Sashe 46
Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ɗaga kanta Anaam tayi tana kallon motocin dake zuwa kamar ana kwararo su dan babban titi ne mai hanya biyu wasu na zuwa wasu na tafiya.... numfashi taja ta riƙo hannun tsohon...da kulawa dan tsohon baida ƙiba kamar ayi iska ya tafi dashi...suka fara tafiya...motocin sai honking suke da ƙarfi...zuciyar Anaam ta dinga bugu da ƙarfi...tsohon kuma duk ya firgita jikin shi nata rawa idonshi sun fito kamar zasu faɗi...wasu daga cikin motocin kamar bazasu tsaya ba..kamar zasu bi takansu su wuce
Da ƙyar Anaam ta tsallakar dasu zuwa ɗayan gefen inda akwai bishiya a wurin ta zaunar da tsohon saman benci...itama ta zauna tana sauke ajiyar zuciya...'' na gode sosai yar nan Allah shiyi albarka ya kawo miji na gari..yasa a gama da duniya lafiya...'' duk addu'oin da yake mata ta amsa da Amin banda addu'ar aure..not when she saw yanda babanta ke treating mamanta da sauran matan shi...not when she saw yanda babanta yayi neglecting duties ɗin da yake dashi akan ya'yan shi..Anaam bazata taɓa yin magana akan babanta ba..dan babu wani abin da yake dashi na faɗa na alkhairi...da ace ita keda zaɓi bazata taɓa yarda ta kasance yarshi ba...sai dai mutum baya zaɓan yanayin haihuwar shi....
Gani tayi tsohon zai miƙe ta kalle shi tare da faɗin '' kana buƙatar wani abu ne?" Yana cigaba da miƙewar yace '' zan yi sallah ne...''
'' to ka zauna bari in kawo maka ruwa...'' zama tsohon yayi Anaam ta miƙe tana kalle kalle.. can ta hangi pamfo harda masallacin da dafarko ma bata lura dashi ba...isa wurin tayi ta ɗauki buta ta cika mashi da ruwa ta ajiye gaban shi '' Allah shiyi albarka...'' yake maimaitawa kafin ya naɗe rigarshi data gama tsufa ta dagargaje ya fara alwala...Anaam ta tsugunna daga gefe tana kallon shi..amma a zahiri tayi nisa cikin tunani ne...bata roƙon Allah ya kawo ranar da zata sake komawa mahaifinta...kuma ta gode Allah da auren shi da mamarta ya mutu har abada...
'' na gama...'' Muryar tsohon ta fito da ita daga tunanin data shiga ta iso inda yake ta taya shi miƙewa har bakin masallacin ta isar dashi..ta gyara mashi mat ɗin dake gaban wurin...ya dafa bangon wurin yana tafiya da ƙyar ya shiga Masallacin ita kuma ta tsaya daga waje tana kallon shi...daga baki baki ya tsaya da alamu nan zai yi sallar ya juyo one last time yace '' Allah ya raba ki da mummunar ƙaddara ya baki zuri'a na gari...wanda zai kula dake da ya'ya na gari da zasu kula dake kamar yanda kika kula Dani...''
Murmushi Anaam tayi tana amsa addu'ar farko sauran kuwa taɓ ɗi jam...
Jin yanda idanun mutanen dake masallacin ke yawo a jikinta yasa ta bar wurin...yanayinta ba daɗi...wani makahon tsoho ta gani yana dungura sandar shi da robar Bara a hannunshi...ɗari uku ɗin da batayi amfani dasu ba wurin hawa abin hawa ta miƙa mashi bayan ta isa inda yake... Nan ma tasha godiya da addu'a ...ita dai nata murmushi...har tsohon yabar wurin tabi bayanshi da kallo...a niyarta shine Allah yaba su abinda suke nema ita dasu Abeedah kuma har abada kada ya ƙara haɗa fuskarta data babanta...
Ta juyo kenan idonta ya sauka akan Abeed daya daÉ—e yana kallonta da burgewa...gabanta ya shiga faÉ—uwa..da sauri ta juya ta fara tafiya kamar zata tashi sams
Shiga motar shi Abeed yayi ya biyo bayanta...a daidai saitin ta yayi ƙasa da glass ɗin shi '' yar fullo ba magana?" bata tanka shi ba sai sauri data ƙara..shi kuma ya cigaba da bibiyarta da mota...a fusace ta tsaya Tare Da Juyowa...sai dai ta kasa sauke masa tsiwar data yi niyar yi saboda yanda ya cika mata ido ..samun kanta tayi da jan tsaki ƙasa ƙasa...
'' shigo in kai sauke ki...'' da sauri tace
'' a'a kabarshi kawai ...zan ƙarasa da ƙafa...''
'' okay bari in sauko sai mu tafi tare...'' ganin yana shirin saukowa kuma dai ita bazata so a ganta tana tafiya da wani namiji ba yasa tayi saurin faÉ—in
'' Allah ka tafi zan iya tafiya gida da kainaaa...'' taja kalmar ƙarshe a shagwaɓe batareda tasan tayi hakan ba...
Jinginar da bayan shi Abeed yayi '' a'a sai dai ki shigo in sauke ki...'' ganin bazai bari ta tsere ba idan ba'a yi É—aya cikin biyu ba yasa taja dogon numfashi ta shiga motar kawai badan taso ba... Abeed yaja motar suka bar wurin... through out jinta take kamar ta zauna saman allurai...zaman ma da rabin jiki tayi shi..rabin kuma a É—age...yana lure da ita amma bai tanka ba sai can yace
'' nayi kama da mugun mutum ne?"
'' mugu ai bashi da kama,amma tambayar ta tabbatar min da mugunta kake shirin aiwatar wa...don't'' maganar ta fito daga bakinta ba shiri murmushin gefen baki Abeed yayi yana kallon hanya
'' meye sunan ki...''
Haushin shi take ji sosai irin wa'yannan maganganun takaici suke bata take ganin su kamar ɓata lokaci kawai'' Anaam...''
'' Anaaam'' ya maimaita ƙasan maƙoshi..' bana son munafunci..' tayi maganar a ranta tana juya ido jin yanda ya kira sunan wai shi a san ya iya ...shiru ne ya biyo baya babu wanda ya sake cewa komai cikin su har suka iso...bakin ƙofar gidan su yayi parking...tayi ƙoƙarin buɗe motar taji ta gam...kallon shi tayi..shima ita yake kallo ta haɗe girar sama da ƙasa duk da kwarjinin da yake mata...well to hell with that
Brown envelope ya ɗauko ya miƙa mata... tabi hannun shi da kallo amma bata karɓa ba kuma bata da alamun zata karɓa '' amsa..'' ya furta.. girgiza kanta tayi tace '' a'a ka barshi kawai...koma meye Inna bazatayi farin ciki ba ...''
'' sai kice Abeed yayan Jadeedah ya baki zasu fahimta...'' persistently Anaam taƙi..shi kuma yace idan bata karɓa ba bazai buɗe mata motar Ba ta gama tafasa da fushi ba yanda ta iya ta warce envelope ɗin daga hannun shi...'' AN GODE TOH...'' ta bashi dariya ba kaɗan ba... buɗe mata motar yayi da sauri ta tura zata sauka
'' SHA'AWAH...'' dakatawa tayi daga ƙoƙarin saukar da take da jin sunan da ya kira ta dan ko a unguwar babu wanda yasan ainihin sunan ta ya akayi shi ya sani ta juyo ta ga ita yake kallo, murya ƙasa yace'' My wife!'' ba shiri Anaam ta sauka daga motar blushing furiously ta banko ƙofar... fuskarta tayi ja kumatun ta suka ɗau zafi...take tafiya kamar zata kife..sauke glass yayi ya sake faɗin '' in five years...''
Tsayawa tayi a zaure tana shafa kumatun ta,lokaci guda kuma haushin Abeed ya cika ranta kamar ita É—in kaya ne dake jiran wani ya mallake su ko shine da gobe bale har yayi maganar shekaru biyar...dogon tsuki taja tare da buga sallama
'' wa'alaikumussalam..mun ɗauka kin ɓata...'' Asma'u ce ta amsa mata sallamar tana tsantsame hijabin data gama wanke wa... da takaici Anaam tace '' tunda kun ɗauka ai sai ku ajiye...''
Asma'u bata tanka ba...Mama ta fito daga É—akin '' kin dawo Sha'awanatu...''
jingina kanta kawai Anaam tayi ta miƙa ma Mama abubuwan data siyo... kula da envelope ɗin hannunta yasa Mama tambayar '' waya baki?"
Zare hijabinta tayi ta zauna sannan tace '' É—an uwan Jadeedah ne,shi ya dawo dani...'' Mama tace
'' Allah sarki ashe bada shi aka tafi umrah'r ba?" Anaam bata tanka ba ta buɗe envelope ɗin kuɗi taga ni a ciki tayi frowning fuskarta ta zazzage kuɗin duka.. yan dubu dubu sababbi Asma'u na shanya hijabinta tace '' Uhmm... addu'ar ki ta karɓu da alamu ...''
Da gaskiyar Asma'u,addu'ar ta ta karɓu ta yanda bata yi tsammani ba.amma hakan bai mata daɗi ba,ajiyar zuciya ta sauke tana furta ' alhmadulillah ' ta nuna ma Mama kuɗin '' TOH kin gode ai
'' tashi tayi ta wuce wurin inna sarai itama ta nuna mata...
Fitowa nayi daga baye na wuce ɗakin mu,samun Anaam nayi kwance tana kallon ceiling hannunta saman goshinta tayi nisa cikin tunani abinda ban taɓa gani tattare da ita ba... kamar zan share ta sai kuma na zauna kusa da ita '' lafiyar ki kuwa?"
'' me kika gani?" Ta tambaya tana harara ta..'' naga kinyi shiru...''
'' tadabburi nake..kada ki dame ni'' taban dariya da tace tadabburi take ...amma tunda tace kada in dame ta yasa ban cigaba da matsa mata ba...nima na shiga tawa duniyar tunanin har bacci ya É—auke ni
Har aka sha ruwa Anaam ba kamar kullum ba yau ko magana bata cika yiba...juyin duniya an tambaye ta tace ba komai... lokacin taraweeh bacci ta ɓuge dashi..sallar tahajjud ɗin ma batayi ba..washe gari nake gano ashe buƙatarta ta biya..na jinjina kaina bayan ta faɗa min yanda ta samu kuɗin..idan har tata buƙatar zata biya... surely...nima zan samu tawa ko? Duk da abinda nake roƙa yafi wanda ita take nema girma...duk da haka na ƙarawa kaina ƙwarin guiwa...
Kwanaki goman da suka biyo baya na ƙara ƙaimi wurin ibada duk da yanda zuciya ta take a sage..banga alamun nasara ba..amma na ƙuduri aniyar yin kamar yanda Jay d ta faɗa min positive thinking a koda yaushe...
Duk yan canjin dana samu a wurin sadaka suke ƙarewa...nakan shagaltar da kaina da ibada da roƙon abubuwan da nake buƙata...a rana ta ashirin da biyar nida Asma'u baƙon mu na wata yazo...ba ƙaramin baƙin ciki hakan ya haddasa mana ba.. amma banyi ƙasa a guiwa ba wurin cigaba da ibaduna...nake ƙoƙarin rufe idona daga rashin nasarar da nake gani tattare da yanayi na...nake convincing kaina cewa daga ƙarshe kafin ranar salla komai zai canja...akwai lokaci...amma nima Nasan zuciya ta abu daban take hanga....a yan kwanakin nan kuma mutane kusan kullum sai sun cika gidan mu wurin kitso da lalle..tun Asma'u nayi ita kaɗai har dai dan dole na nima na dinga taya ta badan naso ba...dan na tsani kitso da lalle
Mutane sai suyita cewa sun fi son nawa suna ƙara sani a wahala...hakan bai yima Asma'u daɗi ba dan dai sana'ar tace...amma take ɗauke kai kamar bata damu ba....