← Book details Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 67

Sashe 54

Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Damƙo hannu na Mukhtar yayi ya miƙe ya ware faffaɗan tafin hannun shi zai zabga min mari,na tsorata iya tsorata musamman dana san babu wanda zai taimake ni,wasu daga cikin tsofaffin ma'aikatan na basu tausayi..banda Fauziyya da take ji kamar ta zuba ruwa ƙasa ta sha...

Runtse idona nayi hawaye na silalowa na sadaukar...sukuma sauran mutanen gani suke hakan daidai ne...jin marin bai sauka ba yasa na buɗe idona ɗaya bayan ɗaya...gayen nan dana haɗu dashi a wurin ƙofar nan ne...

'' Ah,ya Farzan!!?" Kusan yan mata da samarin dake zaune a table ɗin suka kira da mamaki a muryoyinsu...sauke ma Mukhtar hannun shi yayi...sannan ya warware ɗayan hannun dake riƙe da nawa

'' can you not be such an embarrassment?!" Ya ture Mukhtar...ya kalle ni,nayi ƙasa da kaina...

Dunƙule hannun shi Mukhtar yayi yabar dining ɗin bayan ya jefa min kallon daya sa zuciya ta tsalle ta faɗa cikin cikina..

Wurin Hajjo ya isa ya gaisheta ta hanyar sumbatar goshinta '' ja'irin yaro,ai ban san ka tuna dani ba!"

'' taya zan manta da tsohuwar nan mai yawan takuramin...'' wannan maganar da yayi ta dawo da peaceful atmosphere a dining É—in...sauran suka shiga gaishe shi...

Ya kalli Hajiya Hafsa Maman shi kenan ya sakar mata murmushi...gyaÉ—a kanta tayi da basarwa...ya gaishe da sauran Manyan dake table É—in...Alhaji Hussein ya kalli yaron nashi da alfahari..

Fauziyya na kalla naga tana harara ta kamar zata kama da wuta,share hawaye na nayi nakasa motsi...

Daga ƙarshe na tattaro ƙwarin guiwan da yayi min saura na ɗauki izini nabar wurin ban koma ɗaki ba,na tafi 5th floor bayan nayi amfani da katin ma'aikata daban daɗe da karɓa ba, ...sashe huɗu ne a wurin akwai wurin motsa jiki, swimming pool da barbecue da kuma wani abun da ban sani ba kamar asibiti...daga ƙarshe ƙarshe naga lambu da sauri na isa wurin na ɓoye tsakanin shuke shuken dake wurin da aka haskaka da yellow lights..na zauna ƙasa na sha kuka sosai... Bayan na gama nake zagaye wurin dayake ɗauke da fulawowi masu kyau..daga roses,lilies,sun flowers...tulips,da sauran su,harda wasu baƙaƙen roses na gani...ban taɓa sanin akwai ba...ko waye dasu?

Saman wurin glass ne ana hango sama...na É—aga kaina ina kallon taurari da makeken watan da suka fito...inama ace nima tauraruwa ce...

Na daɗe wurin kafin na fito na nufi first floor kafin elevator ta rufe Mukhtar ya faɗo ciki... directly wurina yayo ya jawo ni da ƙarfi ya rungume...

Innalillahi wa inna ilaihi raji'una...Ni Abeedatu na shiga tashin hankalin daban taɓa shiga irin shiba na kasa ƙwatar kaina..kuma sai ƙoƙarin zura hannun shi yake cikin riga ta yana faɗin '' sauran masu aikin abinda ake dasu kenan..kawai ki bada haɗin kai...''

Da ace hawaye na ƙarewa da nawa sun ƙare a wannan rana inata roƙonshi amma ko saurarena bai yiba...

Har yayi sa'a wurin shafar cikina elevator ta kawo ƙasa ta buɗe,banyi wata wata ba na gantsara mashi cizo a kunne na kwasa da gudu na barshi da kururuwa...

A guje na iso sashen mu,samun dayawa nayi cikin su zaune suna kallo... Fauziyya ta sha gabana hakan ya tsayar da guduna...

''.ke dan uw...'' hankaɗe ta nayi na haye sama da sauri dan gani nake kamar zai biyo ni..ɓoyewa nayi cikin bargo jikina na tsananin rawa...hawayen sun dena zuba sai tsoron daya rage a zuciya ta...

Idona biyu har ƙarfe biyun dare bayan kowa yayi bacci..a wannan gaɓar tsoro ya gama kashe min jiki..dan duk sanda na rufe idona abinda yayi min kawai nake mafalki...

Da safe da ƙarfe huɗu na tashi ban samu damar yin Bacci sosai ba amma kuma ban gaji ba ... Bayan nayi nafila nayi zaune wurin ina gudun abinda zaije ya dawo...

Amma ga mamakina, normal akayi break fast yau babu wanda ya faÉ—a min wani abun cin mutunci sannan Mukhtar bai ko kalli sashen da nake zaune ba...

Da ƙarfe tara aka tara mu duka yan aiki..aka rarraba mana ayukkan gyara gida wasu daga yan gidan zasu dawo daga tafiya...

Wani ƙaton hall mu goma akayi assigning da gyarawa ciki harda Fauziyya da muƙarabanta sai harara ta suke..amma ni basu gabana

Aiki muka shiga yina share wurin kuma fa ƙal wurin yake..bayan mun gama muka goge tagogi da kuma mopping ƙasar wurin sannan muka dinga jido kujeru muna ajiye wa a wurin..irin kujerun yan gayu da table

Dukan mu muka yi kwance Rashe rashe a gaban wurin bayan mun gama aikin duka

'' gaskiya naji daÉ—in wannan aikin duk da akwai gajiya...'' Aina'u ta faÉ—a tana Juyowa sashen da nake...

'' nima,kamar kada mu gama..duk da wayan'can mugayen mutanen!" Fadeelah É—aya daga cikin tsofaffin masu aikin kenan..

'' sauran ko wane aiki aka haÉ—asu dashi?"Nake mamaki

Muna tsaka da hirar mu Fauziyya ta iso inda muke ba zato ba tsammani naji an jiƙe ni da ruwa...kafin ta finciko ni...

'' ke dan ubanki jiya ina...''

''.badai ubana ba sai naki!" Na katse tada takaicin zagin da take min...ƙawayenta sukayo gaba suka tarar min su uku suna bugu na...su Aina'u suka shigar min wurin ya kacame da faɗa.. sai hankaɗe kujeru muke

'' Iyyeh!!!!" Malama Amina shugar Madam Aatika ta riƙe baki tare da gwalalo ido tana kallon mu...da sauri muka rabu kowa na huci...

Da tsantsar ɓacin rai take tambayar mai ya faru...ba ɓata lokaci Mariya ɗaya daga cikin waya'nda basu yi faɗa ba ta faɗi abinda ya faru...

'' ku bani katin ku na yan aiki.. '' tayi maganar a kausashe ba damar musu muka miƙa mata..muda bamu daɗe da karɓar namu ba gashi mun rasa

Tunda party ɗin su Fauziyya ne masu laifi nasu katin sai nan da sati biyu mu kuma namu zamu karɓa bayan sati ɗaya...kafin nan ƙafafun mu sun gama karyewa da hawan stairs ...

Sake gyara wurin mukayi kowa na hararar kowa Fauziyya tace '' zamu sake haÉ—uwa...'' É—age kafaÉ—una nayi a yanayin ko in kula...bayan mun rabu ina tsaka da tafiya a 4th floor naci karo da Mukhtar... murmushin mugunta ya sakar min...nake kallon shi ido waje kafin na juya da gudu shima biye dani....

Ban san inda nake sa ƙafa ba kuma ban san tsawon yaushe na ɗauka ina gudu a dogon hallway ba bayan na dinga tsallake stairs da biyu biyu sai jinayi na shige jikin mutum...

Riƙe kafaɗuna yayi ya jani baya... fuskarshi a haɗe...Farzan ne...ina haki nace '' excercise nake!" bana tunanin akwai amfanin faɗin dalilin gudu na shine yasa na faɗi hakan...

'' biyo ni...'' ya sake ni tare da yin gaba...babu yanda na iya dole na bishi É—in..koba komai a idona kasancewa dashi yafi kasancewa da wannan mugun Mukhtar É—in ko?

Maimakon mu shiga elevator gani nayi munbi ta stairs...zaro ido nayi '' yallaɓai ba elevator zamu shiga ba?"

'' ba excercise kike ba?" iska na haɗe ido waje...daga first floor har fifth floor muka kai da ƙafa.. sai kuma muka sake juyowa...duk na gaji ƙafafuna kamar ana sare min su...bayan mun kawo first floor muka sake komawa fifth floor sai dana roƙe shi sannan yabar ni zaune a cikin fulawowi yayi tafiyarshi....

'' Mugu...''

+2349138091955

RU'UYAA…📖

₦500 ne idan ya kammala zai koma 800

Biya ta wannan account É—in 9138091955..Salma Aliyu opay

Shaidar biya ta +2349138091955

Autumn writes 📖🖋️

RU'UYAA
The dreams we never lived
By Autumn 17 🍁🍁

23. ... Kitten...🖊️

Washegari Lahadi,da sassafe Mama Asabe ta kawo min wani haɗin da ban san ko a ina ta samu ba, Karɓa nayi na shanye koba komai meye ciki?

Yau gaba É—aya ma'aikata kamar jiya muka haÉ—u muna aiki kamar ba gobe. wani sashe mai É—akuna uku da ya tsaru ya gaji da tsaruwa aka buÉ—e,kusan mu dayawa aka tura wurin gyara shi,bayan ko mutum É—aya ya isa ya gyara É—akin ya goge...

A kitchen ma'aikatan sai gudu suke nan da can kamar kaji..su Seraphina da yan uwanta aka kwasa aka tafi wurin gyaran jiki hakan ya cecemu daga matsalolin su...wurin ƙarfe sha biyu wata mata mai jiki ta iso da wasu yan mata uku masu shegen jiji da kai,kowace fuska ta babbake tsabar bleaching...sai girman kai da ɗagawa...ashe ƙanwarsu Alhaji ce Hajiya safara'u da ake kira Hajiya Momma...

Parlor ta zauna tarin ma'aikata suka yi kanta wasu na mata tausa,wasu suna cika gabanta da abun ci da abun sha amma sai ashar take ɗura masu...yan matan nan suma suka fara bada oda nan da can... nikam ɓoyewa nayi daga ganin su dan bana son raini...

Gidan ya ƙara duhu bawai duhu na duhu da haske ba...duhun yanayi dan ni wa'yannan mutanen kallon matsala nake musu...sai data gama ci ta ƙoshi sannan ita da ya'yan ta suka haura sama...oh ashe kowacce cikin su tana da ɗaki a gidan...

Kitchen na wuce ɗaya daga cikin ma'aikatan ya kirani,plate ya nuna min dake ɗauke da kayan ciye ciye na gida Nigeria da ƙasar waje yace in kai 3rd floor wanda shine ɓangaren Alhazozan da matayensu....wannan shine karo na farko da zan tafi wurin...

Ɗaukar plate ɗin nayi nabi stairs fuska ba walwala..kusan stairs talatin da shida na taka kafin in iso makeken parlorn daya haɗu ya gama haɗuwa...komai na wurin golden ne harda kujerun,da labulayen...sai carpet ɗin daya kasance ja...daga tsakiya akwai ƙaramin table..sai TV... dispenser daga can gefe,da flowers da aka jera saman wani shafaffen faranti cike da ƙasa...wurin ya game da ƙamshin turarukan su da kuma air freshener...

samun matan gidan nayi zaune suna hira kowa cikin shigar alfarma harda hajiya Momma dabata daÉ—e da zuwa ba... gaishe su nayi na ajiye abinda ke hannu na sun amsa gaisuwar ko akasin hakan? Ban sani ba...

Nake jin idonsu na yawo a kaina ba dalili..ɗagowa nayi idona ya shige cikin na Hajiya Momma ta dafe ƙirji harda zabura ta zaro ƙananan idonta

'' Innalillahi wa inna ilaihi raji'una...harda Mayu kuka koma ɗauka a matsayin masu aiki Ruqayyah? Duba min idon yarinyar nan...'' ƙara kafe ni sukayi da kaifafan idonsu nikam na rasa abunyi ko in tsuguna ko in tashi...

'' Ba mayya bace Ni,haka idona suke...''
Chapter 54 · 0% Book details