← Book details Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 67

Sashe 64

Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Slowly Roman yace '' da gaskiyar ki...i suggest kafin Kiyi magana akan wasu,ki fara duba naki ya'yan..after all we won't want you eating your words do we?" Ya ƙarashe yana kallon Mukhtar,Wurin yayi tsit bayan ya faɗi hakan...

'' baka da kirki yaron nan! Baka san ka girmama na gaba da kai ba!" inji Hajiya Zeenatu

'' unfortunately wannan kalmar 'girmamawa' babu ta acikin dictionary É—ina.. especially ga mutanen da basu girmama kansu ba first!"

Ya miƙe tsaye yana kallon Hajiya Momma yace '' you talk big on morals...idan akan tarbiyya ne,baki kama ƙafarta ba...'' Hajiya Momma ta ƙwalalo ido dining yayi tsit

Ya juya zai bar wurin ya ƙara da faɗin '' none of you are qualified to talk about her with your contaminated mouths!"

Hajiya Momma kamar zata kama da wuta tsabar haushi da takaici... Farzan bai ce komai ba...suma sauran matan sai hura hanci suke

naji Roman ya ƙara bani tausayi...rashin uwa ba ƙaramin abu bane ... amma ina take? ko tabar gidan ne?

Da ƙarfe tara na yanke shawarar zuwa ɗakin Khalil in duba tunda kwana biyu ban ganshi ba...
Tura ƙofar nayi na ganshi kwance saman gado rabin jikin shi rufe da bargo..ƙarasawa ciki nayi ɗakin ba haske sosai nake kallon fuskar shi datayi alamun rashin lafiya...ashe baida lafiya? wake kula dashi to?

Buɗe ƙofar akayi,da sauri na juyo naga Roman ne ya shigo saye da kayan bacci baƙaƙe da takalmi masu laushi suma baƙaƙe hannunshi riƙe da plate...ƙarasowa yayi ya tsaya ɗayan gefen bai cemin komai ba ya yaye bargon ya taɓa gefen wuyan Khalil..sai ya tashi ya shiga Baye ya ɗebo ruwa cikin rober ya zauna gefen shi yana goge mashi goshi da kulawa...bayan lokaci kaɗan Khalil ya buɗe idonshi kafin ya yunƙura ya tashi zaune...

abinda ke cikin robar ya fara ba Khalil a baki...sai ya mutse fuska yake alamun bai so...'' if you don't eat,taya zaka ji sauƙi?"

Khalil yace '' wannan Italian recipe ɗin naka ne ba daɗi.. '' muryar shi da rashin lafiya...nake kallon su biyun yanda Roman keta ƙara cusa ma Khalil koma meye shi kuma yana ƙoƙarin kauda kanshi...daga ƙarshe dai sai daya shanye tass, Roman ya share mashi bakinshi sannan ya kwanta...ya gyara mashi blanket..

Ya tashi zai tafi Khalil ya riƙe hannun shi,ya juyo slowly yace '' thanks Rome...'' gyaɗa kanshi Roman yayi...ya nufi ƙofa..da alamu Khalil bai ganni ba yasa nima na fita cikin shiru

Lokacin har Roman ya ɓace..naso inyi mashi magana amma ba dama...

Washegari ban tafi makaranta ba dan Nasan babu abinda zamu yi... babban dalilina na zama gida kawai ina so in haÉ—u da Roman ne...

Zagaye gidan na fara yi har na kawo wurin ƙofar XXX...babu kowa a corridor'n kuma ƙofar da alamu buɗe take yasa na tura na shiga...cikin sanɗa...

ƙanshin turpentine (ruwan wanke brush) da zaitun da tsofaffin littattafai ya daki hancina...ƙanƙame jikina nayi cikin hijabi saboda sanyi

Babban taga daga ƙasa zuwa rufi, gilashinsa fari ƙal . Hasken safiyar ya shiga ya faɗa akan wani ƙaramin akwati baƙi mai ratsin zinari mai bala'in kyau

Baƙar kujera ta fata a tsakiya, . A kusa da ita akwai easel na itace, an fara painting akai amma ba'a gama ba

Bangon dama duka shelves ne. Akwai 🖌️🖌️ painting brush ko wane size , sai wasu ƙananan drawers da diary ɗinsa a sama mai baƙin cover
Bangon hagu kuwa... komai baƙi ne. Yana cike da zane-zanen da idan mutum ya kalla zai iya jin emotions da kuma ciwon da suke fuskanta

A ƙasa akwai tabo-tabon paint. Ja, baki, blue. Kamar taswirar raunukansa....

Akwai wani rubutu da Yaren daban gane ba da alamu da baƙin painting aka yi shi da hannu
Questo è il mio mondo... dove esisto da solo.`**
(Wannan duniyata ce... inda nake wanzuwa ni kaÉ—ai.)

Ɗauko allon nayi daga inda yake na ajiye a gaban bangon glass ɗin nan na ɗauki brush da painting na cigaba daga inda yatsaya kamar wata ƙwararriya a harkar zane...daga ƙasa na rubuta sunana nayi signing

Ja baya nayi na goge zufar data tsatstsafo min a goshi da murmushi a fuskata kamar na cinye lottery... sosai zanen yayi kyau a idona,ba wata yarinya bace yake drawing ni kuma na iyar mashi...

''WAYA CE KI TAƁA MUN?'' muryar shi ɗauke da fushi da sanyi mai illatarwa ta sauka a kunne na, a firgice na juyo hakan yasa plate ɗin dake kai yabar hannu na yayi sama kamar ana controlling ɗinshi ya sauka akan fuskar shi sannan yayi ƙasa ya ɓata rigar dake jikinshi kafin ya faɗi ƙasa ya baltsu a takalmin shi farare...nima garin Juyowa na rasa balance na faɗa cikin painting ɗin dana gama yi yanzu nida allon painting ɗin crashed on the floor...datse bakina nayi dan hana ƙarar data kawo maƙogwarona fita...

Tsabar yanda ɗuwawuna suka sauka akan katakon da ƙarfin daya sa na ɗauka for a second baxan sake iya zama ba...ido waje ina numfashi sama sama

Ƙafafuna buɗe gashi babu damar sosawa tsabar yanda yake kallona da takaici.. fuskarshi tayi ja..ƙirjin shina sama da ƙasa bakin shi a tsuke kamar yana hana kanshi magana

Nuna ni yayi jikin shi na tsuma yace '' You...! Why does my painting have to pay the price for your clumsiness!" Sai ya koma shafa goshin shi kamar tsohon daya gaji da rashin jin jikokinshi

Da ƙyar na miƙe tsaye nace '' ba kaine ka tsorata niba...'' idonshi ya sauka akan painting ɗin shi dana lalata

'' Oh my God what have you done?'' ya ɗaura hannunshi saman kai..ya wuce ni zuwa allon dake kwance ƙasa....ya ɗauki brush ɗin daya karye sanda muka faɗi

Da matsanancin fushi a fuskar shi ya miƙe yayi cikina samun kaina nayi daja baya zuciya ta na tsananin bugu....hancin shi har wani huci mai zafi yake fitar wa

Hannu na ya damƙo yaja ni da ƙarfi ya fitar dani daga ɗakin....na juyo zan bashi haƙuri ya buga ƙofar da ƙarfi kamar zai ruguje gidan duka...

Kin ƙetare iya ka...hajiyar su🤭

+2349138091955

RU'UYAA…📖

₦500 ne idan ya kammala zai koma 800

Biya ta wannan account É—in 9138091955..Salma Aliyu opay

Shaidar biya ta +2349138091955

Autumn writes 📖🖋️

RU'UYAA
The dreams we never lived
By Autumn 17 🍁🍁

29. ...tayi mashi magana...🖊️

Da sauri Roman ya isa wurin allon bai bi takan painting ɗin ba ya ɗauki brush ɗin daya karye yana kallo like it's the most precious thing in the world...idon shi turned blood shot numfashin shina fita da zafi..taune leɓenshi yayi feeling sick to the pit of his tummy...

Wannan brush É—in yana daga cikin memories É—in da mahaifiyar shi tabar masa...shine farkon kyautar ta a gareshi bayan ya fara zane...she was the one who taught him painting..and now this clumsy girl...

Miƙewa yayi ya gyara komai da komai a studio ɗin ya kashe wutar ya fito..ɗakin shi
Ya shiga ya sauya kaya zuwa baƙaƙe daga sama har ƙasa ya tattare sumar shi into a bun ya fito... elevator ya shiga kafin ta rufe Farzan ya faɗo ciki... Roman bai kalle shiba...da wani smug face Farzan ya tsaya gefen Roman yana cin chewing gum yana ƙaras ƙaras... Wayar Farzan ce tayi ringing ya duba yaga Hajiya Hafsah ce.. ɗaukar wayar yayi yasa a speaker

'' Hello Farzan,ina kake ne?" Slowly yace '' zan fita ne MAMA'' ya kalli sashen Roman daga cikin wayar Hajiya tace '' okay,ina fatan kaci abinci ko?"

'' eh MAMA!"

'' ka dawo da wuri... Allah ya tsare min kai!"

Ya amsa da Ameen kafin ya katse kiran

'' Ah! It's such a wonderful feeling to have a mother...amma wasu Mutane ba zasu fahimci hakan ba ko kaÉ—an...'' ya jinginar da kanshi da elevator da murmushi a fuskar shi, however Roman bai nuna kamar yaji abinda Farzan ya faÉ—a ba if anything he was aloof

Hakan yaba Farzan haushi '' da yake yan wasu basu da ita ai baza su sani ba...'' dunƙule hannunshi Roman yayi zuciyar shina kaikawo... Farzan daya fahimci hakan ya tsaya da kyau

'' what's wrong? Na tado da tsohon ciwo?"

'' You are right it's a wonderful feeling having a mother...amma da irin uwar da kake da ita zama maraya is absolutely best...'' Roman ya amsa with a cold voice, batareda ya kalli Farzan ba

sai kuma ya matso kusa dashi face flat bakinshi saitin kunnen Farzan yace

'' come on,kayi saurin mantawa da baya do you need a recall?''

Dunƙule hannun shi yayi zai kaima Roman naushi.. Roman ya riƙe hannun ya juya sannan ya jefar da Farzan ta kafaɗar shi...

Yakai zuƙunne gaban shi '' you're embarrassing yourself... weakling!" Tsallake shi yayi ya fita daga elevator yabar Farzan kwance a ƙasa groaning in pain...

Parking lot ya isa bike É—in shi ya hawo yau ko helmet É—in bai saba ya fita da gudu...

Khalil na zaune saman gadonshi saye da farar riga mai V neck ƙirjinshi slightly out yana kallon gefe yayi nisa cikin tunani wayarshi ta fara ringing ganin mamar shice ke kira ya ɗauka murya sanyaye

'' ya kake Ibrahim?'' shiru yayi na lokaci kafin yace '' yaushe zaki zo?"

'' i can't come akwai abubuwa da yawa...''

'' that need your attention..what about me? Ni bana buƙatar kulawar kone?" Ya iyar mata,shiru akayi daga can ɓangaren

'' manta kawai...lafiya ta lau.. thanks for checking!" Ya katse kiran...tare da jinginar da kanshi...idonshi ya sauka akan ƙofar shi that was slightly ajar...gani yayi kamar akwai mutum a wurin....their eyes met...da sauri aka ja baya

'' zo nan!" Ya faɗa da muryar shi mai zurfi...ƙifta idonta Diyaam tayi several times kafin ta tura ƙofar ta shiga ciki zuciyarta na lugude...kanta ƙasa tayi tsaye daga bakin ƙofa...saye take da jar atamfa ta ɗaura farin hijabi sama.. average in height extremely fair in complexion..wasa take da hannun ta nervously

'' meyasa kike leƙe?" Taune jan leɓenta tayi murya na rawa da Fulani accent tace '' Uhmm..d..dama...ina neman...Ham..ma ne''

Khalil looking a bit disappointed yace '' forget it..na É—auka kinzo ki duba ni ne...'' panicking Diyaam tace '' h..harda wannan..''
Chapter 64 · 0% Book details