← Book details Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 67

Sashe 18

Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'' lafiya kawai dai banji daÉ—i daban samu komai ba..''

ta faɗa a fili amma cikin zuciyarta ta ƙara da faɗin ' Tuwo kuma ta samu gida da kuɗi bayan ni ya kamata ace nasamu wannan...'

Murmushin yaƙe ta sakar mana sannan ta rataya hijabin ta da igiya ta ɗauki buta ta wuce baye

Mama ta bita da kallo, zuciyarta na rawa dan idan ta gane kamar Asma'u kishi take kawai,bataso ko kaɗan ɗaya daga cikin yayanta ya zama me baƙar zuciya kuma dai tayi ƙoƙari sosai wurin ganin ta basu tarbiyya me kyau... infact ita ta fahimci yanayin Abeedah dan ita bata ɓoye abu..amma Asma'u..?

'' Ya Allah gani gare ka..kaji ƙaina!"

Ta furta da karyayyar murya kafin itama ta wuce cikin É—aki

Nidai tuni ina kitchen wurin neman abinci,amma babu

A hankali muka fara sanar ma da mutane zamu tashi zuwa wata unguwa daban,wasu suna ƙorafin ba'a faɗa musu da wuri ba,amma dai mutane dayawa sunzo taya mu murna...

Washegari da muka tashi akwai hadari sosai garin yayi duhu, a gurguje muka shirya dan zuwa makaranta.. kallon Asma'u nayi daga inda nake zaune inasa socks ita kuma tana sa rigar sanyin saƙa brown color kamar wandon mu,gaba ɗaya babu walwala a kyakkyawar fuskar ta ji nake kamar daga ni har ita mun canja kamar bamu ba...

Miƙewa nayi na matsa kusa da ita na tsaya bayanta,ta cikin madubi ta kalle ni sai kuma ta ɗauke idonta tana parking gashinta

'' Asm na miki laifi ne?"

na tambaya murya a sanyaye idona suka ciko da hawaye batare da ta kalle niba tace

'' ni na faÉ—a maki hakan?"

Girgiza kaina nayi kamar itace yaya nice ƙarama

Hula ta É—auka tasa, ta juyo muna fuskantar juna

'' baki yimin komai ba Tuwo kawai ina buƙatar lokaci ne,idan komai ya daidaita zan dawo!"

Ta faɗa idonta ƙasa kamar tana ɓoye wani abun datake jin tsoron kallon idonta zai fallasa, wuce ni zatayi nayi saurin riƙo hannun ta zuciya ta ba daɗi

'' jinake kamar bamu ba...kamar mun canja mun dena farin ciki kamar da Asm,dan Allah mudawo kamar da!"

Na roƙa a matuƙar raunace

Kallon hannun mu tayi kafin ta kalli idona da suka ciko da hawaye ,a hankali ta zare hannunta

'' wasu lokutan abubuwa basa taɓa kasancewa kamar da Abeedah,canji...dole mu karɓi canji! Baza mu iya komawa kamar da ba... A halin yanzu dai!"

Ta bani amsar kai tsaye hannayen ta cikin aljihun wondo

'' Meyasa?" Na tambaya hawaye na sauka a fuskata

'' Ban sani ba nima '' ta amsa batare da ta kalli idona ba ta fita daga É—akin tabarni tsaye

na share hawaye ,nake ji kamar Asma'u ta tsane ni yanzu kamar tana jin haushi na, zuciya ta takarye bazan taɓa kasancewa cikin farin ciki ba idan Asma'u bata farin ciki

Matsawa gaban madubi nayi da ƙyar na iya kallon fuskata kafin sauran sassan jikina na sauke ajiyar zuciya WASU LOKUTAN MAFI WUYAR WANDA ZAKA SO SHINE KANKA... Na kasa son kaina ,na kasa ganin ƙimar kaina bare har inyarda dani kyakkyawa ce ko zan iya yin wani abu babba

A duk sanda naji kamar na fara iya koyon yanda zan rayu da kaina,sai ingane cewa ba hakan bane... Taya zan so kaina bayan banida kyau? Bayan bani da diri? Bayan babu abinda zan iya tsinana wa na azo a gani? Bayan mutane suna faÉ—amin kuma nima ina yarda da maganganun su?

Na fahimci cewa idan dai har ina so in rayu da kaina dole in koyi yanda zan yarda da kaina kuma kada maganganun mutane suyi tasiri a zuciyata amma niÉ—in mai rauni ce, bazan iya ba!!

Bazan taɓa iyawa ba! Wannan tunanin ya haifar da mummunan ciwo a zuciya ta babu yanda na iya

'' Abeedah ki fito ki karya ku samu ku wuce kafin a fara ruwa!"

Naji Muryar Mama daga kitchen,saida naja dogon numfashi sannan nace

'' Toh Mama!''

nayi hakan ne kada taji murya tata canja

Hula da rigar saƙar sanyi nasa sannan na ɗaura hijabi na sama na ɗauki jakar leda ta na fito sandals nasa sannan na shiga kitchen ɗin,duk da yanda Mama ke kallo na ban bari idon mu ya haɗu ba

ÆŠaukar kunu nayi na juye cikin wata gora na jefa cikin jaka na fito daga kitchen É—in

'' mama yau ayi É—an wake ''

Asma'u dake tsaye bakin ƙofa ta faɗa

'' kina da garin É—an waken ne?"

Mama ta tambaye ta, girgiza kanta tayi

'' ba'a kwai abubuwa ba? Ki kawo in kai niƙa''

'' ke kin cika rigima wallahi''

turo baki tayi nidai ina daga gefe ina kallo,tashi mama tayi ta ɗebo rogo da dawa da wake da sauran abubuwan ɗan wake ta zuba cikin buhu ta miƙama Asma'u ta karɓa,Mama ta bamu kuɗin break sannan muka tafi

Haka muke tafiya babu wanda yace komai cikin mu...daga lokaci zuwa lokaci nakan kalli gefen datake amma ita ko kallo na bata yi ba...sai da mukayi tafiya mai nisa sannan muka iso wurin sani me niƙa... Ta ajiye niƙan kafin muka ɗauki hanyar makaranta...sai ƙoƙarin janta hira nake ita kuma tana ban amsa ƙire ƙire daga uhmm.. sai a'a ba ragi ba ƙari...dole na nayi shiru badan maso ba

Tare muka shigo makarantar da Jay d data fito daga motar su fuska a murtuke...tana ganina ta sakar min murmushin nan nata me haske dake sa wanda ke kallon ta shima yaji kamar yayi murmushi

'' Bee! Ina kwana!" Ta faɗa bayan ta ƙaraso ta zagayo hannun ta a wuya na,nima murmushi na sakar mata na amsawa cike da murna

'' lafiya lau! Now is my nat!''

na faɗa wai ni ina ƙoƙarin yin turanci

Asma'u ta saki dariya ta juyo ta kalle ni

'' ke Ni ina mamakin yanda akai kika kawo SS3 yar gaisuwar ma da turanci shine kike nan kina akwaɓa...wai now is my nat... hahaha waya ga now is my nat!"

'' To sai uban me dan bata faɗa da kyau ba? Su turawan ma ai ba duka ne suka iya turancin ba ko? Idan har kina ganin rashin iya turanci wani babban abu ne to kinyi kuskure '..ƙasashe da dama da suka cigaba kamar korea ta kudu, China da japan dukan su basu wani cika jin turanci ba da Yaren su suke magana...that didn't make them any less... Kuma ita ma Abeedah ai ta iya yarenta dan haka banga dalilin da zaisa ki wani dinga sa tana jin ba daɗi ba!"

Jay d ta faɗa a fusace..nidai nayi ƙasa da kaina raina ba daɗi

Tsuki Asma'u taja tare da faÉ—in

'' Toh uwar shiga shara ba shanu..waya kasa dake balle ki É—auka? Kega advocate ko to sannun ki! Ita bata da bakin magana sai ke aku...kin wani bi kin cika mutane da zance caaaa! Pls badake nake ba so mind your business!"

Wani lallausan murmushi Jay d ta sakar ma Asma'u '' ke nifa na daÉ—e da halbo jirgin ki Asma'u!.."

dakatawa Asma'u tayi itama Jay d saita tsaya nima haka... Asma'u take binta da wani banzan kallo daga sama har ƙasa

'' The truth is you're jealous of ABEEDAH! Kina fakewa da duk wannan gatsen da kike mata kina ƙara ƙuntata mata.. sannan kina jin daɗin ganin Abeedah cikin ƙunci... wannan kyaun da kike dashi bai hanaki jin insecurities ba..bai hanaki kishi ba..kina tsoron kada wata rana Abeedah ta fiki... Kada adinga maganar ta fiye dake..kada a zaɓeta sama dake...
Kina ji inama ace kece da idonta sabida yanda mutane ke son idonta amma basu iya tunkarar ta sufaÉ—a mata saidai su biyo ta wajenki...nasan komai Asma'u...nasan komai!"

Asma'u tayi tsaye wurin kamar an É—asa ta, ahankali na É—ago idona na kalli Asma'u kafin na kalli Jay d data yi maganar

zuciya ta ɗebi Asma'u tayo kan Jay d zata dake ta,aiko Jay D ta riƙe hannun ta wanka mata mari...

'' JADEEDAH!!''

na kira da ƙarfi ina riƙe Asma'u data sha mari,hankaɗe ni Asma'u tayi hawaye nabin fuskarta ta ƙara yin cikin Jay D su biyun suka fara faɗa..kafin kasani sai gasu ƙasa... mutanen dake wucewa sukayi tsaye suna kallon yanda yan matan ke tumurmusar juna a ƙasa...

Ganin Jay D a saman Asma'u yasa na finciko ta..na bangaje ta gefe... Ina huci

'' KI RABU DA ITA KI ƘYALE MU!!!

Ni tayi wa laifi bake ba dan haka ki rabu damu!!"

Jay d ta kalleni da hawaye a idon ta amma batace komai ba,ita tana ƙoƙarin ta tsaya min shine ni kuma zan Gara ta a gaban mutane...ta cije leɓenta kafin ta ɗauki jakarta da aka yasar gefe ta kakkaɓe tabar wurin

Mutane sai magana suke suna ƙus ƙus
Asma'u dake kwance ƙasa na kalla

'' Asma'u..''

na kira ina riƙo hannun ta,fisge hannun ta tayi ta ture ni,na faɗi wurin zaune

'' Dalla rabu dani...ai ƙawarki ta fini muhimmanci kina ganin abinda tayi min tsabar munafuncir shine zaki wani zo kina jana..baƙar munafuka!!"

Ta faÉ—i duk wannan tana kallon cikin idona,nata idon sunyi jawur..kamar yanda nima nawan sukayi ja

Uniforms ɗinta suka ɓaci..haka ma nawa...nabi bayanta da kallo tana tafe tana kakkaɓe uniforms ɗinta

Mutane babu wanda yace min ko sannu, ahankali na miƙe na fara tafiya sai kuma naji ban kyauta da abinda nayi ma Jay D ba...da sauri na ƙarasa aji amma sai naga bata zauna seat ɗin mu ba,ta zauna a seat ɗin masu kuɗin ajin mu... Dama babu malami sai hira suke suna dariya ko kallon inda nake batayi ba,ajiye jakata nayi tare da ɗaura kaina akan benchi... Inaji sanda English ya shigo aka tashi aka gaishe shi amma banda Ni dana cigaba da zama na

Izini ya basu akan su zauna sannan ya fara rubutu akan Allah kafin ya juyo yana kallon yan aji yace

'' Our topic for today is..Comrehension...'' sai ya fara bayani akan zai kira mutum biyu suzo su karanta shafi biyu cikin text book..kowa shafi É—aya

Ya kira wata yarinya mai suna Jameelah Umar... yarinyar tana da kunya Sosai,take tafiya kamar wacce bata da laka..yan ajin mu taliya suke kiranta...haushin yanda take tafiya yaji

'' ke dallah kiyi sauri kina wani tafiya kamar nazo gidan ku taÉ—i!"
Chapter 18 · 0% Book details