← Book details Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 67

Sashe 45

Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'' Allah ya dawo dasu lafiya...'' Asma'u tayi addu'ar tare da shigewa É—akin mu

Da safe da ƙarfe goma na sake fita kamar koda yaushe ko Allah zai sa in dace..dan ji nake jiyan da ban fita ba nayi missing... amma kamar kullum daga masu cewa basa ɗaukar sabbabin ma'aikata sai masu cewa bani da qualifications...sai masu cewa in dawo nan gaba...raina yayi ɗaci har na kasa haɗiye ƙololon baƙin cikin dana keji...na samu wuri na zauna nasha kuka sannan na cigaba da tafiya

A wani masallaci nayi sallar zuhr da Asr,ina zaune aka fara tafsir a cikin tafsirin shine malamin ke faɗin wata addu'a da idan mutum yayi ta zai samu biyan buƙata

Addu'ar itace za'ayi raka'a biyu na sallar nafila...idan angama ko acikin sallar a fara neman gafara,a yabi Allah ayi ma Annabi salati....sai ace ' Laila illah Allahu Akbar... Lailaha illal lah wahdahu lasharikalah lahul mulk wa wahul hamd wahuwa ala kulli shai'in qadir... Lailaha illallah wala haula wala quwwata ilabillahil aliyul adheem...,lailaha illallahul adheemul haleem lailaha illallahu rabbul arshil adheem alhmadulillahi rabbul alaamin as'aluka muujibaati rahmatik,wa idhaami maghfiratik..wassalamata min kulli ithmin walghaniy matu min kulli birrin,la tadha'ali dhamban illa gafarta wala hamman illa farrajta wala haajatan hiya laka ridan illa qadaita bi rahmatika ya Ar hamurraahimin...'' ya ƙara da faɗin '' duk wanda yayi wannan addu'ar ya roƙi Allah da yaƙini Allah zai bashi..amma matsalar itace Mutanen mu basu da yaƙini kuma basu da haƙuri...'' ban zauna har ƙarshen tafsir ɗin ba amma dai na ƙudiri aniyar yin wannan addu'a sannan idan ma yaƙinin ne banda shi da gaske nayi alƙwarin zan yishi...zan yi iyakar ƙoƙarina kuma a watan Ramadan...bana tunanin addu'a ta zata ƙi amsuwa ga lailatul qadr da nake fake ko?...

Asma'u ain't the villain,__ just a girl insecure

Anaam ain't bad __ just sharp mouthed

Jay D__ everyone needs a friend like her trust me 😇

Khalil__ girls are having a crushing crush on you ooo🤣

+2349138091955

RU'UYAA…📖

₦500 ne idan ya kammala zai koma 800

Biya ta wannan account É—in 9138091955..Salma Aliyu opay

Shaidar biya ta +2349138091955

Autumn writes 📖🖋️

RU'UYAA
The dreams we never lived
By Autumn 17 🍁🍁

19. ...bayan komai sai tawakkali...🖊️

Da wannan tunanin na isa unguwar mu da tafsir ke tashi ta kowane lungu da saƙo...wasu yara na gani kamar almajirai kwance a ƙarƙashin bishiya azumi ya musu dukan bala'i ga wasu suna wasa da lilo cikin nishaɗi da alamu basu azumi na kalli ranar data fara shigewa kalarta ya canja zuwa miyan goro na sauke ajiyar zuciya...da sallama na shiga gidan mu inna sarai dake tatar ƙullu ta amsa min '' har kin dawo kenan?" Gyaɗa kaina nayi

ina kallon Anaam dake kwance tana kallon sama kanta saman cinyar Mama.. Asma'u daga zaune a bakin ƙofar ɗakin mu na cire hijabi na '' Mama ina yini...'' na gaisheta tareda kwantawa a ɗayan gefen na kwantar da kaina saman cinyarta kamar koda yaushe Anaam ta juya idonta tare da fitar da sauti na rashin jin daɗin kwantawar da nayi saman jikin Mama...

'' lafiya lau...wai ba zaki dena wahalar da kanki ba?" Tana shafa kaina tayi maganar da dasashshiyar murya Asma'u tace

'' kuma na tabbar yauma baki samu aikin ba...yanzu fitar da kikayi mai ta ƙara maki?" Murmushi nayi mai sauti batareda na amsa ba...fitar da nayi ta ƙare ni da koyon addu'ar biyan buƙata...daga ƙarshe nima zan samu cikar burina..hakan ba ƙaramin farantawa zuciya ta yayi ba...

Taɓe baki Asma'u tayi ta ɗauke kanta...da ƙarfe biyar da rabi muka tashi taya inna sarai aikin haɗa abubuwan shan ruwa...Anaam ta tafi siyo ƙanƙara da tiyara... bada daɗewa ba aka sha ruwa... Sai da nayi addu'ar nan dana koya na ƙara koro duka buƙatuna sannan nasha ruwa...

'' É—azu dana tafi sayen tiyara baki ga wasu takalmi dana gani ba masu shegen kyau wallahi sun burgeni kuma sai na saye su insha Allah....''

'' nawa ne kuɗin?" Inna sarai ta tambayi Anaam...haɗiye ƙosan dake bakinta tayi sannan tace '' dubu biyar ne...''

''kuuut! ana maganar ina za'a samu kuÉ—in jarabawa wa zai baki dubu biyar?"
Asma'u ta zaro ido tana kallon Anaam...nima ita nake kallo taja tsuki sannan tace

'' yanzu ni danayi maganar nace wani yaban kuÉ—i? KuÉ—in jarabawa ba damuwa ta bane amma dai na tabbatar wa'yannan takalmi dana gani wallahi sai na mallake su....''

'' hada rantsuwa?" Ta kalli saitin da nake zaune da karsashi a muryar ta

''.ƙwarai kuwa Allah bazai bari inyi kaffara ba...'' na gyaɗa kaina

'' yanzu ke Sha'awanatu ina zaki samu wa'yannan kuÉ—in?" Mama ta tambaye ta...tana murmushi tace

'' wurin Allah mana gare shi nake nema shine yasa ma tun farko bance kowa ya bani ba....''

Babu wanda ya sake yin magana cikin mu... lokacin da muka tafi taraweeh ina jinta tana addu'a bayan gama sallah...

Tsakiyar dare na tashi itama ta tashi don yin sallar dare '' yanzu takalmin kika tashi ki roƙa?" Da alamun jin haushi a muryarta tace

'' koke ke bayarwa ne in koma ?" na girgiza kaina da ƙaramin murmushi muna tsaka da alwala sai ga Asma'u itama ta fito...tare muka gama muka shiga kowa ya tada sallar shi daban addu'ar dana koya a kowace sujuuda da tahiya da duk inda ake addu'a a salla sai na karanto ta sannan in roƙi Allah abinda nake so...ban taɓa jin ina kusa da cimma burina ba sama da yanzu

'' Allah ka bani dubu biyar in saye takalmin nan wallahi sun mini kyau...ya al wahhabu ya al fattahu ya Ar razzaqu kaji ƙaina...'' Anaam ta cigaba da addu'ar ta nida Asma'u muka bita da ido ita kam ko a jikinta...maimakon tace Allah yasa mu samu kuɗin jarabawa...ina tsaka da wannan tunanin naji tace

'' Allah ka kawo ma Abeedah aikin da take nema mu huta..kaba Asma'u abinda take so..ka dawo dasu Jadeedah lafiya kasa tayi min tsaraba...kasa muci jarabawar mu harda Diyaam...Ameen...'' daga nan ta miƙe tana yar waƙa..bata ko kalle mu ba ta koma ta kwanta abunta...banyi tsammanin Anaam ta damu dani har haka ba...da take koda yaushe nuna kamar jira take abu ya haɗa mu ta hayayyaƙo min,naji ɗumi ya sauka a zuciya ta game da ita Asma'u ma tayi mamaki...

Daga wannan lokacin a kowane dare sai nayi sallar dare komai gajiyar da nayi komai baccin da nake ji...haka da rana ma nakan ƙara yawaita aikin lada.. wa'yannan suna bani tabbacin cewa addu'a ta zata amsu...duk da wasu lokutan ina shiga yanayi na damuwa da waswasi da sauri nake koɓar kaina daga wa'yannan tunanikan...

Azumi yayi nisa har an kai na sha takwas yau...Anaam zaune take daga gaban ɗakin mu tana cin shinkafa da miya kasancewar bata azumi yau..sai washe mana baki take irin kun gani ƙwalelen ku...juya idona nayi..ni idan dai azumin Ramadan ne,mutum ko abinda yafi duniya daɗi zai ci bazai tayar min da hankali ba...sam sam...

'' Abeedah naga kina haÉ—iyar yawu.. Bismillah to?" Inna sarai da itama abin yake bata haushi ta kaima Anaam duka a cinya

'' bata so...gyandiya kawai...'' turo baki Anaam tayi '' kai Innalillahi Inna...''

Harzuƙo mata da inna sarai tayi yasa ta tashi da gudu ta bar wurin... Mama ta ɗaga labulen ɗaki ta fito '' Anaam zo ki tafi nan kasuwa ki siyo min abu...''

daga nesa Anaam ta cika bakinta da abinci tana karkaɗa kai...tsuki inna sarai taja muka cigaba da hirar yanda kwanakin farautar lailatul qadr ya ƙarato...farin ciki mai haɗe da faɗuwar gaba suke ziyarta ta a duk sanda aka yi maganar wannan dare...idan fa bana cikin waya'nda zasu ga daren? Tunanin sake jira har wata shekara kassara ni yake ... Anaam ta shiga ciki ba daɗewa ta fito saye da hijab pink rabin guiwa ta shafa ma idonta masu kyau kwalli ta shafa man baki...

'' duk shirin zuwa kasuwar ne haka?" Asma'u ta zolaya

Anaam na juya idon ta tace '' eh mana...dole in zama presentable...'' murmushi nayi dan na fahimci abinda take nufi da presentable...

Ɗakin Mama ta shiga ta karɓi kuɗi tayi mana sallama sannan ta tafi bayan ta gama tsokanar mu...

****

Tafiya Anaam take cikin nutsuwa da kamala kamar ba itace Anaam ɗin da koda yaushe take faɗa dasu Abeedah ba...duk da Mama ta bata kuɗin abin hawa ta zaɓi tayi tafiyar ƙasa..a cewar ta can garinsu suna tafiyar data fi wannan nisa da ƙafa wurin samo ruwa dan haka wannan ba komai bane....minti sha biyar ta ɗauka kafin ta isa kasuwar...ganin yanda mazan dake zaune daga baki baki suka kafe ta da ido yasa ta ƙara ɗaure fuska amma bata canja yanayin tafiyar taba...

Wurin da ake sayarda kayan ƙamshi ta nufa..ta fadi abubuwan da take so mai wurin ya shiga auna mata..wani magidanci ne daga gefe sai kallon Anaam yake yana lasar baki kafin can ya kasa haƙura '' yan mata ji mana?"

Yi Anaam tayi kamar bata ji shiba ya sake maimaitawa nan ma ta share shi..sauran dake zaune daga gefen shi sukayi hiri hiri da ido...

'' yan mata salama alaikum...''

A ƙufule Anaam ta juyo tana ɓalla mashi harara tace '' wai Meye ne? Naci bashin kane? Baka da aikin yine? Ko tsaye nake a tsakiyar kanka ko na tare maka wani abu ...''

Rasa abin faɗa mutumin yayi ya girgiza kai jajayen idonshi waje '' ehm...kabi ka ishe ni da ji mana...hayn..bana son takura!" Ta ƙarashe maganar da finality a muryarta yanda bata bar wani ƙofar gardama ko cigaba da bibiyarta ba...ta juyo ta biya kuɗin ta karɓi kayanta tabar wurin tana huci...the guys were speechless...abokan mutumin suke dariya ƙasa ƙasa shiko kunya ta lulluɓe shi...

Anaam tana tafiya tana bala'i duk da ba kowa tare da ita,mutane sai matsa mata suke ..a cikin azumin ma akwai wa'yanda ba zasu iya controlling kansu ba sai sunzo suna abubuwa irin wannan...taja dogon tsuki tare da kawar da kanta gefe..idonta ya sauka akan wani tsoho daya gama tsufa tuguf tuguf da ƙyar yake tafiya zai tsallaka titi...amma motoci sai shararowa suke da gudu suna tsorata shi...mutane kowa sai harkar gaban shi yake babu wanda ya kulashi...da sassarfa ta iso wurin tsohon ta gaishe shi da girmamawa

'' tsallaka wa kake so kayi?''

'' eh amma motocin nan sun hana ni...''
Chapter 45 · 0% Book details