani...

Ina kallon kitchen ɗin shima dai ba ƙaramin kuɗi aka kashe ba...

'' yan mata...'' a hankali na juyo,ganin shi nayi tsaye daga bayana...gayen nan ne daya zage ni a dining jiya irin kallon nan na rashin ɗa'a yake bina dashi kamar jiya...da ɗan iskan murmushi a fuskar shi yana shafa ƙaramin gemon shi kamar na bunsuru...sauka nayi daga saman kujerar na matsa nesa dashi yake bin duk wani motsi nawa da idon rashin kunya,na buɗe baki zanyi magana kenan Hansa'u tashigo kitchen ɗin tana botsare botsaren ƙirji..cikin maƙe murya tace

'' Abeedah,Mama Asabe na neman ki...'' take wani fari da ido...da ace kallo na kashe mutum data kashe ni,batareda na sake kallon kowa cikin su ba na fita daga kitchen É—in...

Bin bayan Abeedah yayi da kallo dirty things na yawo a kanshi,her gray eyes were a massive turn on for him.. idonshi suka ƙanƙance ya sake shafa fuskar shi... Hansa'u take kallon tsakanin ƙofar da Abeedah ta fita da kuma gayen da yayi tsaye yana bin ƙofar da kallo like a fool..tsuki taja a ranta...sai kuma ta fara takowa cikin jan hankali

'' Barka dai yallaɓai...kana buƙatar wani abu ne...?" Kallon idonta da take jujjuyawa kamar na kwaɗo yayi...yaja dogon tsuki out loud..hakan ya soki zuciyar Hansa'u...ya zagaye ta zai fita sai kuma ya tsaya ya juyo ya ƙare mata kallo...the girl was curvy amma baƙa ce mummuna... however,zai iya maneji besides itama ai abinda take nema kenan ko...

'' ki kawo red wine...22'' ya fice daga kitchen bayan faÉ—ar hakan... Hansa'u ta É—anyi jim tana tunanin Meye 22...nan ta fahimci É—akin shi yake nufi...zaro ido tayi ta dafe kumatun ta...damn! She landed a jackpot É—akin shifa ya kirata....

Sashen muna koma na, anan parlor naga da yawa cikin masu aiki sun dawo harda Fauziyya gaishe su nayi dayawa cikin su sun amsa harda tambaya ta ya ranar farko murmushi nayi '' ba sauƙi ko kaɗan...''

Na basu amsa sannan na wuce É—akin mu,samun Mama Asabe nayi saman sallaya tana tasbihi da alamu salatul duha tayi..hijabina na cire na É—an kwanta da niyar idan tagama inji kiran datake min...

'' Abeedah ki tashi karfe biyu...'' naji ana jijjigani..buÉ—e idona nayi..lokaci guda na tashi zaune ina murza ido da sauri na faÉ—a Baye nayi alwala nazo nayi sallah...taya akayi nayi bacci har haka

'' bacci lokacin aiki nasa a rage ma mutum albashi ki kiyaye...'' Mama Asabe dake jirana ta faɗa..gyaɗa kaina nayi dai dai nan Hansa'u ta shigo tana tafiya da ɗingishi..ƙila ƙafarta ta buge..amma kallon da Mama Asabe take yimata ya faɗi wani labari daban...well,ba ruwana da yima kowa hukunci...

'' Mutafi Mama Asabe...'' na miƙe na ninke daddumar na mayar da hijabi na sannan muka fita zuwa babban gida.... kitchen muka shiga naga su Aina'u da Waleeda suna cikin wa'yanda ke jera abinci dining.. murmushi muka sakarwa juna kafin suka fita... Mama Asabe itama fita tayi daga kitchen ɗin da alamu tana da aikin yi...

'' yarinya zoki ɗauki wannan salad ɗin ki kai musu a can...'' ɗaya daga cikin masu girkin ne yayi magana... numfashi naja..na ɗauki Salad ɗin na fita zuwa dining...ina ƙara matsowa ina jin hargagi na tashi ana yima wata faɗa

'' stupid girl,kin ɓata min kaya dan baki san ciwon kuɗi ba...''

'' come on, ya'yan talakawan nan yan baƙin ciki ne...''

'' shine yasa bana so suna zuwa kusa Dani kada su goga min tsiya!"

Wa'yannan sune maganganun dake tashi...dana matso kusa naga wata yarinya daga cikin ma'aikatan duƙe a saman guiwowinta..kuma fa duk manyan gidan na nan..a gaban su ake komai

Zuciyata ta kusa faɗawa cikin ciki na sanda naga ashe waleeda ce yarinyar da ake yima wannan cin kashin... Sauran kuma sunyi tsaye kansu ƙasa...

'' Seraphina..ya isa haka...'' hajiya Wareesha ta harare yar ta...

'' But mom,kina ganin yanda dumb girl É—in nan ta zubar min da juice on my expensive dress...''

''.babu kuÉ—in sayen wani ne?" Hajiya Wareesha ta katse ta

'' this is my favorite....''

'' come on sera, kibar shi kawai zan maki transfer ki sayi wani is that okay?'' Alhaji Sulaiman yayi ma yar tashi murmushi tare da zaro wayarshi yayi mata transfer É—in

Tasowa tayi daga inda take zaune tazo ta rungume shi

'' thank you dad... you're the best..I love you...'' shafa doguwar sumar kanta yayi yana murmushi dan sosai yake son ta

'' Hmmp! Dad nima fa ina buƙatar kuɗi...''

Khaleesat tayi maganar tana kallon mahaifinta Alhaji Kabeer...É—aure fuska yayi shikam '' saboda wani yayi abu kema sai kin yi ko?" Turo baki tayi idonta ya ciko da hawaye ta juyo tana kallon hajjo dake kallon ya'yan nata da jikoki da murmushi a fuskar ta

'' Hajjo kin gani ko?'' Tea'n dake hannunta hajjo ta karɓa da Muryar ta mai ɗauke da isa da izza tace '' zan baki kada ki damu...''

Da murna Khaleesat tayi godiya...sauran ma suka shiga ƙorafi akan akwai abubuwan da suke buƙata...

Gaba É—aya mutanen nan sun manta da baiwar Allah'r da suka sa tayi kneel down a guiwarta...

Jiki a sanyaye na shigo wurin,ido na ya haɗu dana Waleeda..naji zuciya ta ta ƙara karyewa...salad ɗin na sauke a saman dining jiki ba ƙwari

'' Oh Sera...ki kalli yarinyar nan mai fuska kamar anyi hatsari....'' Aryana ta faÉ—a tana dariya...sauran ma suka bita....

'' Ke,bana ce kada in sake ganin ki a wurin nan ba?" kamar sun samu TV dayawan su suke kallon dramar dake faruwa...

''Oh....ban jiba kenan...''

'' ke! Kina yar talakawa ƙasƙantacciya kina aiki ana faɗa kina faɗa?" Armani ta daki table ɗin ta miƙe tsaye tana nuna ni da hannunta kamar zata haɗiye ni

'' Ni,ba ƙasƙantacciya bace! Kamar yanda kika faɗa aiki nake ana biya na..bawai kyauta ake bani kuɗin ba! Ke...'' Mama Asabe tayi saurin ƙarasowa ta jaye ni da sauri... mutanen dining ɗin suke bina da kallo...

'' Dan Allah kuyi haƙuri,sabuwar zuwa ce bata san yanda abubuwa suke tafiya a gidan nan ba,ai mata afuwa zan mata bayani...''

'' a matsayin ta na yar aiki,tasan wannan idan masu gida suna magana,bai kamata ta amsa ba har sai an bata izini...'' Hajiya Bushrah ta katse Mama Asabe muryarta da zafi a ciki

'' kuma idan ana magana ƙasa ya kamata tayi da kanta bata dinga kallon mutane ba cikin ido...'' Hajiya Ruƙayyah ta ƙara batareda ta kalli inda muke ba ... Sauran ma kowa sai zagin mu suke suna faɗin yanda ya kamata inyi a matsayi na na yar aiki...

Zuciya ta tafasa takeyi musamman dana ga Mama Asabe ta zage tana bada haƙuri...dungura ta tayi akan in bada haƙuri...dogon numfashi naja badan naso ba na bada haƙurin wanda nayi nadamar badawa saboda yanda suke kallonq...

Mama Asabe ta riƙa hannu na zamu bar wurin '' wayace ita zata iya tafi? Ta tsaya nan!"inji Mukhtar...sakin hannu na Mama Asabe tayi tana kallona da idonta alamun in kama kaina...

Badan naso ba na dawo na tsaya...

'' Oya zonan zoki dinga ɓanɓare fatar wannan grapes 🍇 ɗin...'' Heedayah ta nuna min wasu inibi dake tsakiyar table ɗin,sauran suna kaɗakai kamar wannan shine hukunci mafi tsauri...kallon ta nayi na ɗan zaro ido...

'' Madam,bawai ina ƙin abinda kika sani bane,amma bakya gudun kada inyi contaminating ɗinsu?"

Haɗe fuska tayi kafin tayi magana Seraphina ta rigata faɗin '' ba damuwar ki bane, besides babu wanda zai ci abinda kika taɓa..so just do as you're told!"

Na kalli yarinyar da bazata wuce shekaru sha takwas ba yanda take bani oda kamar uwata...da yake suna da kuÉ—i ai dole suyi yanda suka ga dama...

Zagayowa nayi na fara yi kamar yanda ta faɗa,ba abu bane mai sauƙi,sauran yan aikin suke kallona da tausayi..nima dai na fahimci wauta ta... Da ɗaya ɗaya manyan suka fara barin table ɗin ya rage saura samari da yan mata suna magana akan abubuwa kafin maganar su ta dawo akan mu yan aiki...suna zagin mu da ci mana mutunci...

'' Ke!" Armani ta nuna waleeda da idonta sunyi jawur...a firgice waleeda ta kalle ta '' bar wurin nan!" Miƙewa tayi da sauri amma sai dai ƙafafunta sunyi tsami dan haka ta faɗi...taune leɓenta tayi kafin ta sake tashi tana ɗingishi ta bar wurin da hawaye a idonta...

Tunda na tsaya wurin nake jin ido na yawo ajikina É—agowa nayi idona ya sauka a cikin na Mukhtar dake kallona kamar tsohon maye...nake ji kamar in zube mashi plate É—in inibin nan a jiki...amma ba dama...

'' wannan yarinyar is too flat..dalla sai wani kallonta kake...bata da gaba bare baya...can you not disgrace us pls!" Seraphina ce tayi maganar kowa dake wurin suka kwashe da dariya...jikina ya fara rawa dan Nasan dani take...duka mazan suka juyo suna ƙare min kallo..da farko Mukhtar kaɗai ne......

A zahiri hankalina kwance yake..amma a baÉ—ini ni kaÉ—ai Nasan yanda nake ji...

Jameelah tace'' da gaskiyar ki fa Sera...I wonder idan tayi aure mai mijinta zai taɓa yaji laushi...'' suka sake dariya...sauran yan aikin kuwa kansu na ƙasa bansan meye tunanin suba...

'' come on, don't be dirty minded ...'' Ayaan ne yayi maganar yana latsa wayarshi

'' na yarda she's flat like board...amma gray eyes É—in nan..Are a big turn on don't you think?" Imam ya furta

'' ka rigani furtawa ne É—an uwa...'' suka kashe shida Mukhtar kamar mata...

'' Awwn...kuka take fa...da alama kun tsallake iya ka!" Kareema ce ta faɗi hakan da nuna tausayin ƙarya...

Ashe kuka nake? Ni ban ma sani ba sai da tayi maganar naga hawaye na sauka akan hannu na...

'' yanzu ma ta fara..badai tana da baki ba? Bakin zai mutu kafin tabar gidan nan...haka wannan shegiyar yarinyar itama a da baso tayi ta botsare ba...yanzu ta isa ko kallon mu cikin ido tayi?" Cewar Mufeedah
Chapter 52 · 0% Book details