← Book details Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 67

Sashe 67

Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Da ƙarfe huɗu muka gama jarabawa...muda bamu biya kuɗi an bamu amsa ba,cewa suke mu jira ranar mathematics..dole muma mu shigo layi... nikam insha Allah har ƙarshe da kaina zanyi...

Ƙarfe biyar da rabi muka isa gida nida Diyaam..muna tafe muna magana akan jarabawar duk da nidai nace kada ta faɗa min wanda ke daidai da wanda ba daidai ba gudun anxiety...

Sashen mu na tafi ita kuma ta shige babban gida...

Wanka nayi na canja kaya naci abinci cikin kwanciyar hankali... tunanin haɗuwa da Roman yasa bugun zuciya ta ya ƙaru kafin nishaɗi ya mamaye ilahirin jikina...

Da sauri na gama cin abincin na shiga can ciki... sashen Khalil na fara zuwa na same shi yana kallon ƙwallo...yana ganina ya saki murmushi '' Oh.. kitten!" Murmushi nayi mai haɗe da dariya kullum haka yake cewa '' oh kitten..''

'' Oh Khalil..." Nima na faɗa tare da zama can ƙarshen kujerar dake gefen shi,shafa ƙeyarshi yayi '' ashe kaima kana ɓata lokaci haka? '' ɗage gira yayi nace '' wai mutum yayi ta guje guje cikin fili ana sharɓe shi yana faɗuwa...wai duk dan ya kamo waccan abun!"

'' it's entertaining...'' ya ban amsa taɓe baki nayi nace '' ai nikam idan nayi aure mijina yace zai kalli wannan abun sai dai ya kwana waje!" Sosai yayi dariya...sai ya miƙo min remote yace '' to ki kalli abinda kike so..''

'' a'a ka barshi kawai tunda kallo kake...''bai saurare niba ya turo min remote É—in...É—auka nayi na canja zuwa YouTube na nemo MSA

Ya É—an zaro ido '' Cartoons kike kallo?"

'' nayi girma da yawa?" ya girgiza kanshi sai muka mayarda hankalin mu muna kallon tare...

'' ya exam?" Can ya tambaya..ai ko kamar an buÉ—e tap na fara bashi bayani yanda yan kaÉ—an cikin mu kaÉ—ai sukayi jarabawar da kansu...

Da kuma yanda ake karɓar kuɗi aba mutum amsa harda invigilators ɗin.. duk cikin bashi labarin ne na taso daga inda nake zaune na zauna gefenshi..

'' You did well,kada ki bada kuɗi a baki amsa, kiyi da kanki kinji?" gyaɗa kaina nayi ya sakar min murmushi na dawo da kallona akan tv'n dai dai an kawo wani wuri a cartoon ɗin, inda akwai wasu kaloli da yawa kamar hayaƙi suna bin sama..kalolin akwai green,pink,blue da sauran su...

Sosai idona ke ƙyalli '' ya maki kyau ne?" Khalil daya lura da yanda nake kallon wurin ina zallo kamar zan shiga cikin TV'N ya tambaya '' sosai ma...akwai wuri irin haka da gaske?" gyaɗa kanshi yayi '' it's called Aurora..ko northern lights...''

'' Innalillahi ina so in tafi wurin...'' na faÉ—a cike da murna '' I'll take you some day...'' yaban amsa '' da gaske? amma ai babu a Nigeria...''

'' akwai a Norway...da Canada da sauran ƙasashe...''

'' xan yi farin ciki kuwa...'' na faɗa da gaskiya..ya ɗan matso yace '' kin san a US idan mutum yana farin ciki...they used to give a hug like this...'' ya matso zai rungume ni, pillow'n dana rungume na tura mashi na miƙe ina dariya nayi ƙofa '' idan ka kaini sai nima inyi maka...''

Shafa gefen fuskar shi yayi '' remember your words!" Ya faÉ—a daga bayana...

Ƙofar ɗakin Roman na tafi na bubbuga amma ba'a buɗe ba kuma ba'a bani izinin shigowa ba...ƙila bai nan...studio ɗin shi na tafi nan ma bai nan

Naji yanayi na ya koma na rashin farin ciki...wurin lambu na tafi a can na same shi ya ajiye painting tools É—inshi yana painting

Zuciya na zallo na ƙarasa wurin...'' Roman...kayi haƙuri..'' na riƙe gefen hannun rigar shi...mutumin nan ko gezau kamar bai san dani a wurin ba

'' kaji...'' na ƙara jijjiga hannunshi ina turo baki...'' kaji Romeo...'' cije bakina nayi kada inyi dariya dana kira shi Romeo hannunshi dake shafa painting ya daskare

'' Kaji..bazan sake ba!"

'' Are You trying to annoy me,cuz it's working!" Ya faÉ—a sharply tare da Juyowa ya kalleni da fushi a idonshi

'' a'a..''

'' to bar wurin nan!" Ya nuna min hanyar fita sakin hannun rigarshi nayi...sai kuma na lakato painting na shafa mashi a kumatu ba zato ba tsammani...sakin plate É—in painting yayi ya fara tattare hannun rigar shi kamar zai kama da wuta da alamu..abinda yayi ma securities É—in nan zai yimin...da gudu na juya na fita

Daga nan ya dena yimin magana kona mashi bazai amsa ba,bazai kalle niba..duk nabi na damu.. fara'a ta ta ragu...su Jay d sun lura da wannan dan haka...ranar juma'a ta titsiye ni akan sai na faɗa mata abinda ya faru...cikin kuka na zayyane mata gidan su Khalil nake aiki...kuma yanzu...well ban sani ba ko sonshi nake amma dai baya min magana kuma hakan na sani a baƙin ciki...

Rufe bakinta tayi bayan na gama kafin ta saki dariya hakan ya ƙara ƙular dani..tsagaitawa tayi ta fara lallashina sannan ta faɗamin abubuwan da zan yi dan ya kula ni..harda..bashi haushi, tambayar shi abubuwa marasa ma'ana...da flirting...nidai ban san ko wannan good ideas bane...but I was determined to try!

masu cewa Roman ya fara son Abeedah..toh nidai na faɗa tun farko yarinyar tana da rawar kai..ga shi harta faɗa tun kan aje ko ina 🙆🤣

shi kuwa bamu masan abunda ke wakana a ranshi ba....tsabar kamun kai😏😏

+2349138091955

RU'UYAA…📖

₦500 ne idan ya kammala zai koma 800

Biya ta wannan account É—in 9138091955..Salma Aliyu opay

Shaidar biya ta +2349138091955

Autumn writes 📖🖋️
Chapter 67 · 0% Book details