Sashe 47
Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tun kafin sallar taxo Nasan da cewa bazatayi min daɗi ba...kamar kowa ce sallah da nake ɓoyewa in sha kuka na..wannan ma bazata kasance ta daban ba...da duk nayi ƙoƙarin kwantar wa da kaina hankali akan har yanzu akwai sauran lokaci da zuciya ta take ƙara karyewa....dan wani sashe na zuciya ta..ya riga da yasan gaskiyar ko kuma ya riga da ya zaɓi gaskiyar abinda zai faru....
Nakan yi murmushi a gaban kowa da kowa bayan daga ciki ...ina rushewa...nakan yi dariya bayan abinda kawai zuciya ta take so shine tayi kuka a fili...nakan nuna jarumta bayan niɗin mai rauni ce...nayi iyakar bakin ƙoƙarina wurin danne ɗaci da raɗaɗin dake mamaye da zuciya ta kamar baƙin hayaƙi mai kauri...kowa na rayuwa a irin yanayin da har abada Ni baxan taɓa iya alaƙantar hakan ba...nake ji kamar na zama fatalwar dake kallon komai amma bazata iya zama daga cikin komai ɗin ba sai dai kallo...
Anaaam ma ta sayi takalmin data ke ta son siya har damu ta siya mawa tace '' ai na faɗa maki... Allah bazai ban kunya ba...'' nayi ƙasa da idona..da gaskiyar ta...murya ta na rawa numfashina na fita sama sama nace da dariyar da bata kai zuci ba '' haha haka fa...nima nan gaba ki haɗa dani cikin addu'ar ki....''
kwanakin suka zo suka wuce kamar basu taɓa wanzuwa ba...nake jina kamar kawai ina tafiya da rayuwa ne ba ruhi..na kuma fahimci cewa a tawa rayuwar ba fari sai dai baƙi da ruwan toka...only Black and gray...never white...
Finally gobe sallah ... Zaune muke dukan mu saman baranda bayan sallar isha'i kowa na bayyana farin cikin kasancewar gobe sallah..jin su nake batareda nace komai ba...tun kafin ranar tazo...zaren farin cikina ya gama katsewa duka...na tabbatar baƙin cikin da zan kwasa gobe sai yafi wanda nake ji a yanzu da kuma wanda na kwasa a sauran kwanakin... Amma duk da haka...
Sanda zamu kwanta...na daɗe ina kallon ceiling bayan an kashe wutar ɗakin.... nunfashina na fita a wahale.... idanu na sunyi ja amma ba hawaye ina ayyana wa a raina yanda zan ji da za'a ce gobe kawai zan tashi inga duk wani abu da nayi addu'a nayi kuka akai..ya zama.... Na juya gefe na idanu na buɗe ina sauraron bugun zuciya ta.. abinda nake ji hauhawa yake kawai...sallar ma baxan iya yiba saboda banda tsalki,ƙila niɗin...abinda nake fatan samu ɗin..har abada... Yawu na haɗiye tare da dafe ƙirjina...ban san tsawon yaushe na ɗauka ba kafin bacci ya sace ni
Washegari da sassafe kowa ya tashi ana ta barka da sallah...su Asma'u murmushi har kunne...maneji nayi ina tayi musu murmushi da murnar yaƙe dan ko kaɗan babu wa'yannan a raina...daga ƙarshe dai tsorona ya kasance gaskiya...da ganin yanda iska ke kaɗawa da yanda sama take ɗauke da gajimare masu duhu zai tabbatar maka da akwai hadari...wannan yanayi yayi daidai da yanda nake ji a raina...sai dai ni a cikina,akwai tsawa harda walƙiya...
Da ƙarfe tara daidai muka isa masallaci cikin tsofaffin kayan sallar mu..dukan mu babu wanda ya damu ,Allah yasa mu ba masu son abun duniya bane...
Nayi zaune zugum na kasa gane yanayin da nake a ciki yanzu... Bayan abinda malamin dake wa'azi ya faÉ—a na cewa wasu lokutan mutum zai iya yin addu'a yaga kamar ba'a amsa ba...nan ko Allah ya amsa kuma yana shirya mashi gagarumin abu...sannan Allah na gwada wa'yanda yake so... murmushi mai ciwo na saki...ni Abeedah a suwa É—an wake a hotel..mai ma nake yi da Allah zai soni? bayan ko gode mashi akan ni'imar shi na kasa yi sai hangen nesa...
Badaɗewa liman ya iso aka tada sallah..bayan an gama naji inama ace su Asma'u basa tare dani dana bi doguwar hanya na saki kukan da nake dannewa..wata sallar batareda cikar burina ba...suna tafiya suna murmushi dukan su ba ƙaramin kyau sukayi ba...naji ina ma ace nice ɗaya daga cikinsu..ƙila in zama Anaam tafi kowa zama free spirited a gidan mu...
ðŸ: naji kina banko mana manya manyan turanci Abeedah...
Abeedah: ina ƙoƙarin in ƙara ƙwarewa ne otum...
A duk sanda suka sako ni cikin maganar su nakanyi iya ƙoƙarina wurin ɓoye sirrin dake raina...
Muna komawa gida..na cire kayan sallar na saka kayan gida na shige ɗakin su Mama da ƙaryar ciwon kai...nayi kwance bacci ya ɗauke ni..a duk sanda nake cikin baƙin ciki,bacci shine hanyar da nake samun kaina... Nayi ƙoƙari sosai wurin ganin ban kalli madubi ba...
Sai da ƙarfe ɗaya na tashi da kaina...kuma da gaske naji ni wasayau...badan ciwon zuciyar ya tafi ba...sai dai don na ƙara jefa shi a wani ramen dake zuciya ta..na cigaba da harkokin gaba na gida je da yawa suka kawo mana abinci...muma mun kai...yan tukuicin da muke samowa duk na bayarda nawa a sadaƙa...duk da zuciya tana faɗamin in cire rai in huta...na kasa... nake ji kamar ina ƙara bayarda sadaka...ina ƙara kusanto cikar burina...
Bayan salla da kwana biyu na cigaba da neman aiki na...Mama tace in dena Allah zai kawo mafita amma baxan iya ba...zama babu aikin yi..zai iya sa tunani ya halakani...
amma kamar ko yaushe ƙunshe da baƙin ciki nake dawowa ba cigaba..ga makaranta da aka kusa dawowa...
Yau asabar da ƙarfe huɗu da rabi na fito daga wani restaurant bayan sun gama ɓata min lokaci sunsa nasa rai a samun aiki a wurin su..daga ƙarshe sai cewa sukayi sun fasa ɗaukata ba gaira ba sabar...tunda na fito gida restaurant ɗaya kawai na shiga kafin na iso nan...suka zaunar dani kuma yanzu shine tsabar wulaƙanci zasu ce bazasu ɗauke niba...
Ba ƙaramin baƙin ciki naji ba..na cigaba da tafiya har na kawo ƙarƙashin wata bishiya da benci ba kowa a wurin gidaje ma sunyi nesa nesa..wurin na ɗauke da yashi mai laushi...ganyen bishiyar sai kaɗawa yake da iska yana bayarda sauti da kuma fitarda sanyi mai ratsa jiki.... ganyayyakin sun baje sosai sun hana rana shigowa wurin sosai...sai kaɗan kaɗan daga space ɗin da suka bari tsakaninsu....zama nayi a wurin na damƙe hijabina a cinyata...ina taune leɓena...kafin naja numfashi domin hana hawayen da suka taru a idona damar saukowa...komai da yake faruwa a rayuwa ta ya shiga playing kamar a tv...ban san na fara kuka ba sai da hawayen suka sauka a hannu na...nafara sheshsheƙa kafin kuka mai ƙarfi ya biyo baya...amma banida mai lallashina...na gaji da duniyar duka..a wannan gaɓar mutuwa shine yafi dacewa a tunani na...duk da dai ba hakan nake fata ba....
Na kasa fahimtar abinda yake faruwa dani... nake kuka kamar raina zai fita..inama ace mutum zai iya koke duka damuwowin shi... danayi
Tsagaita kukan nayi ina kallon ba komai...ban san inda kalaman suka fito ba naji ina waƙa
🎶 Da akwai ciwo cikin zuciya ta...
....bamai faɗa bamai sani sai wanda ke ji..🎶
🎶Hawayena na zuba...zuciya da rauni..
.....Naso ace rayuwa ta,tazo da sauƙi
Allahu ne mai magani shine wanda ke ji🎶
Sake fashewa nayi da kuka..na daɗe a wurin saida rana ta faɗi sannan na tashi na cigaba da tafiya...ana kiran magrib na iso gida... Mama duk ta damu...kowa sai tambayar abinda ya faru yake da ganin idona... Banyi ƙarya ba na faɗa masu abinda restaurant ɗin sukayi min na ƙara da faɗin '' baxan sake zuwa neman aiki ba..''
'' Duk abinda kika zaɓa..matsawar daidai ne muna bayan ki Abeedahtu..'' Inna sarai ce tayi maganar kowa ya gyaɗa kanshi Mama tana shafa kaina da ƙaramin murmushi a fuskar ta..na tabbar wani abu take tunani da yanda idonta ya kafe wuri guda...
Muna zaune cikin shiru wayarta ta ɗau ƙara.. nida Asma'u mun yi mamaki.... wayar Mama tana ɗaukar wata da watanni kafin tayi ringing har mantawa ake da ita a gidan...
Anaam ta miƙowa Mama wayar bayan ta ɗauka tasa a handsfree..kafin Mama ta fara magana wata murya daga ɗayan gefen ta katse ta da faɗi a mugun fusace kamar zai fasa screen
'' a dana gaisuwar ki Ameenatu....baki tashi gaishe dani ba sai da na kira? Tunda Abdul wahhabu yabar duniya kika raba mu da ya'yan daya bari a baya..bayan kin san da dangin uba ake ado idan babu uba,yara mata ba maza ba balle kice zasu iya aurar da kansu...idan Kinga abinda kike shine dai dai ki cigaba ...''
'' ayi...'' katse kiran akayi daga can...Mama ta kafe wayar da ido fuskarta kamar an jaye jini firgici da tsoro ɓaro ɓaro...mu da mukaji abinda koma wane marar mutuncin ne ya faɗa... muka yi shiru kamar babu mu a wurin amma naji zafin kalaman da aka gayawa Mama...
Inna sarai take kallon Mama da kulawa a idonta..
'' Mama wane marar...''
'' Na hane ki!" Mama ta katse Asma'u..sannan ta juyo gare mu '' ku tashi kuje kuyi sallah...'' jiki ba ƙwari muka fito daga ɗakin..nake jin sanyin yau akan fata ta.. yafi na koda yaushe kasancewa mai tsanani ba lallai dan hakan gaskiya bane sai dai saboda abinda ya faru a ciki...
Bayan munci abinci muka sake komawa É—akin Mama amma Inna sarai ta hana mu shiga tace muje mu kwanta kada mu dame Mama...
Koda safiya ta waye muka tafi gaishe da Mama yanayinta bai zama kamar irin na koda yaushe ba..na tabbatar harda sunan baba da koma waye daga can ƙarshen ya kira yasa ta a yanayin da take...naga kamar idonta sunyi ja kaɗan... duk da haka bata bawa Kowa damar tambaya game da abinda muka ji ba...yanayinta yasa nima naji nawa yanayin ba daɗi...haka ma sauran
Sai wurin yamma sannan naga kamar taɗan wartsake sai murmushi ya dawo a fuskar kowa...da ƙarfe huɗu da rabi muna zaune saman baranda mu duka iska na kaɗawa a hankali a hankali da sanyi mai sanyaya zuciya...kai na a saman cinyar Mama kamar koda yaushe Asma'u nayi ma Anaam kitso inna sarai na tsintar shinkafa muna hira da nishaɗi
'' Assalamu Alaikum...masu gidan nan ana sayen gwanjo'' Muryar matar ta karaÉ—e ilahirin gidan
'' waih...speaker!" Inji Anaam
'' ke ba'a son wulaƙanci...'' inna sarai ta kwaɓe ta
'' wa'alaikumussalam...ba'a saye...'' Asma'u ta É—aga murya itama dan matar taji
'' dan Allah a sammin baye...'' matar ta sake faÉ—a...kallon kallo mukayi...ko matar so take ta shigo ta gama gane mana gida? Koda yake ance fa wai idan mutum yazo gidan ku yace wai ku samma shi toilet kada ku yarda yan tsafi ne