Sashe 50
Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ruwan dake gabanta ta É—auka ta wanke fuskata dasu..naja dogon numfashi..dan banyi tsammani ba...da alama akwai wa'yanda suke jin daÉ—in abinda ke faruwa ciki harda Hansa'u
'' Subhanallahi..''Mama Asabe ta koka...amma Fauziyya bata ko kalle taba.. ta miƙe tsaye tare da ranƙwafowa hannayenta dafe da table tana kallona da tsana a idonta tace
.
'' manta da abinda Ateeka ta faɗa...idan har baki shiga taitayin kiba na miki alƙwarin zama a gidan nan sai ya gagare ki!" Tsoron da ya kamani na haɗiye dole ne in koyi tsayawa kaina idan ba haka ba kowa zai dinga takani yanda yaga dama...
'' Bismillah.. tsoron ki ake ne? Yanzu dai Madam Atika ta gama faɗar babu seniority ko...koda yake...'' murmushin gefen baki na saki batareda na iyarda abinda nayi niyar faɗi ba..gray eyes ɗina suka ƙara duhu abin ban tsoro...firgici ya bayyana a fuskar kowa dake wurin...na miƙe tsaye batare da na gama cin abincin ba na koma ɗakin mu daga lokacin dana rufe ƙofar duk wani jarumta ya rushe hawaye suka wanke fuska ta...(Su Abeedah masu super power ido🤣)
'' kamar yarinyar nan is a bad omen, kunga idonta kuwa...ruwan toka?" Rasheedah ta faÉ—a tana aza hannu saman kai idonta kamar zasu faÉ—o
'' kodai mayya ce?" Wata daban tayi maganar
'' You're very stupid!" Fauziyya ta daka musu tsawa a fusace haushi da takaici ya ƙumeta...wannan sabuwar yarinyar tana ƙoƙarin zamar mata sartse a nama...dole ta koya mata hankali...
Wurin yayi tsit da shiru mai nauyi babu wanda ya isa yayi magana ...
*****
Wayata dake ringin na lalubo daga cikin komatsai na...lambar inna sarai ke yawo akan ƙaramin glass ɗin,kukan dana tsagaita naji yana neman dawomin sabo..ɗage kaina sama nayi ina jan numfashi sannan na amsa kiran
'' Abeedah...'' lallausar Muryar Mama ta faso wayar bayan tayi sallama..damƙe baki na nayi ina haɗiye kuka na '' N...na..am...Mamaaaaa'' daga ƙarshe dai na saki kuka...da yanda take ta rattafo min tambayoyi naji ba daɗi dan nasan hankalin ta ya tashi su Inna Sarai suma suka yo kan wayar kowa na tambaya ta lafiya...zama nayi bakin gado bayan yunƙuri da yawa na samu na haɗiye kukan '' ..bba komai...nn..ayi kewar kune.mm... sosai kuma ....wann..an shine karo na farko dana yi nesa daku...''
na faɗa a rarrabe..daga cikin wayar naji mama ta sauke nannauyan ajiyar zuciya kafin ta fara lallashina..su Anaam da Asma'u muryoyin su,sun ƙara jefani a yanayi...mun ɓata lokaci muna waya kafin daga baya mukayi sallama,kalaman Mama na ƙarin ƙwarin guiwa sun sa naji sauƙi a raina..na shiga baye na wanke fuska ta...
Bayan sallar isha'i,Madam Atika ce gaba muna biye da ita a baya mu biyar zuwa babban gidan...gaban babbar ƙofar mai Black and golden muka tsaya ta danna ƙaraurawa..wata na'ura ce tayo gaba kamar zata ɗauke mu hoto alamun scanning ɗin mu ake...kafin ƙofar ta buɗe... Sumar tsaye ni Abdeedah nayi da ganin haɗuwar wurin..ashe gidan su Jay d wasa ne idan an haɗa da wannan..bare tun kafin na shiga daga ciki na fahimci gidan hawa shida ne... Ga wani ƙaton bookshelf a wata kusurwar stairs ɗin,sai ƙaton bishiyar cherry blossom dake waje bishiyar tayi tsayi har ana hangowa ta window'n sama
Kamar yanda nake kalle kalle kamar baƙauya haka sauran suma suke al'ajabi,wata yar coner Madam Atika ta nufa damu,isar mu wurin ta zaro ƙaramin kati ta nuna a ƙaramin glass fari maƙale da wurin.. take ya buɗe ashe elevator ce ...
'' ko in É—auke kune?" Maganar ta tasa munyi rububin shiga cikin elevator ta wuce damu first floor, take nuna mana abubuwa
Floor B1, Sashen ma’aikata, wurin wanki, ɗakunan ajiya, da genetors room
2nd Floor: Babbar ƙofar shiga, babban falon baƙi, ɗakunan cin abinci biyu na musamman, da banɗakunan baƙi.
Floor 1: Falon iyali, É—akin TV, babban kicin, wurin karin kumallo, da tafkin iyo na cikin gida...
- Floor 2: Ɗakunan baƙi guda biyar tare da ɗakin sallah.
- Floor 3: Bangaren Alhazozan gidan da matayensu Kowacce sashe yana da É—akin kwana da falo
- Floor 4: sashen yaran gidan,samari da yan mata
- Floor 5 (Rooftop): Gym, tafkin iyo na waje, wurin barbecue da lambu ...
Lif yana aiki ne kawai da katin ma’aikata. Matakalar hawa kuma tana da ƙofofi biyu masu kama da juna. Har akwai wata doguwar hanya da idan ka bi ta sai ta kai ka wata doguwar hanyar daban.
Tana nuna mana wurare tana bayani...muke binta kamar wasu mutum mutumi...taga ma bayani amma akwai sauran wurare da bata faÉ—i komai akai ba
'' na kawai nuna maku inda zakuyi aiki ne,sauran wuraren baku ba yawace yawace ko taɓa wannan taɓa wancan..Na hane ku..ba ruwanku da shige shige..a duk sanda kuka haɗu da yan gida,ku kasance a mafi kyaun halayen ku...kun gane?''
'' eh mun gane!"amsar mu tazo da haɗa baki kamar yan primary'n dake amsa tambayar malamar su... Cikin elevator muka ƙara shiga muka iso kitchen ɗin a first floor,nan muka iske masu dafa abinci..turawa uku ɗan Najeriya ɗaya suna nan da can domin shirya abinci..magana tayi da shugaban wurin...ya kalle mu kafin ya isa wurin ƙaramar cupboard ya ɗauka wasu papers ya miƙa mana...karɓa mukayi muna karatun wuraren da zamu dinga kula dasu
- Tafkin iyo na cikin gida(swimming pool): Goge tayal, cire ganyen da ya faÉ—a, da duba sinadaran ruwan kowane Asabar.
- Wuraren cin abinci uku: Babban É—akin cin abinci mai kujeru 20, na iyali, da na saman rufi... A tsaftace a gyara a canja table cloth a goge kujerun
- Gidan kallon fim(movie room): Share kujeru da injin vacuum, goge remote,
- Dakunan ajiyar kayan abinci biyu: Ɗaya na busassun kayan abinci, ɗaya kuma na abubuwan sha...a kowane ƙarshen mako,a duba aga abinda ya ƙare... A fitarda wanda ba'a buƙata
- Ɗakin wasanni: Teburin billiards, PS5, da ƙaramin mashaya...a tabbatar komai a gyare kuma a kimtse...
Ƙaton ɗakin taro a tsaftace bayan kowane kwana uku...
Yawan aikin yasa naji kaina harya sara..nida ban taɓa yin aiki mai yawa har haka ba taya zan fara? Wai ma nan akwai wuraren da bamu sani ba sai nan gaba
''.kada ku damu...akwai duty roster..kowa zai san ranar aikin shi...'' ganin kamar mun shiga damuwa mutumin yayi ƙoƙarin kwantar mana da hankali... Ajiyar zuciya na sauke da ƙarfi daya sa kowa kallona kamar nayi laifi....
Munanan tsaye tsofaffin ma'aikatan suka shigo cikin uniforms ɗinsu ash,babu wacce tasa hijabi suka fara kwasar,abincin da aka dafa ba ƙarya ba sun kusan kai kala goma...
Yanda suke sauri sauri kamar suna tsoron ɓatawa masu gidan rai...nake binsu da kallo...Madam Atika ta juyo tace '' ku shirya yanzu zamu je ku gaishe da mutan gida ..''
Dukan mu daka kalle mu zaka san ba daidai muke ba, duk jikin mu yayi sanyi...kafin nan Madam atika ta gabatar mana da masu girkin...ta fara da wasu masu kama da larabawa '' wannan shine Alexander laroi, Muhammad Salah...yan ƙasar turki...'' suka risina mana cikin girmamawa mukayi tsaye rashin sanin yanda zamu yi..kawai nima sai nayi musu yanda sukayi mana..sauran ma suka bini
Ta nuna É—ayan baturen '' wannan shine Leonardo daga italy...''
'' Ciao ragazze, piacere di conoscervi (sannun ku yan mata,naji daÉ—in haÉ—uwa daku)'' kallon shi mukayi kamar yanda kurma ke kallon wanda ke magana dashi dan bai fahimta ba..batareda damuwa ba ya juya ya cigaba da girkin shi...
'' sai Na'em...daga nan Kano!" Ya juyo da murmushi '' sannun ku...''
''.yauwa sannu dai...'' muka amsa mashi
'' mu tafi...'' Madam Atika tayi gaba muna biye da ita muna tunkaro dining...wurin yayi tsit ba'a ganin mutanen dake zaune wurin sakamakon irin wannan labulen da yake kamar zare da aka saukar... bangon wurin painting shi sky blue...wata chandelier babba daga sama...an jera abinci kala kala... ma'aikata tsaye daga bayan su duk wanda ke buƙatar wani abu da sauri ma'aikatan ke miƙa masu...
'' ina zuwa...'' ta dakatar damu a wurin..ta isa ita kaɗai ta rusina da girmamawa ta nemi izini sannan ta jagorance mu zuwa wurin...muka tsaya a layi guda mu biyar ɗin muna fuskantar iyalan da suna da yawa sosai...wata dattijuwar matace zaune a farkon table ɗin,kallo guda mutum zai san itace mai faɗa aji a gabaki ɗaya gidan...daga gefenta dattijai ne da basu kaita tsufa ba,da alamu ya'yan tane daga babban cikin su zuwa ƙarami...daga gabansu a ɗayan gefen table ɗin kenan,suma wasu matane zaune cikin shigar alfarma da alamu matan sune...sai yan mata da samari..a kowane gefe...
Madam Aatika ta fara gabatar mana dasu bayan mun gaishe su da ko kallo bamu ishe suba tsohuwar itace Hajjo shugabar gidan duka..duk abinda ta faɗa ya zauna babu ɗaya daga cikin ya'yan nata dake burin ɓata mata rai...
Sai mutum na farko bayan ita shine Alhaji Mansir da matarshi Hajiya Ruƙayya,shine babban ɗan hajjo... ƴaƴan su huɗu,Huriyya,juwairiyya,Khadeeja da Jawaad...
Sai Alhaji sulaiman da balarabar matarshi Hajiya Wareesha... ya'yan su biyar suma, Kareema,Nu'aymah,kulthum, Seraphina da Mukhtar
Alhaji Hussein da matar shi Hafsah, da ya'yan su, Farzan,Abdul Jalal,Isa,Ayan da kuma Imam...
Alhaji Kabeer da Hajiya Bushrah, da ya'yan su Mufeedah,Heedayah,Khaleesat, Jameelah
Alhaji Sa'eed da Matar shi Hajiya Zeenatu ya'yan su, Armani,Arman,Aryan , da Aryana...
Wa'yannan sune wa'yanda ke wurin a yanzu..akwai sauran da suke a ƙasar waje sai wanda ya rasu Alhaji Muhammad na biyu bayan Alhaji Mansir
Ban sani ba kona riƙe sunan mutanen da aka faɗa mana,dan yanda suke kallon mu kamar bamu cancanci dasu kulamu ba ya soki zuciya ta...shine yasa bana son masu kuɗi...amma ƙaddara ta shilloni a hanyar su dole in haƙure
'' ban taɓa sanin akwai baƙaƙen mutane masu idon mage ba ai...'' ɗaya daga cikin mazan ya faɗa da shaƙiyanci...sai sauran suka kalle ni,duk na jini a takure hannayena a gaban hijabina
'' Atika kada yarinyar nan ta dinga shiga kitchen dan gudun contaminating abincin mu...'' inji É—aya daga cikin yan matan
'' Come on.. she's pretty...after all''inji Mukhtar yanda yake kallona yasa naji kamar ƙasa ta tsage in shiga...babu ladabi a kallon nashi ko kaɗan
duh!🙄 har naji abincin ya fita daga raina...Atika pls take this dirty kids away...''
Dariya suka saka dacin mutuncin da yarinyar tayi muna musamman ni.....ƙasa nayi da idona hawaye suka taru a ciki..ta gefen ido naga Hansa'u namin dariya..na muzanta ƙwarai...
Tsofaffin masu aikin suma a ɓoye suke min dariya kamar sunji daɗin abinda ya faru dani...