← Book details Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 67

Sashe 25

Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'' na gaya maki,ki wuce ki zauna '' kamar zata haukace ta shigo ɗakin kuka wiwiii tayo kaina da sauri na miƙe daga saman gadon ina dariya sosai na fito daga ɗakin a guje na fita daga gidan

Ina tsaka da magana da wata yar ajin mu Khalil É—in ya fito,sallama yarinyar tayi min sannan ta tafi sai na É—an kalle shi,sai kuma na É—auke idona fuska haÉ—iye

'' to muje ki rakani ko?" Ya furta da murmushi

'' Ni nace dan zan raka ka na fito?" Na tambaya batareda na kalli inda yake ba

'' wayyo Allah kitten kina Min wulaƙanci.. shikenan Allah na sama na kallo !"

Yayi maganar tare da langaɓar da kai kamar ƙaramin yaron da aka zalunta.... rufe baki na nayi da hijabi ina dariya ƙasa ƙasa

Nace '' ashe kaima ka san da wannan? Na ɗauka ya'yan talakawa kaɗai ke faɗan haka!" Ya shafa ƙeyarshi yace '' ɗazu dazamu zo naji wani yaro ya faɗi hakan!"

'' shine kai kuma ka ara ka yafe?"

Na furta cikin dariya muna tafiya gefe da gefe

'' a'a sabon ilimi na koya!" Muka cigaba da hira sosai yake da sauƙin kai da daɗin kasancewa, muka isa motar tare da jingina muna cigaba da hira

'' yanzu dai zamu iya zama ƙawaye ko?" Na juya idona nace '' a'a!" Ya ƙwalalo min manyan idonshi kamar mace yace '' to meyasa?" Na fashe da dariya sannan nace

'' sai in ka dena kallo na...'' gemun shi da babu gemun ya shafa yace '' zan gwada!"

Muna nan tsaye naga yana kalle kalle '' ina Rom?"

'' wannan farin gayen mesa fes mas kamar me korona!" Ya gyaÉ—a kai

murya sama nace '' yana can baya yana zuƙa kashi!"

Khalil ya saki dariya nima ina taya shi, sai gani mukayi gayen ya raɓa mu ya shige cikin motar bai ko kalle mu ba, hannunshi riƙe da madubi da kuma abun aski na dakata da dariya ina kallon Khalil nace

'' da alama fa yaji abinda nace!" Ɗage kafaɗarshi Khalil yayi,ya ɗan ranƙwafa yace

'' Rome...Meya faru da sumar ka?"

Batareda ya kalli Khalil ba yace '' mind your business!"

Nidai mamaki ya kashe ni,wai dan na taɓa gashin shine yaje yayi aski taɓe baki nayi dama can mummuna ne yanzu duk da akwai fes mas a fuskar shi na tabbatar ya ƙara muni...

'' ƙila ƙwarƙwata tasha mashi kai!" na raɗawa Khalil a kunne,ya dafe bakin shi yana cigaba da dariya

Asma'u ta leƙo ta kira ni '' toh sai anjima!" na ɗaga mashi hannu kafin yace wani abu na bar wurin da murmushi a tawa fuskar

Da Isha'i muna zaune tsakar gida saman tabarma dan babu wuta...sama ta ƙarayin duhu saboda hadari ga sanyayyar iskan dake kaɗawa kaina saman cinyar Mama Asma'u idonta sun kunbura saboda ba ƙaramin kuka tasha ba,nidai ko a slippers ɗina, tunanin Jay d nake Allah yasa idan naje makaranta mu shirya a haka har bacci ya ɗauke ni

Mama ta kalli Asma'u dake wasa da yatsunta bayan Abeedah tayi bacci,jin idon Mama akanta yasa taja dogon numfashi tace

'' wasu lokutan sai inga kamar kinfi son Abeedah...Meya sa?" Mama tayi matuƙar mamaki da abinda Asma'u ta faɗa sai ta girgiza kanta murya a sanyaye tace

'' ban taɓa jin nafison ɗaya sama da ɗayanku ba Asma'u, abinda kikayi baki kyauta ba shine yasa...ban san dalilin ki nason fitarda tsiraici ba a gaban yaron nan abinda nasan ba ɗabi'arki bane meya faru?"

Asma'u dake kuka ta ƙara yin ƙasa da kanta daga inda take zaune tana taunar lips ɗinta kamar tana weighing a ranta idan ta faɗi maganar dake bakinta ko a'a

'' zaki iya faÉ—a min komai zan saurara!" Mama ta furta gently

'' Mama...na kamu da sonshi...daga sanda na fara ganin shi ... Kawai ina so inja hankalin shine Mama..duk da nasan ba kyau!" Mama tayi jim bayan abinda Asma'u ta faÉ—a,sai kuma ta nuna ma Asma'u gefenta tazo ta zauna, slowly Asma'u ta isa wurin ta zauna

Mama ta É—aura hannunta a sumar Asma'un tana shafawa slowly

'' na fahimta...bake kika ɗaurawa kanki ba....amma Asma'u ki saurare ni da kyau ba'a jan hankalin na miji da surar jiki,sai dai da halaye da ɗabi'u masu kyau mace mai ƙoƙarin jan hankalin na miji da surar jiki zata kai kanta ta baro ne kawai bana fatan hakan ta faru da kowa bare kuma akan ya'yana ina fatan kin fahimta?" Asma'u ta gyaɗa kanta tare da kwantawa a ɗayar cinyar Mama

'' kiyi haƙuri bazan sake ba!" suna a haka har bacci ya ɗauke Asma'u,ajiyar zuciya Mama ta sauke,a hannu ɗaya akwai Abeedah ɗayan hannun kuma ga Asma'u

'' ya Allah kada ka haÉ—amu da Abinda bazamu iya ba!" Ta faÉ—a tana sauke ajiyar zuciya.

___

Kwanakin da suka biyo baya suka wuce kamar ba'a taɓa yinsu ba,a makaranta Jay d ta cigaba da share ni na kasance cikin tsananin kaɗaici kullum ina nan laƙe a duk inda nasan zata kasance amma bata kulani kuma itama tayi kewa ta Ranar Alhamis na tare ta na faɗa mata zamu tashi daga Unguwar mu cewa tayi

'' yayi da kyau... Allah ya bada sa'a!"

Ba ƙaramin ɗaci raina yayi ba na riƙe kukan dake cina ina tafiya ɗaya ɗaya ban tafi gida ba na wuce gulbi a wannan lokacin ne hawaye suka fara sauka akan fuska ta na samu na zauna saman dakalin da aka zagaye wurin dashi dan dama wurin ba ƙasa bane interlock ne sai aka zagaye gulbin da bulo saboda yara masu ƙiriniya

Na zauna ina ta kuka kamar raina zai fita hadari ya fara haÉ—uwa amma akwai rana har lokacin

'' Tuwo me ya faru?" Saleh ne ya zauna kusa dani ya jinginar da ƙarafun shi

'' ƙawata ta dena kula ni bata sona!" Na bashi amsa ina mutsutstsukar fuska ta da hijabina

'' me kika yi mata?" Ya sake tambaya

'' yah dai da tambaya?" Na É—ago jajayen idona ina hararar shi,rufe bakinshi yayi yana dariya yace '' wai har na fara tunanin yanda zaki shawo kanta ne..amma tunda harara ta kike shikenan!''

Yayi maganar tare da riƙe ƙarafunshi zai tashi '' Toh kayi haƙuri!" Na furta ina sake sakin wasu hawaye ajiye ƙarafun yayi ya jawo jakata ya ɗauke pen da paper yayi rubutu a sama '' ungo nan!" Ya miƙo min paper..share fuska ta nayi sannan na karɓa,na tsare paper da ido ganin da turanci yayi rubutun na fara ƙoƙarin karantawa '' I was a hor rible frind..for' give mey....''

da Hausa nake karantawa Saleh da ya saki baki yana jin karatun ya kwashe da dariya harda faɗuwa ƙasa dakatawa nayi tare da ɗaure fuska wane irin iskancine wannan

'' Abe...ed..ah...hahaha... Meye kike karantawa haka?" Ya faÉ—a cikin dariya

Ganin babu wasa a tattare dani yasa ya tashi zaune yaja wani dogon numfashi yana ƙoƙarin riƙe dariyar shi yace

'' ai ba haka ake karantawa ba kawo ki gani!" Ya amshi paper ya fara karantawa....har ya gama ina binshi da kallo kamar zan rufe shi da duka

'' nifa ban iya turanci ba!"

'' exactly!" Ya faɗa yana kallona '' idan kika karanta mata wannan taƙi yarda sai ki ɗan rungumeta kice..Kinga saboda ke har da turanci na koya kiyi haƙuri sai ki ɗan fara kuka kin gane ai?"

'' kace kai ma ka iya markici har haka?" Na faɗa da annashuwa dan ji nake kamar an ɗauke wani ƙaton abun da ya danne min ƙirji..'' zama da maɗaukakin kanwa...''

'' shike Kawo farin Kai!" Na iyar mashi mukayi dariya tare,sai muka miƙe tare muna tafe muna hira har bakin ƙofa ya ajiye ni sosai nayi mashi godiya kafin na shige Ina gama cin abinci na shiga haddar rubutun Mama da Asma'u suka bini da ido daga lokaci zuwa lokaci Mama take yimin gyara kafin ta tambaye ni wa zan bawa haƙuri haka '' Jadeedah!" Bata matsa min da tambaya ba...

Washegari lokacin MSS bayan an taru kafin malamin dazai gabatar da mss ɗin ya shigo na miƙe,dama nayi ma piripoper (prefects) magana wurin yayi tsit aka bini da ido naja dogon numfashi ina kallon inda Jay D take zaune da wasu masu kuɗin dake bina da kallon rainin wayo

Na fara magana '' Jay D.. I'm so sorry...I was sace a hor'rible fri'end...'' da farko dana fara karanta abun da kyau sai sukayi shiru suna sauraro amma jin na fara karanta abun da Hausa yasa suka fashe da dariya naji kunya ta kamani....

'' kai kai! Duniya kana ganin abubuwa iri iri''

'' Horo'ribu'le fri'end..haha''

'' turanci take ko hausa?"

'' Silence!" Headgirl dake tsaye tun daga lokacin dana fara karanta takardar haƙurin nawa ta faɗa tsit wurin yayi masu dariya suka daina duk da na rasa karsashi na cigaba '' Yo'u trey toh stand uu'f for Mey...boot I was un'gretful... I'm sorry...I missd you... for'gibe mey!" Na ƙarashe a kunyace kaina ƙasa da hawaye a idona

Jadeedah ta taso daga inda take zaune har zuwa inda nake itama da hawaye a idon ta..ta riƙon hannu na '' nima nayi kewarki sosai Bee kada ki ƙara yimin abinda kika yimin kinji?"

Ta faɗa tana rungume ni ƙam

''bazan sake ba!'' na bata amsa

'' Ohhhh...masoya... soyayya ruwan zuma ce yara kusha...'' wurin ya kaure da wasu suna kiran mu wai Lailah da majanunu wasu suka hau table suna duka kamar sun samu ganga ta riƙo hannu na muka samu wani seat daban muka zauna

'' iyye amma yaran nan anyi ja'irai!"

Wani Malam Auwal ya leƙo hannunshi riƙe da zungureriyar bulala ɗayan kuma a haɓa... muryar shi kamar ta mata laƙabin da aka yi mashi shine ' yanga dot com ' tsabar yanda yake magana cike da yanga amma fa baƙin mugune na ƙarshe ma kuwa

aka fara rububi wurin zama,shiru ya cika ajin.. prefects ɗin dake wurin suka yi ƙasa dan idan aka gansu punishment ɗin su zaifi na kowa ƙwafa yayi kafin ya bar wurin sai macijin sari ka noƙe ya shigo yan matan suka ƙara bada hankali na musamman wurin sauraren shi nidai a wannan lokacin Abu mai muhimmanci shine Jadeedah ta dawo.. naji ni a matsayin mutum a karon farko na tsawon lokacin da bama tare...
Chapter 25 · 0% Book details